Taskira TV

Taskira TV Kafar yada labarai mai samar da ingantattu kuma sahihan bayanai akan abubuwan dake faruwa a Najeriya Public Enlightenment

Wata mata ta kwanta da kayan barci masu k**a da fatar macijiCikin magagin barci, mijin yadauka maciji ne, wajen kokarin ...
03/01/2024

Wata mata ta kwanta da kayan barci masu k**a da fatar maciji

Cikin magagin barci, mijin yadauka maciji ne, wajen kokarin kashe macijin ya karya mata kafa, Yanzu dai tana asibiti

Ana cigiyar wannan matashinMuna ci giyar bacewar  wannan matashin Mai suna Salisu  Hassan ( Abba) ya bar gidan su dake K...
30/12/2023

Ana cigiyar wannan matashin

Muna ci giyar bacewar wannan matashin Mai suna Salisu Hassan ( Abba) ya bar gidan su dake Kwarun Badarawa Kaduna, kwana biyu ba a sake jin duriyarsa ba.

Saboda haka duk Wanda Allah yasa ya ganshi ko kuma yaji duriyarsa ya kira wannan Lambar 08038896861 ko kuma wata Hukuma Mafi kusa, Allah ya sa mu da ce.

Ikon Allah!Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Sabon Gari Zaria ta samu nasarar ceto wata budurwa mai suna Rabi'ah Salisu ...
30/12/2023

Ikon Allah!

Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Sabon Gari Zaria ta samu nasarar ceto wata budurwa mai suna Rabi'ah Salisu ƴar kimanin shekaru 22 da wani saurayi mai suna Joe Abdulmumin ɗan kimanin shekaru 30 ya ɓoyeta kimanin shekaru 7 da s**a wuce a gidan su dake unguwar Dogarawa a karamar Hukumar sabon Gari,kuma har ta haifa masa yara guda uku(3) biyu2 mata ɗaya 1 namiji a yau 28/12/2023 da misalin karfe 1:30pm.(na Rana).

A hirar mu da mahaifinsa wanda yake makaho ne ya shaida mana cewa yayi yayi ɗan nasa ya mayar da yarinyar amma abin yafi karfin sa.
Mahaifin ya shaida mana cewa a salinsa ɗan garin Madobi ne dake Jihar Kano Amma kuma shi ba musulmi bane Kirista ne.

Har ila yau munyi hira da ƴaƴan Rabi'ah Malam Abdullahi Salisu kuma yace mana shekaru bakwai kenan suna neman ƙanwarta su da ta baro gida daga gidan su a unguwar jaba daga nan basu ƙara jin ɗuriyar ta ba sunyi adduah daga baya s**a mayar da komai zuwa ga mahaliccin su.

Tuni dai muka mika shi ga Jimi'an tsaron ƴan sanda domin cigaba da bincike da kuma gurfanar dashi gaban ƙulliya domin ya girbi sak**akon wannan mummunan aikin da ya aika ta.

Allah Ya ƙara mana Nasara ya kuma kare mu daga sharrin bin son zuciya.

'YAN DAMFARA SUN SHIGO DA SALO IRI IRI Yanzu Yanzu wani dan damfara yazo shagon dake kallon gidana  dake unguwar kofar H...
28/12/2023

'YAN DAMFARA SUN SHIGO DA SALO IRI IRI

Yanzu Yanzu wani dan damfara yazo shagon dake kallon gidana dake unguwar kofar Halliru Gashua, da niyya sayan kaya. Bayan sun kammala ciniki da mai shagon sai ya nemi a bashi number Account, bayan an bashi number Account sai yace ya tura kuɗin mai shago yace kuɗi bai shigo ba fa.

Dan damfarar yazo da wadannan kwalaye da kuke gani guda biyar makare da kaya harda bacco bacco sabbi a cike da kaya. Sai yace wa mai shagon ga kayan sa zai koma kasuwa ya dawo Amma mai shagon ya bashi kuɗi #30,000 kafin ya dawo ga kayan sa nan.

Mai shago dai yaki bada kuɗi, sai Dan damfara yace to yana zuwa a jire masa kayan sa. Haryanzu dai bai dawo ba tin da safe, mai shago yace bari muga menene a ciki kar ya dawo yayi mana sharri.

Ya kira mu mukazo a matsayin shedu muna budewa sai mukaga kwalaye cike da yayi da duwatsu, kasa da sauran tarkace.

Ya jama'a mu kara kula sosai da irin wannan damfara da yan damfara ke yi a cikin Al'umma.

Allah ya raba mu da dukkan sharrin masu sharri.
Shehu A.A Gashua

26/12/2023

Janye tallafin mai farashin Burkutu yayi tashin gwaron zabo

Me zakuce

Allah ne kadai zai yiwa wannan budurwa sakayya da hisabi tsakanin ta da wayanda s**a mata mummunar zato wajen chanza ma'...
26/12/2023

Allah ne kadai zai yiwa wannan budurwa sakayya da hisabi tsakanin ta da wayanda s**a mata mummunar zato wajen chanza ma'anar fassaran wannan suna data rubuta a bayan rigan ta *RABAKAYA*

*RABAKAYA* Ba kalmar iskanci bane k**ar yanda mutane suke tunani suke ta yada hoton wannan baiwar Allah suna daukar alhakin ta

*RABAKAYA* babban family ne a jigawa wanda suna da nasaba da Masarautar Hadejia kuma wannan suna family name dinsu ne k**ar yanda kowa suke da nasu family name din su

Na tabbata duk iskancin yarinya ba zata taba rubuta wannan sunan a bayan rigan ta da niyyar iskanci ba saboda tasan dole wannan hoton zai zagaye duniya daka karshe har iyayen ta su gani

Kamar yanda aka chanza fassaran kalmar KUNU haka aka chanzawa wannan budurwa ma'anar sunan data rubuta, duk wanda yasan ya mata mummunan fassara yayi gaggawa ya neme ta domin yafiya. Muna mata fatan alkhairi mu kuma Allah ya shirya mu da ita baki daya

Copied

26/12/2023

A Gaskiya Iya Abinda Na Sani Tsakanin Nafi'u Da Chuchu Matsananciyar Soyayya Ce, Céwar Jarumar Kannywood Suddeenly

Ku Saurara Kuji Daga Bakin Ta....

Ministar Buhari Saadiya Umar Farouk Ta Shiga hannu, EFCC Ta Lalubo Satar Naira Biliyan 37 a Gwamnatin Baya.Hukumar magan...
24/12/2023

Ministar Buhari Saadiya Umar Farouk Ta Shiga hannu, EFCC Ta Lalubo Satar Naira Biliyan 37 a Gwamnatin Baya.

Hukumar magance cin hanci da rashawa ta ƙasa, wato EFCC ta lalubo badaƙalar kuɗi har biliyan 37 sannan ta cika hannu da tsohuwar ministar walwala da jin ƙai na Nijeriya lokacin mulkin Buhari, Sadiya Umar Farooq.

Wannan sanarwar mun sameta ne daga Gidan Jaridar Punch Newspapers a shafinsu na Twitter, sannan kuma Shugaban Gidan Jaridar Liberty, Ahmad Tijjani Ramalan ya wallafa a shafin sa.

Jama'a miye ra'ayin ku game da wannan batu.?

24/12/2023

Ni nakai takarda Da iznin sheikh Dahiru Bauchi
Takardama kan takardar aka aikema kotun koli wanda daya dagacin yayansa ya musanta

Ya kuke kallon wannan zanga zangarWane suna zaku basu ?
24/12/2023

Ya kuke kallon wannan zanga zangar
Wane suna zaku basu ?

23/12/2023

Hon Husseni Kero Dan majalisar dake wakiltar kaduna ta kudu a Abuja ya kai ziyarar bazata domin duba yadda aikin wadanda ya dauki nauyin duba lafiyar idanunsu ke gudana

NAFI'U SAURAYIN HAFSAT NE:   Ga yadda bincike ya tabbatar min kan labarin Nafi'u da Hafsat...Nafi'u saurayin Hafsat ne d...
22/12/2023

NAFI'U SAURAYIN HAFSAT NE: Ga yadda bincike ya tabbatar min kan labarin Nafi'u da Hafsat...

Nafi'u saurayin Hafsat ne da jumawa bayan Hafsat tayi aure shine s**a ha'da Kai s**a fara kasuwanci (Business) tare da Nafi'u Kuma Allah ya basu sa'a s**a samu ku'di masu yawa har ita Hafsa ta bu'de Shago a zoo road, Hafsat da mijinta Dayyabu suna zama a wani karamin gida sai Allah ya bu'dewa mijin ya samu ya Gina Babban gida kafin domin su koma can da zama tare da matarsa, kafin nan ita Hafsat ta Riga ta ha'da mijin nata da Nafi'u sun saba harya zama k**ar dan Uwa suna harkoki tare ba tare da mijin yasan abinda dake tsakanin matarsa da Nafi'u ba.

A lokacin da su Hafsat za su tare a sabon gidan su shine tace dole sai dai a koma Sabon gidan tare da Nafi'u haka Kuma akayi dole mijin ya amince ance Yana tsoronta kasancewar ta fishi ku'di.

Ana haka ne Nafi'u bashi da lafiya Kuma Already ya Fa'dawa Iyayensa cewa Yana da Ubangida a Kano ko da Iyayen Nafi'u s**a zo Kano daga bauchi sai Nafi'un ya gabatar da Iyayen nasa ga Dayyabu mijin Hafsat amatsayin maigidan sa ne na kasuwanci, ba kowa yasan cewa Nafi'u saurayin Hafsat bane sai abokan Nafi'un da Kawayenta na kusa, ana zargin Yaron da Hafsat ta Haifa Dan Nafi'u ne domin suna k**a sossai.

Ance ko Ina Hafsat za ta tafi tare suke tafiya da Nafi'u har Umrah Kuma mijin Yana kallo ba tare da yace komai ba.

Dalilin wannan rigima da ya sa Hafsat ta Kai kashe Nafi'u shine Nafi'un ne ya Fa'dawa Hafsat cewa zai yi aure ya samu wata matar aure tun lokacin shine ba a sake zaman lafiya ba tsakanin Hafsat da Nafi'u.

Allah ne ya taimakawa mijin Tabbas da shine zai kasance Gawa bisa wannan Dalilin soyayya Dake tsakanin Nafi'u da Hafsat Yanzu dai Hafsat ta kashe Nafi'u, Allah ya jikansa da rahama, jama'a don Allah a kiyaye dokar Allah a zaman aure idan ba haka Bala'i zai Cigaba da faruwa tsakanin Al'ummarmu.

An turamin Hotunan yaron Amma ba zan iya sakawa ba..

Rundunar yan sandan jihar Oyo ta kora tare da kwaɓe kakin wasu yan sanda biyu da aka ɗauki bidiyonsu suna tambayar wata ...
22/12/2023

Rundunar yan sandan jihar Oyo ta kora tare da kwaɓe kakin wasu yan sanda biyu da aka ɗauki bidiyonsu suna tambayar wata Baturiya da ta zo yawon buɗe ido Nijeriya, cewa ta ba su kuɗi

A yau an kore su kwatakwata daga aikin dan sandan, sak**akon samun su da laifin zubar wa rundunar yan sanda mutunci, da saɓa dokar aiki

AL'AJABI: Macijiya Mai Shekaru 963 Da Ta Yi Rayuwa Da Sarauniya Amina Ta Yi Gargaɗi Ga MutaneMacijiyar mai kimananin she...
20/12/2023

AL'AJABI: Macijiya Mai Shekaru 963 Da Ta Yi Rayuwa Da Sarauniya Amina Ta Yi Gargaɗi Ga Mutane

Macijiyar mai kimananin shekaru 963 a Duniya ta yi wa mazauna wajen gargaɗi, gargadin dai ya faru ne ta yadda ta tayar da hankalinsu da kuka da fitar da wani hayaƙi daga kogonta dake kan Dutsen Turunku.

Mazauna wajen dai sun zargi hakan ya faru ne sak**akon wani maciji da aka kashe bayan ya sakko daga dutsen zuwa kasa inda mutane ke gudanar da al'amuransu.

Al'amarin da ya faru a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

18/12/2023
18/12/2023

KASTELEA TAYI ZAMAN WAYAR DA KAI KUNGIYOYIN MASU SUFIRI DAKE JIHAR KADUNA

GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA FARA SHARAR HANYAR TUDUN BIRI GABANIN KADDAMAR DA AYYUKADaga Shuaibu Abdullahi Gwamnatin jihar...
18/12/2023

GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA FARA SHARAR HANYAR TUDUN BIRI GABANIN KADDAMAR DA AYYUKA

Daga Shuaibu Abdullahi

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara sharar hanyar shiga kauyen Tudun-Biri, gabanin kaddamar da ayyukan cigaba da Gwamnatin tayi alkawari.

Tawagar Gwamnatin ciki har da Shugaban KASUPDA dana hukumar tsare tsare gidaje KADGIS da mai temakawa Gwamnan Kaduna kan hulda da jama'a da sauran su ne s**a shiga garin a madadin Gwamnatin.

Kafin yanzu Kauyen Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, shine wanda Sojojin kasa s**a yi kuskuren sakin Bam da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 80 da raunata da dama.

Shugabannin sun yi alkawarin inganta garin tabangaren samar da Titin mota da Makarantu da ofishin yansanda da Asibitin kiwon Lafiya da lantarki da sauran su.

Ko a makon daya gabata Sai da kungiyar Gwamnonin Arewacin kasa karkashin jagorancin Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, s**a baiwa garin Tudun-Birin, tallafin nera miliyan 180.

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, yace ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, kan irin jajircewa da kokarin ganin an gudanar da sahihin bincike game da batun.

Ba Batun Diyya Muke Yi Ba A Halin Yanzu, Tambaya Muke Kan Me Yasa Aka Kashé Mana Mutane? Kuma A Fito Mana Da Waɗanda S**...
14/12/2023

Ba Batun Diyya Muke Yi Ba A Halin Yanzu, Tambaya Muke Kan Me Yasa Aka Kashé Mana Mutane? Kuma A Fito Mana Da Waɗanda S**a Yi Wannan Aika-aikar Mu Gansu, Sannan A Hukunta Su Domin Gudun Sake Faruwar Haka Ko Da Akan Dabbobi Ma Ba Mutane Ba

Cewar Mai Martaba Sarkin Kano Na 14 Muhammadu Sanusi II (Khalifan Tijjaniya Na Najeriya).

CIGIYYA! CIGIYYA!! CIGIYYA!!!Don Allah Ana  Cigiyya Iyayen Wannan Yaro Yace Suna Shi Sadiq, Sun Zo Biki Zariya A Kwarbai...
12/12/2023

CIGIYYA! CIGIYYA!! CIGIYYA!!!

Don Allah Ana Cigiyya Iyayen Wannan Yaro Yace Suna Shi Sadiq, Sun Zo Biki Zariya A Kwarbai Daga Nasarawa Doya, Yanzu Haka An Tsince Shi A Cikin Garin Kaduna. Allah Ya Bayana Iyayen Shi Duk Mai Neman Kari Bayani Ya Kira Wannan Number Waya 08027183008

12/12/2023

Jam'ar British Amerika ta tabbatarma Eng kailani Mohamed da matsayin farfesa a Abuja

CIN AMANAR AUREShi kuma wannan matashin 'yan sanda a jihar Bauchi sun k**ashi saboda yayi yunkurin kashe matarsa da taba...
11/12/2023

CIN AMANAR AURE

Shi kuma wannan matashin 'yan sanda a jihar Bauchi sun k**ashi saboda yayi yunkurin kashe matarsa da tabarya don ya samu damar sayar da kayanta ya kara jari a shagonsa

Matashin mai suna Tijjani Ahmadu Diye bayan ya buge matar nasa da tabarya har ta suma, sai ya kai rahoto cewa wai barayi ne s**a shiga gidansa s**a buge matar

Cikin ikon Allah bayan an kai matarsa Asibitin koyawar na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi ta farfado, kuma tayi bayani wa 'yan sanda cewa rahoton da mijinta ya bayar karya ne

Ba'a yi kasa a gwiwa ba 'yan sanda s**a k**a mijin, kuma ya amsa laifinsa cewa ba barayi bane, shine yayi niyyar kasheta don ya sayar da kayanta ya kara jari a shagonsa

Wannan itace irin rayuwar da mukeyi a yau, kusan kowa idonsa ya rufe, ana neman kudi ta kowace irin hanya, abin mamaki wai miji da yunkurin kashe matarsa don ya mallaki dukiyarta

Allah Ya sauwake, Ya nesanta tsakanin mu da masoyan karya

09/12/2023

Wasu da ba'asansu ko suwaye ba sun sari wani matashi a kaduna yanzu haka yana asibitin Barau Dikko

09/12/2023

Yau Ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya hukumar EFCC ta Gudanar da zagayen wayar da kan Al'uma da hadin guiwar sauran rundunonin tsaro dake jihar

07/12/2023

Wani Dan majalisar kano ya kwashe yan mazabar shi ya dawo dasu Zaria a zauren majalisar ana ganin fate yasha ya shi wannan tukuici
Me zakuce

JERIN SUNAYEN SHUWAGABANNIN KARAMAR HUKUMAR ZARIYA DAGA 1973 ZUWA YAU1. Alh. Mijinyawa Dikko 1973-19772. Alh. Ahmadu Fat...
07/12/2023

JERIN SUNAYEN SHUWAGABANNIN KARAMAR HUKUMAR ZARIYA DAGA 1973 ZUWA YAU

1. Alh. Mijinyawa Dikko 1973-1977
2. Alh. Ahmadu Fatika 1977-1979
3. Alh. Salisu Ahmad 1980-1983
4. Alh. Dayyabu Kurfi 1984-1986
5. Alh. Muhammadu Lawal 1986-1988
6. Alh. Hamidu Yahaya 1988-1989
7. Alh. Muhammad Amfani 1989-1989
8. Mr Thomas Kazah 1989-1991
9. Alh. Armiyau Suleiman 1991-1993
10. Alh. Jafaru Suleiman 1994-1996
11. Alh. Bashir Ismail Ahmad 1997-1997
12. Alh. Mohammed Bashir Ali 1997-1997
13. Alh. Muhammad Tukur 1997-1997
14. Alh. Samaila Nabara 1997-1998
15. Alh. Idris Adamu 1998-1999
16. Alh. Musa Iyah 1999-2003
17. Alh. Abdussalam Baba Ahmad 2003-2003
18. Alh. Mohammed Tukur Abashe 2003-2004
19. Alh. Yahaya Aminu 2004-2007
20. Alh. Lukuman Musa 2007-2007
21. Major Muhammad Aliyu 2007-2008
22. Alh. Yahaya Aminu
23. Alh. Lukuman Musa 2008-2008
24. Muhammad Umar Raba Gardama
25. Hon. Lawal Balarabe 2012-2014
26. Yusuf Bature Mai zarman 2014-2015
26. Barr Jafar Abbas 2016-2016
27. Eng Abubakar Maude 2016-2018
29. Eng Aliyu Idris Ibrahim 2018-Date


06/12/2023

Wai ya dace a irin wannan lokacin malaminan yayi irin wannan maganar

06/12/2023

Gara basa !
Gara basa !!
Gara basa !!!

Kudinka kalilan ka kwashi kasiran sai yardan Allah

06/12/2023

Dolene abiya diyar wadanda aka kashe a gurin mauludi a kaduna bazamu yarda ya zama k**ar yan uwamu da aka kashe a filato ba Inji Sheikh Dahiru Usman bauchi

05/12/2023

Yadda Aka Gudanar Da Jana'izar sama da mutane 80 da harin bom ya kashe a kaduna

04/12/2023

Ba sojojin sama bane s**a jefa bom a gurin mauludi a kaduna

04/12/2023

Korafin wani daga yankin da aka jefa bom kan masu mauludi a tudun biri dake yankin buruku a karamar hukumar Chikun kenan

04/12/2023

Hon Mamadi yayima masu hudar shanu kyautar da wani bai taba yi musu ba sama da shekaru 50 Karamar hukumar Igabi
Ga rahoton saurara kaji

Dan Dumi Dumi Wani jirgin yakin sojojin saman najeriya ya jefa bam kan wasu masu mauludi a kaduna karin bayani na zuwa n...
04/12/2023

Dan Dumi Dumi Wani jirgin yakin sojojin saman najeriya ya jefa bam kan wasu masu mauludi a kaduna karin bayani na zuwa nan gaba kadan

LABARAI DA DUMI-DUMI !!  Tsohon Shugaban Mulkin Soja Na Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida, Yayi Kira Tare Dajan Hankal...
03/12/2023

LABARAI DA DUMI-DUMI !!
Tsohon Shugaban Mulkin Soja Na Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida, Yayi Kira Tare Dajan Hankali Ga Babban Mai Shari'a Na Kasa Alkalin Kotun Koli, Yasani Cewa: Zaman Lafiyar Najeriya Yarataya Awuyan Bangaran Shari'a, Kasancewar Yanzu Mulkin Najeriya Na Dimokaradiyane Mai Cike Da Kalubale Da Sarkakiya, Akwai Bukatar Asamu Adalchi Awajan Hukunce Hukuncen Kararrakin 'Yansiyasa, Ayi Kokarin Kaucewa Sanrai Ko Bukatun Wasu Manya Ko Shuwaga Bannin Siyasa, Domin Cigaba Dasamun Dawwamamman Zaman Lafiya A Najeriya Kasarmu Tagado, Yazama Wajibi Ayi Hattara Wajan Zartar Da Hukunci Tahanyar Adalci Bangaran Mai Kara Da Wanda Ake Kara, Kada Ayadda Ayi Anfani Da Bangara n Shari'a Don Biyan Bukatun Wasu Tsirari Don Atozarta Wasu, Saboda Gudun Abinda Zai Biyo Baya Bazaiwa Kowa Dadiba Harda Mu Kanmu Tsofaffin Iyayan Kasa !

SAKON GODIYA DA KUMA BAN GAJIYAAssalamu Alaikum. Ina amfani da wannan dama domin mika godiya a gareku bisa kauna, karamc...
02/12/2023

SAKON GODIYA DA KUMA BAN GAJIYA

Assalamu Alaikum.

Ina amfani da wannan dama domin mika godiya a gareku bisa kauna, karamci da kuma mutuntawa da kuka nuna a gareni, na halartar bikin nadin sarauta na a matsayin SARKIN SAMARIN GONA da kukayi wanda mai martaba Lamido Gona ya karramani da ita, hakika ba zan manta da wannan halacci naku gareni ba.
Ina adduar Allah ya sakawa kowa da alheri ya kuma huce gajiya.

Nagode.
Bilya Yaro Dawakin Tofa
SARKIN SAMARIN GONA

MUTUM NA FARKO DA YA GINA  ISLAMIYYA A GARIN  KADUNA Marigayi Alhaji Abdu Kwangila, shahararren attajiri mai son cigaban...
01/12/2023

MUTUM NA FARKO DA YA GINA ISLAMIYYA A GARIN KADUNA

Marigayi Alhaji Abdu Kwangila, shahararren attajiri mai son cigaban addinin musulunci. Mutum na farko daya fara kafa makarantar Islamiyya a garin Kaduna. Asalinsa mutumin kasar Bidda ne, ya komo Kaduna da zama a wajejen 1935. Mutum ne mai gaskiya, da kwazo da son malamai da yawan taimako. Shine mai masaukin malamai da yawa a Kaduna. Allah Ya Jikan Shi Yayi Mishi Rahama Yasa Yana Kyakyawan Matsayi.

30/11/2023

Shugabannin kungiyar dakon mai ta PTD sunyi kira ga membobin kungiyar dasu zauna lafiya su kaucema masu kiran suyi zanga zanga ko yajin aiki

29/11/2023

Wani Dan sanda ya harbe mutane biyu a kaduna saboda takaddamar labule da me adaidaita sahu

Address

Kaduna

Telephone

+2348036559217

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskira TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other News & Media Websites in Kaduna

Show All

You may also like