05/09/2022
LITTAFI NA UKU
LAILA DA MAJNUN...
Bayan ya farfad’o jakada ya ce masa, “ba na so a ganka, domin jama’a na iya k**a ka su yi maka wulak’anci kafin ka ga Laila. Ga wani kango can ka shiga ka zauna a ciki ka huta domin ka yi tafiya mai yawa. Zan isar da sak’onka ga Laila yanzun nan.” Majnun ya yarda da shawarar jakada ya shiga kangon nan ya zauna zuciyarsa na harbawa k**ar ta tsage. Sak**akon tafiyar da ya sha duk yayi futu – futu. Tufafinsa sun yi jawur da k’ura, gashin kansa duk ya kukkulle, ga kafafunsa sun yi fato – fato da kura da faso da kaushi. Ga shi nan dai yarbajila da shi. Duk da haka, da ya tuna cewar yana garin da Laila ta ke gaba d’aya sai ya ji ransa ya yi fari fat. Ya cika da murna da farin ciki, zuciyarsa ta cika da bege ya rik’a rera wak’a yana cewa:
Na aika sako na wajen masoyiya,
Zuciyata da rayukana gaba daya,
Na mika su dukansu wajenki gimbiya,
Ke ce tawa hakika na fadi gaskiya.
Na sallama miki kaina lahira da duniya.
Daga nan sai gajiya ta k**a shi, ya ji yana so ya kwanta. To amma sai ya rika tunanin shin a wanne bangare Laila take? Domin baya so ya kwanta inda k'afarsa zata rika kallon jihar da take domin a wajensa hakan cin amanar kauna ne.
Zai iya shurinta bai sani ba. Ya tsaya yana tunani, shin tana gabas ne ko yamma ko kudu ko kuwa arewa? Duk inda ya sa kansa sai ya tuna kila a wannan bangaren take, sai yayi maza ya sake waje. Daga baya dai sai ya samo igiya ya daura a kafarsa ya samu gini ya daura kafar, yana zamana yana reto k**ar jemage. A wannan yanayi kuma bai fasa rera mata wak'a ba yana cewa:
Hajjina da Umarata na wajenki,
Makka ta da Madina sune ganinki,
Baitil Mukdis wurina murmushinki,
Arzikina duk ni dai in ga dariyarki,
Na sallama kaina gabadaya a wurinki
Kishin ruwa na damunsa amma babu ruwa a kurkusa, haka ya hakura wutar bege na hura shi, tana kone masa sassan jiki da zuciya. Jakada ya yi sallama k'ofar gidansu Laila ta fito, ya ce mata, "na yi kokari da gaske domin na yi miki magana, game da masoyinki Majnun wanda ban taba ganin tamkarsa ba a fagen so." Ya kwashe labarin duk yadda s**a yi ya fad'a mata. Sannan ya kara da cewa, "yanzu haka na bar shi a bayan gari domin gudun kada a wulak'anta shi idan jama'a s**a ganshi." Da Laila ta ji haka sai tausayinsa ya k**a ta. Ta tafi wajen uwar goyonta ta ce mata, "me yake faruwa ga mutumin da ya yi tafiyar mil dari da ashirin a kasa ba tare da ya huta ba?"
Tsohuwa ta ce, "wannan mutumin ba zai rayu ba mutuwa zai yi." Laila na jin haka sai ta ji ta shiga damuwa, ta sake ce mata, "babu wani magani?" "Magani daya ne a sanina. Dole ya sha ruwan saman da aka ajiye shi akalla shekara d'aya, kuma dole ruwan ya zamana maciji ya sha daga gare shi. Sannan ya daura igiya a kafarsa ya zamana kansa na kallon kasa zuwa wani lokaci. Idan ya aikata hakan watakila zai tsira da ransa."
Da ta ji haka sai ta yi tagumi tana cewa, "wannan magani akwai wahalar samu, kai ba ma zai yiwu ba." Ta d'aga hannu sama tana rok'on Allah ta ce, "Ya Allah mai kulla soyayya, mai bayarwa mai hanawa ka taimaki Qays Majnun ya samu wannan magani." Ta shafa sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "soyayya bata da magani sai ita kanta." Allah da ikonsa, Majnun na rataye da kafarsa a sama ga kishirwa na addabarsa sai ya kwance igiyar ya tafi neman ruwa. Bai samu ruwa ba sai wani tsohon kasko a wani lungu. Ya tarar wani zabgegen maciji na shan ruwan. Ya kore shi sannan ya kafa kai ya shanye ruwan gaba daya. Ya samu waje ya zauna yana wake - wakensa.
Da gari ya waye Laila ta shirya abinci mai rai da lafiya ta kirawo kuyanga a boye ta fada mata komai sannan ta nemi ta kai wa Majnun inda yake a bayan gari. Kuma ta bata sakon a fada masa cewar ita ma tana nan tana kaunarsa kuma tana son ganinsa, amma da zarar ta samu dama zata zo ta ganshi. Yayin da kuyanga ta je wajen sai ta tarar da mutane biyu. Daya ya hada kai da gwiwa kuma duk ya rame ga kansa nan duguzunzum, dayan kuma mai kiba jawur da shi, sai dai ya manyanta. Kuyangar ta dube su duka biyun ta ga babu wanda ya cancanci Laila ta so shi.
Ita kanta ma ta ji duk basu kwanta mata a rai ba, b***e kuma Laila. Duk da haka domin cika umarni sai ta ce, "a cikinku waye Majnun?" Mai kibar ne kadai ya ji sai ya taso wajenta ya ce, "me ya faru?" Sai ta nuna kwandon abinci ta ce, "cewa aka yi na kawo masa wannan daga Laila." Nan da nan ya karbe abincin yana cewa "ni ne Majnun." Ta fada masa sakon Laila ya yi mata dan wasa haka sannan ya sa abinci a gaba ya cinye. Ya ragewa Majnun dan kadan. Daga wannan rana kullum sai ta kawo masa abinci da sakon baka, shi kuma sai ya cinye ya rage kadan domin Majnun. Kullum Laila kan tambayi kuyanga, "me ya ce ki fada min?" Sai kuyanga ta ce, "wai ya gode madalla da abinci." Laila ta shiga kokwanto anya kuwa Majnun dinta ne? Bayan kwana uku dai da ta gaji sai ta ce da kuyanga, "yaya kika ga k**annin Majnun din?" Kuyanga ta ce, "wani mai kiba yana da saje da kasumba...ya manyanta..." Farat Laila ta ce, "wallahi ba shi ba ne, wannan jakada ne wanda ya kawo min sakonsa. Majnun ba tsoho ba ne kuma ba shi da kiba." Ta dubi kuyanga ta ce, "su nawa ne a wurin?" Kuyanga ta ce, "su biyu ne." Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce, "to yau ba za a kai abinci ba, amma zan sa ki musu wata jarrabawa domin mu gane Majnun na gaskiya." Ta bata wuka ta fad'a mata abin da zata yi da ita.
~ Great Uncle Ahmad 🥰.