18/03/2023
YANZU-YANZU: Gamayyar wasu Dattawa masu kishin Kaduna, Malamai da matasa da Kiristoci da mata sun zabi dan takarar APC, Malam Uba Sani a matsaya wanda ya fi cancanta a zaba a matsayin Gwamnan Kaduna bayan sun duba duka yan takarar
Sun bayar da dalilai kamar haka:
"Uba Sani ɗan siyasa ne wanda ya sha bamban da saura, bai taɓa faɗa da malaman addini ba, bai taɓa hawa mumbarin siyasa ya yi katobarar da ta nuna ba shi da ilimin addini ba. Kalamansa cike su ke da ƙanƙan da kai da bar wa Allah ikonsa kan komai. wannan mutum ya cancanta mu zaɓe shi".
"Mu na kiran kowa da kowa da ke cikin kowace jam'iyya, Lallai a zaɓi Malam Uba Sani a matsayin gwamnan Jahar Kaduna domin cigaban Jihar Kaduna da gina goben matasa da ganin kima da mutuncin kowa".
"Ina amfani da wannan dama na yi kira ga masu zaɓe a Jahar Kaduna lallai a zaɓi Uba Sani domin kare mutuncin addini, al'adu da gina rayuwar matasa masu tasowa".
"Uba Sani mutum ne mai cikar kamala da koyi da sunnonin ma'aiki S.A.W wanda zaɓensa masalaha ne ga al'umma da yi wa musulunci gata".
"Muna kyautata zato ga ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Jahar Kaduna, Malam Uba Sani don haka mu na kira ga jama'ar Kaduna a tabbatar an zaɓe shi domin ya cancanta ta kowace fuska".
A yada wannan sako
Share this...