25/05/2023
LABARI MAI CIKE DA TAUSAYI.
Yake cewa: Naje chirar kudi a wani POS. Sai naga wasu yara su hudu uku mata da namiji yaya, s**a mika ATM s**a ce aciro naira dubu day aka sanya sai yanuna kudin ciki bas**ai hakanba, s**ace sanya dari tara, nanma basu kaiba, to ka sanya dari takwas da dari bakwai duk basu kaiba.
Fuskokin yarannan cikeda damuwa s**a tafi, bayan minti uku sai ga uwarsu tadawo tareda yaranta fuskarta cike da damuwa, sai uwar taceda mai POS din don Allah asake jarraba dari shida namma baikai ba tace to gwada dari biyar ko zaiyi yace to.
In takaice muku bayani sai da aka sanya dari hudu sannan kudi s**a fito, sai naga hawaye na neman fitowa daga idanunta ta kar6i dari hudun tayi hodiya.
Ina biye dasu abaya sai naji tacewa ya'yan nata cewa... Da alama yau 500 ya tura mana amma hakanma mungode da kokarinsa, ta sake cewa to amma ya zamuyi da ita.?
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN
Bansan sanda na matsa kusa dasuba nashiga maganarba, ashe kanintane ke tura mata da dubu daya duk sanda yasami dama yau kuma dari biyar aka samu
Ashe mijinta ne yarasu kusan shekara daya da rabi kuma a haka suke rayuwa
Najasu gefe nayi abinda zan iya wanda zai faranta rayuwarsu zuwa wani lokaci sannan nabasu lambar wayata zuwa gaba.
ABIN DUBAWAR SHINE.
Ina masu kudinmu.?
Ina imaninmu.?
Ina tausayinmu.?
Ina hakkin makoftaka.?
Da yawan mutane sun dauka Sallah da Azumi sune kadai yadace muyi, a'ah ba haka bane harda taimakon Al'umma wajen inganta rayuwar su da abinda yadace.
Wannan Rubutun Hannunka Mai Sanda Nayi Domin Kawo Chanji Ga Al'ummar Mu.