19/07/2022
Faɗuwar APC a Osun darasi ne gare mu - Abdullahi Adamu.
Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce kayen da jam’iyyar ta sha a zaɓen gwamnan jihar Osun jarrabawa ce daga Allah.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC, Adamu ya ce ya zama wajibi ga 'ya’yan jam'iyyar su gyara abubuwan da suke yi waɗanda ba daidai ba ne game da tafiyar da lamuran siyasar ƙasar gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce "Wannan ya nuna cewa akwai aiki a gabanmu, dole ne mu ga abin da muke iya yi, mu canza salo."
Ya ƙara da cewa "Dole ne mu dubi kawunanmu, mu ga mene ne abubuwan da muke yi a tafiyar nan waɗanda daidai ne, mene ne wanda ba daidai ba, mene ne ke neman gyara, domin mu gano mece ce mafita a tafiyar nan."
Sai dai shugaban jam'iyyar na APC ya ce wannan faɗuwa ba ita ce ke nufin jam'iyyar za ta faɗi a babban zaɓen ƙasar na 2023 ba.
A cewarsa jam'iyyar za ta yi nazarin abubuwan da s**a sanya jam'iyyar ta faɗi zaɓen na jihar Osun domin ta samu nasara a zaɓen ƙasa mai zuwa.
A cikin wannan wata na Yuni ne dai Senata Ademola Adeleke na jam`iyyar PDP ya samu nasara a kan gwamna Gboyega Oyetola na APC, wanda ya nemi wa`adi na biyu, da ratar ƙuri`a kusan dubu talatin.
Hakan ya faru ne kuwa duk da cewar jihar Osun tana a kudu-maso-yammacin Najeriya ne, yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya fito.
'Baraka tsakanin ‘yan jam’iyya'
Shugaban na jam'iyyar APC na ƙasa ya kuma tabbatar da cewa ɓarakar da ke tsakanin manyan 'yayan jam'iyyar ne ya haifar da faɗuwar ta a zaɓen na Osun.
Ya ce "Ya tabbata akwai rashin jituwa tsakanin magabata, masu isa a tafiyar siyasar jihar Osun na jam'iyyar APC."
Ya ce waɗannan jiga-jigai na jam'iyyar APC jihar ta Osun sun rinƙa s**ar da zargin junansu.
Ya ƙara da cewa "Idan s**a buɗe baki cewa suke yi ba za su yi zaɓe ba idan ba a yi masu abin da suke so ba."
Ya tabbatar da cewa jiga-jigan na APC a jihar ta Osun sun kasa jituwa tsakanin su duk da cewa suna a jam'iyya ɗaya.
'Mun karɓi ƙaddara'
"Harka ta siyasa kamar sauran lamurra ne na rayuwa, kana iya nema ka samu ko kuma ka rasa. Iko ne na Allah, babu yadda muka iya" in ji Abdullahi Adamu.
Sai dai Abdullahi Adamu ya ce ba an kayar da APC ne saboda ba ta iya siyasa ba, sai dai saboda abubuwan da s**a faru tsakanin 'yayan jam'iyyar gabanin zaɓen.
A cewarsa, jam'iyyar ta amince da ikon Allah.