11/12/2021
AREWA! 😭
Tun ina yarinya na lura da duk shugaban da ya hau mulki sai ya sa Arewa zubda hawaye. Ban taɓa ganin Arewa ta yi murmushi har ta yi dariya na tsawon lokaci ba, yau ga shi nima na girma har ina shirin ajje iyali amma yankina ba ta samu 'yancin kanta ba. A da mutanen Arewa basu da yawa amma ana cikin matsin rayuwa cin nama da shan jar miya sai gidan da suke da mota kuma ake kuna generator in babu wuta ko transformer ta lalace. A da kuma har a yanzu ina transformer ta lalace ana ɗaukar watanni huɗu zuwa biyar kafin a gyara kuma wai a haka da akwai waɗanda alhakin gyarar ke kan su.
Malamina ya faɗa min idan aka kashe rai guda ɗaya ba da hujja ba to duka garin za a haɗa a kashe domin babu abinda Ubangiji ya fi girmamawa sama da ran ɗan adam. Amma a yanzu fa? Rayuka nawa aka kashe ba tare da hujja ba? Yara nawa aka mayar marayu ba tare da an tallafi rayuwar su ba? Mata nawa aka maida zaurawa? Duk a cikin yankina ake wannan ɗanyen aikin.
To ya ishe mu haka! Mun gaji da kisar gillar da ake mana, ku bamu kariya da tsaro. Ba mu ce ku bamu kuɗi ba mu rayukanmu muke bukatar ku kare mana!
Babanmu ka dube mu da wan nan tausayin da muka san ka da shi! Ka ce zaka kare rayukanmu daga mugayen da suke kashe mu amma Baba har yanzu mun ji ka yi shiru! Arewa taka ce kuma mu ma naka ne don haka muke rokon da ka yi duba zuwa ga tsaron Arewa, ka cire min tunanin da nake yi tun daga yaranta har zuwa yau kan cewar Arewa ba ta da 'yanci kuma shuwagabanninta kansu da 'ya'yansu ne kawai suke gani a cikin yankina ta Arewa.
Gare ka haziƙin Gwamna Malam Nasiru Elrufa'i na sani kuma kowa ma ya san yadda kake ta fafutukar yaƙi da mutanen nan amma Malam muna bukatar ka ƙara saka idanu a ɓangaren tsaro jihata, adali ne kai shi ya sa muke bukatar da ka kara nemo mana hakkinmu a garun wanda suke tunanin ba mu kai ba.
Ina addu'ar Allah Ya shigo cikin lamarin yankina da jihata.
Basira Sabo Nadabo