Gandun Kalmomi

Gandun Kalmomi Gandun Kalmomi fage ne na baje kolin fasaha da fikira da sharhi kan rubutu da marubutan Hausa | Gandun Kalmomi is a platform showcasing Hausa Literature

Coming to your screen, very soon!Hausa International Reading Festival!Keep a date!
02/07/2024

Coming to your screen, very soon!

Hausa International Reading Festival!

Keep a date!

02/07/2024

DUNIYAR UMMU SALMA:

Ba ta fara don ta daina ba!

Gandun Kalmomi na tare da ke ISA!

17/06/2024

Open Arts Da Haɗin Gwiwar Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe, KASU, Kaduna.

RANAR TUNAWA DA SHATA!

Gobe Take Salla! (18 ga watan Yuni, 2024)

A Dandalin Wasan Kwaikwayo, na jami'ar Jihar Kaduna da misalin ƙarfe 3 na rana, ISA.

2:00-3:00 na rana: Zuwan manyan baƙi da sauran mahalarta.

3:00-3:10 na rana: Jawabin Buɗewa daga Salma Ja’eh, Gidauniyar Open Arts, Kaduna.

3:10-3:20: Baje Kolin Hikimar Mawaƙa Daga Ɗaliban KASU, Kaduna

3:20-3:30: Jawabin Maraba daga Muƙaddashin Shugaban Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, KASU, Kaduna, Dakta Alamuna Nuhu.

3:30-3:40: Ci Gaban Baje Kolin Hikimar Mawaƙa Daga Ɗaliban KASU, Kaduna.

Shaƙatawa/Salla

4:30-4:40: Baje Kolin Hikimar Mawaƙa Daga Mahalarta Taro.

4:40-5:30: Tattaunawar Musamman: WANE NE SHATA? Tare da Farfesa Audee T. Giwa da Dakta Lawal Ɗanƙwari, bisa jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi.

5:30-5:40: Jawabin Godiya daga Sada Malumfashi, Daraktan Gidauniyar Open Arts, Kaduna.

5:45-7:00: Gwangwaje Waƙoƙin Marigayi Shata daga bakin ɗansa, Alhaji Sanusi Mamman Shata.

15/12/2023

Kunnenku Nawa?

GANDUN KALMOMI Na Gabatar Muku Da Mujallar TANTABARA, Fitowa Ta Musamman Kan Batun – Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa!

A tarba a: gandunkalmomi.org

Sanarwar Ta Musamman!MUJALLAR TANTABARA ZA TA SAUKO ƊAUKE DA BAYANAI MASU ILMANTARWA DA NISHAƊANTARWA A YAU 15 GA WATAN ...
15/12/2023

Sanarwar Ta Musamman!

MUJALLAR TANTABARA ZA TA SAUKO ƊAUKE DA BAYANAI MASU ILMANTARWA DA NISHAƊANTARWA A YAU 15 GA WATAN DISAMBA 2023, SAI A TARBA A SAHAR gandunkalmomi.org!

Gandun kalmomi is a platform of thought stimulating questions and ideas, a place where facts are provided as basis for learning, de-learning and relearning processes. Where there’s exchange amongst the Hausa people and a conversational gateway to the global community.

Kada A Shagala!Ina Marubutan Hausa?GANDUN KALMOMI Na Shirin Gabatar Da Mujallar TANTABARA,  Fitowa Ta Musamman Kan Batun...
10/10/2023

Kada A Shagala!

Ina Marubutan Hausa?

GANDUN KALMOMI Na Shirin Gabatar Da Mujallar TANTABARA, Fitowa Ta Musamman Kan Batun – Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa!

Shin kuna da sha’awar rubutu ko karatu kan al’amurran da s**a shafi Hausa da Hausawa, musamman abin da ya shafi tarihi ko al’adu ko harshe ko adabin Hausawa? Kuna da waɗansu rantsattsun rubuce-rubuce ko waƙoƙi da s**a shafi Hausa da Hausawa? Mujallar TANTABARA na kira gare ku da ku aiko da su domin bugawa a fitowa ta musamman a cikin mujallar. Taken wannan fitowa shi ne, ‘Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa’ da za a wallafa a Yanar Gizo ta bazar GANDUN KALMOMI.

Mujallar na buƙatar karɓar sharhi na musamman ko waƙoƙi da suke tattauna rayuwar Hausawa jiya da yau, ko kuma bayanai da suke tattaɓa tarihin Hausawa da al’adu da adabi da harshe da siyasa da addini da zamantakewa baki ɗaya, a tsawon tarihi. Haka za mu so mu ga an aiko da sharhi kan batutuwa da s**a shafi gwarazan ƙasar Hausa, ko waɗansu manyan garuruwa da biranen tarihi da duwatsu ko mazaunai na ƙasar Hausa cikin tsawon tarihi.

Ƙa’idojin Aiko Da Bayanai:

Duk abin da za a turo, a tabbata ya shafi taken wannan fitowa ta musamman, wato “Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa'

Babu wata ƙa’ida kan yadda za a yi rubutun ko waƙar, a dai tabbata an sa gwanintar harshe da iya rubutu domin burgewa da ƙayatarwa, ana kuma iya turo da batutuwa da s**a shafi sharhi da labarai ko taƙaitaccen tarihin wani ko wata ko kuma wasu ko hira da aka yi da waɗansu daga al’ummar ƙasar Hausa.

Waƙoƙi kuwa za su iya zuwa da kowace fuska, ko waɗanda ke bin ƙa’idojin rubutun waƙa ko kuma ballagaza, madamar sun taɓo tarihin Hausa ko al’adu da al’ummar ƙasar Hausa.

Haka kuma duk wani rubutu na burgewa da tsimawa, in dai ya shafi taken wannan fita ta musamman, za su samu gurbi a ciki.

Duk rubutun da za a yi kada ya wuce kalmomi 1,500, waƙoki kuwa kada su wuce baiti 15 ɗauke da kowane tafarki na ƙwar ɗin waƙa.

Hanyar turo da saƙo:

Ana iya turo da saƙon sharhin ko waƙa zuwa ga: [email protected]
A tabbata an saƙala ‘Saƙon Bugun Mujallar TANTABARA' a cikin wasiƙar da za a haɗo.

A turo da saƙon ta manhajar WORD ba PDF ba, a kuma tabbata an sa cikakken suna da imel da ɗan taƙaitaccen tarihi na waɗanda s**a turo da saƙon.

Ranaku Na Musamman:

Duk saƙonni da za a turo ana buƙatar su iso zuwa ranar 30 ga Watan Oktoba, 2023.

Za a sanar da waɗanda sharhinsu ko waƙokinsu, s**a gamsar, s**a kuma fi burgewa, aka kuna amince za a buga su zuwa ranar 7 ga Watan Nuwamba, 2023.

Wannan fitowa ta musamman ta Mujallar TA TANTABARA za a ƙaddamar da ita a Yanar gizo a bargar GANDUN KALMOMI da kuma wajen BIKIN BAJE KOLIN LITTATTAFAI DA FASAHOHIN HAUSAWA (HIBAF) na shekarar 2023, tsakanin ranakun 15 da 16, na watan Disamba, 2023.

Awalajar Da Za A Samu:

Mun san ba za mu iya biyan wannan gagarumin aiki da za a turo ba, amma duk da haka waɗanda aka zaɓi rubutunsu domin bugawa za su samu tukuici na musamman, kuma za a dinga ganin rubuce-rubucen nasu taskace a cikin Mujallar TANTABARA da ke fitowa a cikin GANDUN KALMOMI a kodayaushe a Yanar Gizo da ke wataye dukkan sassan duniya da ke mu’amala da Hausawa da harshe da adabi da al’adun Hausawa.

Muna kira ga zaƙaƙarun marubutan sharhi da waƙoƙi da su kasance tare da mu a wannan fitowa ta musamman in da za mu baje kolin rayuwa da tarihin Hausa da Hausawa a doron ƙasa domin musayar ra’ayi da ilmantarwa da nishaɗantarwa da taskace tarihi na har abada.

Domin ƙarin bayani sai a tuntuɓi: [email protected]

Naku a kullum,

Ibrahim Malumfashi
Babban Edita, Mujallar TANTABARA

Ina Marubutan Hausa?GANDUN KALMOMI Na Shirin Gabatar Da Mujallar TANTABARA,  Fitowa Ta Musamman Kan Batun – Hausa Da Hau...
29/09/2023

Call for Submissions: TANTABARA Magazine - Exploring Hausa People in HistoryAre you fascinated by the rich history, cult...
29/09/2023

Call for Submissions: TANTABARA Magazine - Exploring Hausa People in History

Are you fascinated by the rich history, culture, and language of the Hausa people? Do you have a story to tell, a poem to share, or insightful commentary that sheds light on the vibrant tapestry of Hausa heritage? TANTABARA Magazine invites you to submit your work on the theme "Hausa People in History" for our upcoming feature on the GANDUN KALMOMI website.

We are seeking diverse and engaging articles, poems, and commentaries that highlight the remarkable contributions, traditions, and evolution of the Hausa people throughout history. Whether you have knowledge of influential historical figures, iconic landmarks, language evolution, or captivating cultural aspects, your unique insights and perspectives are welcomed.

Submission Guidelines:
- All submissions must adhere to the theme "Hausa People in History."
- Articles may take any form, including essays, narratives, biographies, or interviews.
- Poems reflecting Hausa history, language, or cultural experiences are also encouraged.
- Commentaries that offer thought-provoking analysis or exploration of Hausa heritage will be considered.
- Submissions should be a maximum of 1,500 words for essays and poems of not more that 20 lines.

How to Submit:
- Interested contributors should email their submissions to:
[email protected]
- Please include "TANTABARA Magazine Submission" in the subject line.
- Attach your submission as a Word document, making sure to include your name, email address, and a brief bio in the file.

Important Dates:
- The submission deadline is October 30,2023.
- Selected submissions will be notified via email by November 7, 2023.
- The feature will be published on the GANDUN KALMOMI website and launched during HIBAF23 on 15 December, 2023.

Benefits for Contributors:
- Your work will be prominently featured in TANTABARA Magazine on the reputable GANDUN KALMOMI website, reaching a wide audience interested in Hausa culture and history.
- Gain recognition for your unique perspectives and writing skills.
- Selected contributors will receive a token as appreciation, an honorable mention and have the opportunity to be featured in future publications by GANDUN KALMOMI.

Join us in celebrating and exploring the fascinating world of Hausa People in History through TANTABARA Magazine. Open the doors to cultural understanding, inspire curiosity, and share your knowledge by submitting your work today!

For any queries or additional information, please contact us at: [email protected]

We look forward to reading your compelling submissions!

Warm regards,

Ibrahim Malumfashi
Editor-in-Chief, TANTABARA Magazine

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gandun Kalmomi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category

Other Magazines in Kaduna

Show All