23/02/2023
(4): Ɗan takarar da zan zaɓa
A wannan fitowar, zan bayyana ɗan takarata haɗe da dalilan da ya sa zan zaɓe shi. Kuma zan kawo wasu daga cikin ƙorafin da wasu jama'a suke yi gameda shi, haɗe da tsokacina.
Kowa ya san matsalolin Najeriya a yau fanni-fanni ne. Amma na fahimci galibin matsalolin suna da alaƙa da karayar tattalin arzikin da ya same mu. Karayar tattalin arziki yana kawo taɓarɓarewar tsaro, ya illata harkar ilimi, ya kawo cikas a fannin kiwon lafiya, da sauran al'amuran rayuwa. Sai na fahimci gyaran Najeriya za'a faro shi ne daga ceto tattalin arzikin ƙasar.
Bayan na kalli ƴan takarar baki ɗaya, sai na ga cikinsu akwai wanda ya fi sauran kyakkyawar fahimta gameda tattalin arziki. Bugu da ƙari, har ya taɓa jagorantar wasu masana da s**a kawowa Najeriya sauyin yanayi a lokacin da ta taɓa samun karayar arziki fiye da shekaru 20 baya. Don haka na zaɓi wannan ɗan takarar a matsayin wanda ni Ibrahiym zan jefawa ƙuri'ata. Ɗan takarar kuwa shine Alhaji Atiku Abubakar, na jam'iyyar People's Democratic Party (PDP).
Ma'abota hankali sun koyi darasi mai yawan gaske a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa yau. Sun fahimci cewa baka cika-baki gameda ɗan siyasa, kace lallai zai yi kataɓus. Kai dai faɗi abubuwan da ka fahimta, kayi zaɓe, kayi addu'a. Amma shi kansa ɗan takara bai san yadda mulkinsa zai zama ba. Dalilin hakane zan bayyana iyakar abinda na gamsu da shi gameda Atiku Abubakar, ba tareda na cika baki ba cewa lallai idan ya samu Shugabanci zai maida ƙasar tamkar wata Ingila. A'a. Sanin wannan sai Allah, Wanda ya kaɗaita da sanin gaibu.
Waɗannan sune mafiya nauyin ƙorafe-ƙorafen da wasu jama'a suke yi gameda Atiku Abubakar, haɗe da abinda nake fahimta:
1. Adawa da dokar Shari’ar Musulinci a Najeriya: Nayi bincike mai zurfi ta hanyar bibiyar maganganun Atiku Abubakar da kanshi akan Shari’ar Musulinci a Najeriya tun farowarta a shekarar 1999. Na samu maganganun shi suna cin karo da juna. A farkon al'amari, Atiku ya goyi bayan Shari