Banza7

Banza7 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Banza7, News & Media Website, No67 Raba Close Kaduna, Kaduna.

13/02/2022

Gidauniyar taimakon Aa’ummam Dahiru Barau Mangal Foundation ta dauki nauyin gudanar da yiwa al’umma tiyata kyauta a Katsina. Gidauniyar jin kai ta Dahiru Mangal Foundation ta dauki nauyin bada magani da aikin tiyata ga marasa lafiya sama da 700 dake fama da lalurori a Katsina Jaridar Rana24 ta s...

Masu Kasuwancin Giya Zuwa Kano Sun Koka Da Shugaban Hukumar KAROTA Dr Baffa Babba 'Dan'agundiDaga Indabawa Aliyu ImamShu...
23/06/2021

Masu Kasuwancin Giya Zuwa Kano Sun Koka Da Shugaban Hukumar KAROTA Dr Baffa Babba 'Dan'agundi

Daga Indabawa Aliyu Imam

Shugaban hukumomin KAROTA/CPC a jihar Kano Dr Baffa Babba 'Danagundi ya zamowa masu safarar giya zuwa jihar Kano tashin hankali duba da muguwar asara da suke tafkawa ta hanyar kame motocinsu da hukumar KAROTA ke yi karkashin Dr Baffa Babba 'Dan'agundi tare da mika su hukumar Hisba.

Masu kasuwancin sun koka da Dr Dan'agundi ne bisa hana su bacci da ido biyu da ya jima ya na yi, suna masu cewa yana janyo musu mummunar asara a kasuwancinsu.

Sun kuma yi korafin cewa hukumar hisba ce ke da alhakin kamun giya a jihar Kano ba hukumar KAROTA ba.

Sai dai Dr Dan'agundi ya jaddada cewa zai kara kaimi wajen dakile kasuwancin giya a jihar Kano k**ar yadda addinin musulunci da dokar jihar Kano s**a tanada, bugu da kari dokar kasa tuni ta bada dama ga kowanne dan kasa wajen dakile abin da ya gani ana yi ba daidai ba, haka addini ma ya yi umarni da hana mummuna.

Tun zuwansa hukumar KAROTA Dr 'Dan'agundi, masu safarar magungunan bogi zuwa Kano da masu siyar da gurbatattun kayan masarufi a jihar Kano s**a shiga halin ni 'yasu bisa hana su rawar gaban hantsi da Dr Baffa Babba ya ke yi, kokari da jajircewarsa ce ta sa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi a matsayin shugaban hukumar CPC, hukumar kula da hakkin siye da siyarwa ta jihar Kano.

Labari mai dadinji Da dumi-duminshi:An Kubutar Da 'Daliban Makarantar Jangebe Dake Jihar Zamfara.Gwamnatin jihar Zamfara...
02/03/2021

Labari mai dadinji Da dumi-duminshi:

An Kubutar Da 'Daliban Makarantar Jangebe Dake Jihar Zamfara.

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kubutar da Daliban Makarabatar Sakandiran Jangebe da Mahara s**a kwashe a daren juma'ar da ta gabata Ɗaliban su 279.

Gwamnan jihar Bello Muhammad Matawallalle ya tabbatar da hakan.

07/02/2021

Wani dalibin da ya kammala karatun aikin injiniya daga kwalejin fasaha ta Ramat da ke Maiduguri, mai suna Engr. Abubakar

RA'AYIN MUTANEN KATSINA AKAN SANATAN KATSINA TA AREWA.      Wannan shine Sanatan Katsina ta Arewa Sen. Ahmed Babba Kaita...
17/01/2021

RA'AYIN MUTANEN KATSINA AKAN SANATAN KATSINA TA AREWA.

Wannan shine Sanatan Katsina ta Arewa Sen. Ahmed Babba Kaita

Wane irin fata kuke mashi bayan kammala Wa'adin shi na wannan Zangon?

30/12/2020
22/12/2020

Wasu takardun shaida a Kotu sun nuna yanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shigo da Dala Miliyan 30, kwatankwacin Naira Biliyan 13.5 a shekarar 2019 dan ya kasa shugaban kasa, Mu…

YANZU-YANZU: 'Yan ta'adda sunyi awon gaba da yara a kalla guda 'Dari a  garin Mahuta karamar hukumar 'Dandume jihar Kats...
19/12/2020

YANZU-YANZU:
'Yan ta'adda sunyi awon gaba da yara a kalla guda 'Dari a garin Mahuta karamar hukumar 'Dandume jihar Katsina

Yaran sunje wani K'auye ne dake kusa da mahuta domin yin mauludi, a hanyar dawowar su s**a had'u da b'arayin, s**ai awon gaba da su😥.

Allah ya bayyana su.

DA ICCE MAIKAMA AKE KOTA👉  Abubakar Usman Yantumaki shine mafita ga jagorantar matasan jihar Katsina domin kaimu tudun m...
06/10/2020

DA ICCE MAIKAMA AKE KOTA👉

Abubakar Usman Yantumaki shine mafita ga jagorantar matasan jihar Katsina domin kaimu tudun muntsira.

•Hankali ds, Aiki dashi.
•Ilmin Addani Dana Zamani.
•Sanin Girman Nagaba dashi.
•Rokon Amana Aikin Shine.
•Ba Ci Ceto Da Sunan Kungiya.
•Nemawa Matasa Hakin su.

Domin haka matasan jahar katsina Abubakar Usman Yantumaki naku 'Danku, kaninku, yayanku maineman cigabanku dakuma jajircewa akan al, ,amuranku yafito takara na
shugabantar majalisar matasan jahar katsina (NYCN) .

Allah yataimaki Comrd. Abubakar Usman Yantumaki.

SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. Comr Abubakar Usman Yantumaki matashi ne da yayi Fice wajen kawo cigaba a tsakanin Al'u...
20/09/2020

SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI.

Comr Abubakar Usman Yantumaki matashi ne da yayi Fice wajen kawo cigaba a tsakanin Al'ummar da yake cikin ta.
Wannan yasa muke kara kira ga matasan jihar Katsina dasu Marawa Comr Yantumaki Baya domin samun wakilci nagari.

KwamishinaGwamnatin Jihar Katsina ta gina sabbin rukunin ajujuwa 1,026 a makarantun firamaren ta karkashin Kwalejin Ilim...
18/09/2020

Kwamishina

Gwamnatin Jihar Katsina ta gina sabbin rukunin ajujuwa 1,026 a makarantun firamaren ta karkashin Kwalejin Ilimin Bai-Daya (UBE) / Kudin shiga Na Musamman na Jiha daga 2015 zuwa 2018.

Kwamishinan Ilimi, Farfesa Badamasi Lawal, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da ma'aikatar ta samu a lokacin da ake dubawa.

Ya ce an gyara karin ajujuwa 1,268 a duk fadin jihar a tsawon lokacin.

Kwamishinan ya kara da cewa an gina sabbin ofisoshi 135 yayin da aka gyara wasu 532.

Kwamishinan ya ce an gina ban-daki 930 a duk fadin makarantun firamare a jihar.

A cewarsa, an rufe makarantun firamare 15, yayin da aka haka rijiyoyin burtsatse 70 a makarantun firamare daban-daban a jihar.

Ya ce an gyara makarantun firamare tara tare da daukaka su zuwa gine-ginen bene.

Lawal ya bayyana cewa an yi amfani da Naira biliyan 5 don gyara da inganta makarantun.

A kan makarantun sakandare, ya ce gwamnati ta gyara makarantu 25 a cikin wannan lokacin har zuwa biliyan N3.1.

Ya kara da cewa an gyara makarantun sakandare na Kimiyya da Fasaha da Kere-kere guda 13 tare da inganta su kan naira biliyan 1.9.

Kwamishinan ya ce gwamnati za ta ci gaba da bai wa bangaren ilimi fifiko saboda mahimmancinsa ga ci gaban tattalin arziki da gina kasa.

Gwamnatin Nijeriya ta umurci da a bude makarantu Kwamitin yaki da cutar corona na Nijeriya yace gwamnatin tarayya ta umu...
29/06/2020

Gwamnatin Nijeriya ta umurci da a bude makarantu


Kwamitin yaki da cutar corona na Nijeriya yace gwamnatin tarayya ta umurci da a bude makarantun bokon kasar.

To sai dai, umurnin ya tsaya ne kan daliban karshe da za su zauna jarabawa na aji 6 firamare, da na aji ukun karamar sakandare da na aji ukun babbar sakandare.

Share this:

NAHIYAR YAMMACIN AFIRKA Da niyya tarayyar turai s**a reni 'yan tawayen Libya, s**a kawo musu agajin dakarun tsaron hadin...
08/06/2020

NAHIYAR YAMMACIN AFIRKA

Da niyya tarayyar turai s**a reni 'yan tawayen Libya, s**a kawo musu agajin dakarun tsaron hadin gwiwarsu na NATO wajen taimakawa 'yan tawayen Libya aka kashe tsohon shugaban Kasar Libya Muhammad Ghaddafi domin a bude kofar wanzuwar ayyukan ta'addanci da tsageranci a nahiyar Afirka

Mak**an da 'yan ta'adda da barayin shanu da masu garkuwa da mutane suke amfani dashi a yanzu a yammacin Afirka kusan kashi 90 cikin 100 na mak**an da s**a fito ne daga Kasar Libya ne

Lokacin da dakarun NATO s**a tabbatar da kashe Gaddafi, da s**a tashi komawa turai sai s**a bar muggan mak**an a hannun 'yan tawaye, su kuma 'yan tawayen Libya sai s**a koma cinikin mak**an tsakaninsu da 'yan ta'adda da barayi

Wannan shine siyasar turai a bisa doron manufarsu na sake sabunta sabon tsarin mulkin mallaka a karo na biyu akan nahiyar Afirka, wallahi ba zasu taba barinmu mu zauna lafiya ba, tashin hankalinmu shine ribarsu

Yaa Allah Ka karemu, Ka 'yanto mana nahiyarmu daga sharrin turawa

16/05/2020
An K**a Kayan Agaji Kunshe da Mak**ai da Alburusai.Ana zargin Kasar Faransa da Hannu akan wasu kayan Agaji da aka Turo z...
04/01/2020

An K**a Kayan Agaji Kunshe da Mak**ai da Alburusai.

Ana zargin Kasar Faransa da Hannu akan wasu kayan Agaji da aka Turo zuwa Jahar Borno domin Yan Gudun Hijira Dauke da Mak**ai da Alburusai.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da wannan kamun Kayan.

Allah yachigaba da tsare mu sharrin wadannan miyagun Amin

Me Ya Sa Malamai S**a Yi Shiru A Yanzu Da Ake Tsadar Rayuwa A Nijeriya?Daga Sheik Nuru KhalidA halin da ake ciki na kunc...
11/11/2019

Me Ya Sa Malamai S**a Yi Shiru A Yanzu Da Ake Tsadar Rayuwa A Nijeriya?

Daga Sheik Nuru Khalid

A halin da ake ciki na kunci da tsadar rayuwa, da dama daga cikin Malamai sun zabi su yi gum da bakunan su.

Amma in lokacin za be ya zo su ne a gaba gaba wajen magana.

Domin sauke nauyin da ke kaina duk da cewa Ina da rauni, Ina so in Yi amfani da wannan kafa don ba da shawara.

Wajibi ne Malamai su wa talaka adalci wajen Kira ga shuwagabanni, a lokacin da aka Sami tsadar rayiwa, don shuwagabanni su tuna hakkin da ke kansu.

Rashin yin haka ya saba wa manhajin magabata na kwarai.

Domin kada wanda bai sani ba ya tsanmaci cewa ra'ayi na ne wannan, ga hoton daya daga cikin dunbin wasiku da manyan magabata ke rubutawa a kan haka.

Al Imam Nawawi ne ya rubuta wa Sarki Alzahir yana tunatar da shi hakkin da ke kan shi na ba talaka kulawa.

Allah Ya sa mun dace.

Hasbunallahu Waniimal Wakil....Wasu gungun Yan Fashi da Makami sun Duro Garin Tsanni a cikin Daren nan, Alhamdulillah an...
06/11/2019

Hasbunallahu Waniimal Wakil....

Wasu gungun Yan Fashi da Makami sun Duro Garin Tsanni a cikin Daren nan, Alhamdulillah anyi Nasarar Fatattakarsu tareda K**a.Daya Daga cikin su.

Zaa samu cikakken Bayani nan gaba kadan.

Allah ya tsare dukkan Musulmi Amin

Gwamnatin Jihar Katsina Tayi Magana Gameda Biyan Kudin Tallafi Ga Daliban Manyan Makarantu Na Shekarar 2018/2019Daga: Ra...
04/11/2019

Gwamnatin Jihar Katsina Tayi Magana Gameda Biyan Kudin Tallafi Ga Daliban Manyan Makarantu Na Shekarar 2018/2019

Daga: Rana24

Darakta-Janar na hukumar bayar da tallafin karatun na jihar Katsina, Alhaji Isa Ahmed ya ce shirye-shiryen biyan kudin tallafin karatu ga daliban jihar Katsina na shekara ta 2018/2019 sababbin daliban jihar Katsina a duk manyan makarantu suna kan mataki na karshe.

Alhaji Isa ya sanar da hakan ne ga wakilin Jaridar Rana24 a wata tattaunawa da yayi ayau ranar Litinin, 4 ga Nuwamba, 2019.

A cewarsa, hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryenta na cikin gida wadanda s**a hada da tattarawa da kuma lissafa muhimman takardu don biyan kudin kuma suna nan suna jiran mataki na karshe na Ma’aikatar kudi kafin fara biyan.

"Mun gama komai daga karshenmu kuma yanzu muna jiran amincewar gwamna da kuma sake sakin kudin daga ma'aikatar kudi.

Ya kara da cewa "A cikin wani lokaci mai nisa, duk sashin karatun jami'a na jihar Katsina na shekarar 2018/20 a duk manyan makarantu zasu fara karbar kudin su", in ji shi.

Allah ya tabbatar da hakan.

10 to tell others
19/10/2019

10 to tell others

Tirkashi: An Samu Naira Miliyan 324 A Asusun Bankin Wata MabaraciyaMasu Karatu Me Zakuce?
19/10/2019

Tirkashi: An Samu Naira Miliyan 324 A Asusun Bankin Wata Mabaraciya

Masu Karatu Me Zakuce?

KIRA ZUWA GA LAUYOYI MASU YI DAN ALLAH AKAN INUSA YELLOW Na ga kiraye-kiraye da dama ta wannan kafa cewa a yanzu haka In...
19/10/2019

KIRA ZUWA GA LAUYOYI MASU YI DAN ALLAH AKAN INUSA YELLOW

Na ga kiraye-kiraye da dama ta wannan kafa cewa a yanzu haka Inusa Yellow yana tsare a gidan kurkukun Bayalsa kuma saura kiris a yanke masa hukunci.

A hakikanin gaskiya ban san an k**a shi ba. Ganin da na yi masa na karshe shine wata rana da ya je ofishin mu a Kano, lokacin ina can, mu ka gaisa. Amma da alama gaskiya ne an sake k**a shi.

Toh, k**ar yadda da yawa daga cikin ku s**a sani a yanzu bana Najeriya. Saboda haka ba zan iya zuwa in tsaya wa Inusa ba. Don haka, ina kira ga lauyoyin da mu ka yi wancan aiki da su, da kungiyar lauyoyi Musulmai da ma duk lauyan da zai iya cewa su shiga wannan lamari.

Hakika, ana kokarin zaluntar Inusa ne kawai domin addininsa da bangarensa sun banbanta wadanda su ke zargin shi. Kuma matuqa lauyoyi ba su tashi sun taimaka masa ba, toh, lalle za a zalunce shi. Inusa bai aika laifukan da ake zargin da su wannan Kotu ba kuma yana hujjojin da suke nuna hakan sai idan ba lauya, yana matuqar wuya ya iya gamsar da Kotu. Idan ma da wani mai laifi, toh, wannan yarinya ce. Amma gashi yanzu ita tana makaranta yanzu, shi kuma yana fursina.

Ina kuma kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa lauyoyin da za su tsaya masa da ‘yan kudaden da za su yi aikin musamman ma kudin jirgi da na otel. A wancan lokaci ni na dau nauyin kai na, amma ba kowa ba ne zai iya ba da lokacinsa da kuma dukiyarsa. Wani kuma ba shi da ma karfin yin haka. Ga kuma halin kasa ta samu kan ta a ciki yanzu. A takaice dai, ina kira da duk wanda zai iya cewa ya taimaka.

Daga Masu Shinkafa An Tsallaka zuwa ga Masu Motoci.Hukumar Hana Fasa kwabri ta Kwastam tayi dirar Mikiya wajen Masu Said...
01/10/2019

Daga Masu Shinkafa An Tsallaka zuwa ga Masu Motoci.

Hukumar Hana Fasa kwabri ta Kwastam tayi dirar Mikiya wajen Masu Saida Motochi a Jahar katsina.

A cikin daren Jiya ne akaga jamian Hukumar suna ta sintiri tareda Garkame duk wani wurin saida Motochi dake Jahar ta Katsina, tareda Lissafa yawan Motochin dake wuraren.

A bayanin wani da baya son a ambachi sunan sa yace Hukumar tana neman Motochin da basu da Takardun izini wato Kwastam Duty ne shiyasa ake wannan Aikin, koda kau wajenka a rufe yake sai sun haura sun rabbatar da yawan Motochin sannan su rubuta takarda su bari su garkame wurin.

Yanzu haka dai anyi charko charko an rasa ta cewa.

A wani rahoto da ya fita a jiya shi wannan aikin an farashine daga Jahar lagos, inda hukumar ta bayyana aniyarta ta kwato Harajin duk wata Mota da aka shigo da ita ba bisa Qa'ida ba.

A jahar ta lagos lamarin ya shafi manyan kampanoni masu saida motochin irinsu Coscharis, Globe Motors, Skymit, Inehmic Affordable, Carlink

A cikin bayanan mai magana da yawun rundunar Hukumar Joseph Attah, ga manema labarai yabayyana cewa Hukumar ta samu bayanan cewa akwai Motochin da ake shigowa dasu ba bisa Qa'ida ba baa biya masu haraji ba, dan haka bawai sun kulle wuraren bane har abada zasu binchika idan babu irin wadannan motochin zasu bada damar a bude wuraren.

Attah ya tabbatar da cewa yazuwa yanzu babu wanda Hukumar ta k**a, kuma hukumar batada niyyar kuntatama kowa abunda kawai sukeyi shine neman kudaden shiga ga gwamnati.

Wani aki kenan akaramar hukumar Kankara da kanyomar ke gudanarwa.Ya za akira wannan aikine ko aika aka?
30/09/2019

Wani aki kenan akaramar hukumar Kankara da kanyomar ke gudanarwa.

Ya za akira wannan aikine ko aika aka?

30/09/2019

Saurari Hirar Matashin Dan Siyasa Hon. Saifillahi Mato Yayi Abisa Yanda Ake Wulagigi Da Kudin Yan Gidun Hirar Yankinsu.(KANKARA)

ALMAJIRIN SHEIKH IBRAHIM INYASS RtaZAI GINA CIBIYAR ADDININ MUSULUNCI MAFI GIRMA A AFRICA.Shahararren mashahurin shehin ...
30/09/2019

ALMAJIRIN SHEIKH IBRAHIM INYASS Rta
ZAI GINA CIBIYAR ADDININ MUSULUNCI MAFI GIRMA A AFRICA.

Shahararren mashahurin shehin Malamin hadisi na Duniya, kuma daya daga cikin jiga-jigan jagororin Darikar Tijjaniyya a kasashen K**aroun, Chad, Egypt, Nijar, Marocco Da Kuma Nigeria, wato Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Ya assasa gidauniyar gina katafariyar cibiyar Addinin musulunci mafi girma a Africa,

A taron kwanaki biyu da aka shirya, domin assasa gidauniyar bude asusun aikin gina wannan cibiya, ansamu halartar manyan baki k**ar haka

* Shugaban kasar Nigeria.
* Sarkin Musulmin Nigeria.
* Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Rta).
* Cheif Imam Na India
* Sheikhul Islam Of K**aru
* Mufty Na Kasar Ghana.
* Cheif Judge Of Libiya.
* Amirul Muminina Of Morocco.
* Sheikh Abdulsamad S. Ishaq Rabi'u.
* Sarkin Katsinan Gusau.
* Deputy Gov. Of Bauchi.
* Gov. Of Sokoto.
* Professor Sidi Muhammad Daga Morocco.
* Da dimbin Mahalarta taro daga ciki da wajen wannan kasa da baza su lissafu ba.

Wadanda s**a sanya hannun jarin su cikin wannan gidauniya da aka assasa,

∆ Sheikh Dahiru U. Bauchi Yabada N. Milliyan 25

∆ Prof. Maqary, Da Abokan Sa Sun Bada N. Milliyan 3

∆ Gobnan Yobe Ya Bada Miliyan 20

∆ Gobnan Sokoto Ya Bada Miliyan 40

∆ Musal Kazeem Bin Sheikh Sharif Saleh Ya Bada Miliyan 5
∆ H. Maryam Sani Abacha, N. Miliyan 5.
∆ Gobnan Borbo Miliyan 10

∆ Shehun Borno Miliyan 1
∆ Alh Dahiru Mangal Miliyan 25.

∆ Dangote Foundation Miliyan Miliyan 100.

∆ Kasar Chadi Miliyan Dala Dubu 300 da sefa Dubu 200

∆ Saudiya Dollar Miliyan 15

∆ Kasar Oman Dala Dubu 2

∆ Kasar K**aru Miliyan 300
∆ Saudiya Ta Sake Bada Riyal Dubu 15
∆ Bola Tinubu Miliyan 25

∆ Olawiyyo Miliyan 5

∆ Abdul-samad Ishaq Rabi'u Milin 500
Sannan Ya bada Miliyan 50 hadiya ga ruhin mahaifin sa da ciminti na naira Miliyan 500

∆ Da Sauran wadanda sunayen su bai shigo hannun mu ba.
Za'a gina wannan cibiya ne a birnin Abuja.

Muna taya Al'ummar Musulmi Murnar Wannan Nasara Da Al'ummar Musulmin Nigeria S**a Samu.

MUHAMMADU BUHARI MODEL PRIMARY SCHOOL (WACCE AKAFI SANI DA BARNI) WADDA TAKE KUSADA ASIBITIN KWARARRU WATO FMC A CIKIN B...
30/09/2019

MUHAMMADU BUHARI MODEL PRIMARY SCHOOL (WACCE AKAFI SANI DA BARNI) WADDA TAKE KUSADA ASIBITIN KWARARRU WATO FMC A CIKIN BABAN BIRNIN KATSINA GWAMNA YA CIKA ALKAWARI....

A cikin watan Austan Dubu Biyu da Sha Bakwai ne Alummomin wannan yankin s**a Mika kokensu ga Mahukunta cewa suna bukatar Gwamnati ta saka Makarantar cikin wadanda take gyarawa tareda yimasu Kwaskwarima.

Gwamnati ta Karba Kiran Alummar tayi Alkawarin gyarawa tareda zuba masu kujeru, Gwamnatin ta cika Alkawari kuma ta gyara wannan Makaranta itama ta shiga cikin wadanda aka gyra, gwanin ban shaawa, sai dai kujerun basu zoba yazuwa yanzu.

Alummar wannan wuri sunyi matukar Murna da Farin cikin wannan Aikin, sunyima Mai Girma Gwamna Godiya bisa wannan Aiki da akayi masu.

Sannan suna amfani da wannan damar wajen Sanar da Mai Girma Gwamna cewa Anyi Gyaran amma Kujerun Zama basu iso ba, suna tuni da cewa Mai Girma Gwamna ya kara sa baki domin yaransu su samu abun zama.

Allah yasaka da Alkhairi Amin

Address

No67 Raba Close Kaduna
Kaduna

Telephone

+2348023214152

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Banza7 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other News & Media Websites in Kaduna

Show All