19/09/2020
A Cikin Wayannan Magidantan Waye Dolo?
**************************************
👳Wani balarabe ne me mata hudu ya dawo gida sai yaji matansa suna hayaniya suna sa-in-sa tsakanin su
👳Sai yace miye ya kawo haka?!
👳Sai ya nuna daya daga cikin matansa yace: duk kece kanwa uwar gami ke kika haddasa duk wannan hatsaniyar to saboda haka ki tafi kawai na sake ki!
👼Sai wata daga cikin matan tace:Tir haba wannan irin saurin Saki haka! Ranta ya baci!
👳Sai yace: kema jeki na sake ki!
👸Sai daya daga ciki tace: haba megida! Matannan daka saka su biyu suna kyautata ma sannan suna fifita ka akan kowa!
👳Sai yace: kema me gaya min kyawawan halayensu kema na sake ki!
👩Sai ta hudun tace: Ala-wadaran-halinka Kai baka da yanda zaka ladabtar da matanka sai dai Saki!
👳Sai yace: kema na sake ki!
🙆Sai maqobciyarsu taji hayaniya saita shigo gidan tace: a gaskiya a tarihin larabawa ba'a taba samun mutum ya Saki mata hudu ba a Rana daya a lokaci daya ba irin wannan
👳Sai yace :kema kin saku in har mijinki ya yarde min to na sake ki!
👱Mijin maqobciyar yana cikin daki kawai daga ji sai ya daga murya da qarfi yace: "na yarda na yarda na yarda"
A lokaci guda a Rana guda saida ya Saki mata biyar
Ran maza ya baci
Wai da me sakin matansa hudu da Wanda ya yarda aka sakan mai matarsa daya cikin su wa yafi wawanci?