Ahalancy Trust

Ahalancy Trust Muna muku barka da zuwa Ahalancy Trust (ahancytrust.com.ng) . Wannan shafi ne da zai na kawo muku a

18/12/2023

Hausa Amazon KDP From A to Z

15/11/2023
29/07/2023

Yadda Kwanaki Ke Saurin Tafiya Yana Da Ban Tsoro!
Da mun aza kanmu a kan filo, yanzu kana jin an fara kiran sallar asuba, da mun yi sallar azahar da ɗan lokaci kaɗan sai ka ga rana tana batun faɗuwa, abubuwa suna faruwa da sauri, fitintinu suna ta tsoratar da mu, mutane yanzu kamar suna gasar mutuwa ake! Lallai mai hankali shi ne wanda ya yi ƙoƙarin cika littafinsa da kyawawan ayukka kafin mai ziyara na ƙarshe ya zo masa!

السلام عليكم ورحمة الله وبركاتهWannan bidiyo ne na ziyarar da DR. Abdullahi Gadon Kaya ya kai wa masu ɓautar Macizai da ...
10/07/2023

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته
Wannan bidiyo ne na ziyarar da DR. Abdullahi Gadon Kaya ya kai wa masu ɓautar Macizai da Bushiya domin yi masu wa'azi (Part One 1)


👇👇👇👇👇

Wannan bidiyo ne na ziyarar da dr. Abdullahi ya kai wa masu bautar macizai da bushiya domin yi musu wa'azi a Kasar Benin Republic. Assalamu Alaikum Warahamat...

Wa 'azi bá laifi amma sutura ta yi muni. Allah ya bamu ikon gyarawa. 👉
02/07/2023

Wa 'azi bá laifi amma sutura ta yi muni. Allah ya bamu ikon gyarawa. 👉

👉🌹VIDEO DESCRIPTION 🌹Allah ya ba da ikon gyara kusakuranmu. Wannan wani ɓangare ne na shirin Izzar so domin faɗakar da masu shirin da al'ummar musulmi. Da...

30/06/2023

DALILANMU NA BAYYANA SHUBUHOHIN ƳAN FILM!!!
Aslm. Ýan uwa mun lura da cewa wasu na ganin cewa fito da shubuhohin ýan film da mu ke yi laifi ne, kuma wai hassada ce. To ku Saurara ku ji DALILANMU na bayyana shubuhohinsu. Dalilan su ne :-
1. Da yawa daga cikin lalacewar da al'umma ta ke yi musamman mata ya samo asali ne daga ýan film. Misali sanya sì tura marasa kyau da yin maganganun banza da sauran su.
2. Abu na biyu Idan aka yi kokarin yi wa masu shirya films na Hausa magana sai ka ga sun ƙi kula mutane.
3. Dalili na uku shi ne kusakuren da suke aiwatarwa da sunan suna koyar da addini da kuma al'ada ne. Wato malamai duk shirme su ke yi ke nan. Suna saɓo amma wai koyar da al'umma addini su ke yi.
4. Abu na gaba shi ne suna kusakure wurin bayyana fassarori na wasu ayoyin Alkur'ani da hadisan Annabi Muhammad S A W. Kun ga ya zama dole mu fito mu bayyana wa kowa da kowa ya san cewa kuskure ne waɗansu abubuwan da su ke aikatawa.
5. Abu na gaba Manzon Allah S A W yana cewa :من رأى منكم منكرا فليغيره بيده فإن لم يستطيع فبلسانه فإن لم يستطيع فبقلبه وذالك أضعف الإيمان. Ma'ana duk wanda ya ga ana abun ƙi (wato saɓon Allah) to ya kawar da hannunsa idan ba zai iya ba to ya kawar da harshensa idan ba zai iya ba to ya ki abun da ake aikatawa da zuciyarsa hakan shi ne mafi raunin imani. To tunda ba za mu iya Hanasu ba, kuma ba za su amsa ba idan aka nemi a yi magana da su ba sa ba da haɗinkai, ai kunga sai mu yi wa'azi da nasiha domin su kiyaye faɗawa a cikin laifi.
6. Dalili na gaba shi ne ba ma son Allah da dukkan halittu su tsine mana kamar yadda Allah ya bayyana mana a cikin suratul Bakara da take nuna an tsine wa mai ɓoye Ilimin da Allah ya ba shi musamman idan ana ta aikata saɓon Allah.
Daga karshe ba dan hujjojinmu sun kare ba ne, a a sai domin ba lokaci. Amma duk wanda ya ke da ja ko sharhi ko ƙarin bayani sai ya mana magana ta comment da dm. Bissalam mun gode

Aslm.WALWALE SHUBUHAR SHIRIN IZZAR SO 2Mun fito da abubuwa ne guda 3Ku kalla lafiya👇👇👇
30/06/2023

Aslm.
WALWALE SHUBUHAR SHIRIN IZZAR SO 2
Mun fito da abubuwa ne guda 3
Ku kalla lafiya
👇👇👇

29/06/2023

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته
TONA ASIRIN IZZAR SO!!!
Kamar yadda mu ka faɗi za mu soma wá ýan Izzar so tonon silili domin a fito da shubuhar da ya ke ciki, domin abun nasu ya fara wuce ƙa'ida.
A yau in sha Allah za mu yi bayani ne akan abubuwa kamar haka:-
1. Menene hukuncin a cuci mazan da ýan cikin shirin su ke yi, shin Shima addini ake koyarwa?
2. Menene hukuncin karin gashin da ýan cikin shirin naku su ke yi, shin Shima addini ne?
3. Menene hukuncin maza da mata da su ke zama a kan kujera ɗaya, shin Shima addini ne?
4. Menene hukuncin tallata wa bokaye kayan hajarsu a cikin shirinku. Ko Shima addini ne?
5. Menene hukuncin kiɗar da ku ke sakawa a cikin shirin naku ko hakanma addini ne?
6. Menene hukuncin sanya gyalen tatan kamun da mata ke sanya wa a cikin shirin, kò haka addini ya umarce su suna sanyawa.
Wallahi Tallahi wanga shirme ne tsantsa ku ke koyar da al'ummar musulmai.
Ku latsa kasa ku gani. .......الآن حمي
👇👇👇👇👇👇👇
Mu haɗu a kashi na biyu gobe in sha Allah

✍By Ahlulbayan bayan

28/06/2023

Allah ya kai mu

28/06/2023

Aslm. Kamar yadda na sanar da cewa yau Ranar Salla babba zan soma sharhi a kan shirin /film ɗin Izzar so da ikon Allah. Wannan sharhin zai shafi abubuwa ne kamar haka :
1. Cewa da su ke cewa gaskiya addini ne ya sasu haka shin gaskiya ko zuki ta malle?
2. Kurakurai da su ke tabbkawa a ciki da sunan addini
3. Saɓon Allahn da ake tabbkawa a cikin shirin.
4. Cin mutuncin da su ke yi wa addini da sunan kare Annabi S A W
5. Tambayoyi da mu ke so masu Izzar so su amsa mana.
6. Shin kuɗin da su ke samu daga shirin Halal ne ko haramun ne?
7. Shawarwari ga masu izzar so da masu kallonsu domin nishaɗantarwa ko domin addini
8. Ta yaya ya kamata a ɗaga addini?
9. Hukuncin masu kallon shirin.
10. Da sauran abubuwa masu yawa
In sha Allah duka waɗannan abubuwan za mu tattaunasu da yardar Allah.

Ɗaliban Nijeriya muna tayaku Murna. Sai Baba Tinibu up up....
12/06/2023

Ɗaliban Nijeriya muna tayaku Murna. Sai Baba Tinibu up up....

Tinubu signs the student loan bill, Tinibu, Nigerian students

GANDUJE VS KWANKWA*O AT A*O ROCK. IN ABUJA
11/06/2023

GANDUJE VS KWANKWA*O AT A*O ROCK. IN ABUJA

Ganduje my political boy, can’t look at my face’ – Kwankwaso on slap threatPublished

NASIRU EL RUFAI VS CAN
09/06/2023

NASIRU EL RUFAI VS CAN

Transcript of El Rufai’s controversial statement about Peter Obi, Tinubu, CAN, 2023 elections

05/03/2023

Assalamu alaikum jama'a. اللهم صل وسلم على نبينا محمد. Kamar yadda mu ka alkawaranta muku cewa za mu soma koyar da al'ummar harkan samun abun dogaro da AMAZON KDP da harshen Hausa, kuma a kyauta. To a takaice dai lokaci ya yi. Za mu soma ne a rana kamar haka :
TALATA:- 7/03/2023
Lokaci:- 9:30 na dare zuwa 10:30 na dare. Allah ya bamu ikon shigowa. Amin thumma Amin.
Domin shigowa sai ka mana magana ta whatsapp 09066551810 kò ka latsa nan:👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/FXpdpzY5LrZAPj3TyMjjqy
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Dan Allah a yi wa ýan uwa shearing domin su amfana. Domin ku sani الدال على الخير كفاعله والدال على الشر كفاعله ايضا
SHARE, LIKE AND FOLLOW
🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅
KU SANI IDAN ADADIN YA KAI YADDA MU KE SO ZA MU KULLE KARƁAN ƊALIBAI.
✍Ahalancy Tech
IN SHA ALLAH
IN SHA ALLAH
IN SHA ALLAH

نصيحة للمسلمين النيجيريين !!! 👆👆👆👆👆👆👆👆🖕 السلام عليكم ورحمة الله بالطبع الخيار للأحياء.  نصيحتي أن نعلم نحن المسلمين أن ا...
17/02/2023

نصيحة للمسلمين النيجيريين !!!
👆👆👆👆👆👆👆👆🖕
السلام عليكم ورحمة الله
بالطبع الخيار للأحياء. نصيحتي أن نعلم نحن المسلمين أن الدين الإسلامي لا يسمح لنا بخسارة المزيد. لذلك يجب ألا نفعل ما لا يقبله الإسلام باسم السياسة أو الانتخابات. لأنك ستنتهي في المعاناة بسبب السياسيين غدًا وفي يوم القيامة ستقابل غضب الله. وتشمل هذه العيوب
1. القذف
2. العرق
3. التحيز
4. الكراهية
5. نحن نكره زاتو
6. إهانة المعلمين.
7. الكذب ونحوه
والله من فعل شيئًا من هذه الأمور يعلم أن الله قد غضب عليه.
مناظرة!!!!
1. أطع قادتك ومعلميك سلامك. ولا يوجد فيها شيء بدون دين ، فمن الجهل القول بعدم وجود دين في السياسة. لم يمنع وجود السياسة "الديمقراطية" من وجوده في الدين. الشيء الذي يجب معرفته هو أن الدين هو الذي وضعنا في الفصل الديمقراطي. إذا رفضنا ذلك وعصينا الله ، فقد نتضرر في الطريق. إذا كان هناك دين ، فيجب أن نتصرف تجاه معلمينا.
نظرًا لأننا قلنا أنه لا يمكن القول بأن أيًا منهم هو الأفضل ، يجب أن نهنئ معلمينا ونصلي من أجل اختيار الأفضل لنا. لأن العلماء ينظرون ويدرسون بنور الله تعالى.
والله في كل مرة تقول فيها ان المعلمين غير قادرين والله نحن موجودون في هذا البلد والوطن لما رأنا شيئا.
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم على نبينا محمد امرء مسلم السمع والطاعة فيما أحب و كره (او كما قال صلى الله عليه وسلم) مرحبا يأني إذا أمره قائده أن يفعل ما يحبه أو يكره فليفعل ، ما لم يكن فيه كفر بالله.
2. لنصلي هكذا:
بارك الله فينا الهدى الذي قدمتموه لمعلمينا ، وفقنا الله خير القيادات لنا.
ينور الله معلمينا في اختيار القيادات الصالحة لنا سواء أحببناهم أم لا.
3. دعونا نتجنب القبلية والطائفية والعصبية حتى لو كانت ضدنا ، لأننا في الإسلام يحرمنا الله ، حتى لو فعلوا ، الله يوقفهم.
4. احرص على عدم التفكير في أنه مضر للإنسان المسلم لأن لا أحد يعرف الغيب ، ظنو بالمؤمنين خيرا
5. أعدك بمن يقول الشيخ ساني الحاج يحيى جينج أن ينتخبهم ، سأنتخبهم حتى لو لم يكونوامن نحبهم ، لأنه هو قائدنا وإمامنا في جوس و... ،. ماذا عنك؟
أخيرًا ، أدعو الله أن يختار لنا قادة صالحين. وعسى الله أن ينهي السياسة بالسلام. أعطانا الله أيضًا القدرة على طاعة معلمينا.
👈 من هل البيان جوس

ADVICE TO NIGERIAN MUSLIMS!!! 👆👆👆👆👆👆👆👆🖕 ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH Of course, the choice is for the living.  My adv...
17/02/2023

ADVICE TO NIGERIAN MUSLIMS!!!
👆👆👆👆👆👆👆👆🖕
ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH
Of course, the choice is for the living. My advice is that we Muslims should know that the Islamic religion does not allow us to lose more. Therefore, we should not do anything that is not acceptable to Islam in the name of politics or elections. Because you will end up suffering because of the politicians tomorrow and in the judgment day you will meet the wrath of God. Such disadvantages include
1. Slander
2. Ethnicity
3. Partiality
4. Hatred
5. We hate Zatto
6. Insulting teachers.
7. Lying d. S
By God, whoever does one of these things knows that God is angry with him.
Advices!!!
1. Obey your leaders and your teachers is your peace. And there is nothing without religion in it, it is ignorance to say that there is no religion in politics. The existence of "Democratic" politics did not prevent his presence in religion. The thing to know is that it is the religion that has put us in the Democratic chapter. If we refuse to do it and we disobey God, because we can be harmed in the way. If there is a religion, we must behave towards our teachers.
Since we have said that none of them can be said to be the best, we should congratulate our teachers and pray that they choose the best one for us. Because the scholars are looking and studying with the light of God Almighty.
By God, every time you say that the teachers are not capable, by God, we have been in this country for three years, we have not seen anything yet.
The Messenger of God صلى الله عليه وسلم said on a Muslim man, if his leader orders him, he should do what he likes or dislikes, as long as there is no blasphemy against God in it.
2. Let's pray like this:
May God bless us with the guidance you have given to our teachers. May God choose the best leaders for us.
May God enlighten our teachers in choosing good leaders for us whether we like them or not.
3. Let's avoid tribalism and sectarianism even if it is against us, because we in Islam, God forbids us, even if they do, God makes them stop.
4. Be careful not to think that it is bad for a Muslim person because no one knows the unseen, let alone who will be wronged if he eats it.
5. I promise whoever Sheikh Sani Alhaji Yahaya Jingir says to elect them, I will elect them even if it is not us, because Mallam is our leader in Jos and Ma........., because also I am safe tomorrow, I will hate God. What about you?
Finally, I pray that God will choose good leaders for us. And may God bring peace to the end of politics. God also gave us the ability to obey our teachers.
From 👉Ahlulbayan Jos

NASIHA GA MUSULMAN NIGERIA!!!👆👆👆👆👆👆👆👆🖕ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHBa shakka dai zaɓe ya iso ga mai rai. Nasihata ita ...
17/02/2023

NASIHA GA MUSULMAN NIGERIA!!!
👆👆👆👆👆👆👆👆🖕
ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH
Ba shakka dai zaɓe ya iso ga mai rai. Nasihata ita ce mu musulmai mu sani cewa Addinin Musulunci bai bar mu kara zube ba. Sabila kada mu aikata duk wani abun da musulunci bai yadda da shi ba da sunan siyasa ko kuma zaɓe. Domin za ka gama shan wahala ne a kan ýan siyasa a gobe kuma kiyama ka haɗu da fushin Allah. Irin waɗannan abubuwan da babu kyau sun haɗa da
1. Zage-zage
2. Ƙabilanci
3. Ɓangaranci
4. Kiyayya
5. Munana Zatto
6. Cin mutuncin malamai.
7. Yín karya d. S
Wallahi duk wanda ya aikata ɗayan waɗannan abubuwan ya sani Allah na fushi da shi.
SHAWARWARI!!!!
1. Ku yi wa shugabanninku kuma malamanku biyayya shi ne zaman lafiyarku. Kuma babu abunda babu addini a cikinsa, jahilci ne ka ce babu addini a siyasa. Kasantuwar siyasar" Democratic"bai kore samuwarsa a addini. Abun sani shi ne ai addinin ne ya sanya mana Democratic a babin lalura. Idan aka ki yi kuma mun saɓa wa Allah, domin za a iya cutar da mu ta hanyar. Idan ko akwai addini ya zama tilas mu yi wa malumanmu ɗa'a.
Tunda mun ce dukansu babu wanda za a ce shi yafi to mu taya malumanmu da addu'a su zaɓa mana na kwarai. Domin su malamai suna dubi da nazari ne da hasken Allah maɗaukakin sarki.
Wallahi duk lokacin da mu ka ce malamai basu iya ba wallahi mun shiga uku a Kasar nan, ba mu ga kome ba ma tukunna.
Manzon Allah صلىya ce a kan mutum musulmi idan shugabansa ya umarceshi, shi ne ya ɗa'a cikin abun da ya so ko ya ƙi, matukar babu saɓon Allah na ƙarara a cikinsa.
2. Mu yi addu'a kamar haka :
Allah muna tawassuli da ɗa'ar da mu ka yi wa malumanmu Allah ka zaɓa mana shuwagabanni na alkhairi.
Allah ka haska wa malumanmu wajen zaɓo mana shuwagabanni na alkhairi ko ba ma sonsu.
3. Mu guji Ƙabilanci da Ɓangaranci ko da ana mana, domin mu a Musulunci Allah ya hanamu, ma su yi Allah ya sa su bari. من دعا إلى عصبية فليس منا
4. A kiyaye yín zatto mara kyau ga mutum musulmi domin kuwa babu wanda ya san gaibu b***e mu ce wane idan ya ci zai zaluncemu.
5. Ní dai na yi alkawari duk wanda Sheikh Sani Alhaji Yahaya Jingir ya ce mu zaɓa wallahi su zan zaɓa ko da ba su mun ba, domin Mallam shi ne shugabanmu a Jos da ma........., domin kuma na tsira a gobe ƙiyama a guna Allah. Ku fa?
Daga karshen ina adduar Allah ya zaɓa mana shuwagabanni na gari. Kuma Allah ya sa a kammala siyasar lafiya Lumui lumui. Allah kuma ya bamu ikon biyayya wa malumanmu.
Daga 👉Ahlulbayan Jos

06/02/2023
SAƘON MUSULUNCI GA IYAYE MATAAbun mamaki mutanen zamanin nan sun dawo kwaikwayan Baragadodi da kiran iyayensu da suna "A...
05/02/2023

SAƘON MUSULUNCI GA IYAYE MATA
Abun mamaki mutanen zamanin nan sun dawo kwaikwayan Baragadodi da kiran iyayensu da suna "ANTEEY" amadadin BABA / INNA/MOMY. Wata ƙila SUNA hakan ne domin abubuwa kamar haka :-
1) Domin ɗa'a wa iyayensu waɗanda s**a ce ýaýansu suna kiransu da hakan ( wai su ba sa son girma. d. S).
2) Kò kuma domin koyi da wasu kamar wasu ɓangare daga ýan a wasu kasashe.
3) Ko saboda rashin sanin hukuncin sa.
4) kò Kuma domin koyi da masu film.
HUKUNCIN MUSULUNCI AKAI
1. Bai halasta ba, saboda babu wani Annabin Allah عليهم السلام da su ke kiran mahaifansu da suna ANTEEY ko UNCLE. Hasili ma sai dai ka ji suna cewa :وبرم لوالدتي............ Kamar yadda Annabi Isa ya faɗi. Hakannan Annabi Ibrahim ya ce:ياأبتي لا تعبد الشيطان.................. Hakannan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ýa CE a wani hadisi إن أبي وأمي..............
A takaice dai idan dai za mu yi koyi ne da ANNABI To lallai mu gyara wannan mummunar ɗabi'a.
2. Bai halasta ba, domin ko al'adarmu ta Afirka ko Nijeriya ba ta yarda da haka ba. Kuma ƙa'idar malamai shi ne idan abu جائز ne a addini, idan ya zamanto a al'ada ba a yarda da hakan ba to barinshi shi ya fi. Ballantana ma ba جائزba ne a addini.
3. Malam tarbiya sun ce daga cikin tarbiya shi ne kada mutum ya kira iyayensa da sunansu sai da Bábá ko Bàbà/màmá. To ke nan mai kiransu da suna ANTEEY ba su da tarbiya.
4. Haramun ne koyi da masu film idan s**a aikata kuskure.
SHAWARWARI!!!
1. KO DA MAHAIFANKU SUN CE KUNA KIRANSU DA WANGA SUNA, KU MUSU NASIHA DA HAKAN BA KYAU, IDAN KO S**A KÍ BÍ KADA KU KUMA KIRASU DA SUNA ANTY. DOMIN KUWA :لا طاعة لمخلوق في معصية الخالقDOKAR ALLAH TA FI KARFI A KAN NA IYAYE
2. IYAYE KU SANI ƊAURA ƳAƳANKU AKAN HAKAN ZAI LALATAR DA ƳAƳANKU. IN KUNNE YA JI JIKI YA TSIRA.
3. WAJIBI NE MAZA KU HANA MATANKU WANNAN MUMMUNAR ƊABI'A MARA Kyau.
4. IYAYE KU DAINA GUDUN GIRMAN DA ALLAH YA BAKU, IDAN AN GIRMA A SAN ANGIRMA. HAKAN BA ZAI RAGE MUKU SHEKARU BA.
To a nan zan ɗan tsaya mai ƙarin bayani sai ya mana a COMMENT. BISSALAM
✍AHLULBAYAN أهل البيان

03/02/2023

Juma'atul Mubarakah Allah sadamu da alkhairin cikinta. Ina da tsarabar juma'a ga masu iyali kawai idan ana so mu haɗe a comment

13/11/2022

Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu SANARWA!!! SANARWA!! SANARWA!!!
KU YI KOKARI KU KARANTA

Wallahi wannan kam ba addini ba ne👉
11/10/2022

Wallahi wannan kam ba addini ba ne
👉

Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu You are welcome to One Islam Tv. If you are a Muslim this Channel is belong to you, don't go without hitting the...

Listen to beautiful Qur'an Recitation from these beautiful kids. Say MASHA ALLAH👉❤️https://youtu.be/54mB-pG_pOQ
11/10/2022

Listen to beautiful Qur'an Recitation from these beautiful kids. Say MASHA ALLAH
👉❤️https://youtu.be/54mB-pG_pOQ

Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu You are welcome to One Islam Tv. If you are a Muslim this Channel is belong to you, don't go without hitting the...

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH WABARAKATUHU.🌹MAULUDIN ANNABI SAW 🌹👉Ma'anarsa👉Hukuncinsa👉Sauran Bayanai A kansa✍️MA'ANAR...
09/10/2022

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH WABARAKATUHU.
🌹MAULUDIN ANNABI SAW 🌹
👉Ma'anarsa
👉Hukuncinsa
👉Sauran Bayanai A kansa
✍️MA'ANAR MAULUDI A GUN MASU YI:- Idan aka ce mauludi shi ne Birthday da Ingilishi. Saboda haka murna ake yi domin nuna farin ciki akan haihuwar Annabi SAW.
Kusan kowa ya yarda da wannan ma'anar ta Mauludin.
✍️HUKUNCINSA A MUSULUNCI
Kusan kowa ya yarda akan cewa bidi'a ce sai dai masu yi suna ganin cewa Bidi'a ce mai kyau da za a iya samun lada. Sauran masu hanawa kuma sun ɗaukeshi ne a matsayin bidi'a ce ta haramun. Domin Annabi SAW ya ce و كل بدعة ضلالة وكل ضلالة في النار. Shi kuma bidi'a ita ce aikata wani abu da babu shi a cikin addini kuma Annabi ko Sahabbai ko tàbí ai bá su aikata ba kuma da niyar ibada ko ba shi wani matsayi a cikin addini . Idan kana wani abu amma ba ka ba shi matsayi ba a cikin addini ba kuma ba ka ce yinsa addini ba ne. To wannan babu laifi, sai dai kawai mu ce a kiyaye Dokokin Allah a cikin abun. Kuma ku sani kana iya samun lada da abun da ka kirkiro amma ba ka ce addini ba ne. Abun nufi idan abun zai taimaka wa wani abu na addininka. Misali yin Musabaka ana iya samun lada ta hanyarsa, amma fa ba addini ba ne na kai tsaye, amma yana taimaka wa addini. Ku kuma MAULUDINku rusa addini ya ke yi a gaskiya. Domin kuwa da yawa suna munanan shiga da cewa farin ciki ne, wasu zinace zinacensu su ke yi da cewa Mauludi.
✍️ A gaskiya mauludi musamman irin na wannan zamani wallahi Haramun ne. Dalili kuwa ɓarnar da ake yi ya fi Alkhairinsa yawa, kuma ina fatan ba ku manta da ƙa'idar malaman Usuul ba da s**a ce duk abun da ya ke Mustahabbi ne amma kuma zai sabbaba haramun to ya zamanto haramun ne aikata shi, tunda zai janyo haramun ne to a bari mana.
✍️Da ya ke ba addini ba ne MAULUDI shi ya sa kullum ake daɗa masa kwaskwarima. Salla ana mata kwaskwarima ne? A a domin menene? Domin ita addini ne.
✍️Nana Aisha ta ruwaito hadisi cewa Annabi S A W ya ce duk wanda ya kirkiro wani abu da ba bu umarninmu a cikinsa to amma mayar masa. Ka ga kenan ya san za a sami ýan bidi'a da za su shigo da wasu abubuwa, shi ya sa ya yi wannan hadisin. Hadisin nan da ku ya ke yi ýan bidi'a. A wani hadisin Annabi S A W ya bayyana mana cewa a ranar kiyama akwai waɗanda za a hanasu zuwa wurin Annabi S A W duk da suna kiran kansu musulmai ne, su ne ƴan bidi'a. BIDI'A DAMUWA CE KU TUBA KU DAINA DAN ALLAH.
✍️Ya za kuna murnar abun da ba a yi matsaya akai ba. Tunda wasu na ganin cewa ma ba a 12 ga watan 3 ba ne aka haifi Annabi S A W. Kuma ba bu wanda ya isa ya ce wannan ne daidai. Kuma a watan ne ya koma ga Allah maɗaukaki. To mu nuna bakin ciki mana kawai ta hanyar yin sadakoki. Kamar yadda ƴan Shi'a ku ka ce idan bakin ciki da farin ciki su ka haɗu to barin farin cikin ake yi sai a nuna baƙin ciki, to ya kuma ba mu ga kuna haka ba.
✍️Daga
09066551810 (WhatsApp).✋
👉 Akwai saura wannan soman taɓi ne.

08/10/2022

Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu. Barka da zuwa wannan Tashan mai Albarka. Wannan bidiyo ne da zai mana bayani akan Kuɗin da ake samu ta YouTube ...

FILIN FATAWOWIAssalamu alaikum warahamatullah Wabarakatuhu. Da fatan kowa ƙalau ya ke. Yau za mu yi tsokaci ne akan wani...
06/10/2022

FILIN FATAWOWI
Assalamu alaikum warahamatullah Wabarakatuhu. Da fatan kowa ƙalau ya ke. Yau za mu yi tsokaci ne akan wani abu da ya ke faruwa a tsakankanin Matasa kuma gauraye musamman masu zuwa wurin masu shayi. Abun kuwa shi ne idan matashi ya je wurin mai shayi domin siyan shayi da buredi, sai ka ga mutum ya shanye shayin sai ya bar sauran buredin akan teburin mai shayi wai hakanma gaye ne. Wani lokacinma za ka ga har da ruwan shayinma suna barinsa a wurin mai shayi wai duk a cikin gaye ne kuma wai wayewa ce.
Ɗan uwa ko ýan uwa mu sani cewa komai fa Allah ya faɗi mana yadda za a aikata a cikin addinin musulunci. Kuma mu sani cewa babu wani wayewa da ya wuce wayewar da ke cikin addininka na musulunci. Kuma babu wani gaye idan ya saɓawa addini na musulunci. Hukuncin wannan aiki a addini na musulunci shi ne :
👉 Hakan aikata almubazzaranci ne. Kuma Allah maɗaukaki ya bayyana mana cewa lallai masu almubazzaranci ýan uwan sheɗanu ne. إن المزربن كانوا إخوان الشياطين......... إلخ
👉 Lallai sauran guntun buredin da ka bari da shayin da ka bari su ne albarkan cikin abuncinka kuma su ne su ka fi aiki wa jiki. Saboda Manzon Allah SAW ya bayyana mana a cikin hadisinsa cewa أخر الطعام أكثره بركات...... الخ
👉 Ai hakan rashin wayo ne, ya abun da ka siya za kana wulakantashi?
👉 Ka sani cewa Abun da ka bari a wajen idan aka zubar da shi zai na tsinemaka albarka kamar yadda hadisi ya bayyana mana cewa Abuncin da aka zubar yana la'antar wanda ya zubar da shi.
Idan kunne ya ji jiki ya tsira. والله تعالى أعلم
✍️بقلم اهل البيان

Address

Jos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahalancy Trust posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ahalancy Trust:

Videos

Share

Category