Sheikh Ja'afar Mahmood Adam

Sheikh Ja'afar Mahmood Adam Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Ja'afar Mahmood Adam, Media/News Company, Sambolei road emir Drive kofar yamma jama'are, Jama'are.

MAZAN GIDANMU1. Abu Sheikh Salim Ja'afar Mahmoud 2. Muhammad Ja'afar Mahmud3. Ahmad Ja'afar Mahmud Waɗannan su ne ƙannen...
12/04/2024

MAZAN GIDANMU

1. Abu Sheikh Salim Ja'afar Mahmoud
2. Muhammad Ja'afar Mahmud
3. Ahmad Ja'afar Mahmud

Waɗannan su ne ƙannena maza halak-malak, ku taya ni addu'ar Allah Ya albarkaci rayuwarsu Ya shiga lamuransu, Ya ji ƙan magabatanmu amin.

Barka da sallah

22/10/2023

*_ZIKIRORI (AZKAR) GUDA GOMA DA YAKAMATA MUSULMI YAYI SU BAYAN SALLAR FARILLAH_*

Darasi na farko-(1)

Akwai wasu abubuwa guda goma da ake so kowane musulmi yayi su lokacin da yai sallama daga sallah. Duk wanda yai waɗannan azkar ɗin shine yayi koyi da sunnar Manzon Allah ﷺ. Waɗannan abubuwa gasu kamar haka:

1. Faɗar *Astagfirullah* sau uku

2. Faɗar *Allahumma antas salamu wa minkas Salam, tabarak'ta ya jal jalali wal ikram.* Sau ɗaya

*Daga Sauban Allah ya yarda dashi yace "Manzon Allah ﷺ yakasance idan ya juyo daga sallah (idan ya gama sallah) sai ya nemi gafarar Allah sau uku. sannan sai yace Allahumma antas salamu wa minkas Salam, tabarak'ta ya jal jalali wal ikram"*
@أََخْرَجَهُ مُسْلِمْ

أََلإِمَامُ النَّوَوِی رَحِمَهُ اللَّهُ
Yace
*"An tambayi أَلْإِمَامُ اللأَوْزاعِي yaya Manzon Allah ﷺ yake neman gafarar"? Sai yace yana cewa "Astagfirullah Astagfirullah Astagfirullah"*

A wata ruyawar
*Daga A'isha Allah ya yarda da ita tace "Manzon Allah ﷺ yakasance idan yayi sallama daga sallah, baya zama gurin da yai sallar, face gwargwadon yadda zai ce "Allahumma antas salamu wa minkas Salam, tabarak'ta jal jalali wal ikram"*
@أَخْرَجَهُ مُسْلِمْ

Malamai suna cewa "Bai kamata ga liman ya juyo fuskarsa ba, lokacin da yai ma mutane limanci har sai ya faɗi waɗannan zikirorin guda biyu" *(Astagfirullah Astagfirullah Astagfirullah. Allahumma antas salamu wa minkas Salam, tabarak'ta ya jal jalali wal ikram)* kuma da ya faɗesu to sai ya juyo ya fuskanci mamu".

Waɗannan abubuwan guda biyu haka ake so mutum ya kawo su a jere, ba'a so mutum ya rabasu. Kuma dasu mutum zai fara da zarar ya yi sallama.
Wallahu a'alam

3. Faɗar *La'ilaha illahu, wahdahu lasharika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa ala kulli shai'in Qadiir. La haula wala Quwwata illa billah, la'ilaha illallahu, wala na'abuda illa iyyahu, lahun ni'imata walahul fadhlu, walahus sana'ul hasan. La'ilaha illallahu muk'lisina lahuddini walau karihal kafirun.* Sau 1

*Daga Abdullahi Binul Zubair Allah ya yar

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum' shaaidan zai bar gidan!.2- K...
16/10/2023

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI

1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum' shaaidan zai bar gidan!.

2- Ka rika yawan bata labarai. Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu dan Adam yana son labari.

3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta ka nuna 6acin ranka.

4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya.

5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta. Ka nuna baka ma san ta yi ba. Kuma ka dauka a matsayin abinda ya shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.

6- Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada.

7- Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu).

8- Ka nuna mata babu wata budurwa dake gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurinka.

9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku.

10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyatayi da kake mata, kamar siyan abinci,Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata,sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.

11- Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba,Lokuta da dama idan mata da miji s**a dan samu sa6ani har takai ana maida martani cikin fushi,To katuna ba daga ita bane shaaidan ne ke zugata, Saboda shi yana mutukar son ayi saki.

12- Ka dauki abinci ka saka mata abaki. Annabi (s.a.w) ya ce, "abincin ba cikinta kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta."

13- Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara'a domin Manzo (s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya nunawa matarsa fara'arsa to dai-dai yake da yin sadaka."

14- Ka zama mai yawan neman shawararta. (wasu suna ce wa ba,a shawara da mata). To ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matansa.

15- Kar ka 6oye mata damuwar ka, farin cikinka ko bakin cikinka. Domin ita magani ce a tattare dakai.

08/10/2023

Zamu shiga Aljannah in shaa Allahu.

A wata lecture ta Sheikh Jaafar Mahmud Adam (Rahimahullah) mai suna Sa'adah...Yace "Da za'a tarawa Namiji duka matan dun...
30/09/2023

A wata lecture ta Sheikh Jaafar Mahmud Adam (Rahimahullah) mai suna Sa'adah...

Yace "Da za'a tarawa Namiji duka matan duniya a bashi su a matsayin matan aurensa shi kad'ai, sai a ware guda daya a killaceta ace ban da ita"

Yace to da gaba daya hankalinsa zai koma kan wannan matar ne, zai dinga tunanin watakila akwai wani abu da take da shi wanda sauran matan duniya gaba daya basu da shi, kuma da zaka duba a cikin matan nasa akwai wadanda s**a fita duk abin da take taqama da shi din.

Dan haka mata ku daina wahalar da kanku akan maza duk haka muke, duk irin kyau ko tarbiyyarki idan har namiji ya mallakeki a matsayin matarsa to sai dai ki had'a da hakuri, amma ba zaki iya hanashi qara aure ko kula wata mata a waje ba sai dai idan Allah ne kawai ya kareshi...

Su kuma Mata kullum tunaninsu idan zaka qara aure shine me nayi masa? Me na rageshi da shi? Me yarinyar nan ta fini? Me take da shi wanda ni ban da shi? Basu san cewa halittar 'yan mazan ce a haka ba.
© Copied audio lecture

Allah Ya jiƙan malam da Rahama, Ya sa aljanna ce makoma agareshi.

29/09/2023

Hold on to the sunnah of Prophet Muhammad s.a.w because it will lead you to Alannah in sha Allah, but if you hold heresy then it will lead you nowhere but hell, may God protect our Iman. Amin

28/09/2023

WAYE SHEIKH ABUBAKAR MAHMOUD GUMI A GUNA?
An Haifi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a Jahar Zamfara, Karamar Hukumar Gumi Ranar Juma'ar Karshe a Watan Ramadan, a Shekarar 1992 Miladiyya daidai da 1343 Hijiriyya. Sheikh Abubakar Gumi Ya rubuta Littattafai da Dama da Harshen Hausa da Kuma Larabci. Daga Cikin Littafan da Ya rubuta akwai:-
1. NAZAMUL KADIDATU LAMIYYA
2. RADDUL AZHAAN ILAA MA'AANIL QUR'ANI
3. AKIDATUS SAHIHA
4. DA WATA KASIDA MAI BAITOTI 34 WACCE YAYI DAN TA'AZIYYAR RASUWAR SARKIN KANO ABDULLAHI BAYERO.

Meyasa Na Fara tinanin Sanin waye shi?
Wata Rana Ina sauraron Marigayi Sheikh Hamzah Muhammad Lawal a wata Lecture da Yayiwa Suna TARIHINA A HARKA. Lokacin da Sheikh Hamzah Yake Fadan Malaman da Sukayi tasiri a Rayuwarsa wajen Kauwanashi Yazama Mutum (Malami) se naji Ya Ambaci Sheikh Abubakar Gumi, Inda Sheikh Hamzah Yake cewa "Sheikh Abubakar Gumi Yayi tasiri sosai a Rayuwata wajen Sanin Tarjamar Littafin Allah (Alqur'ani) Duk da cewa Yanzu nasaba dashi a wajen Tarjamar wasu ayoyin" Lallai naji Dadin wannan Kalmomin Ganin Yanda naji Sheikh Ya Girmama wannan Lamarin, Kuma naji Ya Girmama Rubuce rubucen shehun Malamin, Wanne Dalilin ne Yasa na Fara Sauraron Malamin, Kuma Gaskiya Nasamu Karuwa sosai agunsa, sannan Na Fahimci cewa A wasu wararen ma Yakan Iya sabawa da Wasu Manyan Malamai a ra'ayinsa, Kamar Misali: Ra'ayinsa Ya Saba da na Imamu Muslim akan Hadisin da Yace Iyayen Annabi suna wata.
Sannan na Fahimci Yakan Tattauna da dalibansa akan wata Mas'ala Dan Yabasu damar Fadan abinda s**a Fahimta, Sannan na Fahumci cewa Mafi Yawan Ra'ayinsa da Yasawa wasu Malamai zaka samu Yana da madogara, bawai Haka kawai yake sabawa dasu Dan Ra'ayinsa ba. Kamar Misali Wani Ra'ayinsa da ya Shahara dashi cewa "Siyasa tafi Sallah" Maganar Gaskiya Shehun Malamin Yafi Dayawa da suke Jayayya dashi Gaskiya. Saboda a Mahangar Sunnah Lokacin da Annabi Muhammadu (SAWA) Yayi wafati ba'a Yiwa Gawarsa Sallah ba har seda aka zabi KHALIFA Wannan Madogarace me Karfi.

Zanci Gaba.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN!Allah Yayiwa Sheikh Giro Argungu Rasuwa.Allah yaji kanshi da Rahma yasa aljanna Fidaus...
06/09/2023

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN!

Allah Yayiwa Sheikh Giro Argungu Rasuwa.
Allah yaji kanshi da Rahma yasa aljanna Fidausi ce makoma agareshi.

19/07/2023

Ruwan Ido Da Dogon Buri Ma Yana Hana Wasu Samun Mijin Aure!

27/05/2023

ZINA

Duk dadin zina bata wuce minti 10,15,20,30 sai tarun zunubi Allah katsare mu daga aikata ZINA duk masoyin ANNABI yace Amin.

27/05/2023

A wata lecture ta Sheikh Jaafar Mahmud Adam (Rahimahullah) mai suna Sa'adah...

Yace "Da za'a tarawa Namiji duka matan duniya a bashi su a matsayin matan aurensa shi kad'ai, sai a ware guda daya a killaceta ace ban da ita"

Yace to da gaba daya hankalinsa zai koma kan wannan matar ne, zai dinga tunanin watakila akwai wani abu da take da shi wanda sauran matan duniya gaba daya basu da shi, kuma da zaka duba a cikin matan nasa akwai wadanda s**a fita duk abin da take taqama da shi din🤣

Dan haka mata ku daina wahalar da kanku akan maza duk haka muke, duk irin kyau ko tarbiyyarki idan har namiji ya mallakeki a matsayin matarsa to sai dai ki had'a da hakuri, amma ba zaki iya hanashi qara aure ko kula wata mata a waje ba sai dai idan Allah ne kawai ya kareshi...

Su kuma Mata kullum tunaninsu idan zaka qara aure shine me nayi masa? Me na rageshi da shi? Me yarinyar nan ta fini? Me take da shi wanda ni ban da shi? Basu san cewa halittar 'yan mazan ce a haka ba🤣

Allah Ya jiƙan malam da Rahama, Ya sa aljanna ce makoma agareshi.

An ruwaito daga Mu'az ɗan Jabal Allah ya ƙara yarda da shi, yace: Nakasance ina tafe tare da Annabi Muhammad صلى الله عل...
11/04/2023

An ruwaito daga Mu'az ɗan Jabal Allah ya ƙara yarda da shi, yace: Nakasance ina tafe tare da Annabi Muhammad صلى الله عليه وآله وسلم akan jaki yana goye dani, sai yace dani صلى الله عليه وآله وسلم: Ya kai Mu'az shin kasan haƙƙin Allah akan bayinsa?, da kuma haƙƙin bayi akan Allah?.

Mu'az ɗan Jabal yace Allah da manzonsa ne s**a sani.

Manzon Allah صلى الله عليه وآله وسلم yace haƙƙin Allah akan bayi shi ne, su bauta masa batare da haɗashi da abokin tarayya ba, Haƙƙin bayi kuma akan Allah, shi ne bazai yiwa wanda baiyi shirka da shi azaba ba.

Mu'az ɗan Jabal Allah ya kara yarda da shi yace, Ya Rasulullah, yanzu na yiwa mutane bushara da wannan magana?.

Annabi Muhammad صلى الله عليه وآله وسلم yace a'a kada kayi musu bushara sai su dogara da haka.

Wannan hadisi yana nan a cikin sahihai guda biyu (Bukhari da Muslim)

Barkanmu da shiga goman karshe, Allah ya karbi Ibadun mu ya gafarta mana.

Daga: Abdallah Amdaz

Assalamu Alaikum kamar yadda muka ce gasar mu ta yau,  zaayi ta akan karatun da aka gabatar jiya na Tafsirin da Malama Z...
07/04/2023

Assalamu Alaikum

kamar yadda muka ce gasar mu ta yau, zaayi ta akan karatun da aka gabatar jiya na Tafsirin da Malama Zainab Ja'afar Mahmud takeyi a Othman Bin Affan Gadon kaya

Tambayoyin mu na yau

Q1, Karqashin Tafseerin Ayar

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَدْخُلُوا۟ بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ حَتَّىٰ تَسْتَأْنِسُوا۟ وَتُسَلِّمُوا۟ عَلَىٰٓ أَهْلِهَا ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ

Malama ta faɗa mana cewa ana neman izinin shiga gida sau uku ne, kuma ta kawo mana hadisai akan hakan,
kawo mana hadisi guda ɗaya da malama ta kawo daya nuna cewa sallama sau uku ake yi.

Q,2 Imam Qatada yayi Istinbaɗi akan sallama nan da akeyi guda uku

kawo mana istinbaɗin sallamar guda uku da Imam qatadah yayi kamar yadda Malama ta kawo a cikin Tafseerin.

Allah ya bada Sa'a

Ɗaliban Malama masu ɗaukar nauyin gasa

Maryam Ayagi
Aisha Sagagi
Haleema Idrees Hasheem
Peerdausy Yahya
Saadatu Sulaiman

MALAM JA'AFAR YABAR BAYA DA DUNBIN ALKHAIRI'Yar marigayi sheikh ja'afar mahmood Adam Malama zainab Ja'afar mahmood Adam ...
07/04/2023

MALAM JA'AFAR YABAR BAYA DA DUNBIN ALKHAIRI

'Yar marigayi sheikh ja'afar mahmood Adam Malama zainab Ja'afar mahmood Adam zata fara gudanar da tafsirin alqur'ani maigirma na mata a Babban masallacin Usman BN Affan dake kofar Gadon kaya a jihar kano. Za a bude Tafseer din daga gobe litinin 11/4/2022

Allahu Akbar: wannan ya Nuna mana rikon amana da kuma tarbiya da ya yi mata kenan, duk da baya raye gashi yabar abin da al'ummah zasu rika alfahari dashi. Makisan malam Ja'afar sun kashe maciji basu sare wuyan shi ba. Za a Cigaba da da'awa irin ta malam Ja'afar duk da baya raye InshaAllah

Rubutawa Naziru aliyu gusau

DAGA TASKAR SHEIKHA Zainab Ja'afar Mahmud  HAFIZAHALLAHKiyi ƙoƙari acikin rayuwar ki ta yau da gobe ki  samawar da kanki...
14/03/2023

DAGA TASKAR SHEIKHA Zainab Ja'afar Mahmud HAFIZAHALLAH

Kiyi ƙoƙari acikin rayuwar ki ta yau da gobe ki samawar da kanki abokiya ko ƙawa wadda take mai neman yarda Allah, Saboda wannan shine ake saran cewa zai haifar miki da ɗa mai ido domin zaki ƙwaiƙwayanta ko kin shirya ko baki shirya ba zaki cinci kanki ɗabi'unki suna naso ajikin ta ɗabi'un ta suna naso ajikin ki

Kamar yadda Manzon Allah S A W ya buga mana misali d waɗan nan mutane guda 2 da zaka iya zama dasu ɗaya ka samu Alkhairy ɗaya ka samu akasin haka
ya buga mana misali da mai saida turare duk inda kikayi ƙawa wadda take saida turare kina zama kusa da ita kin more, mafi karancin abunda zaki samu ki shaƙi daddaɗan ƙamshi, to ta iya yiwuwa ta dauki turaran nan ta baki, ta iya iyuwa ki siya kema ki amfana dashi
Alah ayyihalin tarayya da ita y zamo miki cigaba ne da nasara da jin dadi

Kamar yadda in kika zauna ko maqo taka ko kusa da wanda yake maƙeri ne yana amfani da zuga zigi a gaban wuta a maƙera to lalle sai kin cutu zafi ya ishe ki tartsatsin wuta ya naso ki duk ki ƙwashi ƙauri ajikin ki, ki tashi ki fito dg gurin ba tare da nutsuwa ba saboda me baki zauna a waje mai ky...

Ƙwatanƙwacin haka ya kamata mu dinga zabar kawaye da abokan da zamu dinga ƙulla mu'amala dasu a yau da gobe"

Domin ba ana fatan rayuwa bane kaɗai ta zamanto iya ta duniya ba so ake a duniya a taimaki juna a rayu a ƙyaƙƙyawar rayuwa a gobe lahira a sami ƙyaƙƙyawan sakamako"

االأخلاء يومئذ بعضهم لبعض عدو الا المتقين
Haka Allah S W T yace duk wata ƙawance duk wata abota duk wata alaqa tana tashi ne a matsayin adawa a ranar gobe Ƙiyama sai alaƙar da aka ƙullata saboda neman yardar Allah"

Alaƙar da aka gudanar da ita bisa neman yardar Allah bisa abunda Allah da manzon sa suke so dan haka in kina son ki samu ƙyaƙƙaywan rayuwa to kisamawar kanki abokan mu'amala wanda suke Nagartattu da wannan ne za ai fatan cewa lalle rayuwar ki zata iya inganta

02/02/2023

ME KAKE TAKAMA DA SHI:

-Sharri ~ Sai shaidan.

-Iskanci ~ Sai hamana.

-Muni ~ Sai jilaybyby.

-Kyau ~ Sai annabi yusuf.

-Karfin jiki ~ Sai adawa.

-Girman jiki ~ Sai samudawa.

-Taurin kai ~ Sai sukuddaru.

-Mulki ~ Sai annabi sulaiman.

-Iya rubutu ~ Sai annabi isah.

-Kyauta ~ Sai sayyidina usman.

-Yawaitar dukiya ~ Sai karuna.

-Talauci ~ Sai mus'af bin umairu.

-Gaskiya ~ Sai sayyidina abubakar.

-Karya ~ Sai musailamatul kazzabi.

-Munafurci ~ Sai abdullahi bin ubaid bin salul.

-Isar da sakon manzon Allah ~ Sai sayyidina aliyu.

-Bin annabi sau da kafa ~ Sai su sayyidina abubakar.

-Ba da rayuwa saboda manzon Allah ~ Sai sayyidina umar.

-'Yar da aka fi so a duniya ~ Babu kamar nana fadima, 'yar annabi s.a.w.

-Matar da aka fi so a duniya ~ Babu kamar nana aishatu, matar annabi s.a.w.

-Wanda aka fi kauna, a kaf fadin duniya ~ Babu kamar Annabi Muhammad S a w.

-Aminan gaskiya, ma su kaunar aminin su, fiye da son da suke yiwa kan su ~ Babu kamar khalifofin sa, sallahu alaihi wasallim.

Aisha Yakubu✍️

Kina Haduwa Da Namiji Mai Irin Wadannan Halayen Rikeshi Gam Kin Samu Mijin Aure:Kaman yadda muka kawo wasu alamu na dace...
06/10/2022

Kina Haduwa Da Namiji Mai Irin Wadannan Halayen Rikeshi Gam Kin Samu Mijin Aure:

Kaman yadda muka kawo wasu alamu na dacen mijin aure kamin mace ta amince da mai sonta da aure, ga Karin wasu alamomin da suke tabbatar miki da kinyi dacen mijin aure:

1: Namijin daya damu da damuwarki.

2: Namijin da kullum sai ya kiraki ya tambayeki yadda kika kwana, kika wuni da kuma yi miki fatan tashi lafiya.

3: Namijin Da Yake Baki Lokaci Baya fakewa da aiki yayi masa yawa.

4: Namijin da yake sauraronki yake baki hankalinsa a duk lokacin da k**e son zantawa dashi na muhimmi.


5: Namijin da baya jira har sai kin tambayeshi.

6: Namiji mai cika alkawari. Duk alkawarin da ya miki yana kokarin ya cika. Bana naki kadai ba har na wasu daban. Wannan ba mijin yadawa bane, rike shi gam.

7: Namiji mai furta miki kalaman so a fili, a baka da kuma kuna ku biyu.

8: Namiji mai kalamai masu kyau a lokacin farin ciki da kuma bacin ransa.

9: Namijin da yake da zumudin bashi dama yaga iyayenki ko magabatanki.

10: Namiji mai nuna miki farin cikinsa da kuma yi miki godiya a duk lokacinda kika yi abun ayaba miki. Da kallon kwalliyarki ya yaba. Idan kin kawo masa ruwa ko abinci ya jisu daban da wadanda ya saba.

11: Namiji mai amafni da wadannan kalmomin guda biyu, magiya idan zai saki masa wani abun. Ya kuma ce ya gode idan kika masa, (please and thank you).

12: Namijin da baya kunyar a ganki da shi.


Da fatan mata zasu kula da wadannan abubuwan ba su maida hankali akan aljihunsa ko abar hawansa ba.

Idan sha'awa ce ta kawo saurayi gurin ki, kina hana shi za ki ga ya tsane ki, ya nesanta da ke, toh haka in ki kai kusku...
04/10/2022

Idan sha'awa ce ta kawo saurayi gurin ki, kina hana shi za ki ga ya tsane ki, ya nesanta da ke, toh haka in ki kai kuskuren ba shi ma, sakamakon iri daya ne.

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKIDaga Shafin sirrin rike miji1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum' ...
03/10/2022

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI

Daga Shafin sirrin rike miji

1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum' shaaidan zai bar gidan!

2- Ka rika yawan bata labarai. Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu dan Adam yana son labari.

3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta ka nuna 6acin ranka.

4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya.

5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta. Ka nuna baka ma san ta yi ba. Kuma ka dauka a matsayin abinda ya shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.

6- Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada.

7- Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu)

8- Ka nuna mata babu wata budurwa dake gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurinka.

9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku.

10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyatayi da kake mata, kamar siyan abinci,Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata,sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.

11- Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba,Lokuta da dama idan mata da miji s**a dan samu sa6ani har takai ana maida martani cikin fushi,To katuna ba daga ita bane shaaidan ne ke zugata, Saboda shi yana mutukar son ayi saki.

12- Ka dauki abinci ka saka mata abaki. Annabi (s.a.w) ya ce, "abincin ba cikinta kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta."

13- Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara'a domin Manzo (s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya nunawa matarsa fara'arsa to dai-dai yake da yin sadaka."

14- Ka zama mai yawan neman shawararta. (wasu suna ce wa ba,a shawara da mata). To ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matansa.

15- Kar ka 6oye mata damuwar ka, farin cikinka ko bakin cikinka. Domin ita magani ce a tattare dakai.

Sirrin Rike Miji Islamic medical cent

💖 SIRRORIN SOYAYYA GA MIJI DA MATA💖        WAI SUN GIRMA BA'A SOYAYYA: Yanzu dai bari na fara da ke uwargida, ya kamata ...
03/10/2022

💖 SIRRORIN SOYAYYA GA MIJI DA MATA💖


WAI SUN GIRMA BA'A SOYAYYA:

Yanzu dai bari na fara da ke uwargida, ya kamata ki saurari duk nasihohin da zan miki, ki gode wa Allah wurin yin amfani da baiwar da ya yi miki, na kasancewa uwar gida, wato komai dai yana hannunki ne har da shi kansa maigidan naki, a daidai wannan gabar in ka ji mace tana kukar yadda sitiyarin maigidan ya yi qarfi, har ta kai ga cewa ba ta iya juyawa, to ta binciki kanta.
Haqiqa Allah S.W.T. yana cewa:
*"ﺯﻳﻦ ﻟﻠﻨﺎﺱ ﺣﺐ ﺍﻟﺸﻬﻮﺍﺕ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ..."*
"An qawata wa mutane son ababan sha'awa; Kamar mata..."

Asali ke abar sha'awace ko kin yi ado ko ba ki yi ba, to me zai sa ba za ki yi adon domin ki karkato da hankalin maigidanki zuwa gare ki ba? Wasu matan s**an kalli fima-fiman Indiya sai su riqa sha'awar yadda maza suke ma'amalla da matansu, wasu kuma fima-fiman Hausa suke kallo, to amma akwai wani abin lura.
Shin mu a wannan matattarar tamu, mace takan qure adaka ta sha turare ga lalle yana daukar hankali, ta saka kayan da za su riqa fizgar hankalin mai kallo don kawai ta yi rawa a gaban maigidanta ta tasar masa da sha'awarsa ya ji yana buqatarta?

Mai yuwuwa wani ya ce wannan al'adar Yahudu da Nasara ne, ko ita matar malam Bahaushe ta ce "Haba! Wannan ai sai yara mu mun girma" ko ta ce "Sai kuma a ganki tsofe-tsofe da ke ga yara sun isa aure kina yi wa miji rawa!" to amma kuma tana buqatar soyayyarsa.
Asshaikh Nasiruddeen Al'Albani RL ya fitar da wata fatawa a cikin majallar (Mujallatul Asaalah 8/ 74) yake cewa "Rawar da mace za ta yi a gaban maigidanta, rawa kawai da aka saba ba wai na gaban jama'a ba (ba wai a fima-fimai da wuraren bukukuwa ba), kuma ba koyo ta yi masamman don ta riqa yi ana gani ba, wannan ko da za ta motsa sha'awar maigida ba bu wani nassi da ya haramta, amma da sharadin cewa daga ita sai maigidanta kawai".
An tambayi malam cewa: To in ta saka irin kayan da masu rawa a fima-fimai suke sakawa ta tsaya a gaban mijinta, ashe wannan ba koyi da su take yi ba, kuma da n

An wallafa wannan Bayani domin ilmi, Yana da kyau mai karatu ya karanta har karshe domin ya amfana.TSOTSON FARJIN MACE Y...
03/10/2022

An wallafa wannan Bayani domin ilmi, Yana da kyau mai karatu ya karanta har karshe domin ya amfana.

TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA!!!​

Tambaya​‎: Ina matsayin shan azzakarin namiji ko tsotsar farjin mace yayin saduwa?

Assalamu alaikum Malan “Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshen sa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci?

Amsa​‎

To ‘yar’uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.

Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

​Allah ne mafi sani.​

Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406

02/10/2022

Da kaine zanyi
WUFF 😍😍😍

02/10/2022

Kigama feshe shi da turare kina baby kayi kyau Kuma a karshe wajenmu zaizo anty ayi hakuri Muna Nan tafe 😛😛😛

YADDA ZAKA CI RIBAR ZAMA DA MACEImamu Ahmad bn Hambal (Rahimahullah) ya yiwa 'dansa wasiyya da wasu abubuwa guda goma wa...
02/10/2022

YADDA ZAKA CI RIBAR ZAMA DA MACE

Imamu Ahmad bn Hambal (Rahimahullah) ya yiwa 'dansa wasiyya da wasu abubuwa guda goma wadanda za su taimaka wajen zama da Mace lafiya in sha Allah,

Ga wasiyyar nan kamar haka :

Imamu Ahmad Yace ya kai 'Dana! hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye' Dabi'u guda goma da zaka mu'amalanci matarka dasu, don haka ka kiyaye su,

1&2 : Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki, kuma suna son a rika cewe ana sansu ana kaunarsu,

Don haka kada ka rika yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun qarancin soyayya da kauna,

3. Ka sani cewa su Mata basa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima,

Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace, domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakaninku,

4. Tabbas su ma Mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar dadda'dan Qamshi, magana mai
dadi, kyakkyawar Shiga, tashin Qamshi da dai
sauransu, to don haka ka siffantu da dukkan
wadannan halaye a dukkan yanayinka,

5. Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta Mace wadda take jin cikakken iko acikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa.

To ina Jan kunnenka Kada ka kuskura ka rusa wannan
masarautar, kana mai nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tum'buke ta daga kan sarautartar, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa,

6. Dukkan Mace tana son ta yiwa mijinta hidima
amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi
kokarin raba ta da danginta, ta hanyar bata zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to shakka babu
zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga
samu daga gare su,

7. Ya kai dana, Hakika ita Mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji, karkatacce, wannan kuma ba aibu
bane a gareta

Soyayya gamon jini ne, sai kaga BUDURWA taki zaɓen saurayi, ta zaɓi mai mata da ya'ya dattijo kuma ta rayu cikin farin c...
02/10/2022

Soyayya gamon jini ne, sai kaga BUDURWA taki zaɓen saurayi, ta zaɓi mai mata da ya'ya dattijo kuma ta rayu cikin farin ciki kullum saboda KAUNA kamar za ta haɗiye sa, kuma domin ALLAH ba don wani abun duniya ba.

Rasheedah Bintul Islam

30/09/2022

Allah Ta'ala y Tsare mu da Rayuwar Ƙasƙanci🤲😢❤️

ZO NAN, SAURAYI DAN SOYAYYA!1- Kada kaga macen da kake so a yau, kuma ka furta mata kana sonta a yau din, akwai ganganci...
30/09/2022

ZO NAN, SAURAYI DAN SOYAYYA!

1- Kada kaga macen da kake so a yau, kuma ka furta mata kana sonta a yau din, akwai ganganci da rashin sanin soyayya a cikin yin hakan,

Yi kokari ka fara samun kusanci da ita, tare da kulla abota da ita na tsawon wasu yan kwanaki kadan, a nan zaka fahimci irin macen da ta dace kaso ta ce ko kuma akasin haka take?

2- Na haneka da yin doguwar soyayya da mace, irin soyayyar da zaka riski masu yinta sun shafe shekara da shekaru suna yinta, kaso mafi yawa na irin wannan soyayyar karshenta bai cika zuwa dakyau ba, ku takaita soyayya a waje, ayi aure, bayan anyi aure daganan ku dora soyayyarku daga inda kuka tsaya har zuwa karshen rayuwar ku,

3- Ka zamto me sirri a cikin soyayyar ka, dukkan saɓanin da zai gifta tsakanin ka da masoyiyarka, kayi kokarin boyeshi ta yanda babu wanda zai sani, har zuwa lokacin da zaku daidaita tsakanin ku,

Mace da Namiji marasa sirri mutanen dake kewaye dasu suna musu kallon gidadawa waɗanda basu san kansu ba, domin shi wanda kake kawowa sirrin zamanka da matarka/budurwarka shi baya kawo maka nasa sirrin,

4- Ka so macen da take burgeka, kada kaso wadda take burge mutane, ka so wadda kake so, kada ka so wadda mutane ke so, ka auri mace, idan har kana da hali duk rintsi kada ka bari a aure ka,

5- Ka kasance me kyautatawa a cikin soyayya, amman ka kyamaci dabi'ar roko daga wurin dukkan mace, domin mace me roko idan har bata dainaba wannan rokon zai iya zama silar lalacewar rayuwar ta,

Domin samari yan yankan wuta sunfi son mace me roko, domin idan kika rokesu s**a baki, tabbas kema za su rokeki domin ki basu,

Ka rike waɗannan shawarwarin, za su amfaneka anan kusa.

LADUBBAN DAREN FARKO GA MA'AURATA MATASA DA YAN MATAN WANNAN ZAMANIN SAI MU GYARA GASKIYADa ango ya shigo dakin sabuwar ...
28/09/2022

LADUBBAN DAREN FARKO GA MA'AURATA

MATASA DA YAN MATAN WANNAN ZAMANIN SAI MU GYARA GASKIYA

Da ango ya shigo dakin sabuwar amaryarsa, bayan ya zauna, sai ya yi mata sallama cikakkiya, watau: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh,’

Ita ma sai ta amsa da irin haka, watau: ‘wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wabarakatuh.’

Ya fi kyau ya hada da mika mata hannu su yi musabaha tare da sallamar.

Sannan sai ya aza hannunsa na dama bisa saman goshin amaryarsa ya karanta wannan addu’ar:

‘Allahumma Inniy as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alayhi.’

Ita ma Amarya sai ta dora hannunta saman goshin angonta ta karanta kamar haka:
‘Allahumma inniy as’aluka khayrahu wa khayra ma jabaltahu alayhi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alayh.’

To daga nan sai su yo alwalla su yi sallar nafila raka’a biyu tare (watau cikin jam’i, ba daban-daban ba),

In sun idar sai su yi kyawawan addu’o’in duk da ya kamata, su roki Allah Ya sa alheri cikin rayuwar aurensu; Ya ba su zuriya dayyaba; ya ba su tsananin hakurin zama da juna, ya sa su kasance tare har Aljanna, da sauran bukatocin da suke fatan samu cikin rayuwar aurensu.

To bayan nan, ana so su dan tattauna tsakaninsu, kuma tattaunawa ta gaskiya tsagwaro ba tare da wani boye-boye
ba, tun da dai an riga an zama daya.

Ango ya gaya wa amaryarsa dukkan irin abin da yake so da wadanda ba ya so,misali ya ce: ‘Kin ga dai ni mutum ne da ba ya son raini, don haka ki yi kokarin kiyaye dokokina matukar ba su saba wa dokar addininmu ba, sannan kuma ba na son yawan fita ba tare da kwakkwaran dalili ba.

A fannin abinci ni mai son tuwo miyar kuka ne, ina kuma son fura da nono kindirmo,’ da dai sauran bayanai makamantan wadannan.

Haka ita ma amarya sai ta bayyana wa angonta dukkan abin da take so da wadanda ba ta so, kuma su duka su yi niyya mai karfi ta kiyaye hakkin juna, don samun zamantakewa mai kyau, mai dadi, wacce za ta iya fuskantar kowane yanayi na

14/09/2022

Yadda Ake Shagwaɓa Mai Gida A Lokacin Hutu:

Daga amina yusuf gwamna

Akwai waɗansu keɓantattun ranaku da Mai gida ke hutu. Wani ya dauki hutun aiki na wata guda ko ya ɗebi sati . Ko kuma ranakun Asabar da Lahadi. Ya zama babu aiki kuma zaman shi a gidansa zai ƙaru.
To sai ki yi ƙoƙari ki zamo wa maigidanki KARIYA daga kallace-kallace da yawon kawai.

Tun da ga dama ta samu. Sai ki yi iya ƙoƙarinki Ki bi hanyoyin da za ki lulluɓe shi da ƙauna, da kyautatawa. Saboda babu wata rayuwa ta morewa, Irin ki samu ku manne da mijinki cikin soyayya.

*Annabi (saw) ya ce ” Duniya wani ɗan (wuri) ne na jin daɗi ƙanƙani, amma mafi wannan jin daɗin mace ta gari.”

Ko da ba waɗannan ranaku ba, mu yi amfani da ranakun da Maigida bai da aiki wajen samarwa mazaje hutu a cikin gidajemmu. Kasancewar mafi yawansu Litinin har Juma’a suna sintiri wajen aiki.

ABUBUWA DA ZA KI YI:

Ki yi Ƙoƙari ki dinga riga shi tashi daga barci. Ki yi wanka da caba kwalliya, ki sa riga mai shara-shara ko ɗamammiyya mai nuna sirrin jikinki.

Duk ƙarshen Mako (weekend) ya zamo breakfast ya bambamta (inda hali) Ki kammala shi da wuri. Idan hutun na da tsayi. Ki tsara abincinki, in dai da hali.

Ki nemi garwashi, ki turare gidanki. Ki sa turare jikinki wato humra. Kuma ki fesawa kayan da kika sa.

Bayan ya dawo sallah, da kin jiyo takunsa, ki ƙarasa ki taryo shi. Ki gaishe shi cikin girmamawa. Ki ce Bismillah ga abincinka.

Idan ya ce ba yanzu ba, zai dan kwanta ne. sai ki bi shi ki kwanta jikinsa ku huta* Idan ya nuna yana buƙatar ki, good. In kuma barcin ne da gaske, sai ki tafi ki shirya yaranki da gidanki. Kar ki bar su, su yi ta hayaniyar da za ta dame shi.

Da azahar kuma
ki kammala girki da wuri. Ki sake kwalliyya da ado, sai dai kamar atamfa, leshi, shadda ( waɗannan wanda s**a fi kyau cikin kayanki da ki ke ɓoyewa ). kar ki manta da yawan aswaki.

Idan ba a yi komai ba tun asubar nan. To, ki yi ƙoƙari ya kwanta ya huta, da azahar bayan ya ci abinci. Ki tabbata kin yi abin da zai kiɗima shi don ku hu

Address

Sambolei Road Emir Drive Kofar Yamma Jama'are
Jama'are

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Ja'afar Mahmood Adam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Jama'are

Show All

You may also like