30/09/2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
30/09/2023
Ɓatan Dabon Jemage
Kurciya ta kalli Tattabara ta ce "Wai kuwa an gan shi?"
Cikin alamun rashin fahimta, Tattabara ta amsa da "Wa?"
Kurciya ta murmusa ta ce "Shugaba Jemage mana, ai an ce yau mako guda ke nan ba a gan shi ba, tun da aka tashi taron majalissar ɗinke dazuka, ba a sake ganin shi ba "
Kanari da ke gefe ta tuntsire da dariya ta ce "Wannan shi ake kira da ɓatan dabon Jemage!
To ina ƴan rakiyarsa? Su ma ba su san inda ya ke ba?
Gado ya ce "To abin dai an sa kowa a duhu, ni fa wannan labarin na ɓatan Jemage, har ji na yi ana tattauna shi a sheƙar masu kawo rahoto, to mu dai sai dai mu ce "Ubangiji ya haɗa shi da mai irin halinsa"
Hazbiya ta ce "Ha'a! Wannan wacce irin addu'a ce? Maimakon a yi addu'ar bayyanarsa sai a addu'ar ya haɗu da mai halinsa?"
Aiko Kanari sai ta k**a waƙa tana cewa;
"Wanda duk ka ji an ce aniyarsa ta bi shi,
Yana ta faɗa aniyarsa ce....."
"Dakata da Allah!" Bainu ta dakatar da ita, "Yanzu ba lokacin waƙa ba ne, lallai mataimakin Jemage wato Hankaka yak**ata ya baza cigiya, lallai yak**ata a san halin da ya ke ciki, Ubangiji ya bayyana shi!"
Nan Tsuntsaye su kai cirko-cirko, ba wanda ya amsa da "Ameen" Bainu ta ce "Ikon Allah! Addu'a na yi fa, amma ba ku amsa da Ameen ba?"
"Kowa ta sa ta fishe shi kawai!" Gado ya amsa.
"Ya labarin ranar murnar ƴanci Dajin nan ne, gobe ne ko?"
Hazbiya da Kurciya su ka haɗa baki su ka ce "Wani ƴancin?"
*An hango Alhudahuda yana shirye-shirye da rubuce-rubuce a wasu takardu. Sannan an jiyo shi yana cewa "3rd October! 3rd October!!"
Copied from Mukhtar Mudi Sipikin