13/12/2023
TUNA BAYA FURUCIN SARKI ADO A KAN GINA COCI
Ko Jonathan Be Isa Ya Gina Coci A Jamai'ar Bayero ba- Inji marigayi Tsohon Sarkin Kano
Ado Bayero
Zaman babbar kotun Shari'ah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya
Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta
kasa CAN ta kai Masarautar Kano,
saboda Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr
Ado Bayero yasa an rushe wata Coci da
ake ginawa a cikin tsohuwar Jami'ar Bayero Kano (BUK).
A zaman kotun da akayi a ranar Litinin 3
Feb, 2014, kotu ta nemi Mataimakin
Shugaban Jami'ar Bayero Prof Rasheed,
da wakilin kungiyar Kiristoci ta kasa, da
kuma Mai Martaba Sarkin Kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga
Prof Rasheed da mataimakin shugaban
CAN sun mike tare da Lauyoyinsu amma
ba a ga Mai Martaba Sarki ba.
Daga nan sai jagoran Alkalan kotun
Justice Alakola Nweri yace da yake muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari'ar
zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin
kafin wadannan mintoci.
Daga nan sai Justice ya dubi Prof
Rasheed yace a baya Kotu ta baku
umarnin Gina Coci a Jami'ar Bayero, ko kunbi umarnin kotu?
Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa munbi umarnin Kotu, dan sai da ginin Cocin ya
kai linta sannan Mai Martaba Sarkin
Kano ya bamu umarnin tsayar da aikin,
daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano Alh.
Tijjani Hashim ya Jagoranci Rushe ginin gaba daya, Justice yace, kuna nufin kenan kunyi
watsi da umarnin kotu kunbi na Sarki?
Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa saboda
Sarki Ubanmu ne, kuma shine Sarki mai daraja ta daya a kasar nan bayan Sarkin
Musulmi saboda haka, bazamu iya kin yi
masa biyayya ba.
Daga nan sai Justice ya umarci Prof
Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da
wakilin CAN kaji abinda ya fada kana da abin cewa?
Sai yace Eh, wakilin CAN yace gaskiya
ne hukumar Makarantar Jami'ar Bayero
ta fara gina Cocin aka Hanasu saboda
haka muke rokon wannan kotu da ta
hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shima akace ya
zauna.
Sannan kotu ta nemi Sarkin daya
bayyana a gabanta, ana haka sai ga
Sakataren Gwamnatin Tarayya Dr. Anyim
Payios Anyim ya bayyana a gaban kotun, anga Alkalan kotun sun mike tsaye domin
girmamawa ga Dr. Anyim.
Daga nan Dr. Anyim yace ya Mai Shari'ah
ni ne wakilin Mai Martaba Sarkin Kano
Alh. Dr. Ado Bayero, ya umarceni dana
wakilceshi a wannan koto domin amsa kira.
Justice yace, kana nufin kana tsaye anan
a matsayin Maimartaba Sarki kenan?
Dr. Anyim yace kwarai kuwa, kuma duk
abinda zan fada ba ni na fada ba His
Royal Highness ne ya fada. Justice yace, muna jinka.
Dr. Anyim yace, Sarki yace na sanar da
wannan Kotu shi yasa a rushe Cocin,
badan komai ba sai dan basa bukatar
ganin cocin a Jami'ar, Sannan yace na
gayawa wannan kotu mai daraja cewar, idan za'a gina Coci sau 10 a Jami'ar to
kuwa zai sa a rusheta sau 10.
Sannan Galadiman Kano Alh. Tijjani
Hasheem yace na gayawa wannan Kotu
ko Shugaban kasa Goodluck Jonathan
bai isa ya gina Coci ba a harabar Jami'ar Bayero, ba tare da yardar Mai Martaba
Sarki ba, Dr. Anyim ya cigaba da cewa,
wannan shi ne sakon da Mai Martaba
Sarkin Kano da Mai Girma Galadiman
Kano s**a turo ni domin na sanarwa da
wannan kotu na gode. Daga nan, anga Alkalan Kotun suna
tattaunawa a tsakaninsu, kafin daga
bisani akaga Babbansu ya daga waya
yana magana, daga nan sai Alkalin yace
to duk munji baya nan ku, dan haka,
wannan kotu tana kira ga Shugaban kasa daya duba wannan Lamari idan yaga da
yiwuwar gina Cocin to ya bada umarnin
ginin, idan kuma yaga ba sai an gina ba
to shikenan.
Daga karshe Kotu ta Sallami wannan
Kara, kuma tare da yiwa Martaba Sarkin Kano fatan alkhairi da fatan Allah ya kara
masa lafiya da adalci.
Sai dai bayan gama wannan Shari'ah,
Mai Girma Galadiman Kano, ya bayar da
sanarwar cewa Babbar Mai Shari'ah ta
kasa Justice Maryam Aloma Mukhtar da Alkalan kotun da s**a jagoranci Shar'ar
da su gurfana a fadar Mai Martaba Sarkin
Kano, Alh. Dr. Ado Bayero CFR. LLD. JP.
Allah Ya Jaddada Rahama Ga Sarki Ado
Da Dukkan Musulmai, Allah Ya Kai Masa
Ladansa Na Yiwa Addinin Musulunci Hidima amin summa amin.
© Nigeria Reporters Hausa