16/09/2024
Hakan na zuwa ne bayan hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta ga wani bidiyo da ke yawo na zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Seaman Abbas Haruna tsawon shekaru shida.
A wani martani ga wannan zargi, Babban hafsan sojin ƙasar, Janar Christopher Musa ya ba da umarnin fara binciken gaggawa domin gano haƙiƙanin abin da ya faru kuma za a sanar da ƴan ƙasa sakamakon binciken.
Ƙarin bayani - https://bbc.in/3zhfwSX