Musa Algombawy

Musa Algombawy The Light of Islam in Qur'an and sunnah
(1)

Wai ina ya shiga ne?Ya fito in ba tsoro ba.
25/11/2023

Wai ina ya shiga ne?
Ya fito in ba tsoro ba.

15/10/2023
13/07/2023

MTFE kuna yaudarar Mutane wai FOREX ne, to shi Forex din waye ya halarta shi?

11/07/2023

Duk wanda ya riƙe Allah babu wanda zai ci Nasara akan sa.

Wayar ki da Screen Guard da Cover, amma kina tafiya ba Lufaya! Ke wace irin Sakare ce?
22/06/2023

Wayar ki da Screen Guard da Cover, amma kina tafiya ba Lufaya! Ke wace irin Sakare ce?

12/06/2023

Idan kayi nufin aikin Alkhairi kar ka tsaya wani Shawari, domin za'a iya hana ka.

01/06/2023

Assalamu alaikum warahmatullah,
MUHIMMIYAR SANARWA:
Ana sanar da dukkan sabbin dalibai da s**a sayi FORM na makarantar AL-ITQAAN da cewa su halarci makarantar dake GRA (GSADP Quarters) a ranar Asabar 3rd June 2023 da misalin karfe Daya na Azahar tare da form din da kuma sauran takardun su Original da photocopy, domin screening.
Don Allah a baza wannan sanarwa kota ina, domin sabbin daliban. Na gode.
ISA UMAR ABDURRAHMAN

23/05/2023

Da in Mutum zai lalata maka 'Ya sai ya zo har kofar gida, amma yanzu a waya kawai zai ƙira ta ta je ta same shi, Iyaye a lura da Tarbiyya da kyau.

23/05/2023

Haba 'yan Mata! Ubanki ko Jaki bayi da shi kice sai mai Mota za ki Aura, anya kin yiwa kan ki Adalci kuwa?

19/05/2023

Ka gayyato Shaidan Auren ka, anyi Rawa anyi Kaɗe-kaɗe, kuma kayi tsammanin samun Albarka?

13/05/2023

Roƙo yana zubar da Mutunci, don haka mu kiyaye, musan rabon ka duk in da kake zai same ka.

BUKIN RANAR MASOYA (VALENTINE DAY) A MAHANGAR MUSULUNCIAn tambayi Lajnatudda'ima dangane da Idin masoya da akeyi ran 14 ...
14/02/2023

BUKIN RANAR MASOYA (VALENTINE DAY) A MAHANGAR MUSULUNCI

An tambayi Lajnatudda'ima dangane da Idin masoya da akeyi ran 14 February na ko wace shekara, meye Hukuncin sa.

Sai s**a ce" Idi dai a Musulunci guda biyu: Idin Sallar Azumi da na Layya, duk abun da ba su ba na wani Idi da yake da alaka da wani Mutum ko wata Jama'a, Idi ne na Bidi'ah baya Halarta ga Musulmai su aikata shi ko tabbatar da shi ko nuna farin ciki da shi ko taimakon wasu akai, domin hakan ketare iyakokin Allah ne, wanda ko ya ketare iyakokin Allah to hakika ya Zalumci kan sa.

Kuma wannan Buki ne da Kafurai s**a kirkiro, aikata shi yin koyi da su ne, yin koyi da su kuma Haramun ne, kuma Zunubi ne.

Manzon Allah (S.A.W) ya yi hani dangane da koyi da su, yace: "Duk wanda ya koikoyi wasu Mutane to yana cikin su".
Sabo da haka baya Halarta ga Musulmi da yayi Imani da Allah da ranar karshe ya aikata irin wannan aiki ko ya gaida masu aikatawa, abun da ya zama wajibi akan sa shine ya nisanci hakan, ya amsa kiran Allah da Manzon sa, tare da nisantar duk wasu sabuba da za su fusatar da Allah (S.W.T).

Don haka haramun ne Mutum Musulmi ya taimaki wannan Buki ko wanin sa daga Bukin Kiristoci da wani abu na Abinci ko abun sha, domin hakan taimakekeniya ne akan Zunubi da ketare iyaka, kuma sabawa Allah ne da Manzon sa.

فتاوى لجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء برقم (5324 ) وتاريخ 3/11/1420 هـ .

Allah yasa mu dace.
Musa Muhammad Sani
(Algombawy)
B.A Ed.
14/02/2023

24/01/2023

KO YA HALASTA MUTUM YA BADA TSOHON KUDI A BASHI SABO TARE DA BIYAN WANI ABU?

Babu shakka hakan bai Halasta ba, wannan shi ake cewa Riba, idan ka bada Sabon 1,000 aka baka 1,050 misali wannan naira 50 da aka kara maka akai ta zama Riba, wanda hakan Kuma Haramun ne, kamar yadda Allah ya Haramta cikin Alqur'ani Sura ta 2 aya ta 275, da 278-279.

Kuma yazo cikin Hadisi Manzon Allah (S.A.W) ya tsinewa mai cin Riba.

Dukkan Malamai sun tafi akan Haramcin hakan, kuma yin hakan Zalunci ne mai girma, yana daga cikin Manyan Laifuka.

Allah yasa mu dace ya kara nuna mana gaskiya ya bamu ikon bin ta, ya nuna mana karya ya bamu iKon kauce mata.

12/12/2022

Dalibi ya shiga Hanun Gwani

03/08/2021

HAPPY BIRTHDAY

Wannan lamari na Birthday babu shakka yana qara yawaita cikin Musulmai, kuma majority iyaye su suke daura yaran su akai tun suna qanana, za kaga Uba ko Uwa su suke sayowa yaran su Cake da Drinks suna koya musu Dabi'ar Yahudawa tun suna qanana. In banda shiririta da rashin hankali ya za'ayi kwanakin da aka dibawa Mutum zai yi a Duniya suna qarewa yana kusantar Kabari yana murna, maimakon ya tsaya yayi tinanin wani irin ayyuka yake gabatarwa?

Wani abun da yake ban mamaki wannan lamari na Birthday har wasu cikin Daliban Ilimi da Alarammomi za kaga suna posting na Happy Birthday, to meye banbancin su da sauran wanda ba su ba? taya wasu murna don kewayowar ranar Haihuwar su wannan munmunar Al'ada ce data shiga cikin wasu Musulmai, aikata hakan kuma koyi ne da maqiya Allah (Yahudu da Nasara) da kuma kamanceceniya dasu.

Manzon Allah (S.A.W) yace a ma'anar wani Hadisi da Abu Daud ya ruwaito: "duk wanda yayi kamanceceniya da wasu Mutane to yana cikin su".

Sabo da haka baya halatta ga Musulmi ya koikoyi Yahudawa bayan Manzon Allah ya riga ya umurce mu da saba musu da nisantar duk abubuwan da s**a Sunnan ta. Kuma wajibi ne akan dukkan Musulmi su dinga kokarin bin gaskiya da dai-dai cikin al'adun su da koyi da muatanen kirki.

Allah ka gara nuna mana gaskiya ka bamu ikon bin ta.

Musa Muhammad Sani (Algombawy)

24/05/2021

IZU GOMA MATA
MUSABAQAR ALQUR'ANI MAI GIRMA, JIBWIS NHQT JOS, GOMBE SOUTH, GOMBE STATE OF NIGERIA.

24/05/2021

IZU GOMA MATA
MUSABAQAR ALQUR'ANI MAI GIRMA, JIBWIS NHQT, GOMBE SOUTH GOMBE STATE OF NIGERIA.

24/05/2021

Jibwis Nhqt Jos Gombe South Branch
24/05/2021

Daga wajen Musabaqa, yanzu ana Izu uku 3

Address

Gombe

Telephone

+2347033800473

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Musa Algombawy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Musa Algombawy:

Videos

Share

Category