Ruhin Jarumtaka littafin yaki

Ruhin Jarumtaka littafin yaki Domin kasaitattun littatafan Hausa na yaki da novels
(12)

09/05/2024

RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 281: *Halittun daular Ems*
*
★U★M★S★
*
Dedicated to Princess Fatima Zahra.
*
Copyright: ★RUHIN JARUMTAKA littafin yaƙi★
*
*
~Gilasiyàs.
~Garin Aiysi.
~Daular Ems.
*
Girman filin zai iya kai kamu dubu arba'in. Babu komai a wannan fili sai dusar ƙanƙara. Tuni ta cika filin ta zamo tamkar rairayi. Haka kuma tana zubowa daga sama tamkar ruwan sama.
Ba zai yiwu halitta mai jini da tsoka ta rayu a wannan waje, ba tare da ta daskare ta zamo ƙanƙara ba.
Wannan fili shi ake kira da suna, Gilasiyàs. Sunan nasa ya zamo asali ne daga ƙanƙara.
Gilasiyàs yana da ɓangarori guda biyu masu fuskantar juna.
Ɓangare na farko yana ƙofar shiga wani gari ne, ana kiran garin da suna Aiysi.
An gina wani gado na aba'i a wannan ɓangare. A bayan wannan gado ƙasaitattun kujeru ne guda huɗu.
A wannan waje aka yanke shawarar zartarwa mahaifiyar Aymanul Faris hukunci. Rana da lokaci kawai ake jira.
Bayan dogon lokaci wani ƙatoton jirgin ruwa ya ƙaraso wannan fili.
Abin mamaki wannan jirgi a sama yake tafiya maimakon cikin ruwa.
A hankali wannan jirgi ya sauƙo ƙasa.
Jirgi ne ruwan toka wanda aka yiwa ado da layuka baƙaƙe ƙirim. Akwai tutocin Ajalin dake kaɗawa a cikin iska a jikin wannan jirgi.
Yana da ƙofofin shiga guda goma sha-ɗaya waɗanda a wannan lokaci suke rufe.
Wannan jirgi na gama daidaita a ƙasa, ƙofar garin Aiysi ta buɗe.
Wasu zaratan mayaƙa guda goma s**a fito daga cikinta.
Gangar jikin su irin gangar jikin Ajalin ce. Sai dai sun fi Ajalin tsaho da murɗewa.
Dukkansu suna ɗauke da mak**an yaƙi na gani na faɗa. Wani irin kwarjini wanda yake da alaƙa da maɗaukakin iko yana baibaye jikin waɗannan Ajalin.
Ƙofa ta farko daga jikin wannan jirgi ta buɗe.
Sarki Baríf Girna Ajalin da kansa ya tako ya fito.
Waɗannan mayaƙa guda goma suna ganinsa s**a zube ƙasa s**a yi gaisuwa. Sarki Baríf Girna Ajalin ya bi su ɗaya bayan ɗaya yana dafa kafaɗarsu cikin jinjina.
Jim kaɗan sauran mutanen dake cikin wannan jirgi s**a fara firfitowa har saida s**a gama fitowa gaba ɗaya.
Ba wasu bane illa muƙarraban Baríf Girna Ajalin dake daular Yamma.
Akwai wata mata wadda s**a sakata a tsakiya. An lulluɓe wannan mata da wasu irin tufafi masu kaurin gaske.
Ba don an lulluɓe ta da waɗannan tufafi ba da sanyin dake wannan waje ya daskarar da ita.
Sarki Baríf Girna Ajalin ya dubi mutanensa ya basu umarnin kai wannan mata zuwa kan wannan gado na aba'i su durƙusar da ita.
Nan take s**a tunkari inda gadon aba'in yake s**a durƙusar da Hajriya a gaban gadon.
Ana amfani da gadon aba'i wajen sare kan mai laifi a daular Ems.
Lokacin da Baríf Babba ya ɗaga kansa ya hango Hajriya durƙushe akan gwiwowinta, sai ya cika da tsananin farin ciki.
"Ku kirawo dukkan rundunonin mu dake cikin wannan daula," inji Baríf Babba.
Ita dai daular Ems wata babbar daula ce wadda magabatan Baríf Babba s**a yi masa tanadinta domin ya cika aikin da aka bar masa.
Idan mai saurare ba zai manta ba, aikin da aka barwa Baríf Babba dai shi ne, haɗa fasahar Lokaci a waje guda sannan ya tarwatsa ta.
Ta wata fuskar zaka iya cewa, an ajiye tarin mayaƙa a wannan daula ce domin a shirya su da kyau.
Zaka gasgata hakan idan kaga bambancin dake tsakanin waɗannan mayaƙa guda goma da kuma mutanen da Baríf Babba ya taho dasu.
Ance a daular Ems ne kaɗai zaka samu dukkan wani jinsi da mataki na Ajalin.
Ka fara da Ajalin ɗan Farko, Ajalin ka balaga, Ajalin ka isa aure, Ajalin mayaƙi, Ajalin barde, Ajalin tsohon kwano, Kyaftin, kwamanda, Asasin har zuwa Babba.
Sarki Baríf Babba ya taka a hankali ya ƙarasa inda waɗannan kujeru guda huɗu suke ya zauna akan wanda tafi girma.
Yana zama ya fuskanci filin yaƙin Gilasiyàs.
Daidai inda waɗannan kujeru guda huɗu suke da kuma gadon da aka durƙusar da Hajriya, wajen ya ɓuɓɓugo daga ƙasa ya tashi sama tamkar janyo shi aka yi.
Wajen ya taso sama k**ar wani tudu ta yadda ko a ina kake a wannan waje zaka hango abinda ke faruwa a gurin.
Baríf Babba ya tafa hannayensa sau uku tare da ambaton salsa a cikin zuciyarsa.
Taurari guda uku s**a diro daga sararin samaniya s**a bayyana akan tafin hannunsa.
Baríf Babba ya ajiye su ɗaya bayan ɗaya akan waɗannan kujeru guda uku dake bayansa.
Taurarin s**a juye s**a koma siffar waɗannan mutane guda uku masu sanye da baƙaƙen tufafi.
Waɗannan mutane guda uku sune Salsan Baríf Babba.
Dukkansu s**a risina s**a yi gaisuwa.
Baríf Babba ya buɗe shafin hira tsakaninsa da waɗannan mutane guda uku.
Koda yake jin bayaninsu a yanzu ba zaiyi wata ma'ana ba, mai saurare zai fi jin daɗin ganin ƙarfin ikon waɗannan mutane a aikace.
Dakaru rukuni-rukuni s**a fara fitowa daga cikin garin Aiysi suna kewaye wannan tudu wanda Baríf Babba da salsansa suke zaune akansa.
Sai da mayaƙa wajen dubu ɗari huɗu s**a fito daga cikin wannan fili kuma s**a kewaye Baríf Babba da salsansa a tsakiya.
Mutanen sun raba kansu izuwa dubu goma-goma.
Dukkan mayaƙa guda dubu goma suna da kyaftin guda ɗaya wanda zasu bi umarninsa a wannan yaƙi.
Dukkan kyaftin guda biyar suna da kwamanda guda ɗaya da suke karkashinsa.
Kowanne Asasin guda ɗaya akwai kwamandu goma a ƙarkashinsa.
Asasin kuwa suna karɓar umarni kai-tsaye daga ruhin Baríf Babba.
A takaice dai, ana so ka gane cewa Ajalin sun tsara wannan yaƙi yadda ya dace.
Abinda suke jira kawai shi ne, bayyanar Aymanul Faris da rundunarsa.
Ko meye shirin Baríf Babba?
Me yasa ya kawo wannan yaƙi daular Ems?
Samun amsar waɗannan tambayoyi zai iya kasancewa a ranar da za'a fara gwabza wannan yaƙi.
***
~Daular Shaha.
~Fadar Aymanul Faris.
***
Su Aymanul Faris suna kewaye da wani babban teburi a tsakiya.
Babu komai akan wannan teburi sai tarin dusar ƙanƙara. Kai da gani ka san cewa dabarar yaƙi za'a tattauna akan wannan teburi.
Aymanul Faris yana tsaye akan wannan teburi, Marganu, Azman da Helina suna tsaye a hannun damansa.
Ranganu, jaruma Riya, Firziyya, Oksu da Hodon suna tsaitsaye a hannun hagu.
Dukkansu idanunsu suna kan wannan teburi suna ganin abinda ake ƙoƙarin zayyanowa.
Aymanul Faris ya saka hannunsa ya zana wani dogon layi wanda ya raba filin yaƙin gida biyu.
"Ku ɗauka wannan filin yaƙi shi ne, Gilasiyàs." inji Aymanul Faris.
"Gilasiyàs yana da ɓangarori guda biyu. Ɓangare na farko yana kusa da garin Aiysi. Ɓangare na biyu kuwa, ƙarshen filin yaƙin kenan."
Aymanul Faris yana bayani yana nuna musu bangarorin guda biyu.
Daga ta wajen ɓangaren farko Aymanul Faris ya kafa gadon aba'i.
"Mu ɗauka anan zasu ajiye mahaifiyata," inji Aymanul Faris.
"Ko shakka bana yi haka zasu tsara wannan yaƙi.
"Mayaƙan su zasu kewaye wannan gadon aba'i gaba ɗaya."
Aymanul Faris ya samar da shingen sirri sannan ya ci gaba da tattauna al'amarin wannan yaƙi. Ba tare da kowa dake waje ya san abinda aka tattaunawa ba.
Bayan k**ar sa'a uku wannan shinge ya disashe ya ɓace ɓat!
Ranganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ya shugabana! Bari naje na taho da Oksu da sauran mayaƙana!!"
Aymanul Faris ya gyaɗa masa kai, "Ka sanar dashi aikin da zai yi mana a wannan filin yaƙi!"
Ranganu ya gyaɗa kai cikin amincewa sannan ya ɓace ɓat!
Marganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Bari naje na dauko hadimi Isika,"
Shima Aymanul Faris ya sallame shi. Yana shirin tafiya kenan, Firziyya tace zata biyo shi su tafi tare amma sai Aymanul Faris ya dakatar da ita.
Bayan tafiyar Marganu, Azman ya dubi Aymanul Faris ya ce.
"Ana fafata azababben yaƙi a daular Babilá wanda tuni anyi asarar rayuka masu dimbin yawa a cikinsa."
Aymanul Faris ya girgiza kai cikin takaici ya ce, "Kaico! Lallai ba ma buƙatar rasa mutane masu karamci irin su Anwar!!"
Gimbiya Helina ta dube shi ta ce, "Labari yazo min daga Binfiron-1000, sarauniya Amirza tana wannan filin yaƙi..."
Aymanul Faris ya koma kan kujerarsa ya zauna.
A wannan lokaci jaruma Riya da gimbiya Jaanu wani abu suke ayyanawa a ransu.
Ina ma za'a barsu su kaiwa mutanen daular Babilá ɗauki?
Sai da Aymanul Faris ya shafe daƙiƙa ɗari huɗu yana tunani sannan ya dubi gimbiya Helina, gimbiya Firziyya da jaruma Riya ya ce.
"Na umarce ku da zuwa daular Babilá ku kwantar da tarzoma!"
Ya dubi Helina ya ce, "Idan so samu ne, ina so ki yanko kan sarauniya Amirza ki kawo min!!"
Gimbiya Helina tayi murmushi, ita da Firziyya da jaruma Riya s**a fice daga cikin wannan fada.
Dukda gimbiya Jaanu tayi niyyar bin bayansu amma sai taga meye amfanin zuwanta?
Koda taje babu abinda zata yi a filin yaƙin, tun da bata kasance jaruma ba.
Aymanul Faris ya k**a hannunta s**a fice daga cikin wannan ɗaki, Ujuran da Hodon s**a take musu baya.
Tattaunawa akan yaƙi irin wannan abu ne da yake buƙatar sirri shiyasa Aymanul Faris ya tsara dukkan yaƙin a sirrance, ba tare kowa ya sani ba.
Duk mai son ganin abinda zai faru, MU HAƊU A GILASIYÀS 😁.
****
~Ƙarƙashin tsaunin Sudo.
~Ƙabilar Oros.
****
Kasancewar tazarar dake tsakanin filin yaƙin Amru da tsaunin Sudo babu nisa sosai yasa ƙarnin jini da kururuwar mazaje ta addabi ƙabilar Oros.
A wannan lokaci jaruma Faurisa ta fara samun sauƙi daga raunikan da aka yi mata a dajin Zagaga sa'adda za'a sace Lisa Na.
Tun daga lokacin da jaruma Faurisa ta miƙe tsaye hankalinta ya kasa kwanciya.
Ta ya ya hankalinta zai kwanta alhalin mahaifinta, 'yar uwarta da masoyinta suna filin daga?
Jaruma Faurisa ta rasa waje ɗaya da ya k**ata ta fara zuwa domin ganin abinda ke faruwa.
A duk lokacin da ta tuno da gargadin da Anwar yayi mata sai taji ba zata iya barin tsaunin Sudo ba.
To, amma tana zaune ne a cikin tsananin zulumi da fargaba.
Wata rana tana zaune a wani waje tana tunani akan abinda ya k**ata ta fara yi. Ɗaya daga cikin mutanensu wanda s**a yiwa mahaifinta rakiya ya rugo a guje ya dawo.
Jaruma Faurisa tasa aka yi gaggawar kawo mata shi sannan ta tambaye shi abinda ke faruwa.
Jarumin ya kwashe labarin komai ya zayyane mata.
Koda jaruma Faurisa taji labarin inda mahaifinta yake sai tayi gaggawar hawa kan ingarman doki ta tasarwa dajin.
Dakaru guda goma kacal s**a yi mata rakiya.
Sai dai abin baƙin ciki tana ƙarasowa wannan daji ta iske gawar mahaifinta da ta arnen daji Jasaran da kuma ta dukkan jama'arsu.
Jaruma Faurisa ta fashe da kuka ta rungume gawar mahaifinta, waɗannan mutane guda goma s**a shiga rarrashinta.
Jaruma Faurisa ta sa mutanenta s**a ƙone gawar arnen daji Jasaran da ta yaransa gaba ɗaya.
Sa'annan s**a ɗauki mutanensu s**a juya zasu koma ƙarƙashin tsaunin Sudo.
Sai dai basuyi doguwar tafiya ba, Faurisa tayi turjiya.
Mutanen guda goma s**a tsayar da dawakansu su ma.
Faurisa ta dube su ta ce, "Zan je na dubo abinda ke faruwa a wannan filin yaƙi.
"A yiwa Orosi sutura, ina nan dawowa da yamma!"
Dakarun guda goma s**a risina a gabanta sannan s**a nausa cikin daji s**a tafi.
Jaruma Faurisa ta juya dokinta ta sukwane shi da gudu ta dawo filin yaƙin Amru.
Tana zuwa wannan filin yaƙi tayi arba da Anwar tare da Amirza suna fafata azababben yaƙi.
Ganin siffar Amirza kaɗai tayi saida gabanta ya faɗi.
A hankali ta ƙarasa can gefe guda inda Nabilà ke durƙushe ta ɗaga hannayenta biyu sama tana addu'a.
Jarumi Anwar da sarauniya Amirza s**a wanzu suna masu kaiwa junansu muggan sara da s**a.
Jarumi Anwar yana amfani da takobin Saif-Al-Jazeera, ita kuwa Amirza tana amfani da Takobin Mutuwa.
A duk lokacin da waɗannan takubba guda biyu s**a haɗu a waje guda sai an kwararo gagarumar tsawa.
Jarumi Anwar ya cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda sarauniya Amirza ta gagara hallaka shi.
Sarauniya Amirza tana sarrafa wannan takobi dake hannunta tamkar takobin ta kasance wani sashe na jikinta.
Bayan wannan sara ko s**an takobin yana haifar muggan illoli a cikin daji na Amru.
Wani lokacin baƙar ƙanƙara ce take sauƙowa daga sama ta lulluɓe tsaunika da bishiyoyi.
Wani lokacin kuma fai-fai na ƙanƙara ne suke watsuwa ko'ina suna karkashe sauran jama'ar da s**a yi saura daga wannan yaƙi.
Koda mutane s**a ga idan s**a tsaya kallon wannan gumurzu zasu iya mutuwa sai s**a runtuma da gudu.
Dakarun musulunci s**a koma daular Babilá, sauran mayaƙan sadauki Rairud kuwa s**a gudu cikin daji.
Jaruma Faurisa ta lura da wasu gawarwaki guda biyu a gefen Nabilà.
Ga dukkan alamu Nabilà ce ta matso dasu.
Koda ta lura da kyau sai taga akwai k**anceceniya tsakanin gawarwakin da su Nabilà.
Saboda haka cikin sauƙi ta shaida su. Lallai makusanta ne ga su Nabilà.
Nan take tausayin su ya k**a Faurisa.
Tana cikin wannan hali ne taga sarauniya Amirza tayi tsalle izuwa can baya sannan ta ɗaga takobinta sama ta cakata a cikin ƙasa.
Kusan rabin ƙarfen takobin saida ya nutse a cikin ƙasa.
Anwar yayi kabbara ya ruga izuwa kanta da gudu.
Ba tare da ta zaro takobin nata ba, ta ɗago kai tana kallon Anwar tana yi masa murmushin mugunta.
Lokacin da ya rage saura bai fi taku goma ya iso inda take ba, sai ƙasa ta tsage wasu irin ƙwarangwal guda biyu s**a ratso cikinta s**a fito.
Kasusuwan jikinsu sun kasance ruwan toka. Daidai idanunsu wani shuɗin haske ne.
Cikin shammata ɗaya daga cikinsu yasa hannunsa ya ɗauke Anwar sannan yayi jifa dashi uwa-duniya.
Tun su Faurisa suna hango Anwar a sararin samaniya har sai da ya kule.
Waɗannan ƙwarangwal s**a yi wani ihu mara sauti sosai sannan s**a rugo izuwa kan Nabilà da Faurisa.
Nabilà ta sauƙe hannayenta sannan ta zaro takobinta ta dubi Faurisa tayi murmushi.
Kafun su cewa juna komai tuni waɗannan ƙwarangwal sun ƙaraso inda suke.
Jaruma Faurisa ta afkawa ɗaya daga cikinsu da yaƙi, itama Nabilà sai ta tari ɗaya.
Jaruma Faurisa tana yaƙi da Yirz dinta.
Sai da s**a shafe kusan sa'a guda suna fafatawa da waɗannan halittu amma basu kashe su ba.
Musamman jaruma Faurisa tafi Nabilà jikkata.
Nabilà ta karanto wata addu'a a ranta sannan ta sari kafaɗar ƙwarangwal ɗin.
Jikinsa ya narke ya zube ƙasa.
Nabilà ta sake karanto wata addu'ar tayi tsalle ta sari kafaɗar ɗayan. Shima ya narke ya zube ƙasa.
A lokacin s**a fuskanci sarauniya Amirza.
Amirza tayi dariya sannan ta jujjuya jikinta k**ar wata takobi.
Sai dai kafun ta afkawa su Faurisa, waɗansu mutane guda uku s**a bayyana a gabanta.
Bayyanarsu tayi matuƙar baiwa Amirza mamaki tamkar dama can suna wajen.
Ko kuma iskar wajen ce ta samar dasu.
Ko kuma haka kurum s**a bayyana.
Jaruma Riya. Gimbiya Firziyya. Helina [salsa:3].
Hohoho!
***
Next chapter on *11/05/2024* Insha'Allah

06/05/2024

RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 279-280: *Amirza mai Takobin Mutuwa*
*
★U★M★S★
*
Dedicated to Princess Fatima Zahra.
*
Copyright: ★RUHIN JARUMTAKA littafin yaƙi★
*
*
Lokacin da alfijir ya keto Yumani jo Kilzam da Lali San Rauzur basu dawo ba, sai hankalin Faiz zo Zarhak ya tashi. Amma sai ya tara dukkan mutanensa ya sanar dasu, kada wanda ya kuskura ya furta wannan abu da s**a aikata jiya da dare kuma a hankali zasu bincika su gano inda Yumani jo Kilzam yake.
Gari na wayewa aka kawo musu abincin kalaci na alfarma s**a cika cikin su. Bayan k**ar sa'a guda aka aiko daga fada ana kiran su.
Babu gardamar komai Faiz zo Zarhak da rundunarsa s**a yi shiga ta alfarma s**a je fadar.
Suna zuwa s**a iske manyan dakaru na ƙasar tsaitsaye a gaban karagar sarki. A gefensu kuwa, ga mutanen wannan attajiri wanda yace zai bayar da dukiyarsa gudunmawa a wannan yaƙi da ya taso.
A hasale sarkin ya dube su ya ce, "Jiya da dare 'yan fashi sun kai hari gidan attajiri Zarruna kuma har sun yi masa gagarumar illa. Saboda haka abu ne mawuyaci ya samu nutsuwar da zai iya bamu dukiyarsa. Ga mayaƙana guda dubu hudu zaratan gaske, ku tafi tare da su..."
Faiz zo Zarhak yana jin wannan batu fuskarsa ta cika alhini ya shiga jajantawa bisa wannan abu da ya faru.
Kuma nan take ya amince da wannan shawara ta sarkin.
Suna shirin tafiya kenan, s**a ga kekunan dawakai guda goma sha-ɗaya sun shigo cikin wannan fada cike maƙil da mak**an yaƙi da guzuri irin na mayaƙa.
Wani garjejen sadauki na zaune akan ingarman doki a gaba yana jagorantar su.
Mutumin yana sanye da fararen tufafi amma daidai ƙugunsa ya ɗaura wani kambu mai kaurin gaske.
Fuskarsa cike da annuri dukda cewa kana gani ka san bai kai zuci ba.
Wannan mutumi dai ba wani bane illa arnen daji Jasaran.
Ganinsa a wannan waje yayi matuƙar baiwa wannan sarki mamaki. Kafun wannan sarki yace wani abu tuni Jasaran ya riga shi yin magana.
"Rayuwa ta!
"Dukiya ta!!
"Fansa ce ga addinin musulunci. Zan taimaka iyakar iyawata wajen ganin mun yi nasara a wannan yaƙi.
"Ga gudunmawa ta a wannan yaƙi..."
Wannan sarki yana jin abinda Jasaran ya ce ya cika da tsananin farin ciki. Nan take yayi masa godiya.
Sarkin da kansa ya zabo zaratan jarumai guda dubu huɗu ya baiwa su Faiz zo Zarhak sannan ya sallame su s**a tafi. Saboda kwanakin da s**a rage a fara gwabza wannan yaƙi basu da yawa.
Faiz zo Zarhak da arnen daji Jasaran cikin ɓoyayyiyar siffa s**a jagoranci waɗannan dakaru s**a fice daga cikin daular Luhes s**a nausa cikin daji.
Shi dai arnen daji Jasaran har yanzu zuciyarsa kwakwanto take akan su waye Faiz zo Zarhak saboda bai gane su ba. Gashi sun ɓoye duk wata alama da zata nuna ainihin kabilarsu.
Amma ya ƙudurce a ransa zai gano ko su wane ne, ba da daɗewa ba.
A cikin waɗannan dakaru guda dubu hudu akwai yaransa guda talatin da ɗoriya. Jasaran yana matuƙar ji da waɗannan yara nasa.
A zahirin gaskiya Jasaran ba ƙaramar jarumtaka yayi ba domin kuwa a wannan rana aka gama gyara masa wannan rauni da Yumani jo Kilzam yayi masa.
Kawai baya so tawagar da za'a tura daular Babilá ta tafi, ba tare dashi bane shiyasa ya shigo cikin tafiyar dukda akwai rauni a jikinsa.
Faiz zo Zarhak ya riga ya gano Jasaran amma har zuwa wannan lokaci bai gano shirinsa ba. Ko kuma zaka iya cewa bai gano ainihin shirinsa ba.
Mene ne abinda ya haɗa Jasaran da daular Babilá har yake so ya yake su?
Wannan ita ce tambayar da Faiz zo Zarhak yake yiwa kansa. Amma bai samu mai amsa masa ita ba.
Haka dai wannan runduna ta ci gaba da tafiya suna tunkarar daular Babilá.
***
Al'amarin Lali San Rauzur kuwa, lokacin da ya fice daga cikin gidan arnen daji Jasaran ɗauke da Lisa Na akan kafaɗarsa sai ya ci gaba da sharara azababben gudu.
Mutanen Jasaran mutum shida suna biye dashi.
Rauzur yayi ta kutsawa ta cikin lunguna-lunguna da saƙo-saƙo na birnin Luhes tamkar tun da can ya san garin.
Hakan ne yasa waɗannan dakaru s**a gagara cimmasa amma dukda haka basu fasa bibiyarsa da gudu ba.
Tun da dare suke wannan gudu amma basu saurara ba har wajen ketowar alfijir.
A wannan lokaci tuni sun fice daga cikin birnin Luhes sun afka cikin ƙungurmin daji.
Suna shigowa cikin ƙungurmin daji salon tseren nasu ya sauya domin kuwa yaran arnen daji Jasaran ji s**a yi tamkar sun shigo gidansu.
Idan baka manta ba, arnan daji ne. Shi kuwa arnen daji babu abinda ya sani a rayuwarsa idan ba daji ba.
Tun tazarar dake tsakaninsu tana wajen taku ɗari shida har sai da ta dawo saura taku arba'in kacal.
Babban abinda ya taimakawa waɗannan mutane guda shida a wannan lokaci shi ne, tsananin nacinsu da kuma horon da s**a samu akan gudu.
Shi kuwa Rauzur wata irin gajiya ce ta rufe shi. Inda ace shi ɗaya ne yake wannan gudu da da sauƙi, to ga mace akan kafaɗarsa.
Suna cikin gudun, ɗaya daga cikin yaran arnen daji Jasaran ya jefe shi da ƙaton dutse a ka. Dutsen kuwa ya doki kansa da kansa.
Rauzur yayi taga-taga k**ar zai faɗi amma cikin tsananin jarumtaka ya dake sannan ya ci gaba da gudun.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai ya iso wani waje wanda babu hanya. Wata tafkeken dutse ya tare hanyar wucewa gaba ɗaya.
Rauzur yana zuwa wannan waje yayi turjiya sannan ya kwatar da Lisa Na a ƙasa, ya juyo ya fuskanci waɗannan mayaƙa guda shida.
A wannan lokaci in banda haki babu abinda Rauzur yake yi.
Mayaƙan nan guda shida s**a zaro takubbansu sannan s**a fara matso Rauzur a hankali.
Shima sai ya zaro takobinsa sannan ya tunkare su.
Suna haɗewa a tsakiya s**a ruguntsume da azababben yaƙi.
Waɗannan mayaƙa guda shida s**a rufe shi da sara da s**a. Shi kuwa ya fara kare kansa.
Ba'a ɗauki dogon lokaci ba s**a fara samun nasara akan Rauzur.
Wani abin mamaki da ya faru wanda hatta shi kansa Rauzur baiyi tsammani ba shi ne, bayyanar wani rikakken zaki.
Wannan rikakken zaki yayi tsalle ya turmushe mutum biyu daga cikin waɗannan mayaƙa kuma ya kashe su.
A wannan lokaci an yiwa Rauzur raunika manya har guda uku. Yana durƙushe akan gwiwowinsa yaga sauran mayaƙan guda huɗu sun mayar da hankalinsu wajen faɗa da wannan zaki.
Amma ina, wannan zaki fa yafi ƙarfinsu.
Koda Rauzur ya fuskanci cewa, abu ne mawuyaci ya tsira da rayuwarsa sai ya rarrafa ya ƙarasa inda Lisa Na take kwance.
Ya kwance jakar guzurinsa ya ajiye mata a kusa da ita sannan ya ajiye mata battar ruwa. Kawai sai ya ɗinga ɗebo busassun ganyaye yana binneta har sai da ya gama binneta yadda wannan zaki ba zai taɓa gano akwai mutum a wannan waje ba.
A wannan lokaci zakin ya gama karkashe waɗannan mayaƙa guda shida. Abinda ya sake baiwa Rauzur tsoro shi ne, yadda sara da s**a basa tasiri a jikin wannan zaki.
Rikakken zakin ya juyo ya fuskanci Rauzur. Sai da s**a yi kallon-kallo na tsahon daƙiƙu sannan ya dako tsalle ya turmushe Rauzur a ƙasa.
Dukda Rauzur yayi ƙoƙarin kwacewa amma ina tuni zakin ya riga ya kafa haƙoransa a wuyan jarumin.
Kafun a ɗauki tsawon lokaci tuni Rauzur ya mutu.
A wannan waje waɗannan mutane s**a mutu gaba ɗaya. Saboda dabarar da Rauzur yayi wajen ɓoye Lisa Na zakin bai ganta ba.
Ɗaya bayan ɗaya wannan zaki ya ɗinga zuwa yana ɗauke gawarwakinsu har sai da ya ɗauke su gaba ɗaya.
Wannan shi ne abinda ya faru a wannan waje.
Shin Lisa Na zata tsira da rayuwarta kuwa?
Shin ya ya rayuwarta zata kasance?
***
~Garin Amirza.
***
Gashin kanta yana kaɗawa a cikin iska da hasken rana. Da zaka samu dama ka shafa wannan gashi da zaka ji sanyi na musamman a tattare dashi.
Kaifaffun idanunta masu cike da kafiya da tsohon buri na kafe akan abinda take kallo. Zanen baƙar takobi ta maye gurbin ƙwayar idanun ta na dama. Julbat he dayi kuwa, ya maye gurbin ƙwayar idanun ta na hagu.
Mace mai siffar takobi. Mai rawar takobi. Sarauniya Amirza.
Lokaci na ƙarshe da muka kalli wannan mace, lokacin da ake shirye-shiryen yaƙi tsakanin Babilá da ɓangaren sadauki Rairud ne.
A wannan lokaci ta ci alwashin shiga wannan yaƙi domin kashe 'ya'yan Husen da iyalan sarki Ƙuzzurus.
Saboda haka abu ne mai sauƙi ka kintaci abinda take yi a yanzu.
Wani ƙaramin mudubi ne a hannunta tana kallon wani abu dake faruwa.
*
Gawarwaki ne na mayaƙa sun cika filin yaƙi fululu. Ko'ina Amirza ta duba waɗannan gawarwaki ne.
Daga can gefensu kuwa, sansanin mayaƙa ne guda biyu masu fuskantar juna.
Sarauniya Amirza ta saka 'yan yatsunta tana shafa wannan mudubi. Abubuwa s**a ci gaba da sassauyawa.
Da farko, sansanin sadauki Rairud aka nuno.
Sadaukin yana zaune akan wata kujera cikin tsananin baƙin ciki da ƙunar zuciya. Idanunsa sun kaɗa sunyi jajawur.
Ga zabgegiyar takobinsa ɗaure a wuyansa yana jira gari ya gama wayewa.
Amirza tayi arba da tarin mayaƙa a gaban wannan sansani sun jeru sunyi sahu-sahu.
Wani irin murmushin mugunta ya gilma ta gefen bakinta ta sake shafan wannan mudubi.
Anan kuma sai tayi arba da su sarki Antaru, Hassan Saif, Anwar da Nabilà suna zazzaune suna tattaunawa.
Koda kaifaffun idanunta s**a dira akan Anwar sai wani irin baƙin ciki ya turnuƙe ta. Nan take yanayinta ya sauya.
Marmarin yaƙi da tsohon buri na ɗaukar fansa ya fara kaɗawa ta cikin idanunta.
Amirza ta mayar da wannan mudubi cikin aljihunta sannan ta miƙe tsaye.
A lissafinta nan da cikar sa'a guda waɗannan ɓangarori guda biyu zasu ruguntsume da azababben yaƙi.
Daga wannan waje da take zuwa wannan filin yaƙi tafiyar sa'a bakwai ce kacal.
Saboda haka zata isa wannan fili ana tsaka da gwabza wannan yaƙi.
Amirza ta rintse idanunta na dama sannan ta ɗaga hannunta na hagu akan iska.
"Takobin Mutuwa!" inji Amirza.
Nan take iska ta tsage wata zabgegiyar takobi baƙa ƙirim ta ratso iskar ta dira akan hannunta.
Sarauniyar tana buɗe idanun nata gaba ɗaya s**a shafe. Babu zanen takubban sannan babu baƙin. Hasalima wani irin baƙi mai ban tsoro idanuwan s**a yi ko alamun fari baka hangowa.
Amirza ta motsa wannan takobi.
Kamar ana motsa haske a cikin duhu haka inuwar duhun wannan takobi ya ringa raguwa a cikin hasken dake wajen.
"Haha..." Amirza tayi dariya.
Sarauniya Amirza tana ƙoƙarin tashi sama ta ɓace a cikin gajimare ta hango wani ƙatoton jirgin ruwa a sama yana lulluƙawa tamkar a cikin teku.
Koda ta hango wannan jirgi sai ta fasa tashi sama sannan ta durƙusa akan gwiwarta guda tayi biyayya.
Jirgin ruwa ne mai launin toka. Yana tafiya a cikin iska tamkar wanda ke tafiya a cikin teku.
"Mu haɗu a daular Ems!" inji Amirza.
Muryarta na fita da wani irin marmari na musamman tamkar burinta a duniya bai wuce zuwa daular Ems ba.
Tun tana hango wannan jirgi har sai da ya ɓace a cikin duhun giza-gizai.
Sarauniya Amirza ta doki ƙasa da sahunta guda. Nan take ta juye izuwa Julbat he dayi.
Mashin ya cilla da gudu a cikin sararin samaniya ya fara tsala azababben gudu.
***
~Filin yaƙin Amru.
~Daular Babilá.
***
Sadauki Rairud na tsaye a gaban mayaƙansa tsaye akan sawayensa. Yana rataye da zabgegiyar takobinsa a wuya. Ga wasu mak**an yaƙin barkatai a sassa da dama na jikinsa.
Idanuwansa suna tsaye cak akan Anwar.
Yaran arnen daji Jasaran suna tsaitsaye a bayansa amma kasancewar sun yi shiga irinta mayaƙansa, ba lallai ne ka shaida su ba.
A wannan rana babu sulhu ko kuma ka-ce-na-ce. Abu guda da zai faru kuma Rairud da kansa ya yarda da shi shine, ZUBAR DA JINI.
Bayan k**ar rabin sa'a aka busa wani ƙaho mai ƙarar tsiya wanda ya cika wannan daji gaba ɗaya da amsa kuwwa.
Sadauki Rairud da mayakansa suna jin ƙarar wannan ƙaho s**a runtuma da azababben gudu s**a ruga kan musulmai.
Kafun su riski inda su Anwar, Nabilà, Antaru da Hassan Saif suke tuni an fara yi musu ruwan kibbau daga sararin samaniya.
Haka kuma ababen fashewa s**a faɗowa daga sama suna bindiga suna karkashe su.
Amma saboda masifar yawan mayaƙan Rairud tamkar babu abinda ake ragewa a cikinsu.
Sarki Antaru ya dubi Hassan Saif ya ce, "Ka jagoranci dakarun mu ku tarwatsa waɗannan kafurai."
Ya juya ya dubi Anwar da Nabilà ya ce, "Ku taimaka musu wajen ganin mun samu nasara."
Sarki Antaru ya juyo ya dubi Rairud ya ce, "Ni kuma ku barni da wancan ƙaton kafurin!"
Masifa da bala'in dake tunkaro su, bata bari sun yi jayayya akan wannan umarni na sarki Antaru dukda a ganin Anwar wannan tsari sam baiyi ba.
To, amma lokaci ya riga ya ƙure. Tuni kaso na farko daga cikin dakarun Rairud sun iso su saboda haka sai s**a yi kabbara kawai s**a zaro takubbansu sannan s**a ruguntsume da azababben yaƙi.
Kaico! Ya yin da sadauki Rairud ya samu nasarar shiga cikin rundunarsu sai ya fara yin muguwar ɓarna.
Duk inda sadaukin ya saka a gabansa sai dai kaga sassan jikin bil'adama suna ta yawo suna zubowa ƙasa.
Jini ya fara tsartuwa da kwarara izuwa ƙas.
Tun daga kan mutum na farko ya fara amma sai da ya dangana da na ƙarshe dake layin.
Yana ƙoƙarin shiga wani layi kenan, Antaru yayi tsalle ya dira a gabansa.
A wannan lokaci tuni Hassan Saif, Anwar da Nabilà sun daɗe da nutsewa a cikin kafurai.
Duk inda waɗannan jarumai guda uku s**a saka a gaba sai dai kaga mazaje suna zubewa ƙasa matattu.
A wannan lokaci salon wannan yaƙi ya sauya.
Shigowar dakarun arnen daji Jasaran yayi matuƙar sauya akalar yaƙin. Saboda zaratan gaske ne kuma marasa imani.
Saboda haka su ma zubar da jini suke tamkar babu gobe.
Ana cikin wannan hali Hassan Saif ya lura da irin ɓarnar da waɗannan arnan daji suke yi.
Kawai sai yayi kabbara ya daka tsalle ya dira a tsakiyarsu.
Take s**a yanyame shi da sara da s**a. Amma sai ya shiga tarwatsa su da ƙarfin tsiya, yana sare su da takobinsa.
Saif-Al-Jazeera! Duk wanda Anwar ya samu nasarar sara da wannan takobi sai kaga yayi wata irin mutuwa mai ban tsoro.
Irin mutuwar da cikin sauƙi zaka iya gane gawarwakin da Anwar ya kashe a wajen.
Jarumin yana da baƙin zafin nama da tsananin karfi.
Babu wanda waɗannan mayaƙa s**a fi lulluɓewa a wannan filin yaƙi kuma babu wanda ya kai Anwar yi musu barna.
Sai da aka shafe kusan daƙiƙu ɗari biyu da goma ana kallon-kallo tsakanin sadauki Rairud da sarki Antaru.
Sadauki Rairud ya juya wajen da Anwar keta ragargazar mayaƙansa kawai sai zuciyarsa ta ci gaba da tafarfasa.
Ya kwaɗa uban ihu sannan ya ruga kan sarki Antaru s**a ruguntsume da azababben yaƙi.
Sadaukan guda biyu s**a wanzu suna masu kaiwa junansu muggan sara da s**a cikin baƙin zafin zama da tsananin kwarewa.
Tun da sarki Antaru yake gumurzu da mazaje bai taɓa haɗuwa da zarton jarumi k**ar Rairud.
Sadauki Rairud yana da tsananin ƙarfin damtse, baƙin zafin nama da zallar iya yaƙi.
Tunkarar sadauki Rairud a wannan lokaci sai cikakken jarumi.
Kai inda ace da ƙaramin jarumi Rairud yake wannan fafatawa da tuni ya gama da shi.
Shi kansa Antarun faɗan nasu mai ban tsoro ta yadda baka isa ka kintaci abinda zai faru gaba ba. Saboda komai zai iya faruwa.
Im ma dai ɗaya daga cikinsu yayi nasara ko kuma suyi ragas.
Suna cikin wannan fafatawa sadauki Rairud ya tale sawayensa biyu yayi ƙasa sannan ya doki ƙasa da tafin hannunsa guda.
Lamarin da yasa yayi sama tamkar wanda aka harbo kenan, yayi wata alkafira a sama ya samu nasarar kaftawa Antaru sara a kafaɗa.
Lokaci guda kuma ya sake samun nasarar saka gwiwar ƙafarsa ya doki gadon bayan Antaru.
Antaru yayi kabbara da ƙarfi lokacin da jini yayi tsartuwa daga cikin raunin dake kan kafaɗarsa.
Amma cikin tsananin ƙwarewa da salo shima ya shammaci Rairud ya yi masa wawan sara a ƙirji.
Kasancewar akwai sulke a jikin Rairud raunin baiyi zurfi sosai ba amma sai da ya raba sulken gida biyu.
A wannan lokaci dukkansu sai s**a ja baya s**a fara duban juna zuru-zuru. Kana gani ka san lissafi kowa yake a cikin su akan yadda zai kashe ɗan uwansa.
***
A can wani waje mara nisa sosai daga dajin Amru, wani irin azababben yaƙi ne ake gwabzawa.
Ana fafata wannan yaƙi tsakanin arnen daji Jasaran da Faiz zo Zarhak.
Bari mu koma sa'a uku kafun a fara wannan yaƙi.
Rundunar da ta taso daga daular Luhes ta dakarun gudunmawa tana tafe tana tunkarar daular Babilá.
Dukda cewa Jasaran da Faiz zo Zarhak ne akan gaba amma babu wata tattaunawa da take gudana a tsakaninsu sosai.
Wani abin mamaki a wannan lokaci sai aka kawo musu farmaki. Wasu 'yan fashi dake cikin wani daji.
Suna cikin ragargazar 'yan fashin ne idanun Jasaran s**a dira akan wani hatimi da aka zana a bayan wuyan Faiz zo Zarhak.
Dama ɗan leƙen asirinsa da yake cikin kabilar Oros ya taɓa shi labarin wannan hatimi.
Ana amfani da wannan hatimi ne wajen gano shugaban wannan ƙabila.
Suna gama ƙarar da waɗannan 'yan fashi. Arnen daji Jasaran ya tuno irin abinda Yumani jo Kilzam yayi masa, kawai sai zuciyarsa ta tafarfasa ya yi kukan kura ya afkawa rundunar Faiz zo Zarhak da yaƙi.
Cikin daƙiƙa metan ya sare mutum goma.
Faiz zo Zarhak ya kwarara uban ihu ya tari ɗan fashin s**a fara gwabzawa.
Jaruman guda biyu s**a wanzu suna masu gwabza yaki a tsakaninsu.
Yaran arnen daji Jasaran s**a yi tsalle s**a dira a tsakiyar rundunar Oros s**a shiga karkashe su.
Kafun kace kwabo fa tuni wannan waje ya rincaɓe da azababben yaƙi.
Kasuwar rayuka ta buɗe. Ƙarar karafkiyar takubba ta cika dodon kunne.
Dakarun da s**a taso daga daular Luhes s**a rasa yadda zasuyi su raba wannan faɗa wanda basu san abinda ya haddasa shi ba.
A ƙoƙarin rabiyar wajen mutum goma daga cikinsu s**a mutu.
Saboda wannan dalili babban cikinsu ya kirasu gefe guda s**a fara tattaunawa akan yadda zasu shawo kan al'amarin.
A ɓangaren Faiz zo Zarhak da Jasaran har zuwa wannan lokaci ana ta fafatawa.
Dukda cewa sun yiwa junansu muggan raunika amma saboda tsananin jarumtaka da daɗewa sun ƙi faɗuwa ƙasa.
Wannan kenan!
***
Ya yin da aka yi kallon-kallo na ɗan lokaci tsakanin Antaru da Rairud sai s**a rugo da gudu izuwa kan juna.
Koda ya rage saura taku goma su haɗu a tsakiya sai s**a dako tsalle sama s**a kaiwa juna muggan hare-hare.
Sarki Antaru ya samu nasarar fille hannun sadauki Rairud na dama, shi kuwa Rairud sai ya samu nasarar caka masa takobi a ciki har ta faso ta baya.
Dukkansu s**a faɗo ƙasa suna masu kwarara uban ihu.
Lamarin da ya jawo hankalin jama'ar dake wajen kansu.
A wannan lokaci jikin Hassan Saif ma yayi kaca-kaca da raunika amma ya yiwa yaran arnen daji Jasaran muguwar ɓarna kuma ya kusa ƙarar dasu.
Sai dai zai yi wahala ya rayu saboda yawan jinin dake zuba daga jikinsa.
Koda Nabilà da Anwar s**a halin da 'yan uwansu suke ciki sai s**a kwarara kabbara s**a tarwatsa mayaƙan dake lulluɓe dasu sannan s**a ruga izuwa kan su Hassan Saif da Antaru.
Sarki Antaru yafi Rairud jikkata saboda raunin da sadauki Rairud yayi masa ya hana shi miƙewa koda tsaye, yana durƙushe akan gwiwowinsa.
Shi kuwa Rairud cikin tsananin jarumtaka ya miƙe tsaye yana dogara takobinsa k**ar sanda ya tunkari inda Antaru ke durƙushe zai ƙarasa shi.
Akwai tazara mai yawan gaske tsakaninsu da su Anwar saboda haka abu ne mawuyaci su ceci rayuwar Antaru daga sharrinsa.
Sadauki Rairud ya daidaita kaifin takobinsa a wuyan Antaru.
Cikin zafin nama ya ɗaga takobinsa zai sare kan Antaru.
Sai dai a lokacin wani gagarumin sanyi mai k**a da na hunturu ya ziyarci wannan daji.
Lamarin da yasa da dama daga cikin mayaƙan dake wannan daji karkarwa kenan.
Ba zato ba tsammani! Aka jiwo ihun sadauki Rairud ya cika dodon kunne a lokaci guda kuma aka jiwo muryar sarki Antaru ta maimaita kalmar shahada.
Sai da aka tsayar da duk abinda ake a wannan filin yaƙi aka juya domin ganin abinda ke faruwa.
Nan take aka yi arba da wani dogon mashi ya caki ƙirjin sadauki Rairud sannan ya taho ya caki ƙirjin Antaru.
Dukkansu sun mutu kuma fatar jikinsu ta sauya launi.
Anwar yana ganin wannan mashi ya kirawo sunayen Allah sannan ya dubi Nabilà ya ce.
"Sarauniya Amirza ce!"
Kafun Nabilà ta tambaye shi wacece Amirza sai s**a jiwo Hassan Saif yana nishi da ƙarfi.
Cikin gaggawa s**a ruga izuwa inda yake.
Hassan Saif ya dube su ya ce.
"Ya ku yara manyan gobe...
"A yau manyan ku sunyi shahada domin kare daular Babilá.
"Za kuyi nasara a wannan yaƙi da izinin Allah sannan ku ci gaba da tabbatar da adalci a Babilá..."
Dattijon yana gama faɗin haka ya maimaita kalmar shahada shima ya cika.
Ganin mutuwar Antaru da Hassan Saif yasa zuciyar Nabilà karaya ta fashe da kuka.
Anwar ya shiga rarrashinta.
Dukkan jama'ar dake wannan daji sai da s**a razana bisa ganin wannan mashi.
A hankali mashin ya zare kansa daga gangar jikin Rairud da Antaru.
Mutanen biyu s**a zube ƙasa matattu.
Wannan mashi yayi girgiza ya juye izuwa siffar Amirza.
Gashin kanta yana kaɗawa a cikin iska. Komai na jikinta tsarinsa da zubinsa duk irin na takobi ne.
Mace mai siffar takobi!
Tana riƙe da zabgegiyar takobi baƙa ƙirim a hannunta. Takobin Mutuwa.
Hohoho! Ita kanta masifa da bala'i ce ballantana kuma ace tana riƙe da Takobin Mutuwa.
"Yau rana ta ce," inji sarauniya Amirza. "Ko babu komai na fara da ƙafar dama tun da na kashe jinin Ƙuzzurus da jinin Husen!"
Tana gama faɗin haka ta nuna Anwar da Takobin Mutuwa ta ce.
"Ka kashe Sinaragail Ajalin!
"Ka kashe Idjilma'il Ajalin!!
"Ka kashe masoyina Nurban!!!
"Yau nayi rantsuwa da kabarin yaya Zarnail Ajalin sai na ƙarar daku, koda kuwa shi kansa Shamsuddin din zai dawo.
"Bai isa ya hana abinda zai faru ba..."
Anwar ya gyara riƙe Saif-Al-Jazeera sannan ya fuskanci Amirza.
"Na dade ina jiran wannan rana, ranar da zan yi gaba da gaba dake...
"Da izinin Allah sai nayi maganinki k**ar yadda nayi maganin 'yan uwanki...
"Idan kin isa kuma kin cika jaruma, a yau kada ki gudu!!!"
Sarauniya Amirza tana jin wannan batu zuciyarta ta ci gaba da tafarfasa.
***
Yau *06/05/2024*
Babi na gaba zaizo *09/05/2024* INSHA'ALLAH.

Address

Sangaru Street
Gombe

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ruhin Jarumtaka littafin yaki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ruhin Jarumtaka littafin yaki:

Share

Category



You may also like