JIYA DA YAU

JIYA DA YAU Ku Kasance Damu Zamu Dinga Kawo Muku Ingantattun Abubuwa A Koda Yaushe ���Kasance Damu,

17/07/2022
KARIN HOTUNA: Yadda Gagarumin Taron Ƙarawa Juna Sani "National Seminar" Na Kwanaki Biyu Ya Gudana Tare Da Bikin Cikar Ƙu...
17/07/2022

KARIN HOTUNA: Yadda Gagarumin Taron Ƙarawa Juna Sani "National Seminar" Na Kwanaki Biyu Ya Gudana Tare Da Bikin Cikar Ƙungiyar Shekaru Biyu Ya Kasance A Jiya Asabar

A yayin gudanar da taron, an gabatar da maƙaloli masu muhimmanci kamar haka:-

1, Hanyoyin yaƙi da labaran ƙarya a kafofin sada zumunta, wanda shahararran ƙwararran ɗan Jarida Isma'il Karatu Abdullahi ya gabatar da maƙalar.

2, Yadda ake rubutu da aikin Jarida, na yaɗa labarai a kafofin sada zumunta, wanda shahararran ƙwararran dan jarida Shu'aibu Abdullahi Dimokuraɗiyya ya gabatar da maƙalar.

3, Yadda ake neman kuɗi, aiki a kafofin sada zumunta, shahararran gogaggen ɗan jarida Haji Shehu ya gabatar da maƙalar.

Wurin taro; Babban ɗakin taro mai suna Banquet Hall, dake babban masaukin baƙi na ƙasa da ƙasa Zaranda Hotel, cikin kwaryar jihar Bauchi.

17/07/2022

Wannan bawan Allah sunan sa Sheikh Adil Al-Kalbani, yana ɗaya daga cikin limaman Harami. Kamar yadda Marigayi Sheikh Dr. Ahmad Bamba ya faɗa, idan yana karatun Qur'ani sai ya sa ka yi kuka. (Tabbas na saurari karatunsa, kuma karatun ya tsumani).

A ƙarshe ya zama ɗan casu. Annabi ﷺ Ya gama magana da Ya ce zira'i kan ragewa mutum ya shiga Aljannah ko Wuta, sai ƙaddara ta yi aiki a kansa; ya zama ya sami sauyin makoma. Saboda hakan ne ma Annabi ﷺ Ya koyar da mu addu'o'in neman shiriya da tabbata a kan biyayya ga Allah (S.W.T), kamar:

اللهم يامصرف القلوب صرف قلوبنا على طاعتک

Ma'ana: Ya Ubangiji, Mai jujjuya zukata, Ka tabbatar da zukatanmu a kan biyayya a gare Ka.

Ko kuma:
اللهم يامقلب القلوب ثبت قلبي على دينك

Ma'ana: Ya Ubangiji, Mai jujjuya zukata, Ka tabbatar da zuciyata a kan Addininka.

Ya Allah Ka tabbatar da mu bisa Addininka da biyayyarka, shi kuma wannan bawan Allah, muna roƙon Allah (S.W.T) Ya shirye shi. Amin

©️ Aly A. Idreess

17/07/2022
13/07/2021

Y A U B A N G I J I!
Mun kasance masu aikata laifuka gareka, muna neman Afuwar ka da gafartarka ka gafarta mana ka yi rahama a garemu,
YA ARHAMAR RAHIMIN’ "YA RABBU!
Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta.

YA Al-AHAD
Kayi salati ga Annabi Muhammadu da iyalansa da sahabbansa. Allah ka sadar da mu baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.

YA AS-SAMAD
ka daukaka musulunci da musulmai, kuma ka kaskantar da kafirci da kafirai. Ka bamu kariya daga abokan gaba.

YA HAYYU YA QAYYUM.
ka sanya kasar mu Nigeria cikin alkairi da aminci, zama lafiya da wadata da yalwa, ka shiryemu ka shiryar da shugabannimu.
ZUL-JALAALI WAL-IKRAAM!

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai JinkaiAssalamu Alaikum. Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!AlhamdulillahiDuniya...
13/03/2021

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum.

Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!

Alhamdulillahi

Duniya ku shaida, al'ummah, ku tabbatar, cewa an tabbatar wa da masoyin mu, mai martaba, Khalifah Muhammadu Sanusi II khalifancin Tijjaniyyah. A jiyan nan, ranar Juma'ah, 12/03/2021, Sheikh Makki Inyass yayi sanarwa a wurin gabatar da Zikiri, a gidan Gwamnatin jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Ku rubuta wannan, ku ajiye cikin kundin tarihi.

Kuma wadanda ba 'yan Tijjaniyah ba ku sani, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi kadai, wanda ba ya da abokin tarayya, cewa kar ku dauka cewa Sarki Muhammadu Sanusi II na 'yan Tijjaniyah ne kadai, saboda an tabbatar masa da Khalifancin Tijjaniya, a'a, sam ba haka bane. Sarki na kowa ne, shi shugaban kowa da kowa ne, kai har da ma wadanda ba musulmi ba, iyakar ta kenan. Don haka, ku kwantar da hankalin ku, Sarki yana nan tare da ku koda yaushe, komai wuya komai dadi. Farin cikin ku nasa ne, kuma damuwar ku damuwar sa ce.

Allah yasa mu dace, amin.

Juma'ah, 12/03/2021.

Daga Sa'ad Nura Azare

Address

Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JIYA DA YAU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to JIYA DA YAU:

Share



You may also like