08/05/2022
TSOKACIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) KAN HALIN DA KASA KE CIKI
"Wannan irin ƙasa, mutane suna ta ɓaganniya, ana yaƙarku amma ba ku gane ba. (Ana kaɗa ku) kamar shanu. Ka san saniya ina ruwanta in ma ƙwata za a kai ta (a yanka)? Ana tafiya tana cin ciyawarta.... Amma mutum wanda yake da hankali, kuna gani ana neman a ƙarisa ku, a gurgunta ku da ƙarfin tsiya.
"Har ma an riga an gama gurguntawar, ana ta ta yi ne, kudinku baya sayan komai. A 1980 Dala 1 ne Naira 2, Yanzu Naira 570+ ne Dala 1, amma da kuwa Naira 2 ne Dala 1. To kuma amma wai mu ke da 'Golden Zone', amma kudinmu bai da daraja.
"Mu nan irin diban 'Gold' din da suke a kewayen Zamfara din nan, Helicopters suke zuwa da shi su yi ta diba, har mutane sai su ce sun ji karar jirgin sama, wasu Helicoptoci ne, kuma 'Gold' ake diba a yi waje da su, ba tare da biyan ko kwabo ba. Kuma su wadanda ake cewa shugabannin sun sani. Su abin da ya dame su kawai a basu nasu kason.
"Kuma ni na lura magana ma in ka yi ma (kamar) ba amfani, saboda su mutanen kasar nan ma in ka yi maganar ma suna cewa kai mahaukaci ne. Wata rana da nake magana din nan, su wadanda nake maganar don su lura amma ba su damu ba, amma sai aka ce har wani General ya daki tebur, yace wannan mutumin 'is dangerous!' ka ga yana magana da talakawa ne. Lokacin da nake cewa ku gane ba wata Boko Haram, mai suke diba, yanzu haka akwai rijiyar mai 25 a Borno, mai ake diba. Shine ya bugi Tebur yana cewa akwai hadari don ana fadawa talakawa ne. To su kuma talakawar ba su damu ba ma....
"Wato muna wata irin kasa ce da komai ya faru, in musiba ta samu wani mutum, sai ka ga kamar ma har murna suke yi. Sai su yi ta murna. Ka san da ban mamaki ko? Idan musiba ta samu wani sai ka ga wani yana murna. Shima sai tasa ta zo, sai ya yi bakin ciki, sai wani kuma shima ya masa murna. Sai ta je ga wancan, ka ga ba wanda ya san yaushe za ta kare kenan.
"Yanzu wa ya san ya al'amari zai kasance nan da baɗi, ko kuma bayan shekara biyu zuwa uku? Tunda abubuwan suna gudu ne ba kadan ba, gudu suke ba kadan ba. Da ana bin jirgin kasa, an fi aminci, to yanzu jirgin kasan ka ga abin da s**a yi masa. To daga nan kuma ka ga yanzu ba aminci kenan a jirgin ma ko da an gyara shi....
"Su abin da kowanne (daga Mahukuntan Kasar nan) yake da bukata shine a bashi mukami, ala bashi a yi duk abin da aka ga dama. Ko me aka ga dama a yi, shi dai a bashi mukami. To. Idan ka ce ga mafita, mutane s**a ce ba haka nan bane. Ya za ka yi da su? Ba sai ka kyale su ba? Muce to shikenan ku nemi mafita inda za ku samu. Amma an ce musu ga mafitar, sun ce ba haka bane.
"Wasu su kan ce eh gaskiyarka ne, musulunci din ne mafita, amma fa kai kana nufin Shi'a ne, mu kuma ba za mu yi Shi'a ba. Ta wani dan Tawayiyya yace, wai yanzu in ma aka yi 'revolution' a kasar nan za a kafa Gwamnatin Shi'a ne, shi kuma da a yi shiaa gara ma a cigaba da Dimukuradiyyar. Yace gara 'Statuesque' da ISLAM wanda shi a wajensa sunansa Shi'a. To sai mu ce ai ba wata matsala, kai ka yi Sunnah Islam din mana. Shi kuma ba zai yi ba. Sunnah Islam din nasa shine ya bi azzalumai. Ya samu nasa kason.
"To yanzu kuma na ga ko a Shi'a din ma abin da (wasu) suke ta matsawa a kan mu kenan. Wai sai mu hada kai da azzalumai mu rayu. Shi kuma azzalumi ba ruwansa shi, ko me ka masa, ko Sujjada ka masa ma yanka ka zai yi. Ko Sujjada ka masa, kace yanzu ka tuba ka mai she shi ubangiji, zai ce kai Sujada mu gani. In ka yi ya dauko bindiga (ya nemi ya kashe ka). Duk abin da ka masa ba zai ta a yarda da kai ba (matukar ka taba masa bara'a). Amma ta yiwu in tun farko dama baka masa tawaye ba, kana tare da shi ne, ya zama ka samu rabonka a wajensa....."
— Yanki daga bayanan Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) yayin ganawa da Maziyarta a ranar Juma'a 6 ga Shawwal 1443 (6/5/2022).
08/05/2022