Zauran Nasiha Tv

Zauran Nasiha Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zauran Nasiha Tv, TV Channel, Nassarawa Jahun Near Al'ameen Hospital Bauchi, Bauchi.

Assalamu Alaikum We Post Islamic Lecture Videos and Qur'an Recitation From Our Scholars Here and Other Country "TUNATARWA CIKIN VIDEO" Shine Manufar Mu Akullum, ALLAH Yasa Muyi Taraiyya Daku A Aljanna

31/07/2024

ALLAH Yasa Mu Cikin Wadannan Mutane

Assalamu Alaikum warahmatullah.Ƴan'uwa ku sanya Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum acikin Addu'o'inku! Yau kusan sati ke...
17/07/2024

Assalamu Alaikum warahmatullah.

Ƴan'uwa ku sanya Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum acikin Addu'o'inku!

Yau kusan sati kenan malam bayida lafiya, wannan nema dalilin da yasa ba'ayi karatu ba ranar Litinin, kuma yauma bisa dukkan alamu zayyi wahala ayi karatu saboda yanayin jikin.

Allah ya bawa malam lafiya, yasa kaffara ne.

ROƘO GA DUKKAN MALAMAIMuna roko ga Malamai su shiga tsakani k**ar yadda s**a shiga a Nijar. Lallai su nemi ganin shugaba...
14/07/2024

ROƘO GA DUKKAN MALAMAI

Muna roko ga Malamai su shiga tsakani k**ar yadda s**a shiga a Nijar. Lallai su nemi ganin shugaban Ƙasa, da shugaban majalisar dattijai, da na wakilai, da shugaban majalisar gwabnoni, da duk masu faɗa a ji, a gaya musu gaskiya domin kawo ƙarshen wannan tirka-tirka. Aci gaba da haƙuri da aiki.

~ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

WASIKA ZUWA GA MALAMAI!!Assalamu alaikum,Barka da safiya, Yaya iyalai da gwagwarmaya.Hakika sunan da ku ka amsa na magad...
14/07/2024

WASIKA ZUWA GA MALAMAI!!

Assalamu alaikum,

Barka da safiya, Yaya iyalai da gwagwarmaya.

Hakika sunan da ku ka amsa na magada Annabawa ba a banza ku ka cancaceshi ba, Bayan wahalar neman Ilimi da dawainiyar rike wannan kambu, Ku kara juriya, kar s**ar kayoyi da za ku ringa takawa don hawa tsaunin gaskiya ya sa ku ja da baya.

Malaimana fitilar rayuwata, k**ar yadda kowane Allazi da na sa Amanu, Haka kowane Zamani da irin ta sa Fitinar, Fitinar wannan zamanin babu k**ar Social Media.

Iyayena kar ku hangi hayagagar cikin wannan dandali a matsayin mahangar mabiyanku a kanku da Da'awarku bisa hakika, domin wadanda ke cin zarafinku da yi muku kazafi da zarafi, da ma can hamayya su ke da kiranku, duk da yake akwai yan kadan da ke tare da kiranku.

Fusatar da wassu ke yi da ashariya yana gwada tasiri da isar sakonku zuwa yanda kuka aikashi da tsoratarsu ga karbuwarsa domin hakan barazana ce ga manufofinsu.

Malamaina, Kar wanda son zuciyarsa ko siyasa da duniyarsa ke ingizashi don cin zarafinku ya hanaku fada musu abinda ke littafi don su Makafi ne ku ne masu gani, Marasa lafiya ne kune likitocin zuciyarsu.

Ku yafe musu kan shiga hakkinku da su ka yi tare da muku jafa'i, Hakan zai fi tara muku lada a wajen Allah kan gwanjon kayansu da za a yi ran Qiyamah.

Allah ya saka muku da gida. a Aljannah.

Nima ina fatan zamowa irinku, Allah ka shaida na yafewa mai ganganci da kuskure. Wanda ya gabata da wanda za a yi nan gaba.

Dalibinku mai biyayya
Ibrahim Disina

13/07/2024

Iya Maslahar Hada Sallah Cikin Daminan Nan, Malamai Basu Tsira Ba

Me Yasa Haka Ne ?
😔

09/07/2024

Saurara Kaji Wataqila Ka Karu

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

05/07/2024

ALLAH Kasa Mu Cika Da Imani 🤲

Kada kace: Yaushe wannan al'umma za ta gyaru ne?Gyara yana farawa ne daga kan ka, domin kai ma ɗaya ne cikin al'umma.Ka ...
27/06/2024

Kada kace: Yaushe wannan al'umma za ta gyaru ne?
Gyara yana farawa ne daga kan ka, domin kai ma ɗaya ne cikin al'umma.
Ka gyara, ki gyara, in gyara, mu gyara, su gyara yana nufin ɓangarori da dama na al'umma ya gyaru kenan!

Zainab Ja'afar Mahmud ✍️

Asslm alkm,Yazo a sunnah ana son kowa yana wannan addu'ar"Allah ka sanya albarka cikin abinda ka bani"Da haka ne zamu am...
25/06/2024

Asslm alkm,
Yazo a sunnah ana son kowa yana wannan addu'ar

"Allah ka sanya albarka cikin abinda ka bani"

Da haka ne zamu amfana da ni'imar Mulki, Dukiya, lafiya, Aure, Karatu, 'ya'ya, Kasuwanci, Fasaha da sauran ni'imomin da Allah ke yiwa bayin sa

Rashin yin irin wannan addu'ar ne kesa ayi wa bawa ni'ima amma ta zama jarrabawa da masifa ko sanadin halaka da kunci a gareshi

Ya Allah ka karawa rayuwar mu albarka ka tsare mana imanin mu da mutumcin mu

Allah ka tsare mu daga mummunar QADDARA ka bamu dacewa duniya da lahira, amin

Daga Shafin Aliyu Sa'id Gamawa

16/06/2024

Taqabballahu Minna Wa Minkum
😊🙏

YAU TAKE ARAFAH..!! A duk rayuwarka ba ka da rana k**ar yau. Duk wata addu’a ba ta kai ta yau ba. Ballantana kuma yawan ...
15/06/2024

YAU TAKE ARAFAH..!!

A duk rayuwarka ba ka da rana k**ar yau. Duk wata addu’a ba ta kai ta yau ba. Ballantana kuma yawan maimaita hailala.

Yi addu’a cikin qanqan da kai da zubewa a gaban Allah. Kayi naci, magiya, fadanci. Ka roqi gafara tare da fashewa da kuka in zai yiwu. Kuma zai yiwu din. Ka yi wa addu’a cin yunwa.

Ka roqi Allah tare da yaqinin zai amsa maka. Ka tuna fa! Kana roqon mahaliccin sammai da qassai ne mai juya duniya, wanda ba abun da ya gagareShi.

Wadanda ba alhazai ba ku roqi Allah ya karbi azuminku. Duk wanda aka karbi azuminsa na yau tabbas ya more. Su kuwa mahajjata idan aka karbi aikinsu to qarshen magana kenan. (End of discussion).

Allah ya biya muku dukkan buqatunku, ya yaye muku duk wata damuwa. Ameen.

(La ilaha illalLah, wahdahu la sharika lah, lahul mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kulli sha'in Qadeer).

Jameel Muhammad Sadis

07/06/2024

ALLAHU AKBAR 😓

Prof Mansur Isah Yalwa

06/06/2024

Dhul Hijjah
🌙🥰

Ina Kaunar Ku Saboda ALLAH!💞🤗Sheak Ahmad Tijjani Yusuf GuruntumSheak Umar Shehu Zaria
05/06/2024

Ina Kaunar Ku Saboda ALLAH!💞🤗

Sheak Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Sheak Umar Shehu Zaria

KARYA NE SHEIKH AHMAD TIJJANI YUSUF GURUNTUM BAI YI HATSARI BA.Jama’a muji tsoron Allah! Mu daina yaɗa abinda bamu da Ta...
05/06/2024

KARYA NE SHEIKH AHMAD TIJJANI YUSUF GURUNTUM BAI YI HATSARI BA.

Jama’a muji tsoron Allah! Mu daina yaɗa abinda bamu da Tabbaci akai.

Yau da safen nan labarai yana ta yawu akan wai Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntun yayi hatsari!

Wannan maganar ƙarya ne malam bayyi hantsari ba, kuma yana nan cikin ƙoshin Lafiya.

Saboda haka jama'a ku kwantar da hankalinku ba abinda ya samu Malam.

Asalin abinda ya faru shine: ɗaya daga cikin yaran Malam ne ya fita da mota, ya samu tsautsayi ya faɗa kwalbeti, kuma shima Allah ya kiyaye ba abinda ya same shi.

Copied.

Asslm alkm,Halaye hudu idan mutum ya same su to kada ya damu don ya rasa wani abu a duniya:1. kiyaye Amana ta dukiya ko ...
01/06/2024

Asslm alkm,
Halaye hudu idan mutum ya same su to kada ya damu don ya rasa wani abu a duniya:

1. kiyaye Amana ta dukiya ko ta Aiki ko ta magana

2. Gaskiya a magana ko wajen bada labari

3. Kyakkyawar ɗabia tsakaninka da Allah da kuma tsakaninka da mutane

4. Wadatuwa da yin amfani da Halal a wajen ci da sha da tufafi da wajen zama, da sauransu

Sheak Aliyu Sa'id Gamawa
والله أعلم

Ubangiji ALLAH Ka Jaddada Rahamar Ka Ga Wannan Bawa Naka. 😓💔🤲
01/06/2024

Ubangiji ALLAH Ka Jaddada Rahamar Ka Ga Wannan Bawa Naka. 😓💔🤲

31/05/2024

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum 😥🤲

31/05/2024

Ina Kaunar Manzon ALLAH 😓💔

Prof Mansur Isah Yalwa

CIKAKKIYAR NUTSUWA!Za ka ɓata lokacinka kuma ka wahala matuƙar kana tunanin samun aminci da nutsuwa a wurin wani. Ko da ...
25/05/2024

CIKAKKIYAR NUTSUWA!

Za ka ɓata lokacinka kuma ka wahala matuƙar kana tunanin samun aminci da nutsuwa a wurin wani. Ko da ka ga ka samu to taƙaitacce ne ko kasasshe, ko waye wannan mutumin kuwa.

Jama'a mu k**a hanyar Allah, a cikinta dukkanin nutsuwa da aminci yake. Domin duk wani da mu ka ga mun amintu kuma mun nutsu da shi huwacewa ce ta Allah, Ya sanya sinadarin nutsuwar Ya kuma nutsar da mu ɗin da shi.

Ya Allah Ka nutsar da mu da abinda Ka azurta mu da shi amin.

Daga Shafin;
Malama Zainab Ja'afar Mahmud Adam

24/05/2024

ALLAH Ka Tabbatar Da Imani A Zukatanmu Duk Lalacewar Zamani.
💔😓🤲

Duk Wanda Ya Fahimci Addini Bazai Taɓa Zama Mai Jijji Da Kaiba Ballantana Yayi Girman Kai 😓😍ALLAH Kara Girma Da Daraja S...
23/05/2024

Duk Wanda Ya Fahimci Addini Bazai Taɓa Zama Mai Jijji Da Kaiba Ballantana Yayi Girman Kai 😓😍

ALLAH Kara Girma Da Daraja Shaikhana Sheikh Usman Abubakar Abul-Husnain

Duk Wanda Ya Fahimci Addini Bazai Taɓa Zama Mai Jijji Da Kaiba Ballantana Yayi Girman Kai 😓😍ALLAH Kara Girma Da Daraja S...
23/05/2024

Duk Wanda Ya Fahimci Addini Bazai Taɓa Zama Mai Jijji Da Kaiba Ballantana Yayi Girman Kai 😓😍

ALLAH Kara Girma Da Daraja Shaikhana Sheik Abdallah Usman Gadon Kaya

23/05/2024

ALLAH Ka Tabbatar Damu Akan Dai-Dai
🤲

Manaufar zuwanka duniya shine ka kadaita Allah da bauta. Kuma shine mafi girman hakki akanka. A kula kar ayi farkar jaji...
23/04/2024

Manaufar zuwanka duniya shine ka kadaita Allah da bauta.
Kuma shine mafi girman hakki akanka.
A kula kar ayi farkar jaji.

Daga Shafin Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

BARKA DA SALLAHAN RUWAITO JUBAIRU ƊAN NUFAIR YACE :SAHABBAN MANZON ALLAH  ﷺ SUN KASANCE, IDAN SUN HAƊU RANAR IDI SUNA GA...
10/04/2024

BARKA DA SALLAH

AN RUWAITO JUBAIRU ƊAN NUFAIR YACE :
SAHABBAN MANZON ALLAH ﷺ SUN KASANCE, IDAN SUN HAƊU RANAR IDI SUNA GAYAWA JUNAN SU,

"ALLAH YA KARƁA MANA YA KARƁA MUKU"

TAƘABBALLAHU MINNA WA MINKUM

29/03/2024

Kawai Ka Jira Lokaci! 🤗😓

MENE NE AZUMI??1. AZUMI A LUGGA:-Shine kamewa2. ASHARI'ANCE:- Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun ...
12/03/2024

MENE NE AZUMI??

1. AZUMI A LUGGA:-Shine kamewa
2. ASHARI'ANCE:- Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.

RUKUNAN AZUMI

1. Yin niyya

2. Kamewa dagachi ko sha da saduwa da iyali
3. Zamani (lokachin yin azumi).

SUNNONIN AZUMI
1. Gaggauta buda baki
2. Jinkirta sahur
3. Addu'a yayin buda baki
4. Yin sahur da jinkirta shi.

MAKARUHAN AZUMI
1. Kaiwa matuka wajen kurkuran baki
2. Sumba
3. Dauwamar da kallo na sha' awa
4. Tunani akan al'amuran saduwa
5. Shafa ko runguma
6. Dandanan wani abu
7. Sanya tozali
8. Yin kaho.

ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI
1. Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)
2. Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar
3. Saduwa ta hanyar tilasta
4. Chi ko sha da tunanin sauran dare
5. Chi ko sha da gangan
6. Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi
7. Ridda.

ABUBUWAN DA SUKE HALAS
1. Yin asiwaki
2. Sanyaya jiki da ruwa
3. Tafiya ta halas
4. Sanya magani wanda ya dache
5. Tauna wani abu ga karamin yaro
6. Sanya turare.

ABUBUWAN DA AKAYI RANGWAME
1. Hadiye yawu
2. Rinjayen amai da magwas
3. Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi
4. Kuran kan hanya
5. Wayan gari da janaba
6. Yin mafarki da rana.

MUHADARA TA MUSAMMAN KAN AZUMI Kashi Na 7 Shiyasa Haryanxu Ayar Wata Ayace A Suratu Muhammad Tana Daga Cikin Ayoyin Da K...
10/03/2024

MUHADARA TA MUSAMMAN KAN AZUMI

Kashi Na 7

Shiyasa Haryanxu Ayar Wata Ayace A Suratu Muhammad Tana Daga Cikin Ayoyin Da Kusan Kowani Musulmi Ya Hadda Ce Amma Kuma Yana Daga Cikin Ayoyin Da Malamai S**ace Musulmai Basu Fahimce Taba

Shine "إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ يَنْصُرْكُمْ Kusan Kowa Yasan Ayar Amma Ma'anan Ta Kowa Yanzu Damuwan Sa In ALLAH Ya Bashi Zaiyi Kaza To Shikuma ALLAH Cewa Yayi Yanzu Abinda Ke Hanunka Kayi Dashi Ya Gani Saiya Temake Ka
Inkun Temaki Addini ALLAH Yace Zante Make Ku To Mukuma Muna Jirane Saiya Temake Mu Mutemaki Addinin Shiyasa Mutum Shiyasa Baze Temaki Kowa Ba

Anzo Ana Aiki Na Masallaci Ko Ana Aiki Na Marayu Ko Ana Wani Hidima Dakake So Ayi Generator Masallaci Ko Wani Abu Daya Shafi Al'ummah Ko Addini

Saika Ɗauki Wayar Ka Saika Sayar Sai Akayi Wannan Aikin Dashi
Ka Nuna Ma ALLAH Cewa Wannan Abun Inyabaka Da Kayi Amma Indamuwar Ka Ta Taso Ko Kuɗin Makarantan Yara Zaka Saida Wayan Kaga Wannan Shine Kakeyi Dagaske Abunda Kasaida Wayan Ka Danshi Shi Dagaske Kakeyi

Amma Speaker Na Masallacin Ku Ya Ɓaci Anyi Kwana Biyar Bai Gyaruba Generator Wayarka Zata Iya Sayan Generatorn Baka Sayar Ba Kuma Kace Ma ALLAH Dagaske Kakeyi

Wanda In Wani Hidimar Ka Kona 'Ya'yanka Yazo Daka Iya Saida Filin Ka Kayi
To Agun ALLAH Wannan Abun Da Kasaida Filin Shine Kakeyi Dagaske! Shine Kakeyi Dagaske!!

To Abinda Ke Hanunka Abinda Ke Hanunkan Shi ALLAH Yace Kayi Aikin Dashi
Toya Nuna Duk Yawan Abunda Ke Hanunka Daka Iya Amfani Dashi

Amma In Jira Kake Saiya Baka Kafin Kayi
To Wannan Bada Gaske Kakeyi Zakayi Ba

Saboda Haka Shiri Wa Ramadan Tsari Wa Ramadan Wato Shauƙi Da Roƙon ALLAH Ya Riskadda Dakai Watan Ramadan Da Kuma Abinda Kake Da Niyyan Ka Aikata Na Alkairi Awatan Ramadan.

🎤🎤🎤
Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

Muhaɗu Kashi Na Gaba

MUHADARA TA MUSAMMAN KAN AZUMI Kashi Na 5To Abun Danake So Naja Hankalin Mu Akai Duk Wata Ibadah! Duk Wata Ibadah!! Da A...
09/03/2024

MUHADARA TA MUSAMMAN KAN AZUMI

Kashi Na 5

To Abun Danake So Naja Hankalin Mu Akai
Duk Wata Ibadah! Duk Wata Ibadah!! Da ALLAH Ya Sanya Mana To Akwai Tsarin Da Zakabi Matakan Dazaka Bi Domin Riskan Abun Dake Cikin Wannan Tsari Ko Ibadah Da ALLAH Ya Shar'anta Mana

Dayawan Mu Muna Asaran Damam Makin Mu Ta Hanyar Rashin Shirin Karɓan Rahama Ko Gafara Ko Jinƙai Daga Wajan ALLAH Subhanallahi Wata'ala

Inda S**a San Menene Ramadan Me Ake Samu A Ramadan Yanzu A Tsaye Suke Kai Kace Za'a Tada Al'umman Ne
Kowa Yana Shiga Yana Fita Meye Kawai Buƙatassa Meze Shirya A Watan Ramadan! Meze Shirya A Watan Ramadan!!

Kowani Abu Da ALLAH Ya Tsara Yace Rahama Ce Yace Jinƙai Ne Zai Bada Tallafi Ko Gudummawa Ko Nasara To Wannan Abin ALLAH Kan Ɗorashi Akan Waɗan Su Ƙa'idodi Da Ake Buƙata Bawa Ya Kiyaye Wadda Inya Gagara Kiyaye Wannan Ƙa'idodin To Sai Azo Banda Shi

Sai Damar Tazo Har Damar Ta Ƙare Shi Bai Ribata Ba

Annabi Yace Dayawa Dasu Ake Azumi Amma Iya Abinda Suke Samu A Azumin Yinwa Da Ƙishirwa
Annabi Yace Dayawa Dasu Ake Tahajjud Da Qiyamul Laili Amma Iya Rabon Su A Tahajjud Ko Qiyamul Lailin Shine Rashin Bacci Da Basuyi Ba

Saboda ME Akwai Waɗan Su Abubuwa Daya Kamata Ace Bawa Ya Shirya Mishi Ya Kintsa Mishi Domin Ribatar Abunda ALLAH Subhanahu Wata'ala Ya Sauƙaƙe Mishi
To Daga Cikin Abinda Ake Buƙatan Shiri Na Tarban Watan Ramadan Shine Ka Himmatu Ka Shiryawa Neman Gafara Jinƙai Awajan ALLAH Neman Gafaran ALLAH Neman Rahama Neman Dace A Wajan ALLAH Ta Hanyar Himmatuwar Ka Da Kuma Yadda Ka Ɗauki Ramadan

Kamar Yadda Muke Faɗa Wani Ramadan Ɗin Na Zuwa Shi Gabansa Ma Faɗuwa Yake Yi.🤔

🎤🎤🎤
Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

Muhaɗu Kashi Na Gaba 🙏🙏🙏

Address

Nassarawa Jahun Near Al'ameen Hospital Bauchi
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zauran Nasiha Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zauran Nasiha Tv:

Videos

Share

Category


Other TV Channels in Bauchi

Show All