09/12/2024
Burin Tinubu shi ne ko wanne ɗan Nijeriya ya dena kwana da yunwa
Ƙaramin Ministan Noma, Aliyu Abdullahi, ya baiyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya duƙufa ne wajen tabbatar da cewa abinci ya wadaci ƴan Nijeriya.
Da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na Channels TV a yau Litinin, Abdullahi ya ce burin Tinubu shi ne ya tabbatar da cewa ko wanne ɗan Nijeriya ya kwanta barci a ƙsohe.
Ya ce shi ya sa gwamnatin Tinubu ke kirkiro da shirye-shirye daban-daban don tabbatar da wannan ƙudiri na shugaban ƙasa.