Muryar ‘Yanci

Muryar ‘Yanci Domin samun ingantattu, tabbatattun labaru da dumi-dumin su. A biyo mu a wannan shafi don sanin abinda ya shafi labarun yau da kullum.

Kalubalen siyasar Ganduje da El-Rufa'iTsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeri...
19/04/2024

Kalubalen siyasar Ganduje da El-Rufa'i

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na Kano da takwaransa na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i na fuskantar kalubalen siyasa.

Dole El-Rufa'i ya girbi abun da ya shuka tun yana raye -Buba Galadima Engr. Buba Galadima, wanda tsohon jigo ne a jam’iy...
19/04/2024

Dole El-Rufa'i ya girbi abun da ya shuka tun yana raye -Buba Galadima

Engr. Buba Galadima, wanda tsohon jigo ne a jam’iyyar APC, ya caccaki tsohon Gwamna Kaduna Malam Nasir El-Rufai, inda ya zarge shi da bata masa suna a lokaci yana cikin jam’iyyar APC.

Ya bayyana abin da El-Rufai ya yi a matsayin daya daga cikin dalilan ficewar sa daga APC A wani faifan bidiyo da gidan Talabijin na Channels ya watsa a YouTube.

Buba ya ce da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar ciki har da shi, ba sa cikin jam’iyyar APC saboda wasu mutane irin su El-Rufai da ke son mamaye jam’iyyar ta hanyar tozarta wasu.

Buba ya faɗawa Channels cewa, daman ya taɓa fadacewa nan gaba kaɗan Elrufai zai girbi abinda ya shuka sak**akon abin da ya aikata kuma tuni ya fara ganin sakayya.

Buba ya yi zargin cewa El-Rufai ya hana Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi tsayawa takara ne saboda sun ki amincewa da bukatarsa na ciwo bashi.

Ya yi zargin cewa El-Rufai ya tsayar da Uba Sani Sanata ne domin ya zama shugaban kwamitin kudi na Majalisar Dattawa domin ya amince da bukatarsa ta ciyo wa Kaduna bashi.

A cikin kalaman Buba: yace "El-Rufai dole ne ya girbi abunda ya shuka saboda Allah ba ya jira sai mu mutu kafin yayi sakayya.

YAHAYA BELLO: Tsakanin gudun famfalaƙi, gudun-ƙaddara ko gudun Naira biliyan 80A ranar Alhamis ce Hukumar EFCC ta ce Gwa...
19/04/2024

YAHAYA BELLO: Tsakanin gudun famfalaƙi, gudun-ƙaddara ko gudun Naira biliyan 80

A ranar Alhamis ce Hukumar EFCC ta ce Gwamnatin Tarayya za ta iya yin amfani da ƙarfini sojoji domin a kamo tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, domin a gurfanar da shi kotu, bisa zargin ya fatattakar da zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 80 a lokacin da ya ke Gwamnan Kogi.

Bello wanda ya kammala wa’adin sa a ranar 27 ga Janairu, an shirya EFCC za ta gurfanar da shi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 19 ga Afrilu, wato yau Alhamis.

Duk wani ƙoƙarin k**a shi da EFCC ta yi a gidan sa da ke Abuja a ranar Laraba, ya ci tura, domin lauyan EFCC ya shaida wa Mai Shari’a Emeka Nwite cewa ba su samu damar gabatar da Bello ba, duk kuwa shi Mai Shari’a ɗin ne ya ba EFCC sammacin kamo Bello a ranar Laraba ɗin.

Lauyan EFCC, Kemi Pinheiro ya shaida wa kotu cewa Gwamnan Kogi na yanzu, Usman Ododo ne ya ɗauki Yahaya Bello a cikin motar sa, ya arce da shi.

Ya ce ba don jami’an EFCC sun nuna iya aiki da sanin ya-k**ata ba, to da sai sun mummunar arangamar zubar da jinainai su da ‘yan sandan da ke gadin gidan Yahaya Bello, saboda ƙi bari EFCC su damƙe shi.

“Za mu iya yin amfani da Sashe na 12 na Dokar Aikata Manyan Laifuka (ACJA) 2015 domin a kamo Bello, ko ma a gidan wa ya ke a ɓoye.”

Amma lauyan Yahaya Bello mai suna Abdulwahab Muhammad, ya ce Yahaya Bello bai karya umarnin kotu ba.

Ya ce ai akwai umarnin da Babbar Kotun Lokoja ta bayar cewa kada EFCC su k**a Yahaya Bello.

A kan haka ne ya ce Mai Shari’a Nwete ba shi da hurumin sa a kamo Bello, domin akwai kwantai ɗin ƙarar da ya shigar a Babbar Kotun Lokoja.

Rikita-rikitar Kuɗaɗen Da EFCC Ke Nema Cikin Aljihun Banten Yahaya Bello:

EFCC ta ɓallo wa Yahaya Bello ruwan zafi, ta lafta sunan sa cikin harƙallar kuɗaɗen da aka gurfanar da ƙanin sa.

Hukumar EFCC ta bayyana wa kotu cewa tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello na da masaniya da kuma hannu a cikin harƙallar da ta gurfanar da wani ƙanin Yahaya ɗin mai suna Ali Bello da wasu mutane, bisa zargin wawurar maƙudan kuɗaɗe, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis.

EFCC ta yi wa canje-canjen da ta ke wa waɗanda ta gurfanar ɗin a ranar 5 ga Fabrairu, daga caje-caje 10 zuwa 17 kan Ali Bello da Dauda Suleiman, s shari’ar da aka fara tun cikin 2022.

Mai gabatar da ƙara daga EFCC ya bayyana wa kotu cewa tsohon Gwamnan Kogi, Bello a ɗaya daga cikin waɗanda aka ƙara shigo da su waɗanda tuhuma ta hau kan su.

Tuhuma ta ɗaya dai a wurin ne kaɗai sunan Yahaya Bello ya fito. EFCC ta zarge shi da haɗa baki da Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdusalam Hudu cikin Satumba 2015, s**a karkatar da Naira biliyan 70, mallakar gwamnatin Jihar Kogi zuwa amfanin kan su.

EFCC ta bayyana cewa Hudu ya ari takalmin kare, ya tsere.

An zarge su da karkatar da Naira biliyan 100 ta gwamnatin Kogi, a lokacin da Bello ya na gwamnan Kogi.

Laluben Naira Biliyan 80 Cikin Aljifan Yahaya Bello: Gwamnatin Kogi Ta Ce EFCC Ta Kwarkwance, Ta Fara Bilumbituwa:

Tun cikin Fabrairu ne, ƙasa da kwanaki bakwai bayan saukar kan mulki, bayan ya shafe wa’adin shekaru takwas ya na Gwamnan Jihar Kogi, aka gayyaci Yahaya Bello domin gurfana kotu, domin tuhumar sa zargin karkatar da Naira biliyan 80 daga aljihun gwamnati zuwa aljifan sa.

Yahaya Bello ya miƙa mulki ga Usman Ododo a ranar 27 ga Janairu.

EFCC ba ta damu ta gabatar wa kotu wasu sabbin tuhume-tuhume a kan Bello ba, sai kawai ta yi kwaskwarima kan cajin tuhume-tuhumen da kotu ke wa wani ɗan uwan tsohon gwamnan da makusancin sa, waɗanda kotu ke tuhuma kan zargin karkatar da biliyoyin nairorin Jihar Kogi.

Abin da kawai EFCC ta yi shi ne ɗora tuhume-tuhumen da ake wa Yahaya Bello a cikin waccan shari’a da ke gaban kotu.

A shari’ar dai ana tuhumar ƙanen Yahaya Bello mai suna Ali Bello da wani mutum mai suna Dauda Suleiman da laifin karkatar da kuɗaɗe.

To amma a cikin shari’ar yanzu an haɗa da Yahaya Bello, wanda shi kuma aka tuhume shi da zargin karkatar da Naira biliyan 80 zuwa aljifan sa. Adadin kuɗaɗen da EFCC ke nema a hannun da sun kai N80,246,470,089.88.

Tuhume-tuhumen sun nuna cewa abokin jidar kuɗaɗen mai suna Abdulsalami Hud, wanda Jami’in Kula da Harkokin Kuɗaɗe ne Gidan Gwamnatin Jihar Kogi, ya cika wandon sa da iska, ya gudu.

To sai dai kuma tuni har sabuwar Gwamnatin Jihar Kogi ta yi wa EFCC zazzafan raddin cewa bulkara da hauragiya ta ke yi, domin laifukan da ake cajin Yahaya Bello da aikatawa, ta ce an yi su ne tun wajen Satumba, 2015, lokacin Yahaya Bello bai ma zama gwamna ba.

Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, wanda kuma shi ne dai kwamishinan yaɗa labarai a mulkin Yahaya Bello, shi ne ya fito da bayanin da ke ƙunshe da raddin da gwamnatin ta Jihar Kogi ta yi wa EFCC.

Mutane da dama na mamakin gaggawar maka Yahaya Bello kotu, alhali ga irin su Bello Matawalle, maimakon a gurfanar da shi k**ar yadda EFCC ta zarge shi, sai na aka naɗa Ƙaramin Ministan Tsaro.

Haka tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, shi ma maimakon a ji an ce EFCC ta yi cacukui da shi bayan saukar sa, sai ana naɗa shi Shugaban APC, jam’iyya mai mulki.

https://muryaryanci.com/yan-bindiga-sun-kaddamar-da-sabon-hari-a-jihar-kaduna/
18/04/2024

https://muryaryanci.com/yan-bindiga-sun-kaddamar-da-sabon-hari-a-jihar-kaduna/

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa wasu ‘ƴan bindiga sun kashe mutum uku a wani hari da s**a kai wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna. An ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024. Mazauna yankin sun b...

https://muryaryanci.com/dangote-ya-karya-farashin-man-dizel/
18/04/2024

https://muryaryanci.com/dangote-ya-karya-farashin-man-dizel/

A wani yunkuri na rage wahalhalun da ƴan Nijeriya ke fuskanta, matatar man Aliko Dangote ta sanar da ƙara rage farashin man dizel daga naira 1200 zuwa 1,000 kan kowacce lita. A cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Talata ya ce ana sa ran ”rage farashin man dizel ɗin zai yi tasiri sosa...

Yanzu Yanzu Sojin Najeriya Sun Kuɓutar Da 'Yar Chibok Lidiya Simon, tare da 'ya'yanta da ta haifa wa 'yan Boko Haram
18/04/2024

Yanzu Yanzu Sojin Najeriya Sun Kuɓutar Da 'Yar Chibok Lidiya Simon, tare da 'ya'yanta da ta haifa wa 'yan Boko Haram

Tsohon Gwabnan Kaduna Elrufa'i Ya bijirewa Umarnin Majalisar Dokokin Jihar A lokacin da Ya Karbo bashin $350m -Inji Tsoh...
18/04/2024

Tsohon Gwabnan Kaduna Elrufa'i Ya bijirewa Umarnin Majalisar Dokokin Jihar A lokacin da Ya Karbo bashin $350m

-Inji Tsohon Kakakin Majalisa ta 9 Yusuf Zaillani

A Cewar Tsohon kakakin majalisar ta 9 na majalisar dokokin jihar Kaduna, Yace bayi approving Bashin $350m ba Amma El-rufai.

Amma Gwamnatin Elrufa'i tayi fatali da Umarnin Majalisar Inda Ta karbi rancen ba tare da amincewar Majalisar ba.

Ya bayyana hakane a zauren majalissar jihar yayin da aka kafa Committe ta binciko Badakalar da akayi lokacin Mulkin Nasiru El-rufai Daga 2015 Zuwa 2023

Ganduje da El-Rufa'i sun tsinci Talatarsu a LarabaKalubalen siyasar Ganduje da El-Rufa'iTsofaffin gwamnonin jihohin Kano...
18/04/2024

Ganduje da El-Rufa'i sun tsinci Talatarsu a Laraba

Kalubalen siyasar Ganduje da El-Rufa'i

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na Kano da takwaransa na Kaduna Nasiru El-Rufa'i na fuskantar kalubalen siyasa.

Rikicin siysar na jihar Kano dai, na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Kaduna a Najeriyar, ta kafa kwamitin binciken dukkanin basuss**an da tsohon gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya ciwo da kwangiloli da ma bankado harkallar da ake zargin gwamnatin ta tafka tare da sauran ayyukan da aka dakatar.

A wani zaman gaggawa da majalisar dokokin Kadunan ta gudanar kan bukatar binciken tsohun gwamnan kaduna da sauran makarrabansa an bai wa kwamitin binciken bin bahasin wa'adin wata guda, domin tattara rahoton da za a gabatar a gaban 'yan jarida. Kwamitin dai, zai gayyaci duk wani jigo a gwamnatin El-Rufai da s**a hada da kwamishinoninsa da tsohon kakakin majalisa da hadimansa na kusa da kuma shugabannin ma'aikatun gwamnatin da s**a yi aiki a lokacinsa. Al'ummar jihar ta Kaduna, na fatan ganin an yi adalci wajen gabatar da rahoton.

Binciken na El-rufa'i dai na zuwa ne a daidai lokacin da asana da sauran al'umma a jihar Kano, ke ci gaba da fashin baki da martani kan umurnin babbar kotun jihar dangane koken da wasu kusoshin jamiyyar APC a mazabar Ganduje s**a kai gaban kuliya da ke neman tabbatar da dakatar da Gandujen daga jam'iyyar ta APC.

Wasu dai na ganin matakin kotun karkashin Mai Shari'a Usman Na'abba na bayar da takaitaccen umurnin cewa a tsaya a matsayar da ake kai a ranar 15 ga wannan wata na Afirilu da muke ciki, ya tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC me mulki a kasar Dakta Abdullahi Umar Gandujen.

A ranar ta 15 ga watan na Afirilu da muke ciki, aka ayyana dakatar da Gandujen. Sai dai wani abu da ya mayar da umurnin ya zama mai harshen damo shi ne, a wannan ranar ce dai wasu kusoshin jam'iyyar ta APC a mazabar Gandujen da kuma karamar hulumar Dawakin Tofa sun yi watsi da dakatarwar.

Samamen EFCC: Gwamna Ododo Ya yi Ta Kare Da Yahaya BelloRahotanni sun bayyana cewa an yi harbe-harbe a wannan Larabar ya...
18/04/2024

Samamen EFCC: Gwamna Ododo Ya yi Ta Kare Da Yahaya Bello

Rahotanni sun bayyana cewa an yi harbe-harbe a wannan Larabar yayin da Gwamnan Kogi, Usman Ododo, ya tsere da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.

Lamarin na zuwa ne yayin da Ododo ya kai ziyara gidan Yahaya Bello da ke titin Benghazi a Unguwar Wuse Zone 4 da ke Abuja.

Aminiya ta ruwaito yadda jami’an Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) s**a yi wa gidan Yahaya Bello ƙawanya tun da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Laraba da nufin k**a shi.

Sai dai jami’an na EFCC tare jami’an tsaro da s**a haɗa da ’yan sanda da DSS sun shafe sa’o’i ba tare da sun tabbatar da cika aikin nasu ba.

An samu rahoton cewa suna shirin k**a shi da ƙarfin tsiya kafin isowar Gwamna Ododo, wanda ya shiga cikin gidan Yahaya Bello tare da ɗimbin masu zanga-zangar suna rera waƙoƙin nuna goyon baya ga yadda jami’an s**a yi wa gidan ƙawanya.

Sai dai a yayin da Gwamna Ododo ke barin gidan, Aminiya ta samu rahoton cewa Yahaya Bello na cikin motarsa, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaron da s**a kwashe sa’o’i a cikin shirin buɗe wuta.

Masu zanga-zangar, da ’yan jarida da masu kallo da masu wucewa sun yi ta tururuwa don kare lafiyarsu a lokacin da jami’an ke harbin.

Dangote ya karya farashin dizel zuwa N1,000 kan kowace litaKamfanin na fatan karya farashin man dizel daga Naira 1,200 z...
18/04/2024

Dangote ya karya farashin dizel zuwa N1,000 kan kowace lita

Kamfanin na fatan karya farashin man dizel daga Naira 1,200 zuwa 1000 zai yi tasiri sosai a dukkan ɓangarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.

A wani yunkuri na rage wahalhalun da ƴan Nijeriya ke fuskanta, matatar man Aliko Dangote ta sanar da ƙara rage farashin man dizel daga naira 1200 zuwa 1,000 kan kowacce lita.

A cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Talata ya ce ana sa ran ''rage farashin man dizel ɗin zai yi tasiri sosai a dukkan ɓangarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.''

A watan Janairu ne matatar man Dangote ta fara samar da man dizel da na jiragen sama.

Tun daga lokacin matatar take sayar da man dizel a kan farashi mai rahusa na Naira 1,200 a kowace lita, kimanin kashi 30 cikin 100 na ragin farashin kasuwa da ya kai kusan Naira 1,600 kan kowace lita.

A ranar 12 ga watan Disamba 2023 ne kamfanin ya amshin jirgin ɗanyen mansa na farko daga ɗanyen mai na Agbami na kamfanin Shell International Trading and Shipping Company Limited (STASCO), ɗaya daga cikin manyan kamfanonin kasuwanci a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya, wanda ke cinikin ɗanyen mai sama da ganga miliyan 8 a wacce rana.

Kamfanin ya ɗaura ɗamarar fara samar da tataccen man fetur tare da samun ƙarin ganga miliyan ɗaya na ɗanyen man da Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC Ltd) ya kawo.

A farkon watan ne kamfanin ya fara fitar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida.

Yan Bindiga Sun Yi Sabuwar Ta'asa Ta Kashe Mutane a Jihar Kaduna Ƴan bindiga ɗauke da mak**ai sun sake kai harin ta'adda...
18/04/2024

Yan Bindiga Sun Yi Sabuwar Ta'asa Ta Kashe Mutane a Jihar Kaduna

Ƴan bindiga ɗauke da mak**ai sun sake kai harin ta'addanci a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna

Mutum uku sun rasa rayukansu a yayin harin sannan tsagerun sun kuma yi awon gaba da wasu mutum bakwai zuwa cikin daji Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin duk da bai yi cikakken bayani ba

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum uku a wani hari da s**a kai wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna. Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024.

Yadda ƴan bindiga s**a kai harin

Mazauna yankin sun bayyana cewa an hallaka mutum biyu a wani ƙauye da ke kusa da Anguwar Tanko Dogon Sarki da ke ƙarƙashin mazaɓar Kakangi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Ƴan bindigan sun kuma kai hari ƙauyen Rafin Gora mai tazarar kilomita biyu daga yankin Dogon Dawa da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar, inda s**a kashe wani mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutum bakwai.

'Yan bindiga sun dauke mutane a Kaduna

Wani mamban ƙungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, ya tabbatar da faruwar harin na Anguwar Tanko Dogon Sarki. Ya kuma ƙara da cewa a wannan rana ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane a ƙauyen Tashar Kaji da ke ƙarƙashin mazaɓar Kakangi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Me hukumomi s**a ce kan lamarin?

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahaya Musa Dan Salio ya tabbatar da faruwar harin na ƙauyen Rafin Gora sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan sauran abubuwan da s**a faru ba.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba, ASP Mansur Hassan, saboda bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

 Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincikar El-Rufa'ihttps://muryaryanci.com/majalisar-dokokin-jiha...
17/04/2024



Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincikar El-Rufa'i

https://muryaryanci.com/majalisar-dokokin-jihar-kaduna-ta-kaddamar-da-kwamitin-bincikar-el-rufai/

Waɗannan dama ƙarin wasu labaran duk za ku same su a adireshinmu
https://www. muryaryanci.com



Najeriya Za Ta Sake Afkawa Cikin Kwazazzabon Talauci - Masana
https://muryaryanci.com/najeriya-za-ta-sake-afkawa-cikin-kwazazzabon-talauci-masana/

Amurka Ta Gargaɗi Isra'ila Kan Shirin Kai Wa Iran Hari
https://muryaryanci.com/amurka-ta-gargadi-israila-kan-shirin-kai-wa-iran-hari/

An Sace 'Yan Makaranta 1,600 An Kashe 180 Cikin Shekaru 10 A Najeriya - UNICEF
https://muryaryanci.com/an-sace-yan-makaranta-1680-an-kashe-180-cikin-shekaru-10-a-najeriya-unicef/

Ku Harbe Duk Ɗan Dabar Da Ya Shiga Hannu - Umarnin Gwamnan Neja Ga Jami'an Tsaro
https://muryaryanci.com/ku-harbe-duk-dan-dabar-da-ya-shiga-hannu-umarnin-gwamnan-neja-ga-jamian-tsaro/

https://muryaryanci.com/amurka-ta-gargadi-israila-kan-shirin-kai-wa-iran-hari/
17/04/2024

https://muryaryanci.com/amurka-ta-gargadi-israila-kan-shirin-kai-wa-iran-hari/

Gwanatin Amurka ta yi wannan gargadi ne a yayin da Isra’ila ke tunanin kai hari a matsayin martani kan harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata a karshen mako. Gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa Amurka ba za ta sa hannu a hare-haren soji da Isra’ila ke tunanin kaiwa Iran ba, saboda fargabar b...

Duk dan daban da aka samu yana dabanci a harbe shi, gwamnan Neja ya umarci jami’an tsaroGwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ...
17/04/2024

Duk dan daban da aka samu yana dabanci a harbe shi, gwamnan Neja ya umarci jami’an tsaro

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya kafa dokar ta-baci saboda tabarbarewar tsaro a jihar, biyo bayan barkewar faɗace-faɗacen ƴan daba a babban birnin jihar, Minna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin bawan Sallah da tsohon gwamnan jihar, Babangida Aliyu ya shirya a gonarsa da ke Minna.

Bago ya kara da cewa, ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wani dan daba da aka samu yana barazana ga zaman lafiya a jihar.

Umarnin na gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ayyukan yan daba s**a sake dawowa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a daren Juma’a a Minna.

Bago, wanda ya danganta sake barkewar rikicin da ayyukan masu hakar ma’adanai a babban birnin jihar, ya ce ya bayar da umarnin rufe dukkan wuraren hakar ma’adanai.

“Na ayyana dokar ta-baci tare da umarnin harbi kan duk wani dan daba da aka gani a cikin babban birni da kuma cikin jihar.

“Ba mu da hakuri kan rashin tsaro da ‘yan daba. Mun kuma rufe wuraren da masu aikin hakar ma’adanai ke haddasa wannan barna a jihar.

“Duk wanda aka samu a wurin za a harbe shi har lahira. Wadanda ke daukar nauyin su ma za a yi musu hukunci mai tsauri,” in ji Bago

Na hango za a kara shiga wahala a Nijeriya -Primate AyodeleShugaban cocin INRI Evangelical Church, Primate Ayodele ya sh...
17/04/2024

Na hango za a kara shiga wahala a Nijeriya
-Primate Ayodele

Shugaban cocin INRI Evangelical Church, Primate Ayodele ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya canza salonsa na farfado da tabarbarewar tattalin arziki saboda har yanzu akwai tarin matsalolin a fannin tattalin arziki a Nijeriya.

Dclhausa na ruwaito cewa, Ayodele ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu

Ya bayyana cewa har yanzu abubuwa za su ci gaba da tsada kuma za a kara samun hauhawar farashin kayayyaki matukar gwamnati ba ta inganta harkar noma da tabbatar da samar da man fetur mai sauki da kuma ci gaba da samar da wuraren da za rika tace man fetur a kasar.

Majalisar dokokin Kaduna ta kaddamar da binciken bas**an da El-Rufai ya ciwo, kwangiloli, da kuma bankado harkallar da a...
17/04/2024

Majalisar dokokin Kaduna ta kaddamar da binciken bas**an da El-Rufai ya ciwo, kwangiloli, da kuma bankado harkallar da ake zargin gwamnatin ta tafka

Majalisar dokokin Kaduna ta kaddamar da binciken bas**an da El-Rufai ya ciwo, kwangiloli, da kuma bankado harkallar da ake zargin gwamnatin ta tafka

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki kudaden da gwamnati tsohon gwamna Nasir El-Rufai ta kashe, bas**an da aka ciwo, Lamuni da tallafin da gwamnatin ta samu kwangilolin da ka bada, su wa aka ba, wadanda ka kammala, wadanda ba a kammala ba, da dai sauransu.

Hakan ya biyo bayan korafi ne da Gwamna Uba Sani ya yi a wurin taron masu ruwa da tsaki na jihar Kaduna, inda ya koka da wasu basuss**a da s**a kai dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangiloli har na Naira biliyan 115 da gwamnatocin baya s**a bari.

Kwamitin majalisar za ta gayyaci duk wani jigo a gwamnatin El-Rufai da s**a hada da kwamishinonin sa, tsohon kakakin majalisa, hadiman sa na kusa, da kuma shugabannin ma’aikatun gwamnati da sauransu.

Bayan tattaunawa, shugaban majalisar ya bayyana cewa kwamitin wucin gadi zai binciki ayyukan da aka yi watsi da su da kuma basuss**an kasashen waje da gwamnatin da ta gabata ta karba, domin mazauna jihar na da hakkin a sanar da su halin da jihar ke ciki.

Mambobin kwamitin wucin gadi sun hada da Hon Lawal Aminu mai wakiltar mazabar Doka/Gabasawa a matsayin shugaba. Sauran mambobin sun hada da Hon Mugu Yusuf, mai wakiltar mazabar Kaura; Shugaban masu rinjaye Munira Sulaiman Tanimu; da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Shehu Yunusa Pambegua, da dai sauransu.

An Sace ’Yan Makaranta 1680, an Kashe Sama da 180 a Shekaru 10 a Najeriya Inji UNICEF  Binciken Asusun Tallafawa Kananan...
17/04/2024

An Sace ’Yan Makaranta 1680, an Kashe Sama da 180 a Shekaru 10 a Najeriya Inji UNICEF

Binciken Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da cewa a tsawon shekaru 10 an sace 'yan makaranta sama da 1680 a Najeriya Kwararriya a fannin sadarwa ta UNICEF, Susan Akila, ce ta fitar da bahasin yayin wani biki domin tinawa da 'yan matan Chibok bayan shekaru 10 da sace su

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga gwamnatin Najeriya domin inganta tsaro a makarantun kasar

Sama da 'yan makaranta 1,680 ne aka sace tare da kashe kusan 180 a hare-haren da 'yan ta'adda s**a kai a makarantun Najeriya cikin shekaru 10 da s**a gabata.

Abubuwa 4 da Tinubu ya k**ata ya yi domin tabbatar da tsaron makarantu a Najeriya, kungiya

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ne ya fitar da bahasin yayin cika shekara goma da sace 'yan matan Chibok a wani rahoto. Hare-hare kan makarantu na cigaba da barazana ga karatun yara a Najeriya.

Hukumar ta koka da cewa shekaru 10 bayan sace yara ‘yan makaranta na farko a Najeriya, ana ci gaba da kai hare-hare a akalla makarantu 70 a cikin jihohi 10 masu fama da matsalar tsaro, cewar jaridar Vanguard Hakan ya nuna cewa an dauki tsawon shekaru ana sace dalibai da malamai da dama a fadin Najeriya.

A cewar rahoton CNN, a watan Maris din shekarar 2024, sama da dalibai 300 ne wasu ‘yan bindiga dauke da mak**ai s**a sace a makarantar firamare da ke kauyen Kuriga, a gundumar Chikun ta Kaduna.

A watan Maris din 2018, 'yan Boko Haram sun sace 'yan matan makaranta fiye da 100 a garin Dapchi da ke jihar Yobe, k**ar yadda BBC ta ruwaito. Hakan nan dai Premium Times ta kuma ruwaito cewa ‘yan bindiga sun sace dalibai 10, da malami a Katsina a watan Agusta, 2021.

Adadin daliban da aka sace a Najeriya

Hare-haren sun kai ga yin garkuwa da ɗalibai wanda a cikin shekaru 10 da s**a gabata, tashe-tashen hankula masu nasaba da rikici sun kai ga sace daruruwan yara. Sama da yara 1,680 aka sace a lokacin da suke makaranta da sauran wurare; yara 180 ne s**a mutu sak**akon hare-haren da aka kai a makarantu.
An yi garkuwa da ma’aikatan makarantar 60 an kuma kashe 14, da kuma hare-hare sama da 70 a makarantu.

Barazanar sace dalibai na yin illa ga karatun yara sosai. Ya zuwa shekarar 2021, sama da yara miliyan daya ne ke tsoron komawa makaranta.
UNICEF ya ce a shekarar 2020, an rufe makarantu kusan 11,500 saboda hare-haren 'yan bindiga.

Kira ga gwamnatin Najeriya

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi kira da a kara kaimi wajen kare al’ummar kasar da s**a fi fama da ‘rashin tsaro.

Wani sabon rahoton UNICEF ya nuna cewa kashi 37 cikin 100 na makarantu a jihohi 10 ne kawai ke da tsarin kariya ga hare-haren makarantu.

Hanyoyin kare makarantu

UNICEF a Najeriya ta bukaci gwamnati, masu ruwa da tsaki da kasashen duniya da su dauki kwakkwaran mataki domin kare makarantu Matakan sun kun shi tabbatar cewa duk makarantu a faɗin jihohi suna da kayan aikin da za su aiwatar da mafi ƙarancin ƙa'idodin makarantu masu aminci. Ciki harda karfafa jami'an tsaro da matakan tsaro don kare cibiyoyin ilimi da al'umma daga hare-hare da sace-sace.

Satar daliban Cibok ta cika shekara 20

Haka zalika kun ji cewa, an cika shekara 10 da sace ƴan matan Chibok, yayin da har yanzu wasu ke tsare a hannun ƴan ta'addan Boko Haram Wasu daga cikin ɗaliban da aka sako sun dawo gida da yara, k**ar yadda gidauniyar Murtala Muhammed Foundation ta bayyana

Ba tare da Sharaɗi ba Isra'ila ta saki fursunoni 150 da yara 42 da s**a k**a a Falasɗinu, tun bayan jan kunne da Iran ta...
16/04/2024

Ba tare da Sharaɗi ba Isra'ila ta saki fursunoni 150 da yara 42 da s**a k**a a Falasɗinu, tun bayan jan kunne da Iran ta masu na kwana biyu

Shugabannin Bankuna Na Amsa Tambayoyi Kan Badaƙalar Beta Edu Da Sadiya -EFCCBeta Edu da Sadiya na amsa tambayoyi kan kar...
16/04/2024

Shugabannin Bankuna Na Amsa Tambayoyi Kan Badaƙalar Beta Edu Da Sadiya
-EFCC

Beta Edu da Sadiya na amsa tambayoyi kan karkatar da kudaden Abacha, Rancen Bankin Duniya da Tallafin COVID-19

Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta ce tana bincikar shugabannin bankuna da aka gano hannunsu a badaƙalar kudaden ma’aikatar jinƙai da ta sa aka dakatar da Beta Edu daga matsayinta na minista.


Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce, a halin yanzu, “ana gudanar da bincike kan bankuna da ke alaka da badaƙalar.

“Manajan daraktan bankunan sun ba da muhimman bayanai game da badakalar,” wadda kawo yanzu ita ce mafi daukar hankali a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Oyewale ta kara da cewa hukumar EFCC taa kwato karin kimanin Naira miliyan 534 kimanin Dala 445,000 abinciken da take wa dakatacciyar ministar agaji, Beta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar Farouq.

Ma’aikatan wutar lantarki sun nemi a janye ƙarin kuɗin wuta
NATO ta la’anci harin ramuwar gayyar Iran a kan Isra’ila
Hukumar ta bayyana a cewa har yanzu babu wanda ta wanke cikin Sadiya ko Beta Edu da sauran jami’an ma’aikatar daga zargin almundhanar da suke fuskanta.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce Dala 445,000 da kuma Naira biliyan 32.7 da hukumar ta kwato daga matan biyu wani ɓangare ne na kudaden tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba wa ma’aikatarsu domin rage raɗaɗin talauci a tsakanin ’yan Najeriya.

A cewarsa, kuɗaɗen sun hada na tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, da aka dawo wa Najeriya da su daga ƙasashen waje.

Sauran sun haɗa da kuɗaɗen tallafin COVID-19 da kuma rancen da Najeriya ta karɓo daga Bankin Duniya da aka ba wa ma’aikatar domin raba wa al’ummar ƙasa tallafin rage raɗaɗin talauci.

Address

Plot 521, HCR Plaza, Sylvester U. Ugoh Crescent, Behind Eco Bank, Opposite Police Pension Office, Jabi
Abuja
900001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar ‘Yanci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muryar ‘Yanci:

Videos

Share

Category

Nearby media companies


Other Newspapers in Abuja

Show All