Sahara Reporters Hausa

Sahara Reporters Hausa Shafin Sahara Reporters Hausa tana kawo muku sahihan labarai akan lokaci, masu fadakarwa, ilmantarwa

Bamu nemi a soke zaɓen Kano ba - Masu sanya ido kan zaɓeGamayyar ƙungiyoyi da s**a sanya ido a zaɓen Gwamnan Kano sun ne...
25/03/2023

Bamu nemi a soke zaɓen Kano ba - Masu sanya ido kan zaɓe

Gamayyar ƙungiyoyi da s**a sanya ido a zaɓen Gwamnan Kano sun nemi jama'a su yi watsi da wani labari da ake yaɗawa wai sun nemi a soke zaɓen Kano.

Ƙungiyoyin sun ce ba su da alaƙa da kowace jam'iyya su suna aiki ne don jama'a.

Sun kuma ce za su ɗauki mataki kan waɗanda s**a yi amfani da sunansu wajen yaɗa labarin ƙarya.

Daga Yusuf Waziri Journalist

ABIN A YABA: Yadda wani Matashi a Jahar Gombe Mai Suna Muhammad Kwairi Waziri  Ya Rabar Da Zunzurutun kuɗi Naira Dubu 20...
21/03/2023

ABIN A YABA: Yadda wani Matashi a Jahar Gombe Mai Suna Muhammad Kwairi Waziri Ya Rabar Da Zunzurutun kuɗi Naira Dubu 200 Ga Masu Amfani Da Soshiyal Domin Nuna Farin cikin Lashe Zaɓen Da Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya Yayi a karo Na biyu..

Matashin ya rabar da kuɗin ne domin cika alkawarin daya ɗauka Na cewa idan har hukumar zaɓe ta sanar da Malam Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaɓe karo Na biyu zai Bayar dasu Domin nuna farin cikinsa ga mai gidan sa Hon Malam Hashidu.

Ya raba kudadenne wasu ta lambar asusun banki su kuma hanu da hanu wasu kuma Data Da Katin Waya.

Wane fata kuke masa ?

Daga Falalu Lawal Katsina

Gawuna yana daf da lashe zaben gwamnan KanoMajiya ALFIJIR HAUSA
19/03/2023

Gawuna yana daf da lashe zaben gwamnan Kano

Majiya ALFIJIR HAUSA

Ana Zargin Dan Majalisar Wakilai Bala Kelly A Jahar Gombe Da Rashin Ajiye Aikinsa.Ana Zargin Dan Majalisar Wakilai Mai W...
05/03/2023

Ana Zargin Dan Majalisar Wakilai Bala Kelly A Jahar Gombe Da Rashin Ajiye Aikinsa.

Ana Zargin Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Dukku/Nafada A Jihar Gombe Bala Kelly, Da Rashin Ajiye Aikin Sa.

Hon. Abdullahi Kelly shine wanda yayi takara a kar Kashin jam'iyyar PDP da Hon Aisha Dukku, a majalisar tarayya ita kuma kar kashin jam'iyyar APC a ranan 25-22023, inda jam'iyyar PDP tayi nasara lashe zaɓen.

Masana siyasa da dokar kasa sun bayyana cewa, hakan babban laifi ne kuma hakan zai iya sa dan takaran ya rasa kujerar sa a kowanne lokaci idan har abinda ake zargin sa ya zama gaskiya.

Zuwa yanzu dai 'yan majalisu da dama wanda s**a ci Zaɓe sun karbi shedar lashe zaɓen su daga wajen hukumar zabe mai zaman kanta INEC, amma shi bata bashi ba har ila yau.

A wani bangare kuma an ga wani bidiyo daya ke yawo a kafofin sadarwa inda abokiyar hamayyar sa Hon Aisha Dukku, take kara jaddada wa magoya bayan ta cewa, su kwantar da hankalin su basu fadi a Zaɓe ba inda take mai-mai ta hakan sau uku a cikin bidiyon.

Majiya ALFIJIR HAUSA

Kŵadáýi Dà Śòń Ábìn DùniýaPàntàmi (Malam Garbati) ya fara kamun kafa a gurin Tinubu, ga shi nan dai kowa na ganin yadda ...
03/03/2023

Kŵadáýi Dà Śòń Ábìn Dùniýa

Pàntàmi (Malam Garbati) ya fara kamun kafa a gurin Tinubu, ga shi nan dai kowa na ganin yadda pantamin yake sumbatar certificate din da INEC ta baiwa Tunubu na shaidar cin zabe.

Isa Ali Pantami Professor Isa Ali Pantami Allah ya tsare musulman kirki daga kwadayi da son duniya.
Daga Jaridar Labari Da Gaskiya

Kalma daya tak akan wannan hoton
19/09/2021

Kalma daya tak akan wannan hoton

Ƙungiyar kiristoci ta najeriya wato (CAN) ta dakatar da shugabanta na reshen jihar gombe saboda taya murna da yayi wa fa...
17/09/2021

Ƙungiyar kiristoci ta najeriya wato (CAN) ta dakatar da shugabanta na reshen jihar gombe saboda taya murna da yayi wa farfesa isah Ali Pantami kan matsayin farfesan da ya samu.

Za mu dauki mummunan mataki kan Abba Kyari - Rundunar 'yan sandan Najeriya.Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta dau...
27/08/2021

Za mu dauki mummunan mataki kan Abba Kyari - Rundunar 'yan sandan Najeriya.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta dauki matakin da ya dace kan dakataccen jami'inta Abba Kyari matukar aka same shi da laifin da ake zarginsa da shi.

Hukumar ta yi wannan bayani ne bayan karbar wani rahoto na musamman kan binciken da ake yi a kansa.

An mika wa Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya rahoton binciken da ake gudanar wa kan Abba Kyari, wanda aka dakatar da shi daga aiki bayan zarginsa da alaka

26/08/2021

*💞TARKON KAUNA EPS 174💞*
*💟Adini Sen Koy Bolum 174💟*

*

_Na 173 yatsaya daidai inda alev take fadin baqaqen magangu,aranan murnan zagayowan aurensu nihat._

*CIGABA*
```S1
Muzayyince takaraso tace yau rana ne mai muhimmanci awajen wannan yaran,dan Allah alev kada kilalata musu da wa 'yannan zantuka naki da basu da galihu(amfani) tace kaga omer samu waje ku zauna, kuzauna, zuwa omer da zehra s**ai s**a zauna, muzayyin ta zauna kusa da alev,alev hade rai tai tam,

S2
Nihat ne yajuyo ga ayshe yace rabin raina,kallonsa tai tayi murmushi,bude zoben nan yayi,yace bari wannan zobe yazamo tabbacin daurewar farincikinmu,Gyade kai tayi,halaman hakane,sanya mata yai ahanu, omer da zehra suna kallo,omer najin inama da shine,zehra ko tana mai jin bakincikin,rayuwar zallar karya da su sukeyi,bakinta sai motsi yake k**ar wacce keson cewa wani abu,javrie sai murmushi take na jin dadi,muzayyinma haka,anty alev ko basai nace komai ba,fuskar nan haka😡 ,rungumar nihat ayshe tayi tana mai farinciki,

alev ce ta gyara zama tace têktas sunce alamomi dasuke nuni da bayyana tabbataccen aure shine nuni da daurewar soyayya,juyawa omer da zehra s**ai s**a kalli juna,cigaba da magana alev tayi,tace tabbas sunyi gaskiya,javrece ta karbi maganar tace ai dama hakanev 'yar nan,idan babu soyayyar ina shi kanshi auren za a samoshi?,dan haka tsakanin kowasu ma'aurata dole akwai soyayya mai karfi,da ba soyayya da ma'aurata baza kiga sun kwanta akan matashin pillow guda ba,baza suci abinci tare ba,bazasu fita yawo tare ba, yatsina fuska alev tayiwa javre k**ar haka😏, ayshe ce tasaki nihat takalli zoben dake yatsarta tayi murmushi,tace nihat nagode matuka,wannan abu kawataccene,zuwa tai wajen muzayyin tace anné(mama) ya kika gani tana mai nuna musu hannunta muzayyin tace Çök guzel(yayi kyau sosai)tajuyo gasu zehra tace zehra kingani,zehra tace rabin raina yayi kyau sosai ina tayaki murna, komawa wajen nihat ayshe tayi tace nihat nayi tunani sauranma mu gabatar yanzu,rike hannusa tai,yace amhmm da nashiryane akan sai twentieth year,amma dai zanyi yanzu,dadi taji ta rungumesa, muzayyin tace yaran nan ina fatan omer da zehra ma su kasance atare natsawon lokaci k**ar haka,juyowa tai tana mai duban omer da zehra,zehra ce ta juya ta dan kalli omer shima kallontan yayi, nihat yace in sha Allah,in sha Allah,ayshe tace toh shikenan nan da shekara 10 sai mu hadu mi murnan tare,ko?ayshe tana mai kallonsu,cigaba da magana tayi tace kafin nan tare dasu kananun 'yayan karvangclor,wani dadi muzayyin taji,tai dariya, zehra ko razana tayi tafara kefkefta ido,shi ko omer kasa zama yayi, mutsu mutsu yafara🤓🤓🤓 ayshe ta cigaba da magana,dan haka ina jiranku,kui kufito mana dasu da wuri,alev ce ta bata rai tai wani ajiyar zuciya na takaici hummmmm🙄 muzayyince ta juyo ga omer tana mai farinciki,tace da na omer katuna lokacin kana yaro abun da kake cewa, ayshe baza ta zamo uwa ba, omer yace kwarai mama,ayshe tace mama ta na fadin zamowa uwa ba wani abu ne da sai an koya ba,ba sai an kware ba,saboda ba aiki bane,dan haka yaya kayi kuskure, ayayin da zehra zata zamo uwa,toh tabbas kai zaka kasance uba ne ga wa 'yannan 'yaya,daganan zamu gani ko zaka sake furta kalmar nan na zamowa uwa,zehra k**ar zatai kuka,bakin cikinta daya rayuwar karya su kawai sukeyi,agaban mutanen da s**a yadda dasu, javrece tai ajiyar zuciya hmmmm sannan ta mike ta tai tattaki ta nufo inda ayshe da nihat suke tace kasuwanci,karfin iko,aiki,duk basu bane saboda babu abun dazai maye gurbin da, dagowa da sauri ayshe da nihat s**ai s**a kalleta,cigaba da magana tayi tace ako da yaushe sai kuce komai lokacine,amma wani lokaci lokacin na yawa,basai mun sanya lokuta masu yawa ba,nasan kun fahimci me nake nufi,saboda Allah fah, ayshe nihat mamaki suke kallonta s**a tsaya yi,rikota nihat yayi yace hallaçim(antyna)me k**e fada ne haka,me yafaru?rungumarta yayi,k**ar zaiyi kuka,ayshe ma ruqota tayi,idon zehra ne yacika da kwalla,tashi tai da sauri tabar wajen,ba bata lokaci omer yace afwan tashi yai yabi bayanta,kallonsu alev take har s**a bar wajen.

S3
Mehtab ce tsaye tana kallon behton da wannan matar,magana tafara ita kadai tace ehhh haka zaku cigaba da tsayuwa kenan,ba inda zaku, kenan duk wani shirye shirye dama duk akan wannan kakeyi?dan haka bazan sake cemaka komai ba behton,afusace ta nufi inda suke,wayattace tafara ruri,tace kai me haka sai awannan lokacinne, tsayawa tayi tafara ciro wayar ajaka,dauka tai tafara magana,dan jin muryarta behton yayi,dasauri yajuyo,mamaki yayi,tace eh ina ji,nice a ina adreshin kace?,sauri behton s**ai s**a bar wajen, mehtab tace toh bakomai bak**ai kawai kabani adreshin wajen zanje na duba naga wani gidane,toh sai anjima,sauke wayar tai dasauri,taga basa nan,tace ehhh ina kuma s**a bace, ai daga yanzu kun dinga tsalle tsalle k**ar kwallo kenan,

S4
zehra ce tsaye jikin kofa idonta cike da hawaye,magana tafara ita kadai tace Zehra kina aikata karya,karya mafi girma,kina kallon cikin idonsu kina yi musu karya,nayi karya wa mahaifina,haka wa kanwata,zehra kuka take,komai karya ne daidai ta tsayuwata adakinnan duk karya ne,juyowa tai ga wannan photo da ayshe s**a basu,dauka tayi tana kallo.

tunani ta fada

S5
farkon lokacin da omer ke mika mata takardar kontragi akan tasa hanu,tace contragi kuma,yace eh zaki samu kudi ai,maganar likitane yafadowa omer arai,inda yake ce masa yar uwarka tana da wata 6 ne kachal aduniya,amma zaku iya ceto ta in kunso, jikinsa ne yadanyi sanyi,yabar yiwa zehra magana da izza yasaukar dakai,yace zaki nuni da munyi aurene amma na tsawon wata 6 ne kawai zakiyi,daga wata 6 nan shikenan zamu takaita wannan contragi tare da sa hanun lawyer na,maganar zuci zehra tafara,gwara na tafi idan ba haka ba zan iya fadawa ga halaka,mika mata omer yayi yace gashi kifara karantawa kafin kisa hanu,dan kada wani abu yabiyo baya bazan kyakeki ba,kallon takaddar zehra takeyi,sauri tai ta dauka tace babu abun dazai biyo baya,nuna min inda zan sa hanun kawai,yace a'a kifara karantawa mana,tace a'a ai na sallama,yace dakyau,biro yamika mata yace kisani zaki sa hanune akan kowani palle,maganar zuci zehra ta fara, meyake faruwane baba?!

S5
wajen daurin auren bogi na omer da zehra,madaurin aure yace malama zehra kaya shin kin yadda zaki dau malam omer karvanglcolr amatsayin mijinki?zehra tsilli tsilli👀 tayi da ido takasa magana,dagowa tayi ta kalli alev dasu damir dake tsaye gefe,halamu da kai alev take mata akan tace a'a, a'a,tana mai zare mata ido, razana zehra tasakeyi,omer ne yajuya yakalli inda ayshe,muzayyin,alev,dasauran jamaa ke tsaye,yaga duk idonsu akansu,dan buge hanun zehra yayi akan tai magana mana,dan tsoro zehra taji,sannan tace ëvit(eh)alkalin aure yace batare da bata mana lokaci ba k**ar yadda malama zehra kaya tayi,shin malam omer karvangclor ka yadda da zehra kaya amatsayin mata?dan shiru yayi yajuyo yakalli ayshe,yaga fuskarta cike da farinciki tana maiyi masa nuni dakai da kace eh eh yaya,dan murmushi omer yayi mata, alev ce idonta yacika da hawaye yayi jajir,juyowa ga alkali omer yayi yace eh,gaba daya wajen yadau tafi,alkalin aure yace daga yau kun zamo miji da mata,kusa hanu anan,biro alkalin aure yamikawa zehra,karba tayi ta sunkuyo kan takaddar kana tatsaya takasa signing,har alkali yafara kokonton ayya wannan tana son auren kuwa,omer ne yajuya yaga k**ar alkali yafara gano wani abu,dan murmushin karfin hali yaiwa alkali,sannan yajuyo ga zehra yamotso kusa da kunnenta rai bace yace kisa hanun mana,hanu na karkarwa zehra tasa hanu,

wani tunanin aka sake fadawa

S6
Inda alev ke fadin bakaken maganganu, a karshen na 173, omer yace alev inkinso kina iya gyara kalamanki,sannan soyayyarmu ba ta bukatar wata alama,saboda gaskiyace,ko bahaka ba,zehra ta gyada mai kai alamar hakane, dawowa zehra tayi daga dukkanin tunani,

S7
idonta duk hawaye,tace wannan duk karyane,shirine kawai, ajiye photon tayi rai bace,,tace wannan duk ba gaskiya bane,komai karya ne,tana cikin surutan nan saiga omer yashigo,jiki sanyaye shima,ganin yanayinta wani iri yace iyyim sil?(kina lafiya kuwa?hankali tashe tace masa iyyim(lfy)yace amma lokaci daya naga yanayinki yasauya,ko dan akan maganar alev ne?kuka zehra tafara tace azahirin gaskiya bamu da wani dalili najin haushin alev akan wannan,tun farkon wannan wasa take zargi har izuwa yanzu,omer yace ranki yabaci ne,tace a a ni lfy nake,tafiya tafara yace kice baza dai kifadi asalin abun dake faruwa ba,biyo bayanta yayi,tsayawa tai takallesa tace babu komai, ba abun da ya faru, yace,ki gaya min nace,ina jinki,fada min,tace ta ciki....yace eh ina ji, tana kuka tace azahirin gaskiya bana jin dadi ta ciki na kallon idon ayshe da muzayyin da mukeyi muna yi musu karya,yace kenan ba akan alev ko zobe bane ba?tace a'a ba akan ko daya ba, alev ko zobe ba akansu ba ne, akan karya da mukeyi akullum shine,abun na qonani sosai,yayi muni sosai,na so ace munyi musu adalci,duba da yadda suke da mafarkai masu kyau akanmu sosai,suna tsammani daga garemu, jikin omer ne yayi sanyi shima k**ar yayi kukan yake ji, tattaki zehra tayi tabar inda yake,sake biyo bayanta yayi,yace ke...? dan rarraba ido zehra tafara.

S8
Kamfanin karvangloer layla da mard ne a ofishin omer suna 'yan dube duben wasu file......

hmmmmmm nagaji fans, yau gaba daya namanta da cewa taba kalashe ne sai rubutu nake tayi,episode inne gaba daya yasani tausayi nashiga yanayi..........

wannan sati baza mi vidiyo ba sai satin sama in sha Allah, zami na 175,hakan yafaru ne asak**akon ciwon ido da nakeyi bazan iya fassara,editing daura murya, aikin dayawa kuma duk ido dole yakasance akan na'ura,ahalin da ake ciki kuma,idon basa bukatar haske ayanzu,abisa wannan dalili awannan sati kui hakuri da taba kalashen kawai! Nagode, mai yi muku fatan alkhairi

ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA.'Yata, gobe zaki daina amsa sunanki na 'yata. Zakiyi auren far...
14/08/2021

ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA.

'Yata, gobe zaki daina amsa sunanki na 'yata. Zakiyi auren farin ciki kuma zaki auri muradin ranki wanda k**e kauna.

Kada kiyi kewata domin na cika burina na aurar dake ga wanda k**e kauna, yanzu kuma ya rage naki ki cika naki burin.

Daga yarintarki, na samu nabaki tarbiya cikin ikon Allah ko? Kafin ki amsa mini da cewa eh, akwai wani abinda nakeso na fada miki dangane da zama da mijin aure na kasancewarki matar aure.

Kina tuna lokacin da kika rubuta jarabawar WAEC da JAMB?
Kinzo kinsameni na baki #20,000 na registration?
Duk da cewa na baki, toh kudin ba nawa bane. Nasan kin dauka cewa ni na biya miki kudin. Maganar gaskiya shine lokacin bani da sisi, Mahaifiyarki ita tabani. Tanada damar da zata baki kudin da hannunta, amma sai ta bani nikuma na baki.

Ki zamto mai tallafawa mijinki. Wani lokacin rayuwa takan tsananta, mijinki zai iya zamowa a fusace, domin rayuwa tayimar daurin tamtam, zai iya jin tsoron kada ya rasaki domin abin hannunshi ya kare a wannan lokacin, toh a wannan yanayi ne yake bukatar tallafinki, ki zamto mai bashi karfin guiwa sosai.

Babban hanyar da zaki bi wajen nunawa mijinki kina kaunar shi shine kina girmamashi da kuma girmama ra'ayinshi!.

Ta yiyu kuyi jayayya tsakaninku, ko kuma kiki aminta da ra'ayinshi, amma a karshen ranar ki nunamar cewa ya cancanci ki girmamashi. Ki tuna lokacin da nayiwa Mahaifiyarki tsawa? meye tayi lokacin? Shiru tayi.

Kina kuma iya tuna wani lokaci data mini tsawa? Meye nayi? Shiru nayi nima lokacin.

Yake 'yata, ki zamto mai shiru ga mijinki lokacin da yayi fushi. Lokacin da dayanku zuciyarsa ke tafasa, dayanku ya tabbata zuciyarsa tana sanyaye. Idan ma'aurata biyu dukkansu suna tsawa wa juna a tare, ananne babbar matsalar aure ke somawa.

Farkon abinda yak**ata kisani dangane da mijinki shine ki bashi abincin dayafi so! Idan sunada yawa, ki tabbata kin sasu a ranki. Kada kibari sai ya roka kimar hakan, ki zamto kinayi ba sai ya nema ba.

Akwai wani lokacin da Mahaifiyarki ta k**ani ina wasa da hannun wata mata, tabbass matar ta janye hankalina amma bawai ina cutar da mahaifiyarki bane. Lokacin data ganmu, batayi fada da matar ba, kawai k**a hanyar ta tayi ta wuce batacema kowa uffanba. A ranar naji tsoron komawa gida domin ina tsoron abinda zan tarar a gidan idan na koma. Amma sai nayi ta mazan na koma gida. Kuma wallahi batace mun uffan ba. Ta hadamin abinci k**ar yadda ta saba. A hakan a tsorace nake domin nasan abinda na aikata. Sai na fara bata hakuri ta kuma cemun babu komai ya wuce. Daga wannan rana ban sake yima wata mace kallo na biyu ba.

Waye yasan meye zai faru da ta yimin masifa da balbalin bala'i? Watakila dana fita na bar mata gidan na koma wajen waccan matar data k**ani da ita.

Wani lokacin shiru kan zamo silar sulhu maimakon fada da masifa da balbalin bala'i.

Ki manta da wadancan littattafan na soyayya da k**e karantawa lokacin kina budurwarki. Kin tuna wadancan finafinai na soyayya na India da American? Wasu Nollywood Movies dinnan? Ki manta dasu, kada ki tsammanin rayuwar aurenki zata zamto irin wadancan.

Rayuwa a zahiri ba k**ar wacce wasu Directors da marubuta, su Artist da Producers s**a rubuta bane, rayuwar aure Allahu Jalla Wa Azza ne ya ke Directing kuma shine Producer, shine Artist.

Abu na karshe dana bukata kisani shine....... Ki dunga tuna lokacin da aka haifeki?

Bayan aure na da Mahaifiyarki, rayuwa ta tsananta garemu. Mamarki ayyuka biyu takeyi domin ta tallafa mana, bawai bana aiki bane, nima ma'aikaci ne. Ina dawowa gida karfe 6 na yamma, ita kuma karfe 8 na yamma take dawowa a gajiye. A hakan bata ta6a hanani abincin dare ba ko kuma kin kulawa da wajen kwanciyar mu ba. A hakan aka samu aka haifeki cikin ikon Allah.

Kada ki kuskura ki hana mijinki kanki ko abinci komai gajiyanki, ki zamto mace tagari.

GA TAKAITATTUN KANUN LABARAN DUNIYA.............! Daga shafin Al-bayan"Wata uwa ta yaiyanka kafafun diyartata da sabuwar...
14/08/2021

GA TAKAITATTUN KANUN LABARAN DUNIYA.............!

Daga shafin Al-bayan

"Wata uwa ta yaiyanka kafafun diyartata da sabuwar reza fil a garin zariya Jihar Kaduna bisa laifin diyartata na ficewa gida batare da sanar da iyayentaba."

"Hukumar kula da raya birane ta BOGIS ta rushe masallatai 11 da coci 4 a Maiduguri.

"Majalisar Zartarwa a Najeriya ta amince da sake dawo da harajin da ake karba daga motoci a manyan titunan kasarnan.

Gwamnatin Najeriya zata dawo da yin rigakafin cutar COVID19 a ranar 16 ga watan augustannan.

"Wasu matasa 4 sun shiga komar yan sanda bisa k**asu da laifin kai farmaki gidan ruwa a jihar kano a karamar hukumar Gabasawa."

"Wani babban lauya mai suna Malcom Omirhobo a Najeriya ya shigar da kara kan a cire Najeriya daga cikin kasashen musulmin duniya."

Kotu ta dakatar da gwamantin kan gina sabbin shaguna bisa kan hanya a kantin kwari.

Cutar annobar korona ta kashe matar tshohon shugaban kasar Najeriya shehu usman Aliyu shagari hajiya Hadiza."

Mamakon ruwan sama ya cinye mutum 5 yayi dambarwa 1.567 cikin garuruwa daban-daban a jihar Bauchi.

Gwaman zulum ya sake gina coci guda 9 da boko haram s**a lalata."

"Hukumar hizba ta jihar kano ta samarwa da kanta kotu mai zamankanta."

Majalisar dinkin duniya zata kawoma Arewacin Najeriya agajin gaggawa."

Gwamana Amiu Bello Masari yace" yin watsi da ma'adanai da sauran albarkatun kasa ya kara ruruta rashin tsaro a Najeriya."

Shugaban Kungiyar Hizbullah dake kasar labanon Sheikh Hassan Nasrulah yayi aniyar kara daura damaran kaiwa isra'ila harin bazata ba dare ba rana.

"Wutar daji taci ta cinye wani yanki dake kasar Aljeriya."

Gwamna masari yayi kira ga kasar koriya ta kudu data taimak**a Jihar Katsina da sana'oin habaka harkan noma da sauran sana'oin dogaro da kai.

Kotu ta rike wasu makiyaya 8 bisa k**asu da laifin garkuwa da mutane a jihar Oyo.

Yadda mahara s**a addabi wadansu yankuna a jihar sokoto, harin da yayi sandiyyar hijirar dimbin daruruwan al'umma."

Kwamishinan lafiya ta jihar gombe yace" cutar kwalara ta barke a jihar inda inda mutum 44 s**a kamu da cutar a unguwar Shamaki Bolari-Gabas, da Harwagana."

"An yi kuren binne wata matashiya mai suna sa'adatu lawal kafur jihar Katsina bayan da aka gane cewa" doguwar suma tayi.

Gwamnatin Najeriya ta janye harancin amfani da tuwita a Najeriya."

Gwamnatin kasar habasha ta halastama al'ummar kasar su samarwa kan su mak**ai domin kare kai.

Rundunar sojojin Najeriya tayi watsi da rahoton dake cewa" zata saki makaya boko haram dake hannunsu.

"Najeriya ta shiga jerin kasashe 10 da bashi yai fiwa katutu a duniya."

Jami'iyyar APC ta kori Wanda yace inama shugaba buhari ya mutu.

English Premier LeagueHT: Brentford 1-0 ArsenalSergi Canos ⚽bayan shekaru 74 yau Brentford ta zura kwallo a gasar Premie...
13/08/2021

English Premier League

HT: Brentford 1-0 Arsenal
Sergi Canos ⚽

bayan shekaru 74 yau Brentford ta zura kwallo a gasar Premier League, barka da dawowa..

Daga shafin Al-bayan

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar da ya kai a birnin London inda ya je duba lafiyar sa.
13/08/2021

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar da ya kai a birnin London inda ya je duba lafiyar sa.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJU'UN!!!AMBALIYAR RUWA CIKIN GARIN ARGUNGU JIHAR KEBBI.DAGA shafin Al-Bayan Ansamu ambaliya...
13/08/2021

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJU'UN!!!

AMBALIYAR RUWA CIKIN GARIN ARGUNGU JIHAR KEBBI.

DAGA shafin Al-Bayan

Ansamu ambaliyan Ruwan sama mai karfi cikin garin Argungu jahar Kebbi. Inda tayi sanadiyyar raba wasu magidanta da muhallansu, tareda asarar rayuka da dama tare da cinye gonakai acikin garin Argungu Jahar Kebbi.

Lamarin ya faru a yammachin yau Juma'a, ba'asan adadin iya dukiya da rayuka da s**a salwanta.

Wani magidanci maisuna Mal Garba Aliyu Augie ya bayyana wannan ambaliyan a matsayin ambaliyan na farko da ya taba gani arayuwarsa saboda irin ta'adi da ruwan yayi cikin garin Argungu da kewaye.

Al'umar gari neman gwamnati data kawo musu dauki a yashe musu magudanar ruwa domin saman wadatacciyar hanya ruwa.

Musa Garba Augie Yayi Addu'a Allah ya kiyaye na gaba yakara karemu da kariyar sa, Yaa Hayyu Yaa Qayyum. Allah yabada ikon gyarawa.

El rufa'i na cikin koshin lafiya muna tare dashi a kasar London ~Sanata Uba saniDaga Shafin Al-Bayan A wani hoto da Sana...
13/08/2021

El rufa'i na cikin koshin lafiya muna tare dashi a kasar London ~Sanata Uba sani

Daga Shafin Al-Bayan

A wani hoto da Sanatan Kaduna ta tsakiya ya fitar Malam Uba sani
Ya nuna cewa Tabbas Gwamna Nasir Ahmad El rufa'i na jihar Kaduna na cikin koshin lafiya
Sanatan ya wallafa Yana Mai nuna cewa yau da safe suna kasar London tare da El'rufa'i suna tattauna batutuwan da s**a shafi jihar Kaduna da cigaban ta.

Ga bayanin da Sanatan ya wallafa fassara.

Ya ku al'ummarmu ta jihar Kaduna Masoyan zuciyarmu mun kasance a yau tare da Gwamna Nasir El-Rufai cikin yanayi Mai kyau mara misaltuwa duk domin tsara tunani, k**ar yadda muka saba, mun kasance tare da sauran membobinmu a safiyar yau a kasar Landan, kan samar da hanyoyin ci gaba da dorewar cigaba a jihar Kaduna.

Idan baku manta ba dai A yau ne dai kafofin sada zumintar zamani ya cika da ra'de-ra'din cewa an garzaya da Malam Nasiru Ahmad El rufa'i zuwa kasar London sak**akon rashin lafiyar dake damunsa Wanda wasu ke cewa a halin yanzu Gwamnan baisan a Ina yake ba.

Allah ya kuɓutar da iyalan wannan mutum daga hannun ƴan bindiga Daga Shafin Al-Bayan Bawan ALLAH da muka kawo muku labar...
13/08/2021

Allah ya kuɓutar da iyalan wannan mutum daga hannun ƴan bindiga

Daga Shafin Al-Bayan

Bawan ALLAH da muka kawo muku labarinsa a Shekaran jiya, wanda BARAYI 'YAN BINDIGA s**a shiga gidansa a garin Gusau, s**a harbe shi a hannu, sannan s**a tafiya da Matarsa da kuma karamin dansa.

To Alhamdulillahi, yau Matarsa da dan nasa sun kubuta daga hannun 'Yan Ta'addah.

Ka taba zuwa garin Gembu da Ngroje dake hawar mambila? Daga Shafin Al-Bayan Garin yafi ko'ina matan fulani kyawawa a 🇳🇬b...
13/08/2021

Ka taba zuwa garin Gembu da Ngroje dake hawar mambila?

Daga Shafin Al-Bayan

Garin yafi ko'ina matan fulani kyawawa a 🇳🇬banda Yola.

Abubuwa 14 da yak**ata kasani kan Duten Mambila.
1- Dutsen Mambila yana Jahar Taraba 🇳🇬 kuma shine wuri mafi sanyi a Nageriya baki daya.

2-Sabida tsaban sanyi yasa mutanen wurin basa anfani da Firji, AC, ko fanka, domin dunk wani nauin kayan sha ko yaushe da sanyin sa.

3-Kowa a garin ya iya fullanci duk dacewa manyan yaruka da kabilu 4 ne a yankin wanda s**a hada da Mambilawa, Fulani, Panso da Kakah.

4- Hotel yanada araha a yankin domin akuwai dakin ₦500.

5- Garin sunada arzikin duwatsun 💎 daimond da blue sapaya, kana sunada arkin shanu shiyasa nama yake da araha a yankin.

6- Sunada nau'in kayan itace da nau'in abinci daban daban harda wanda baka taba ganiba b***e ci, wanda s**a hada da piya, ayaba, chanis apple, mangoro, bulumji, deppi, dankalin turawa, samaije da sauransu, malam ko malama gwaiba kam tun a hanya zaka tsaya ka tsinka a hanya.

7- idan kanason kaga kyawawan mata kuma idan kaje garin Gembu, jeka Science School, ko kuma ka zauna a legas line ranar jumma'a, wallahi duk wata kyakyawar da ka santa a Bollywood sai kaga wacce ta fita kyau ranar da ake wani taronsu na sallah a kofar sarki da ake kira (baggu boror)

8-kauyukan da suke da kyawawan mata a dutsen mambila su hada da, Kakara, Leme, Yarimaru, Mayo-ndaga, Dorofi, Nguroje, da Galadima.

9- Dutsen yafi ko ina yawan itacen zaiti a 🇳🇬.

10- Kanawa sunfi kowa son auren yan yankin.

11- Babu sauro a garin.

12- Idan kaje otel cin abinci zakaga wani kwano da soyyayyen borkono idan zaka sa kar ya wuce digo 3, don kanasa yawuce hakan abincin bazai ciyu ba don borkononsu nada zafi.

13- Manyan garuruwa da suke kan dutsin mambila sun hada da, Gembu, Nguroje, Mayo-ndaga(dago cede) da Mai samari.

14- Bayan kan duten yanada sanyi akuwai kuma gari 2 da yafi ko ina sanyi a yankin, wanda sune Gurgu da Ngroje.

Idan ka/kin taba zuwa gaya mana yanayin yadda ka samu garin ciki a comment naka/ki

ALHAMDULILLAH yadda Sallar Juma'a ya Gudana a Masallacin Ƙudus (Al'aƙsa )Allah Ya karawa Annabi Daraja
13/08/2021

ALHAMDULILLAH yadda Sallar Juma'a ya Gudana a Masallacin Ƙudus (Al'aƙsa )

Allah Ya karawa Annabi Daraja

Da Dumi-Dumi: An Garzaya Da El Rufa’i Kasar Waje Neman LafiyaRuhotannin da suke shigo mana daga majiyar mu ta fadar gwam...
13/08/2021

Da Dumi-Dumi: An Garzaya Da El Rufa’i Kasar Waje Neman Lafiya

Ruhotannin da suke shigo mana daga majiyar mu ta fadar gwamnatin Jihar Kaduna ya tabbatar mana da cewa Mai girma gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmed El Rufa’i na kwance a wani asibitin ketare ana duba lafiyarsa .

Majiyar mu daya bukaci a sakaya sunansa yace ko a shekaranjiya laraba da shugaban dakarun sojin kasan Najeriya General Yahaya Bello yazo Kaduna ziyarar aiki na musamman akan sha’anin tsaro amma bai samu damar ganawa da gwamnan ba, sai dai yayi wa mataimakiyar gwamna Hajiya Hadiza Balarabe wanda a yanzu ita ke jan ragamar Jihar Kaduna kamin El Rufa’i ya dawo, inda shugaban dakarun sojin yai mata bayanin zuwansa Kaduna.

Duk da dai majiyar mu bai San wani irin ciwo bane yasa aka kai gwamnan asibitin ketare,Amma wakilin mu ya tuntubi Mai taimakawa gwamnan akan sha’anin watsa labarai, Mallam Ibrahim Amma haryanzu da muke rubuta wannan rahoton bai kira yayi mana karin haske ba Kuma bai aiko mana Koda amsar sakon karta kwana da muka tura mai ba.

Zamu kawo maku cikakken rahoton yadda lamarin yake da zarar mun samu sahihin Bayani daga makusanta gwamnan.

Allah ya bashi lafiya da dukkan marasa lafiya dake gida da asibiti Amin

Zan gina jami'ar musulunci ne domin taimakon talakawa, kuma ko sisi ba zasu biya ba--Rochas
10/08/2021

Zan gina jami'ar musulunci ne domin taimakon talakawa, kuma ko sisi ba zasu biya ba--Rochas

Wani fasto a kasar Zambiya ya sa a binneshi da ransa bisa alkawarin zai dawo bayan wani dan lokaci.Faston dai Mai suna J...
08/08/2021

Wani fasto a kasar Zambiya ya sa a binneshi da ransa bisa alkawarin zai dawo bayan wani dan lokaci.

Faston dai Mai suna James Sakala dan asalin kasar Zambiya ne.

Lamarin ya faru ne a kasar Zambiya a wata Babbar Chochi mai suna Zion Church mallakar sa.

Sai dai bayan kwanaki 3 aka tarar da gawarsa ya mutu.

Rahotanni dai sun bayyana cewar Mabiya darikar Chochin ne su ka binne shi tare da yi musu alkawarin zai dawo nan da kwana 3.

Bayan kwana 3 mabiyan nasa sun tono shi, sai su ka ga gawar shi ba rai.

Ya Allah ka rabamu da aikin Jahilci.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIOON!!ALLAH YA KARBI RAN SHEIKH ZARBAN ALGAMIDY!!!Maigidan wadannan Malaman kuma Malaminsu...
06/08/2021

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIOON!!

ALLAH YA KARBI RAN SHEIKH ZARBAN ALGAMIDY!!!

Maigidan wadannan Malaman kuma Malaminsu, Uba garesu!!

(1) Dr Muhd Sani Rijiyar Lemo
(2)Dr Bashir Aliyu Umar
(3) Sheikh Abdulwahab Abdallah
(4) Dr Abubakar Birnin Kudu
(5) Dr Mansoor Sokoto
(6) Dr Jalo jalingo
(8) Dr Muhammadul Hajj Abubakar
(9) Dr Basheer Imam
(10) Dr Muslim Ibrahim

Uban kowanne dan Nigeria a Jami'ar Musulunci ta Madina!!

Ko kun san shi da hannunsa ya dauko ya zabo Malam Ja'afar da Dr Sani donnkaisu karatu Madina!!

Allah yayi maka rahama ya sa ka huta ya sanya Aljanna ce makomarka, ya gafarta maka kurakurenka!!

Shukar da kayi a Nigeria ta tsiro ta yi yabanya!

Maganata da shi ta karshe duk sai da ya tambayeni labaran Manyan malamanmu da Da'awarsu da Iyalansu da rayuwarsu, Ina fada masa ya na zabga musu Addua'a irinta Uba ga 'yayansa!!

Shine mai bugawa dukkansu waya duk Ramalana lokacin tafsiri ya gaida masu sauraroya ya yi musu Nasiha!!

Allah ka hada kan almajiran Dr Sheikh Zarban ka sanyawa Da'awarsu albarka ka kara musu iklasi.
ameen

Da'awah a Nigeria ta yi rashin Uba, Manyan Malaman Sunah a Nigeria sun zama marayu.

Daga Shafin Al-bayan

Da gaske hukumar FBI ta wanke Abba Kyari daga zarginsa kan Hushpuppi? Qarya ne kawaiLabarin da ke iƙirarin an wanke shah...
06/08/2021

Da gaske hukumar FBI ta wanke Abba Kyari daga zarginsa kan Hushpuppi? Qarya ne kawai

Labarin da ke iƙirarin an wanke shahararren dan sandan Najeriya Abba Kyari da ke fuskantar tuhumar rashawa a Amurka ya mamaye shafukan sada zumunta a ƙasar.

Labarin wanda aka fi yaɗa wa a kafar WhatsApp ya ambaci hukumar bincike ta FBI a Amurka da ke cewa "ba a tuhumar DCP Abba Kyari.

"An ambaci sunansa ne kawai amma ba a tuhumarsa da aikata zamba kuma babu wani laifi da ake tuhumarsa," in ji sanarwar da ake ta yaɗawa a kafofin sada zumuntar.

BBC ta yi bincike domin tabbatar da gaskiyar labarin, ko da gaske ba a tuhumar babban jami'in na ƴan sandan Najeriya.

Kuma binciken da BBC ta gudanar ta gano cewa babu ƙamshin gaskiya a labarin domin babu wata sanarwa da ta fito daga rundunar ƴan sandan Najeriya da ke tabbatar da hakan.

Haka kuma hukumar bincike ta FBI ta Amurka ba ta wallafa wani sabon bayani ba da ya ambaci Abba Kyari ko kuma batun wanke shi daga zargin alaƙarsa da matashin ɗan Najeriya da ke fuskantar tuhuma a Amurka bisa hannu a manya-manyan ayyukan zamba na duniya Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Ko da yake jami'in ɗan sandan na Najeriya, Abba Kyari ya musanta karbar rashawa a hannun Raymond 'Hushpuppi' Abbas, amma an dakatar da shi daga muƙaminsa.

Abin da muka sani?

Sashen shari'a na Amurka ya ce ya k**a wasu ƴan Najeriya mazauna Amurka uku da s**a taimaka wa Raymond 'Hushpuppi' Abbas ya yi damfarar dalar Amurka miliyan 1.1.

Cikin wata sanarwa wadda sashen ya fitar a ranar 28 ga watan Yuli , ta ce Hushpuppi ya amsa laifin halasta kudaden haram da wasu laifukan masu alaka da kasuwancin intanet.

Kuma sun yi zargin cewa Hushpuppi ya bai wa mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya Abba Kyari cin hanci domin k**a takwaransa Kelly Chibuzo Vincent, mai shekara 40 da haihuwa.

Bayanin sashen shari'ar ya bayyana hakan ne bayan da Vicent ya yi kokarin tona asiri da kuma ba da bayanai kan zargin abin da s**a yi masa.

"A cewar sanarwar, Abba Kyari wanda babban mataimakin shugaban 'yan sandan Najeriya ne, shi ake zargi da kitsa k**a Vicent tare da aike wa da shi gidan yari, ya kuma dauki hotonsa ya aika wa Abbas.

"Abba Kyari kuma an yi zargin ya aika wa Abbas bayanin asusunsa na banki wanda nan ne Abbas ya aika masa kuɗaɗen ladan k**a Vicent tare da tasa ƙeyarsa gidan yari,"k**ar yadda bayanin kotun ya bayyana.

GA TAKAITATTUN LABARAN DUNIYA Kungiyar samari a Najeriya sun koka kan rashin matsi na tantalin arziki dayake sanyasu ras...
06/08/2021

GA TAKAITATTUN LABARAN DUNIYA

Kungiyar samari a Najeriya sun koka kan rashin matsi na tantalin arziki dayake sanyasu rashin aure a kan lokaci, kungiyar tayi kira ga iyaye dasu sassauta kayan lefe a dawo da hada kayan lefe k**ar nada."

Wata matashiya 'yar kimanin shekara 23 Barr Fa'iza Abdullahi Miko haifaffiyar garin Zariya Jihar Kaduna ta kammala karatun zama cikakkiyar lauya bayan shafe shekaru 5 cur da tayi a jami'ar Ahmadu Bello Dake Zariya."

Cutar amai da gudawa ta kwalera na haddasa asarar rayuka a jihar Jigawa , lamarin da ya sa mutane cikin zaman dar-dar da fargaba.

Jamus da wasu kasashe na taimaka wa Najeriya don cafke hauren giwa da ke fitowa daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 22.

A Jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da auren gida ko auren zumunci wanda a zamanin baya ya zama hantsi leka gidan kowa.

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta janye ma’aikantanta daga daga yankin da ke magana da Ingilishi na Kamaru sak**akon rikicin da ake fama da shi.

A birnin Bagdag, an gudanar da bikin mika wa Iraki kayyakin tarihin fiye da 17,000 da aka wawashe a yayin yakin da Amirkan ta kaddamar, lamarin da ke zama irin sa mafi girma.

"Akalla mutum dubu 278k ne s**a halaka a sanadiyyar wata mummunar gobara a kalfoniya dake kasar Amurka.

"Yan Najeriya miliyan 4.4 ne ke fama da yunwa da batara a Najeriya."

"Tsahon gwamnar kano Dominic Oneya ya mutu.

Rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da yarbawa ya barke a jihar Ogon, inda aka kona mutum 7 tare da kaddarori babban dankasuwarnan ta afirka wato Dangote yadda wannan rikcin yayi sanadiyyar rasa tirelolinshi har guda 11 bayan konasu da akayi guda 4 ne daga cikin motocin s**a kone kurmus.

Gwamnatin tarayya zata saka hannun jarinta a kamfanin matatan man fetur na dangote daya Naira Dala biliyan 276.

Rundunar 'yan sandar jihar Ikawa ibbom ta cafke budurwar data halaka saurayinta ta hanyar caccaka mashi wuka, kana kuma ta arce mashi da sabuwar motarshi kirar (Mercedes Benze).

" An rantsar da sabon shugaban kasar Iran Ebrahim bayan babban zaben da akayi a watan yuni.

Rashin sakinma makiyaya mara suyi fitsari a duk ta dalilin da gwamantin jihar katsina ta rattafa hannu kan hana makiyayan kiwo barkatai fadin jihar ya jawo cecekuce."

Duk shafin Al-Bayan

Address

Abuja
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sahara Reporters Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sahara Reporters Hausa:

Videos

Share

Category


Other Newspapers in Abuja

Show All