Bidiyon yadda aka samu saukar ruwan sama a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Kafin saukar ruwan saman, matakin zafi a ƙasar ya kai maki 47°c.
🎥: Inside The Haramain
Faifan bidiyon yadda maniyyata ke jifan shaidan a Jamrah.
🎥 Inside the Haramain
Faifan bidiyon yadda maniyyata suka gudanar da Sallar Azahar da La'asar a masallacin Nimrah na birnin Mina, karkashin jagorancin Sheikh Maher Al Muaiqly.
🎥 Inside the Haramain
BIDIYO: Yadda ake hada-hadar dabbobin layya a Kasuwar Dabbobi ta Gandun Albasa da ke Jihar Kano a Nijeriya.
Manyan Labarun LEADERSHIP Hausa ta 14/06/2024
Shirin namu na yau zai kawo muku labarai da rahotannin da jaridarmu ta LEADERSHIP Hausa ta wallafa a wannan makon. Inda babban labarinta ya mayar da hankali kan Tsadar Rayuwa da Yadda Magidanta Ke Sama WA Kansu Mafita yayin da ake fuskantar bukukuwan Sallah Babba. Haka nan akwai sashen nan na Madubin Rayuwa da ke kawo muku tsaraba iri-iri game da abubuwan da suka shafi zamantakewa. Sai ɓangaren wasanni da kuma labarun ƙasashen waje.
Faifan bidiyon yadda wasu ƴan ƙasar Syria da yaƙi ya raba su da ƴan uwansu ke rungumar juna cikin farin ciki yayin haɗuwarsu a Saudiyya domin aikin Hajjin bana.
🎥: Aminiya| Facebook
Siyasar Jihar Kaduna Da Cikar Dimokuraɗiyyar Nijeriya Shekara 25
Shirinmu na yau zai fara ne da kawo muku manyan labarun da wasu jaridu suka wallafa a yau Alhamis 13/06/2024. Za kuma mu tattauna al'amuran da suka shafi siyasar Jihar Kaduna da kuma cikar Nijeriya shekara 25 da mulkin dimokuradiyya ba tare da yankewa ba, tare da babban baƙonmu, Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Mazaɓar Zariya a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Mahmoud Lawal. Kana za mu duba batun ci gaba da shari'ar rikicin sarautar Kano a yau.
Yau Ake Bikin Ranar Demokuradiyya A Nijeriya
Shirinmu na yau zai fara ne da kawo muku manyan labarun da wasu jaridu suka wallafa a yau Laraba 12/06/2024 (LEADERSHIP da Vanguard). Za kuma mu tattauna batun ranar bikin demokuradiyya da ake yi yau a Nijeriya.
Labarun wasannin yau Talata 11-06-2024
Benjamin Sesko ya amince zai ci gaba da zama a RB Leipzig
Manchester United za ta bayyana makomar Ten Hag a wannan satin
Ɗan wasa Frankie de Jong ya fita daga tawagar ƙasar Netherlands sakamakon ciwo
Batun Sake Fasalin Wa'adin Mulkin Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni
Shirinmu na yau zai fara ne da kawo muku manyan labarun da wasu jaridu suka wallafa a yau Talata 11/06/2024. Za kuma mu tattauna batun matsananciyar yunwar da ake fuskanta a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya, kana mu duba batun neman sake fasalin wa'adin mulkin shugaban ƙasa da gwamnoni.
Labarun wasannin: Manchester United ta yi wa Jadon Sancho farashi
Labarun wasannin yau Litinin 10-06-2024
Arsenal ce a kan gaba wajen zawarcin Joshua Zirkzee
Manchester United ta yi wa Jadon Sancho farashi
Real Madrid tana ci gaba da tattaunawa da wakilan Alphonso Davis
Manchester City za ta karawa Foden sabon kwantiragi
Barka Da Hantsi Nijeriya: Rashin Amincewar Gwamnoni Kan Biyan N60,000 Mafi Ƙarancin Albashi
Shirn namu na yau zai fara da kawo muku manyan labarun da jaridu suka wallafa a yau Litinin 10/6/2024. Kana za mu duba kalaman da Gwamnoni suka yi na cewa ba za su iya biyan mafi karancin albashi 60,000 ba duk da tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa ƙungiyoyin Kwadago na biyan N62,000.
BIDIYO: Ku kalli yadda wasu fankoki ke fesa turaren ruwa mai daɗin ƙamshi a Masallacin Haramin Makkah, don samar da kyakkyawan yanayi na shakar iska mai daɗi ga maniyyata yayin gudanar da Aikin Hajjin bana.
🎥: Inside the Haramain
Fasahar Shuka Kankana A Tsaye
Tsarin noma na yin shuka a tsaye na taimakawa kasar Sin wajen kyautata aikin samar da kankana
Masu kallonmu, barka da war haka, ta yaya kuke shuka kankana a wajajenku? Yanzu manoma a lardin Shandong dake gabashin kasar Sin suna shuka kankana a tsaitsaye, tare da amfani da ingantattun dabarun rarraba kankana cikin rukunoni daban daban, domin tabbatar da ingancinsu.
A maimakon shuka kankana cikin gonaki kamar yadda aka saba yi, kankanan da aka shuka a tsaye na iya samun isasshen hasken rana, lamarin dake kaiwa ga cimma nasarar kyautata ingancin kankanan. Dabarar shuka kankana a tsaye, tana sanya yin tsimin fili, da saukakawa tare da kyautata ayyukan manoma yadda ya kamata.
Kowace gora ta hada kankana guda daya. Domin kula da kankanan yadda ya kamata, a kan saka alama a kan kowanensu, wadda ke nuna ranar haduwar hodar furanni, ta yadda manoma za su yi girbin kankanan bayan kwanaki 50. Ban da haka kuma, ana amfani da fasahar rarraba kankanan cikin rukunoni daban daban da na’ura mai kwakwalwa, wajen tabbatar da ingancinsu. Kana, kafin a kunshe kankanan, a kan saka lamba a kan kowace kankanar a matsayin katin dake dauke da bayaninta, ta yadda masu sayayya za su iya gani.
To, masu kallonmu, ko kuna son dandana irin wannan kankanar da aka shuka a tsaye?
Yadda Cinikayya Ta Yanar Gizo Ke Bunƙasa A Ƙasar Sin
Cinikayya ta yanar gizo ta samu ci gaba cikin sauri a kasar Sin a watanni hudu na farkon bana
Sabbin alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar a kwanakin baya bayan nan sun nuna cewa, a cikin watanni hudu na farkon bana, wato daga watan Janairu zuwa watan Afrilu, cinikayya ta yanar gizo a kasar tana ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri. Bari mu duba karin haske kan batun ta shirinmu na yau.
Kamfanonin Faransa suna cike da imani kan kasuwar kasar Sin
Sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewa, kamfanonin kasar Faransa suna cike da imani kan boyayyen karfin zuba jari a kasuwar kasar Sin. Bari mu duba karin haske kan batun ta shirinmu na yau.
Harkokin yawon bude yayin hutun bikin ‘yan kwadago a kasar Sin sun kara bunkasa
Yayin hutun bikin ‘yan kwadagon da ya kammala bada dadewa ba, harkokin yawon bude ido na kasar Sin sun bunkasa kwarai da gaske, al’amarin da ya taimaka sosai ga habaka tattalin arziki da kyautata rayuwar al’ummar kasar.
Manyan Labarun LEADERSHIP Hausa ta 7/06/2024
Shirin namu na yau zai kawo muku labarai da rahotannin da jaridarmu ta LEADERSHIP Hausa ta wallafa a wannan makon. Inda babban labarinta ya mayar da hankali kan yadda ƙarin albashi ya zama ƙarfen ƙafa a Nijeriya. Sai batun rikicin sarautar Kano da yadda tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami yake kallon dimokuradiyyar Nijeriya yayin da ta cika shekara 25 ba tare da yankewa ba a Jamhuriya ta huɗu. Haka nan akwai sashen nan na Madubin Rayuwa da ke kawo muku tsaraba iri-iri game da abubuwan da suka shafi zamantakewa. Sai ɓangaren wasanni da kuma labarun ƙasashen waje.
Jama'a da dama a faɗin Nijeriya na ci gaba da kokawa kan tsaɗar Dankalin turawa, wanda a wannan shekara ya yi tashin gwauron zabi da ba a taɓa samun irinsa ba, har a Jihohin da ake nomansa da safararsa zuwa sassa daban-daban na ƙasarnan.
Wasu daga cikin masu sayar da dankalin turawa a Jos, babban birnin Jihar Filato, sun shaida wa wakilinmu dalilan tsadar wanda suka danganta hakan da tashe-tashen hankula a sassan jihar.
Kun Taba Hawa Naurar Matakala Ta Zamani Irin Wannan?
#TafiyaMabudinIlmi# Faiza ta gabatar mana da wata naurar matakala ta zamani kuma irinta ta farko a birnin Beijing.
Bidiyo: CGTN Hausa