Arewasunshine

Arewasunshine Politics And Educational Contents

07/12/2023

💥BREAKING

Dangote Refinery Set To Commence Operations As First Crude Shipment Set To Arrive.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da cibiyar tuntubar cin zarafin mata ta jihar Katsina (SARC) ...
07/12/2023

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da cibiyar tuntubar cin zarafin mata ta jihar Katsina (SARC) da ke ba da agajin gaggawa ga yaya mata da ke fuskantar barazanar cin zarafi.

An kaddamar da Cibiyar ne a gidan yara dake cikin Birnin Katsina ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba 2023.

Isah Miqdad
SSA Digital Media
7/12/2023

08/02/2023

😭

07/08/2022

ABUJA , Federal Capital Territory of Nigeria 🇳🇬 has the street of every African capital cities named .
✍️ Not only African capital cities but African leaders and rivers and mountains used in naming its streets.

📌Notable among them are:

Haile Selassie street, Asokoro Abuja ( named after late Emperor of Ethiopia 🇪🇹).

📌Kwame Nkrumah crescent , Asokoro Abuja ( named after promiment Pan-African leader and Founding Président of Ghana 🇬🇭)

📌 Julius Nyerere crescent,Asokoro, Abuja ( Name after Late Founding Président of United Republic of Tanzania 🇹🇿)

📌 Patrice Lumumba Street , Abuja ( named after the slaughtered Pan-African leader and Founding Président of D.R ,Congo 🇨🇩).

📌Kilimanjaro , Abuja ( Kilimanjaro is in Tanzania 🇹🇿)
📌 Zambezi River crescent, Abuja ( Zambezi is in Zambia 🇿🇲)

📌 Bujumbura street , Wuse 2 ( named after capital of Burundi 🇧🇮).

📌Accra street , Wuse 5 ( named after capital of f Ghana 🇬🇭).
📌Addis Ababa, crescent , Wuse (named after capital of Ethiopia 🇪🇹).

📌 Harare Street, Wuse , Abuja ( named after capital of Zimbawe 🇿🇼) among others.

18/06/2022
Kwana ɗaya ya rage kafin wa'adin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeria na jam'iyyu su gabatar da yan takarar mataim...
16/06/2022

Kwana ɗaya ya rage kafin wa'adin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeria na jam'iyyu su gabatar da yan takarar mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023 ya cika

27/05/2022

Dr Dikko Umar Radda wins Katsina state
APC guber primary election

Are we on the same page?When you attach too much relevance to things that do not really matter, or are rather otiose, yo...
09/01/2022

Are we on the same page?

When you attach too much relevance to things that do not really matter, or are rather otiose, you will not cease to wonder where has the energy and time you often lavishly used go? and that in turn affects your daily productivity.

It is not all about the size or number, and neither the container does matter always. Quality and Content should be the carrdinal indicators in all our endeavors.

What we find ourselves doing daily, either out of compulsion or enthusiasm, is what yields the net effect of who we are today, and unless the riddle changes, the dance will automatically continue to remain the same.

Do not underate what you do today, especially regardless of its quantity, the quality is what counts tomorrow. keep pushing harder, and never get intimidated by the engagement or commitment of others. You either take it a motivation or focus on your consistency.

Develop yourself even if it means doing just one positive thing everyday.

Sabo Ibrahim Hassan

05/08/2021

On Saturday, October 1, 1960, Nigeria became an independent nation. What follows is Sir Abubakar Tafawa Balewa’s speech delivered at Tafawa Balewa Square in Lagos at the Independence Ceremony.

DANDALIN FASAHAWani yaro mazaunin kano mai suna Shuaibu Ibrahim ya kirkiro manhaja wachche da zata  rage kawo rashin nat...
02/05/2021

DANDALIN FASAHA

Wani yaro mazaunin kano mai suna Shuaibu Ibrahim ya kirkiro manhaja wachche da zata rage kawo rashin natsuwa a masallatanmu

A yayin da muke zantawa da shi yaron yache yayi duba da irin yadda wayoyin salula ke saka rashin natsuwa ga al'umma a yayin da ake sallah wanda hakan yana sanadiyyar a kawo kokonto a chikin sallah,sai yaga ya dache ya kirkiro wani abu wanda zai taimaka wajen kawo karshen rashin natsuwar da take faruwa a masallatanmu shine sai ya kirko manhaja mai suna 'Alhikma' wanda zai saka wayarka a chikin silent da zaran ka shiga masallachi.
Wannan manhajar tana da abubuwa k**ar haka.
1:App din zai mayar da wayarka silent da zaran ka shiga masallachi, kuma da angama Sallah zai chire ta daga silent.

2:Idan wani ya kiraka a yayin da kake sallah zai tura mashi da chewa kana Sallah.

3:Ko da ansamu daukewar wuta manhajar zata kunna flashlight watau hasken wayarka take yanke ba tare da ka kunna da kanka ba.

Abun ban mamaki da yaron yache ya fara kirkire kirkiren software tun yana dan shekaru takwas,wanda hakan ya bashi dama ya bugo littafi ba farko mai suna 'LEARN BATCH IN A MINUTES' a sheka runshi na shsbiyu(12 years).

Bayannan yaron ya kirkiri abubuwa da dama Kuma ya samu lambar yabo tare da lashe kyaututtuka da dama a mataki na sakndare.

Domin samun wannan manhajar sai ku shiga wannan link din👇👇👇
http://danjsoft.blogspot.com

Muna fatan Allah ya yawaita mana iri n wannan yaran a Arewa da Nigeria baki daya.

AN TSARA  TA'ADDANCIN BOKO HARAM AKAN RASHIN GASKIYATun kafin a kyasta ashanar rikicin Boko Haram ake k**a shugaban kung...
29/11/2020

AN TSARA TA'ADDANCIN BOKO HARAM AKAN RASHIN GASKIYA

Tun kafin a kyasta ashanar rikicin Boko Haram ake k**a shugaban kungiyar na farko Muhammad Yusuf ana kulleshi a Abuja, amma manyan mutane irin su Professor Jerry Gana suna zuwa su karbo belinsa saboda rashin gaskiya

Har zuwa lokacin da s**a dauki makami aka kashe Muhammad Yusuf, bayan an k**ashi maimakon a kaishi kotu saboda a boye gaskiya sai aka kashe shi, a ranar da s**a shelanta jihadi an harbi Abubakar Shekau da bindiga ya buya a garin Maiduguri, daga nan sai ya gudu Kano, Kaduna, Potiskum, Bama yayi ta jinya kafin ya shiga jejin sambisa a farkon shekarar 2013, tsawon shekaru 3 yana tsara ta'addancinsa ne a cikin gari, an ganoshi amma daga sama anki bada umarni a k**ashi saboda babu gaskiya ana so ya rayu ya cika burin makiyan Arewa

Bayan daukar makamin, Lokacin da Shekau s**a karbi hayan wani gida a Kano kusa da gidan tsohon IGP Hafiz Ringim, a 2012 majalisar shura na Boko Haram s**a kira meeting a Kaduna don su duba yiwuwar sulhu da gwamnati, (ina da sunayensu gaba daya) Shekau ya amince zai halarci tattaunawar, suna jiran zuwan Shekau daga Kano zuwa Kaduna kawai sai ga jami'an tsaro sun gewaye gidan, s**a k**a manyan Malaman na Boko Haram, amma Shekau an barshi ya rayu saboda rashin gaskiya

Daga nan Kaduna sai aka tafi dasu Abuja, maimakon a kaisu kotu sai aka bindigesu a inda suke tsare, sai aka yiwa 'yan Nigeria karya cewa wai sunyi yunkurin guduwa ne saboda rashin gaskiya, idan mazauna Abuja kun tuna, a wannan ranar ne aka tashi jirage masu saukar ungulu suna ta shawagi a saman Abuja musamman a inda aka harbe manyan Malaman kungiyar Boko Haram din wadanda s**a shirya yin sulhu da gwamnati ko su tona asirin Shekau

Salon yadda Boko Haram s**a fara kaddamar da harin bomb a dakunan bautar mabiya addinin kirista domin a hadu a tayar da yakin addini tsakanin Kiristoci da Musulmai a cikin kasa wadanda suke zaune lafiya, abune da aka tsara saboda rashin gaskiya

Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro marigayi Janar Andrew Azazi yace masu kitsa ta'addancin Boko Haram ana shan shayi dasu a fadar shugaban kasa, yana tona wannan asirin sai s**a saukeshi daga mukami, basu barshi ba kwana shida da saukeshi sai s**a dana masa tarko a jirgi s**a hallakashi, na yanzu kuma kwadayin tabbata akan mulki ya hanasu fadin gaskiya

Kisan gillar da aka yiwa Malamai irinsu Malam Ja'afar da Albaniy da zaratan sojoji wadanda s**a sadaukar da rayuwarsa a fagen yaki da Boko Haram, irinsu Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, salon kisan da salon kaddamar da harin babu gaskiya a ciki, shiri ne don a kawar da su saboda sun addabi Boko Haram

Duk wani 'dan Nigeria da ya san sirrin Boko Haram sai da aka masa barazana, aka kashe wasu, zasu k**aka su batar a doron kasa su kulle a kurkukun karkashin kasa don su ma barazana ka dena tona asirinsu, idan kaki sai su ma sharri ko su kashe ka

Manyan kasashen waje suna da hannu a hura rikicin Boko Haram, suna taimakon Boko Harama kai tsaye ta hannun kungiyoyinsu na NGOs, masu iko da gwamnatin Nigeria a takarda ne kawai, amma aiwatarwa ba a hannunsu yake ba, yana hannun dakarun "New World Order" wato dakarun Masoniyyah

Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'ah yake bukata ba tsinuwa ba, domin yaki da Boko Haram babban al'amari ne wanda zamu jya cewa yafi karfin ikonsa

Tabbas mun shiga wani hali a shekarun baya kafin zuwan Shugaba Buhari, amma a haka muka dukufa da rokon Allah Ya kawo mana canjin gwamnati, Tabbas abubuwa sun ragu amma ba yanda muka so ba!

Mun kaunaci shugaba Buhari ne saboda shedar gaskiya, rikon amana wanda hatta makiyansa s**a shaideshi akan wannan kyawawan dabi'u, saboda haka ba muyi nadamar zaben shugaba Buhari ba har yau duk da muna cikin takaici da jin haushi

Gareka shugaba Buhari, tsoron turawa bai k**ata ya hana tsohon janaral rufe ido ya samarwa jama'arsa mafita akan Boko Haram ba, iyakaci turawa su zargeka da laifin take hakkin 'yan ta'adda, su hanaka shiga kasarsu, gwanda suje su rike kasarsu ka zauna a kasarka cikin mutanenka yafi maka daraja da albarka, kafin ka koma ga Mahaliccinmu kana mai abin tuhuma da tambaya ranar Hisabi

Allah Ka agazawa shugaba Buhari
Allah Ka karfafi zuciyar shugaba Buhari
Allah Ka nuna masa hanya mai sauki da zaiyi sanadin kawo karshen ta'addancin Boko Haram da masu garkuwa da mutane
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
✍️ Datti Assalafy

29/11/2020

MACIYA AMANA

Sun ajiyeshi a daki k**ar gunki baya motsi sai yadda s**a juyashi, sun hana Malamai da mutanen kirki masu kaunarsa tsakani da Allah su je kusa da shi b***e su fada masa gaskiya

Basa barinsa ya karanta jarida sai sun tantance, har saye bakin editocin jaridun da s**a san yana karantawa suke su hanasu saka labarin da yake cutar da talakawa saboda cin amana

Amma yau idan wani shirgegen 'dan iska ne, ko wata kazamar karuwa tayi niyyar haduwa dashi babu bata lokaci zasu hadasu, ta isar da bukatarta a biya mata ba tare da bata lokaci ba

Mashaya jini matsafa azzalumai maciya amana 'yan iska kawai, lokaci ne zaku ci kwal ubanku, kamun Allah na zuwa

Yaa Allah Ka wulakantasu k**ar yadda s**a wulakanta bayinka talakawa
Yaa Allah Ka nuna mana kaskantarsu tun anan duniya
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

✍️Datti Assalafy

24/11/2020

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Kanwata ta kira daga garin Magami, Maradun LG, Jihar Zamfara tana sanar da cewa, tun dazu mahara na cikin garin suna abinda s**a ga dama. Ni kaina na ji karar harbin bindiga muna magana da ita.

Wannan shi ne halin da garuruwa da dama suke ciki a jihar Zamfara da wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Mu, bayin Allah, mu yi ta addu'a; Allah ya yi mana maganin abinda ba mu iyawa. Masu iko kuma wajibi ne su dauki matakin kare jinainan al'umma da mutuncinsu.

✍ Dr. Mansur Sokoto
Talata 24 Nuwamba
Karfe 5:55pm

SAI MUN HADA DA ROKO KAFIN A SAIYI MANMU A KASUWAR MAI TA DUNIYAShugaban hukumar kula da danyen mai ta Nigeria (NNPC) mi...
24/11/2020

SAI MUN HADA DA ROKO KAFIN A SAIYI MANMU A KASUWAR MAI TA DUNIYA

Shugaban hukumar kula da danyen mai ta Nigeria (NNPC) mista mele kyari yache muna rokan mutane su siya manmu a kan dala $9 a duk gangar mai daya a watan Aprilu,sakon yana fitowa ne lokachin dayake zantawa da manema labarai

Ya Kuma Kara dachewa yanzu Nigeria ta samu nasar fitar da gangar mai 2.9million a duk rana ,inda ya Kara da chewa kudirinsu na samun fitar da gangar man million ukku(3m) mai tabbatuwa ne.

Sanina kowa ne kasuwar mai ta duniya tayi mummunar fadin da bata taba yi ba tun bayan shekara ta alif 1999 bayan bullowar annobar Corona Corona virus Wanda sanadiyyar hakan yanyo ma tattalin arzikin kasashe tazgaro.

MUSULMI SU KAURACEWA KAYAN FARANSADaga cikin shahararrun kayayyakin da kamfanonin Kasar Faransa suke sayarwa a Nigeria a...
27/10/2020

MUSULMI SU KAURACEWA KAYAN FARANSA

Daga cikin shahararrun kayayyakin da kamfanonin Kasar Faransa suke sayarwa a Nigeria akwai:
👇
(1) Total PMS
(2) Total Engine oil
(3) Ashaka Cement Portland da superset (Lafarge)
(4) BIC

Ya zama wajibi a garemu Musulmai mu kauracewa sayan wadannan kayayyaki na Kasar Faransa domin mu kare martaban fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW)

Allah Ka rusa shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron Amin

ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONUZanga-zangar ENDSARS ta bar baya da kura, yanzu sun koma farfasa dakin ajiyar abinc...
24/10/2020

ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU

Zanga-zangar ENDSARS ta bar baya da kura, yanzu sun koma farfasa dakin ajiyar abinci a wasu jihohin Nigeria suna kwasar abinci na tallafin Coronavirus wanda shugaba Muhammadu Buhari ya bawa gwamnanoni domin su rabawa talakawa amma wasu gwamnonin s**a ki rabawa

Ina tuna lokacin da Ministar jin kai Hajiya Sadiya Umar Farouk ta bada sanarwan cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kashe biliyoyin Naira wajen sayan abincin tallafi na Coronavirus, amma a lokacin aka dinga tsine mata ana karyatata cewa ba'a ga abincin ba, ita ma yau Allah Ya wanke ta

Ga abinci nan shugaba Buhari ya bayar a baku, amma wasu miyagun gwamnoni sun boye sun barku da jin haushin shugaba Buhari kuna ta zaginsa ya kawo yunwa, gashi nan asirin mugayen gwamnonin ya fara tonuwa

Wannan zanga-zangar ENDSARS ta yaye wa masu hankali duhun sharri da aka yiwa shugaba Buhari, yanzu masu hankali sun fahimci gaskiya, hakika shugaba Buhari alheri ne wa Nigeria

Fasa gidan ajiyar abinci na gwamnati laifi ne mai k**a da cin amanar kasa a dokar Constitution, amma ni a fahimtata wannan ba laifi bane, dama hakkin talakawa ne wasu miyagun gwamnoni mugaye s**a boye, wanda inda talakawa ba su daka wawa sun wawushe abincin ba wallahi a haka zai lalace daga karshe a kona

Allah Ka sakawa shugaba Buhari sak**ako da gidan Aljannah
Allah Ka zaunar mana da Kasarmu Nigeria lafiya Amin.

23/10/2020

SUN GINAWA SHUGABA BUHARI RAMIN MUGUNTA SUN FADA CIKI

DAGA Datti Assalafiy

Na tabbata inda miyagun 'yan siyasa da s**a tsara kwangilar zanga-zangar ENDSARS don su kawar da gwamnatin Buhari sun san zai yi sanadin daga martaba da darajar shugaba Muhammadu Buhari tare da dawowar tsoffin masoyansa da s**a sauka daga mota wallahi da ba su fara ba

Miyagun 'yan siyasa azzalumai 'yan jari hujja wadanda s**a saba neman shugabanci ta hanyar zubar da jinin talakawa da murdiyan zabe, ba shakka sunji kunya

Jama'a wannan ya zama darasi a garemu, shugaba Buhari babu abinda yake bamu muke sonshi, gaskiyarsa da adalcinsa shine dalilin da ya sa Allah Ya sanya soyayyarshi a zukatan mutanen kirki, kuma Allah Yake bashi taimako da nasara akan taron dangin miyagu mutanen banza

Don haka duk runtsi duk wuya muyi kokari wajen yin gaskiya da adalci ko da zuciyarmu bai so ba a rayuwa

A 'yan kwanakin nan da aka fara zanga-zangar ENDSARS wanda ya rikide ya koma tarzoma da ta'addanci, na ga tsoffin masoya shugaba Buhari sun dawo sonshi a yanzu saboda sun fahimci gaskiya, hakika wannan babban nasarace

Yaa Allah Ka bawa shugaba Buhari ikon gyara kuskurensa, Allah Ka cika masa burinsa na alheri, Allah Ka bashi taimako da kariya akan miyagu makiya zaman lafiya
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

ME ZA'AYI DA MAI GOYON BAYAN 'YANCIN 'YAN LUWADI DA MADIGO?Karshen rashin wayewa da lalacewa da masifa da bala'i shine a...
22/10/2020

ME ZA'AYI DA MAI GOYON BAYAN 'YANCIN 'YAN LUWADI DA MADIGO?

Karshen rashin wayewa da lalacewa da masifa da bala'i shine a wayi gari wani daga cikin mutane yana goyon bayan Luwadi da Madigo, dabi'ar da ko dabbobi basa yi

Duk wanda ya san bashi da data baya ganin hoto a Facebook kafin ya karanta wannan sakon to ya sayi data ya ga abinda yake kunshe a cikinsa, hakanan wanda baya fahimtar yaren turanci ya nuna ma wanda ya iya fassara ya fassara masa

Jama'a Aisha Yesufu a shekarar 2019 da farkon shekarar 2020 ta wallafa wasu sakonni a shafinta na Twitter k**ar yadda zaku gani a screenshot tana bayyana cikakken goyon bayanta ga kungiyar 'yan Luwadi da Madigo na duniya "Le***an, Gay, Bisexual Transgender" (LGBT), ita a gareta suna da damar da za'a basu 'yancin auren jinsi tunda basa tayar da hankali, bani da tabbacin ko 'yar Madigo ce amma dai tana goyon bayansu a fakaice

An ruwaito Hadisi sahihi daga Manzon Allah (SAW) cewa idan ana Luwadi, Al'arshin Ubangiji yana girgiza saboda tsoron fushin Allah (SWT), sama tayi k**ar zata fado a kan kasa, sai Mala'iku suyi riko da ita, su karanta Qulhuwallahu Ahad.. har karshen surar har sai sun samu nutsuwa daga fushin Allah Madaukakin Sarki akan masu Luwadi

Amma a gurin wannan mata Aisha Yesufu bayahudiya a rigar Musulunci ba laifi bane Luwadi da Madigo da auren jinsi, 'yan Luwadi suna da damar da za'a basu 'yanci

Tsakani da Allah Ya k**ata a samu Musulmin kirki mai hankali da tunani da zai goyi bayan wannan matar ko ya ji yana sonta? Musulmi ka sani cewa tana samun dama da iko zata bada 'yancin ayi Luwadi da Madigo tare da auren jinsi, wannan yana daga cikin dalilan da yasa yahudawa suke kambamata da kokarin daukaka darajarta

Ku dubi irin cin mutunci da ta yiwa 'yan Arewa da Malaman addini a sakon bidiyo da ta fitar jiya don neman tunzura 'yan Arewa, ku ji abinda ta fadi a kan shugaba Buhari wanda a haife yayi jika da ita, bata da kunya, fitsararriyace bayahudiya a rigar Musulunci, tana magana babu kunya tana gantsali sai kace wata tsohuwar kilaki

'Yan uwa Musulmi ya k**ata ku san hatsarin wannan matar, ku dena ganinta a matsayin wata jaruma, tana tattare da boyayyar manufa ga addinin Musulmi da kuma zaman lafiyar mu, gashinan ita da abokan huldarta 'yan kwangila sun kunna wutar rikici wanda Allah ne Kadai Ya san yadda abin zai tsaya

A hukumance mun san ka'idar zanga-zanga wanda duk abinda ya faru na tashin hankali yana wuyan wadanda s**a tsara zanga-zangar, don haka muna kira ga masu iko da tsaron Nigeria su tuhumi Aisha Yesufu da abokanta wadanda aka basu kwangilar shirya wannan masifa

Muna rokon Allah Ya wulakanta wannan mata
Allah Ka kaskantar da darajarta
Allah Ka daidaita al'amarinta
Allah Ka sa wannan masifar ya kare a kanta.

✍️ Datti Assalafy

BABBAN KUSKUREN DA 'YAN AREWA ZASU YIWanda ya rubuta Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga garin Okene, Jihar Kogi, Najeriy...
18/10/2020

BABBAN KUSKUREN DA 'YAN AREWA ZASU YI

Wanda ya rubuta Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga garin Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya k**ar haka: 08038289761.

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum

Ya ku jama’ah! A daidai wannan lokaci da yankin mu na arewacin Najeriya mai albarka yake cikin halin ni-‘ya-su, yake cikin halin damuwa, musamman bangaren rashin tsaro, talauci, rashin ababen more rayuwa, da sauran su...

A lokacin da yankin yake bukatar kulawar shuwagabanni, tun daga zamanin tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Ebele Jonathan har zuwa yau, wallahi ba mu taba yin babban kuskuren da ya kai mu zabi jigon jam’iyyah mai mulki ta APC, kuma tsohon gwamnan Jihar Legas, wato Bola Ahmad Tuninbu ba!

Wallahi duk wanda yake bibiyar siyasar kasar nan, daga shekarar 1999 zuwa yau, ya san irin ta’asa da ta’annati da Tinubu yayi wa al’ummar arewacin Najeriya, kuma babu wani wanda ya isa ya fada muna cewa Tinubu yana son arewa da ‘yan arewa, har mu saurare shi.

Jama’ah, mu tuna fa, su Tinubu ne s**a kirkiri wata jama’ah mai suna Odudua Peoples Congress (OPC), a lokacin da yake gwamnan Jihar Legas, wadannan mutane, wato OPC, duk shekara sai sun kashe ‘yan arewa mazauna Legas. Sun ware ranar June-12 na kowacce shekara domin kisan gilla ga ‘yan arewa mazauna Legas.

Sannan Tinubu yana cikin wadanda s**a hana shugaba Muhammadu Buhari ya bude iyakokin arewa, domin su samu saukin rayuwa, Shine ya tsaya tsayin daka domin ganin cewa sai dai a bude iyakokin Legas kawai, Nufin sa anan shine, duk harajin da ake shigowa da kaya ya kasance sune kawai za su ci gajiyar abun, ban da arewa.
A takaice dai, ina mai shaida maku cewa, wallahi, goyon bayan Tinubu a 2023, yana nuna rashin kishin Arewa, ko kuma rashin sanin ciwon kai, ga duk wanda yayi kuskuren yin hakan, Don haka wallahi sai muyi hattara!

Sannan duk mutumin da yake raye a kasar nan, kuma yake bibiyar al’amurran gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, yana sane da cewa, mutanen nan, wato su Tinubu, sun amfana matuka da gwamnati mai ci, ko kuma in ce wallahi sun fi kowa amfana, amma don rashin godiyar Allah, ku kalli yadda s**a koma can karkashin kasa, suna yiwa gwamnatin bita-da-kulli, suna yi mata zagon-kasa.

S**a koma can a boye, suna zuga ‘yan iska da zauna gari banza, matasa marasa aikin yi, da shugabannin coci-coci, wadanda s**a mayar da addini abun wasa, wadanda yawancin su ‘yan kudu ne, makiya yankin arewa, s**a koma suna yiwa wannan gwamnati tawaye da zanga-zanga.

Wallahi ko dan jahila yasan da cewa wasu hamshakai ne suke daukar nauyin wannan zanga-zanga ta END SARS, kuma ba komai yasa suke wannan ba sai don su tozarta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kuma su tozarta arewa da ‘yan arewa, wannan shine kawai manufar su, Kuma duk suna yi ne domin maganar siyasar 2023, wato dole idan Buhari ya gama ya mika masu mulki da-karfi-da-yaji, saboda haka ina kira ga ‘yan arewa da mu farka, mu san irin kulle-kulle, da makircin da ake kulla muna!

Ni fa ba wai ina nufin cewa babu kura-kurai a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bane, a’a, amma abunda nike kokarin nuna muna shine, makiyan arewa da ‘yan arewa sun sa yankin a gaba, suna amfani da zaluncin da wasu jami’an ‘yan sandan SARS suke yi, domin su durkusar da Arewar baki daya
Duk amfanar da su Tinubu suke yi da wannan gwamnati, amma basu gode ba, sun zama butulu, sun koma can karkashin kasa, suna yiwa arewa zagon-kasa, da kulla mata makirci.

A yau din nan ma Asabar 17-10-2020 Allah ya tona asirin su, wani Farfesa masanin tarihi da harkokin kasashen waje, malami a jami’ar Ibadan, mai suna Farfesa Alexander Adebisi, ya fito ya bayyana wa duniya cewa suna da cikakkun hujjojin da ke nuna cewa su Tinubu ne suke daukar nauyin wannan zanga-zangar ta END SARS, domin ya fara fahimtar cewa k**ar jiga-jigan siyasar arewa ba zasu goyi bayan takarar sa ba, to shine yake daukar nauyin ‘yan iska, domin a bata arewa da ‘yan arewar!

Kuma ance yadda ya samu sa’ar matasan kudu, haka ma yana nan yana kokarin samun sa’ar matasan arewa don su ma su shiga wannan zanga-zanga, don haka wallahi ‘yan uwana, ‘yan arewa sai muyi hattara, bamu da wani wurin da ya kai arewa!

Kuma duk mai hankali zai yarda da wannan Farfesan, domin irin makudan kudade da ake kashewa wurin gudanar da wannan zanga-zanga, wallahi sun wuce hankali, kuma sun wuce tunanin duk wani mai tunani, irin abincin da ake ci da abun sha da sauran su, zai sa mu kara yarda da cewa, wannan abu yafi karfin yara, matasa, a’a, wasu manya ne, marassa kishin Najeriya suke daukar nauyin wannan iskancin, kuma ba don komai ba, sai domin su cimma burin su na siyasa.

Don haka yanzu ya rage namu, shin zamu bari ayi amfani da mu? Shin zamu bari wasu ‘yan iska su lalata muna yanki, saboda biyan bukatar su?
Wassalamu Alaikum,

Allah Ka tsaremu daga sharrin su Tinubu da tawagarsa Amin

17/10/2020

BA SHUGABA BUHARI NE MATSALAR SU BA

Masu jagorantar zanga-zanga da wadanda suke daukar nauyin zanga-zangar suna bayyana tsananin kiyayyarsu ga shugaba Buhari a zahiri, to amma magana ta gaskiya a badini ba shugaba Muhammadu Buhari bane matsalarsu

Babbar matsalar mutanen nan shine 'yan Arewa da Musulunci, 'yan Arewa ake so a yaka, 'yan Arewa ake so a ruguza, duk wannan takalar yaki da fitina da suke yi suna yi ne don 'yan Arewa su amsa, ba Buhari bane suke son ganin bayanshi ba, ajanda suke da shi na son ruguza kasa da shan jini

Makiyanmu sun san shugaba Buhari lamarinsa ya kusa karewa, zamaninsa ya kusa gushewa, duk abinda yake nema a duniya ya samu, shekarun tsufa sun k**ashi, bai da bukatar wani abu kuma, basa ganinshi a matsayin wani babban barazana

Don haka jama'ar Arewa ya k**ata mu fahimci wannan, kada muyi wasa mu salwantar da makomar mu a dalilin wasun mu na jin haushin shugaba Buhari, kar mu yadda suyi amfani da wannan damar su samu hanyar da zasu tunzuramu mu rusa kasarmu da yankin mu, mune ake so a yiwa bukulu ba Buhari ba, ko da Kasae ta rikici Buhari yana da alfarmar samun mafaka a kasashe masu yawa na duniya, mune za'a bari a cikin tashin hankali

Kuma wallahi wannan abin akwai sa hannun manyan makiyanmu na cikin gida da kasashen waje, duk manyan mutane da nake tuntuba daga 'yan siyasa da tsaro wannan shine fahimtarsu, duk wani mai hankali zai fahimci haka, suna da goyon baya mai karfi akan wannan mummunan kuduri nasu da s**a fake da zanga-zangar ENDSARS

Duk abinda suke bukata na taimako a duniya zasu samu daga kasashen yahudu da nasara, ina ganin wannan dalilin yana daga cikin hikimar da ta sa gwamnatin shugaba Buhari take jan kafa wajen duba yiwuwar daukar kwakkwaran matakin dakile su, kafin nayi wannan rubutun sai da na karanta wani labari a jaridar Daily Trust cewa gamayyar manyan kungiyoyin kare hakkin bil'adama na duniya kusan guda 12 suna gargadin gwamnatin Nigeria wajen daukar mataki mai tsauri akan masu zanga-zanga

Don haka ko kusa Buhari ba shine matsalar su ba, jama'ar Arewa sune matsalar su, kar mu basu kofa, idan sunce yaki ko fitina, mu ce da su zaman lafiya muke so tunda mun fisu yawa, mu Musulmai ne, muna tare da taimakon Allah

Yaa Allah Ka tsaremu daga sharrin wadanda basa nufin mu da alheri Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

HATSARIN 'YAR KWANGILAR YAHUDAWA AISHA YESUFU GA RAYUWAR MUSULMAIDuk wani Musulmin kirki da ya san wacece Aisha Yesufu h...
13/10/2020

HATSARIN 'YAR KWANGILAR YAHUDAWA AISHA YESUFU GA RAYUWAR MUSULMAI

Duk wani Musulmin kirki da ya san wacece Aisha Yesufu har yake kaunarta ko yake goyon bayanta matukar ya san muguwar akida da muguwar manufa da take tattare da shi sai yayi nadama ko ya tsani kanshi

Don Allah 'yan uwa Musulmi ku nutsu da kyau ku karanta wannan sakon har karshe wanda 'dan uwa Ibn Adam ya bincika mana akan wannan mata 'yar gwagwarmayar kare 'yancin yahudawa da kungiyoyin 'yan Luwadi da Madigo na duniya

Wani ya tambaye ni wai menene hujja ta na adawa da wannan matar, Maganar gaskiya akwai dalilai masu karfi wanda ya sa bana yinta, a yau Musulmai sai mun zama masu lura sosai da ababen da suke faruwa, in ba haka ba za’a cutar da mu duniya da lahira

Daga cikin Hojjojin da ya zama wajibi duk wani Musulmin kirki ya k**ata ya tsani wannan matar shine:

(1) Tana sanye da hijab” : Duk da tana sanye da hijabi, hakan be hanata yin abubuwa wanda s**a sabawa shariah Musulunci ba, hakan sai ya sa Jahilai da gamagarin mutane su dauke ta “jaruma mai hijabi” harma ta zama abun koyi wa na bayanta musamman mata masu tasowa. Saboda ta shahara kuma tana sanye da hijabi, a dauka ayyukan ta sunyi daidai da abinda musuluncin ya hukunta. Hakan kuma na da illa matuka ga Al'ummar mu.
Ni ba ina magana ne kan zanga-zanga ba, sam ba shine makasudin magana ta ba, duk wanda ya san ta a shafin Twitter ya san irin tsiya da take rubutawa wanda yaci karo da addinin Musulunci karara.

2. Tana da akidar Liberalism, wato tana da akidar cewa abar mutane suyi abinda suke so ko da abin ya saba wa shari'ar Allah, hakan ya sa tayi rubutu a shafin ta na Twitter take magana akan bada 'yanci wa kungiyoyin 'yan Luwadi da Madigo da masu zina da Dabbobi na duniya, wato kungiyar "Le***an, Gay, Bisexual, and Transgender" (LGBT)
Tayi maganganu cewa mutane na da 'yanci suyi auren jinsi, namiji ya auri namiji, mace ta auri mace, harma take kokarin nuna cewa a jihar Kano akwai masu aure jinsi da jinsi kuma ana zaune dasu lafiya kuma ana mu’amala dasu yanda ya k**ata, don haka indai zasu zauna to a basu 'yancin auren juna kawai.
To wannan maganar ma ko a constitution babu 'yancin auren jinsi balantana a tsarin Allah (SWT) da MazonSa (SAW)

3. Tana tare da ArewaMeToo, Duk irin tsiya da da wannan kugiyar take neman ta shuka a arewa, wannan matar tana goyon bayan wannan kungiyar saboda akidar su daya.
Cikin wani sakon Twitter da ta rubutu ta goyi bayan cewa ArewaMeToo suyi magana akan bada 'yancin Madio da Luwadi (Le***anism Homosexuality) saboda akwai irin wadannan mutane a Arewa da dadewa, kuma ba’a cin zarafin su, kuma ba’ayi yinkurin dakatar dasu ba.
Allah Yace: Ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa, Kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da zalunci. Suratu Ma'idah (Q5:2)

4. Cikin 'yan kwanakin nan da aka yanke wa wannan mawakin hukuncin kisa a Kano wanda ya zagi Manzon Allah (SAW) Aisha Yesufu ta nuna rashin amincewar ta akan hukuncin.

A takaice tana da mummunar akida, kuma a zato na Mutum me irin wannan akidar baya bukatar a yaba masa harma ya kai ga ana tallata shi a matsayin jarumi, harma wasu suna cewa jarumtar ta ya samo asali ne daga ainihin me sunar wato Nana Aisha (ra) matar Manzon Allah (SAW) wannan ko shakka babu abin takaici ne sosai a kwatanta wannan bayahudiya da darajar Nana Aisha k**ar yadda wani babban 'dan siyasa a jihar Niger Umar Nasko ya wallafa a shafinsa na facebook saboda cin mutunci

Naji mamaki matuka da naga wasu Musulmai suna daukan ta wata jaruma me sanye da hijabi, har suna sa hotunan ta a matsayin DP dinsu, k**ar Mutane sun manta ko kuma abin duniya ne ya fi damun su.

Zanga-Zanga ba wani abin jarumta bane, kowa ma zai iyayi, alakar ka da mutum da sonsa da kake yi ya samo asali da yanda mutum yake da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Allah da ManzonSa ne, wannan shine ma’auni

Wannan itace jarumar ka wanda kake ganin tayi abin gwaninta ko? , tun da wuri ya k**ata ka fahimta ina aka dosa, kada ta zama abin koyi gun 'ya'yanka ko yaran gidan ku, su taso suna goyon bayan kungiyoyin 'yan Luwadi da Madigo, domin babu mai goyon bayansu sai wanda yake cikinsu

Yana daga cikin hanyoyi da yahudawan duniya suke bi su cutar da Al'ummar Musulmi shine a samu irin wadannan mutane a sa su shahara, ko kuma idan sun shahara a mayar dasu k**ar wasu jarumai har sai ya kai munzilin da an yarda dasu, hakan sai ya basu damar cigaba da tallata mummunar akidarsu, da sunan cewa su jarumai ne na gwagwarmaya da kare 'yanci na dan-Adam.

Nayi wannan rubutu ne da niyar farkar da zaciyoyin Musulmai don su fahimta cewa k**ar yanda bature ke fadi “ not all that glitters is Gold”.

Allah Ya sa mudace.

✍️ Datti Assalafy

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!Allah yayiwa Abdulmalik Dan gidan Sheikh (jafar mahamud Adam R A) Rasuwa sak**akon ...
10/10/2020

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!

Allah yayiwa Abdulmalik Dan gidan Sheikh (jafar mahamud Adam R A) Rasuwa sak**akon Hatsarin Mota

Ya Allah kajikansa da rahama dasauran musulmin duniya Baki Daya🙏🙏🙏

Manyan jiga-jigan jamiyyar PDP/APC sun bayyana a wajen bikin diyar Nuhu Ribadau da Dan tsohon  mataimakin Shugaban kasa ...
03/10/2020

Manyan jiga-jigan jamiyyar PDP/APC sun bayyana a wajen bikin diyar Nuhu Ribadau da Dan tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar

WANI MAI HIDIMA DA UBANGIDANSA.Wani mutum mashayin giya yatara abokanansa don su hadu susha giya, sai ya aika mai hidima...
03/10/2020

WANI MAI HIDIMA DA UBANGIDANSA.

Wani mutum mashayin giya yatara abokanansa don su hadu susha giya, sai ya aika mai hidimansa da dirhami hudu don yasiya musu ya'yan 'itatuwa.

Lokacin damai hidiman nasa yatafi kan hanya, sai yahadu da wani mai gudun duniya wanda ake kira Almansur bn Ammar yana cewa, waye zai bada dirhami hudu ga faqiri bako nikuma inyi masa addu'a hudu? Sai wannan yaro mai hidima yabashi dirhaminnan hudu da aka aikeshi saboda wannan addu'a.

Sai mansur bn ammar yace me kake so inyi maka addu'a akanshi? Sai yaron yace a 'yantani daga bauta, 2 Allah ya maye min dirhaminnan hudu, 3 shugabana yatuba daga shan giya, 4 Allah ya gafarta min da shugabana da kai da mutanen dasuke nan, sai kuwa mansur bn Muhammad ya roka masa.

Sai yaro yadawo wurin shugabansa, sai shugabana ya tambaye shi meyasa kayi jinkiri? Kuma 'ina yayan 'itatuwan? Sai yabashi labarin haduwarsa da mansur mai gudun duniya, da yadda yabashi dirhami hudu a madadin addu'a hudu. Sai shugaban yace kaikuwa wace addu'a ka bukaci yayi maka?

Sai yace farko dai naroka wa kaina yanci daga bauta. Sai shugaban yace kaje na yantaka saboda Allah madaukaki.

Sai yace na biyu, Allah ya maye min dirhami hudun, sai shugaban yace kana da dinari dubu hudu.

Sai shugaban yace wace addu'a kanema ta uku? Sai yaron yace Allah yasa katuba daga shan giya, sai shugaban ya girgiza kansa yayi kuka sannan ya fasa tukunyar giyar yace nadaina shan giya har abada.

Sai yace wace addu'a kanema ta hudu? Sai yaron yace, nace aroka Allah ya gafarta min dani dakai da mansur bn Muhammad da mutane dasuke wurin baki daya. Sai yace wannan bani da 'iko wannan hurumi ne na Allah madaukakin sarki.

Lokacin da shugaban ya kwanta bacci wannan dare sai yayi mafarki ana cemasa, kai kayi abinda zaka 'iya, kana tsammani Allah bazaiyi abinda shi kadai dinne ke iya yiba!? To haqiqa Allah ya gafarta maka dakai da yaron da mansur bn Muhammad da wadanda suke wurin.

Addu'a ibada CE, yin addu'a ga dan'uwanka musulmi ba tareda saninsa ba tana da wani karfi na musamman, ya kake tunani 'idan mala'iku s**a maka kwatankwacinta daga cikin sama kuma ubangijin al'arshi ya amsa daga garesu? Allah yasa mudace.

✍️Datti Assalafy

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewasunshine posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewasunshine:

Share


Other Abuja media companies

Show All