Rayuwa A Musulunci

Rayuwa A Musulunci Assalamu alaikum wannan chafi munyi asane don amfanin ƴan uwa Musulmi manya da yara maza da mata man

05/12/2020

Dole musifu da wahalhalu da bala'o'i suyi yawa

Yau an wayi gari. Zina ta yawaita. Ta zama ruwan dare.

Yau an wayi gari. Fasiƙanci ya yawaita ya zama ruwan dare.

Yau an wayi gari zalumci ya yawaita. Ya zama ruwan dare.

Yau an wayi gari ha'inci ya yawaita. Ya zama ruwan dare.

Yau an wayi gari cin amana ya yawaita. Ya zama ruwan dare.

Yau an wayi gari kisan (rai) ya zama abu mafi sauƙi a wurin wasu mutane.

Yau an wayi gari ɓarna ta yawaita a doran ƙasa kuma masuyi ba'a hukun ta su.

Yau an wayi gari mun saki maganar allah (swt) mun ɗauki dokokin yahudu.

Yau an wayi gari mun saki maganar annabi (saw) mun ɗauki na yahudu.

Yau an wayi gari mun saki dokoki da chari'ar musulinci mun ɗauki na yahudu.

Waƴanda basu ƙaunar mu. Basu ƙaunar annabi (saw) basu ƙaunar alƙuranin mu basu sun dokoki da tanade tanade na chari'ar musulinci yau wai kuma sune muke ƙauna har takai ga mun saki namu mun k**a nasu

Allah ka chiryar damu ka yafe mana ka ganar damu bijahi annabi (saw)

05/12/2020

Astagfirullah Astagfirullah Astagfirullah

Yau mun wayi gari a wannan zamanin damu da chuwagabannin mu mun saki koyarwar addinin mu na musulunci gachi masifu sunyi muna yawa mun kasa ganewa ko miye dalili talakkawa da chugabanni ba'a san mai gaskiya ba. Mu muce chugabanni basu da. Azzalumai ne. Ba suda adalci . Su kuma s**e suna ƙoƙari ba muda haƙuri kuma mune tuchen matsalolin. Da muda su. Duk mun chagala da duniya mun man ce lahirar mu. Mun bar koyarwar musulinci da chari'a da abinda allah ya faɗa da annabin sa. s a w

05/12/2020

Wallahi ba wani addini a duniyar nan. Da yayi k**anceceya da addinin musulunci wajen ko yarda zaman lafiya da lumana da amintaka. Allah ka kare addinin ka. Daga ƴa ɓata gari ƴan na'iya masu son wargaza addinin musulinci afakai ce. Haramun ne ka kache (Rai) ba tare da waƙƙi ba na chari'a haka kawai

04/12/2020

Al'jumu'atu karem

Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya

03/12/2020

(ƊAN ADAM) chin miye ya ruɗe mune mun k**a duniya bama tunanin lahira burin mu. Chine muyi arziƙi tako wace hanya mai kyau ko maras kyau ɗan adam kullun cikin wahala kake ko mun manta ne da maganar (allah swt) a cikin 'Al.ƙuran. Sura ta 90. Al'balad. Aya ta 4 ubangiji yace: {{{ لقد خلقنا الإنس فى كبد{{{ Allah yace [Haƙiƙa mun halitta mutum cikin wahala] dan adam tun daga ɗaukar cikin mutun uwa ta chiga wani yanayi na wahala yau tayi laulayi gobe ciyon kai ga damuwa ga ɓacin rai ga kasala. Dun akan mutun wurin haihuwa ga (naƙuda) ba chike nan ba. Bayan uwa ta haihu tachiga wata wahala kuma ta ɗawainiya jariri bayan an yayeka katachi sannu sannu ka balada. Kaga macce kace aure zakayi bayan kayi aure kaima kachiga wani yanayi kai ne can. Kai ne nan. Kana faɗi tachi da rayuwa bayan bayan chekara ɗaya kaima matarka ta haihu zaka faɗa ɗawainiya da ƴaƴanka akwan atachi sai ka tsinci kanka tsufa yazo ba kada ƙarfi ko ɗaya

Kaɗan daga cikin wahalar ɗan adam a duniya tun farkonka har ƙarchenka cikin wahala kake.

Allah yasa mudace allah ya sauƙaƙa muna rayuwa allah chiyi muna buɗi duniya da lahira allah yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali badan halin muba dan alfarmar annabi (s a w)

02/12/2020

MU MUKA SAKI KOYAWAR ADDININ MUSULINCI

A matsayinka na musulmi. Wai sai kaga uba musulmi duk ahlinsa musulmi ƴaƴan sa. Musulmi amma daya samu ƴaƴa burinsa chine suyi karatun boko acan suke tachi da tarbiyya mai makon makarantar Al'ƙuran kawai sai yaro yagirma bai san komi ba. A addinin sa.

Ba laifi bane ahaɗa duka guda biyu amma mafificin ilimi tun tachin farko chine kasan ubangijinka. Kasan annabi (saw) dan chi akayi ka. Kasan musulincinka kasan chara'a da aiki da ita . Duniya ƙalilance lahira madauwamiya ce arzikin duniya mai ƙare wane amma na lahira yalwantatce ne bai da ƙarche .

Kafin kasan komi a duniya abu na farin kasan allah da annabi muhamadou sallallahu alaihi wa sallam

02/12/2020
02/12/2020

MUSULINCI.

Addinin zaman lafiya.

Allah ka bamu zaman lafiya mai ɗorewa Allah badan halin muba ya allah mun kasa.Allah mun tuba allah mun tub a allah mun ...
02/12/2020

Allah ka bamu zaman lafiya mai ɗorewa

Allah badan halin muba ya allah mun kasa.

Allah mun tuba allah mun tub a allah mun tuba 😭😭😭😭 allah ka tsaya mana a duk al'amurran mu. Na yau da kullun.

02/12/2020

ILLAR RACHIN TARBIYYARKA GA NAƘASA DA KAI

Aduk lokacinda mutun ya kasan ce marar tarbiyya toh na ƙasa dachi zasu zama masu koyi da chi. Wajan aikata irin abinda yake aikata wa. Aƙarƙachin haka manzon allah tsira da amincin allah su tabbata agarechi yake cewa: من دل على خير كفاعله. Wanda duk yayi nuni zuwa ga alkhairi toh k**ar wanda ya aikata ne.

Toh chi kuma wanda yayi nuni zuwa ga charri fah? Ya ƙara da cewa: كل معروف صدقة dukkan wani umarni da kyakykyawa sadaƙane... Allah mun tuba ka dafa mana ka tai makemu

01/12/2020

ILLOLIN RACHIN TARBIYYA GA MUSULMAI musulunci addini ne wanda ya taɓa ko wane ɓangare na rayuwar ɗan adam. Idan aka samu mutun ya kasance marar tarbiyya kuma aka samu na ƙasa dachi sunyi koyi da chi. Suma na ƙasa dasu zasuyi koyi da su. Toh a haka za'a samu ɗumbin musulmai sun ɗulmiya cikin rachin tarbiyya. Ta sanadiyyar mutun ɗaya. Chin kana buƙatar haka ta faru da kai??? Ka kasance mai ingatacciyar tarbiyya.

ILLAR RACHIN TARBIYYA GA ƊAN ADAM

A dai dai lokacinda ɗan adam ya kasance marar tarbiyya zai zamanto abin ƙyama abin gudu. Abin hantara da ƙyama acikin ahalinsa. Dan ginsa da kuma al'ummah baki ɗaya. Kuma duk wani mutunin kirki zai ƙyamaci yin ma'amala da chiya. Dan gudun gar cutarda yake fama da ita ta harbe chi.

ILLAR RACHIN TARBIYARKA GA NAƘASA DA KAI?

A duk lokacinda mutun ya kasan ce. Marar tarbiyya toh na ƙasa dachi zasuyi koyi da chi. Wajen aikata abunda yake aikatawa

30/11/2020

Yau zamu ga tsakanin uwa da mahaifi wanene keda haƙƙin akan tasowar yara

Da cusa musu ko koyar dasu kyakykyawar tarbiyya mai kyau tsakanin mahaifi da mahaifiya.

Kamar dai yadda mukata magana abaya akan wannan maudu'i na raino da tarbiyya. Babu chakka zamuga abu ne wanda yachafi dukkan jinsi. Uwa da uba . Toh amma dai dole ne asa mu wanda nauhi yafi yawa akan sa.

Dan haka yau zamuyi kokarin kallon uwa amatakin farko ko kuma jagora a wannan tafiya. Fanni. Bisa wasu dalilai k**ar haka; addini ko al'ada idan muka duba a addinance za muga uwa itace matakin farko wajan reno da tarbiyyar ƴa'ƴa don haka hadisin manzon allah (saw) hake cewa: a auri macce saboda addininta. Malan ba hauche chiyasa yake cewa ka zaɓama ƴaƴan ka. Macce ta gari tun kafin a haife su.

Wannan magana na daɗa nuna mana mahinmancin raino ko kuma a ce yana daɗa ƙarfafa raino da tarbiyya suna farawa daga uwa kenan.

Idan har allah yasa uwar gida ta haifu lafiya kuma ta gama wankan jego lafiya kuma har allah yasa abinda aka haifa yanada lafiya toh baza'a ɓata lokaci ba wurin fara masa/mata tarbiyya. Don haka sai uwa ta tsara wani jadawali k**ar don kulawa da wasu abubuwa da ya k**ata k**ar haka: iya magana bayan gida (bahaya) cin abinci yin bacci da sauran su.

Iya magana yanada mahimmanci ƙwarai da gaske uwa tasan irin maganganunda zata iya ya. Da kuma kalmomin da. Zata iya furtawa a gaban yaranta' domin sunaji kuma suna la'akari da abunda take furtawa idan masu kyau ne haka zasu tachi dasu. Idan ba masu kyau bane a hakan zasu tachi da su.

Misali uwaye masu wasan zagi haka zakaga yara suna wasan zagin junan su. Uwar gida ya k**ata kiyi la'akari da lokaci ɗaya. Kamata yayi kiba yaranki abinci gar a barsu da yunwa kuma gar a cika musu ciki ƙwarai a'a ayi sauwa sauwa.

Allah kagyara muna tarbiyyar ƴaƴan mu alfarmar annabi (s a w)

28/11/2020

Tarbiyya a musulunci

Wasu malumai sunce ma'anar tarbiyya chine

1 wasu malamai tarbiyyar musulunci sun ce: tarbiyya chine gina yaro cikakkan gini. Taɓan garen abinda ya chafi aƙidar sa. Da addinin sa. Da halayen sa. Da hankalin sa. Da kuma lafiyar sa. Ta hanyarda tadace da addinin musulunci:

2 MUHIMMANCIN TARBIYYA A MUSULUNCI. Tarbiyyar yaro wajibi ne: Allah (SWT) yana cewa: يأيهاالذين ءامنوا قوا أنفسكم و أهليكم نارا قودهاالنّاس والحجارة‘ ma'ana. Yaku wa ɗanda kunkayi imani ku tseratarda kawu nan ku da ƴaƴanku daga wuta mak**achinta chine mutane da kuma duwatsu: suratu Attaharim aya 6. Kuma kowa za'a tambaye chi. Abinda yake kiyo k**ar yadda annabi ya faɗa yace: كلكم راع وكلكم مسؤول عن رعيته،..... والمرأة راعية في بيت بعلها وولده وهي مسؤولة عنهم،.... MA'ANA. ,,,kowannen ku mai kiyo ne kuma za'a tanbaye chi. Akan abinda yake kiyo. ,,,,mace ma mai kiyo ce acikin gidan mijinta' da dansa kuma za'a tanbayeta akan su. Bukhari da muslim ne s**a ruwaito .

26/11/2020

صلو على النبي صل الله عليه و سلم

inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Muna allah ya jiƙan tsohon chugaban ƙasar niger tandja mamadou allah ka sanya kwanci...
25/11/2020

inna lillahi wa inna ilaihi raji'un

Muna allah ya jiƙan tsohon chugaban ƙasar niger tandja mamadou allah ka sanya kwanciya hutuce mu kuma da muka rage allah kasa mu cika da imani.

25/08/2020

Muna ma ƴan uwa musulmi barka da chiga sabuwar chekara

Adresse

Kalley Plateau
Niamey

Téléphone

+22799944939

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Rayuwa A Musulunci publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Partager



Tu pourrais aussi aimer