Nigerian News Hausa

  • Home
  • Nigerian News Hausa

Nigerian News Hausa Nigerian New's Hausa, Jarida Ce Nagartacciyya Mai Ɗauke Da Nagartattun Labarai Cikin Harshen Hausa.

Ku ware mana, wanda yafi iya mugunta da gida-danci a cikin su?
09/12/2023

Ku ware mana, wanda yafi iya mugunta da gida-danci a cikin su?

YANZU-YANZU: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sauyawa garin da Sojoji s**a A kai harin Bam daga Tudun biri  ya koma Tudun M...
09/12/2023

YANZU-YANZU: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sauyawa garin da Sojoji s**a A kai harin Bam daga Tudun biri ya koma Tudun Maulidi

Me zaku ce?

Matasan mu da su ke ɓallewa zuwa wasu ƙasashen don neman sana'a su dakata da ficewa, na can ma su dawo gida saboda na ku...
09/12/2023

Matasan mu da su ke ɓallewa zuwa wasu ƙasashen don neman sana'a su dakata da ficewa, na can ma su dawo gida saboda na kusa kawo ƙarshen Talauci - “Inji Tinubu

Gwamnonin Sojoji da s**a mulki Sokoto Guda 9 aikin gwamna 2 yafi duk aikin da s**a yi tsawon mulikinsu. 1. Usman Faruku ...
09/12/2023

Gwamnonin Sojoji da s**a mulki Sokoto Guda 9 aikin gwamna 2 yafi duk aikin da s**a yi tsawon mulikinsu.

1. Usman Faruku
2. Umaru Mohammed
3. Gado Nasko
4. Garba Duba
5. Garba Mohammed
6. Ahamed Daku
7. Yakubu Mu’azu
8. Adisa Raji
9. Dan Asabe Garba

Ka hade aikinsu kaf ! Shekarun da s**a yi suna mulki , aikin da gwamna biyu s**a yi na farara hula :
1. Shehu Kangiwa
2. Attahiru Bafarawa

Yafi abinda s**a yi a Sokoto.

Kankgiwa cikin kwana 100 na farko mulkinsa yayi makaranta 100 a Sokoto .

Ciki akwai Sultan Bello Secondary School,
Sultan Atiku Secondary School ,
Sultan Attahiru Secondary School
Nana Girls Secondary School
Army Day Secondary School
Sama Secondary School Argungu
Sambo Secondary School Gusau

Kadan kenan .

Kafin ya mutu ya gina Grand fishing Hotel Argungu
Gusau Hotel
Shukura Hotel
Da 5 Star Giginya Hotel Sokoto.
Giginya Housing Estate da yanzu ake kira Shehu Kangiwa Secretariat .
Shi yayi Tagwayen hanyoyin KANO road / Gusau Road a tsakiyar birnin Sokoto , da tagwayen hanyoyi a Ali Akilu .
Alokacinsa aka kare aikin Kasuwa da tashar mota a Sokoto.

Kadan kenan

Bafarawa ya hada Duk headquarter local government da wutar Nepa , yayi kilomita 1000 na t**i a jahar Sokoto . A cikin Birnin Sokoto yayi tagwayen hanyoyi da s**a hada da :

1. Sultan Abubakar Road
2. Sultan Atiku Road
3. Amir Yahaya Road
4. Modibbo Adama Road
5. Muniri Road
6. Diori Hammani Road
7. Kara/Kwanni Road
8. Sudais Road
9. Scas Road
10. Bauchi Road

Yagina flyover ta farko a Arewacin Nigeria .

Kadan kenan

Ya gina College Of Engineering
Ya gina School of remedial studies

Ya kai yara 50 Bulgaria karatun likitoci s**a kare s**a dawo aka basu aiki .
Ya kai yara 80 NDA duka sun kare .

Ya gina Sultan Maccido Institute Of Qur’anic studies

Ya gina Masalacin Jumu’at 1000
Ya yankawa limammai da Ladani albashi, kuma ya baiwa limamai official car.

Ya gina gidajen Malamai a primaries, ya gina manyan tankokin ruwan sha

Ya gina Rima FM da RTV

Sanata Dr. Abdul'aziz Yari, ya bawa wa 'yanda iftila'in Bom ya shafa a jihar Kaduna, kyautar Naira miliyan 58.
08/12/2023

Sanata Dr. Abdul'aziz Yari, ya bawa wa 'yanda iftila'in Bom ya shafa a jihar Kaduna, kyautar Naira miliyan 58.

Yanzu haka cikin daren nan, ma'aikatan kamfanin ABBA PANTAMI DATA, suna zaune a Ofis suna gudanar da aiki tukuru. Duk wa...
08/12/2023

Yanzu haka cikin daren nan, ma'aikatan kamfanin ABBA PANTAMI DATA, suna zaune a Ofis suna gudanar da aiki tukuru.

Duk wanda yake da korafi ko karin bayani, yanzu haka zai iya tuntubar daya daga cikin wa 'yan nan lambobin kai tsaye ta Whatsapp; 07046868000 08126081967 07061347599.

Wanda bai yi ragista ba, ya shiga wannan link din yayi
👇
https://abbapantamidata.com/mobile/register/?referral=08130233375

Ko kuma ya shiga PlayStore ta wannan link din, yayi Download din Application din
👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.abbapantamidata.ng

08/12/2023

Abinda ya faru a garin Tudun Biri ƙaddara ce daga Allah, mu yiwa mamatan fatan rahama,

-Cewar Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah

ABUBUWA GOMA DA ZA SU FARU A NIGERIA, AMMA DA IZININ ALLAH DA YARDAR SA:-Daga Sheikh Dr. Yusuf Ali1- Ƙasar nan Nigeria T...
08/12/2023

ABUBUWA GOMA DA ZA SU FARU A NIGERIA, AMMA DA IZININ ALLAH DA YARDAR SA:-

Daga Sheikh Dr. Yusuf Ali

1- Ƙasar nan Nigeria Tana Kan Hargitsewa Amma Allah zai kare talaka;

2-Za'a daina daba;

3-Duk dan siyasa a Nigeria azzalumi sai na lahira ya fi shi jin dadi;

4-Abin da duk s**a tara ta zalunci sai ya kare;

5-Talakan Nigeria zai zauna lafiya ba da sa hannun hukuma ba, daga ikon Allah;

6-Duk azzalumi sai ya kunya ta na kowace jam'iyya;

7-Duk masu kudin da s**a tara ta hanyar zalunci za su kunyata su rasa farcen susa;

8-Masu kashe-kashe da kowacce manufa za su daina ba da sa hannun kowacce hukuma ba;

9-'Yan Nigeria za su wadata ba da sa hanun kowacce hukuma ba;

10-'Yan Nigeria za su fahimci kansu ba da dadewa ba.

Wanda ya ga dama yana iya yaɗawa (sharing).

Nigeria Reporters Hausa

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gyaran makaranta a garin Limawa. Gwamnan jihar Jigawa, Mala...
08/12/2023

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gyaran makaranta a garin Limawa.

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya buɗe aikin gyaran ajujuwan Makarantar mazabar Limawa da aka kammala, wadda Rundunar Sojin kasa ta gudanar, karkashin jagorancin Major Abdulkadir.

A jawabinsa, Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, yayi alkawarin cigaba da kula da harkokin makarantar, inda yayi godiya da irin wannan hobbasa da rundunar sojin kasa tayi.

Gwamnan yayi kira da al'ummar Limawa da suyi alfahari da dansu Major Abdulkadir, yana mika godiya ta musamman ga Babban Hafson sojin kasa bisa wannan hobbasa ta guda daga cikin hazikan ma'aikatansa.

Malam Umar Namadi, ya kuma yi kira ga al'ummar Garin dasu Bada kulawa ta musamman ga makarantar don cimma burin da aka sa a gaba.

Muhammad Ismael,
S.A Photography And Publication to the Jigawa State Governor.

Shifa wannan Al-kakalin Baya Cikin Al-kalan Da S**a Yanke Hunkunci  Shari'ar Jihar Kano Naga 'yan kwankwasiya suna ta ya...
08/12/2023

Shifa wannan Al-kakalin Baya Cikin Al-kalan Da S**a Yanke Hunkunci Shari'ar Jihar Kano

Naga 'yan kwankwasiya suna ta yaɗa cewa yana cikin alkalan da s**a yanke hukuncin shari'a a zaɓen jihar kano wanda kuma ba haka bane.

Mudai a kullum burin mu shine Gawuna ya zama gomnan jihar Kano.

Daga Shamsu Gwaska

Mai Martaba Khaleefa Muhammad Sanusi II tareda Mal. Nasır El-Rufai da Khalifofin Tijjaniyya sunje kauyen Tudun Biri a Ka...
08/12/2023

Mai Martaba Khaleefa Muhammad Sanusi II tareda Mal. Nasır El-Rufai da Khalifofin Tijjaniyya sunje kauyen Tudun Biri a Kaduna don yin jaje ga wa ‘yanda s**a samu iftila’in na jefa musu bomb da akayi a wajen taron maulidin Annabi Muhammad (SAW) a kauyen su, a wajen Khaleefa ya basu gudun mowar Naira Miliyan Goma a mada din sa da Khalifofin Tijjaniyya haka kuma Mal. Nasır El-Rufai shima ya bada gudun mowar Naira million goma a madadin sa da ‘yan tawagarsa.

An gudanar da taron yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin jam'iyyar APC da NNPP, kan kammala shari'ar zaben Gwamnan jihar K...
08/12/2023

An gudanar da taron yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin jam'iyyar APC da NNPP, kan kammala shari'ar zaben Gwamnan jihar Kano.

Shin ko kunsan cewa an bude babban ofishin kamfanin Data na farko a kaf yankin Arewa. Kamfanin ABBA PANTAMI DATA shine k...
08/12/2023

Shin ko kunsan cewa an bude babban ofishin kamfanin Data na farko a kaf yankin Arewa.

Kamfanin ABBA PANTAMI DATA shine kamfanin Data na farko a yankin Arewa da aka bude babban ofishin kamfanin a jihar Gombe, nan bada dadewa ba zasu bude rassan su a sauran jihohin Arewa domin cigaba da bunkasa kasuwancin.

Kamfanin ABBA PANTAMI DATA, suna da farashi mai matukar sauki, ga network mai kyau dai-dai Gwargwado ga kuma customer care din su, suna matukar kokari wurin kula da kwastomomi da kuma gyara musu duk wasu matsalolin da s**a fuskanta.

Wanda bai yi ragista ba, ya shiga wannan link din yayi
👇
https://abbapantamidata.com/mobile/register/?referral=08130233375

Ko kuma ya shiga PlayStore ta wannan link din, yayi Download din Application din
👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.abbapantamidata.ng

Ga farashin su mai sauki a yanzu;

MTN SME 244
MTN SME2 246
MTN Cooperate CG 288
MTN Cooperate CG2 260
AIRTEL CG 203
GLO CG 222
9Mobile SME 175
9Mobile CG 140.

Duka Data dinsu tana da Quality kuma ta kwanaki 30 ce, basu saida Data din sati guda ko kasa da wata guda. Ina mai tabbatar muku da cewa za kuji dadin amfani da kamfanin ABBA PANTAMI DATA.

Ba dole sai mai saida Data kadai zai yi ba, ko 1GB kake sakawa a wayarka, zaka iya yin ragista domin ka dinga samunta a farashi mai sauki.

Duk wanda yake bukatan karin bayani, don Allah ya tuntubi daya daga cikin customer care ta WhatsApp.

Ga lambobin customer care uku, da suke available a yanzu;
08126081967
07046868000
07061347599.

Bayanin gaskiya game da batun rufe bankunan Online da s**a hada da; Opay, Palmpay, Moniepoint, Kuda, Wema da sauran su. ...
08/12/2023

Bayanin gaskiya game da batun rufe bankunan Online da s**a hada da; Opay, Palmpay, Moniepoint, Kuda, Wema da sauran su.

A makon da ya gabata babban bankin Najeriya ya bawa bankunan ajiyar kudi (DMBs) umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba shi da BVN da NIN daga farkon shekara mai zuwa.

Da yawan bankunan Online irin su Opay, Palmpay, da Kuda na ba mutane damar bude asusu ta hanyar amfani da lambar waya kawai, ba tare da sanya BVN ko NIN ba.

Sabanin bankuna na zahiri da sai kana da BVN da NIN, amma bankunan Online sun takaita shiga ko fitar kudi akan Naira dubu hamsin a asusu mai matakin tsaro na farko.

Sai dai CBN ya fitar da sanarwar da ke cewa: "Dole ne duk masu asusun ajiyar kudi da ke da matakin tsaro na farko ya makala BVN da NIN, kamar yadda yake dole masu mataki na biyu da uku su saka BVN da NIN, gaza hakan zai sa a rufe asusun."

Wannan sanarwa ta saka anata yada labari a kafofin sada zumunta cewa za'a rufe dukkannin Bankunan Online, duba da cewa suna bada damar ana bude asusu ba tare da an saka BVN ko NIN ba.

Wannan chakwakiyar ta shafi bankuna irin su Opay, Palmpay, Kuda da sauran bankunan Online masu yawan gaske, amma bata shafi bankunan Moniepoint da Wema Bank da sauran manyan bankunan zahiri ba.

A yanzu ya zama dole ga kowane bankin Online da ya bukaci BVN da NIN akan kowane asusun ajiyar da aka bude a cikin shi ko kuma a rufe shi.

Itama fadar shugaban kasa ta karyata labarin cewa, za'a rufe dukkannin Bankunan Online, sai dai tace kowane Banki dole yabi tsarin da Gwamnati ta kawo.

A yanzu haka cikin kwanakin nan, bankunan zahiri da dama sun daina nuna bankunan Online idan za'a tura kudi, wanda yake nuni da cewa suna kokarin katse alaka dasu.

Sannan akwai yiwuwar karawa Bankunan Online haraji, wanda hakan zaisa su fara cire Charges mai yawa ga masu ta'ammuli da bankunan.

Daga Comr Abba Sani Pantami

ABIN BURGEWA : Yadda Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda Ya sauke Gilashin Mota  Yana Gaisawa Da Ƙananun Yara B...
08/12/2023

ABIN BURGEWA : Yadda Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda Ya sauke Gilashin Mota Yana Gaisawa Da Ƙananun Yara Batare da Nuna Ƙyama Ko Hantara ba..

Daga Falalu Lawal Katsina

Su Biyar Ƴan Gida Ɗaya Kuma Dukkanin Su Likitoci Da S**a Samu Ƙwarewa A Fannoni Daban-daban, Ƴan Asalin Garin Okene Dake...
08/12/2023

Su Biyar Ƴan Gida Ɗaya Kuma Dukkanin Su Likitoci Da S**a Samu Ƙwarewa A Fannoni Daban-daban, Ƴan Asalin Garin Okene Dake Jihar Kogi

1. Dr. Salamat Aliu (First Female Certified Neurosurgeon In West Africa)

2. Dr Halima Aliu (Plastic Surgeon)

3. Dr. Raliat Aliu (Obstetrician And Gynaecologist)

4. Dr. Khadijah Aliu (Family Physician)

5. Dr. Medinah Aliu (Public Health Physician)

Daga Jamilu Dabawa

AlhamdulillahYau 07/12/2023 an Shiga rana ta 5 da Fara rabon Tallafin Kayan Noman Alkama da Gwabnatin Tarayya takeyi Kar...
07/12/2023

Alhamdulillah

Yau 07/12/2023 an Shiga rana ta 5 da Fara rabon Tallafin Kayan Noman Alkama da Gwabnatin Tarayya takeyi Karkashin Ministan Gona Sen Abubakar Kyari.

Cikin Farin Cikin da Annashuwa Manoma nakarbar Kayan su duk Hectare 1 Zaa baka , NPK 7, Urea 3, irin Alkama Buhu 1 100kg , Maganin Kwari da Na Kashe Ciyawa. Idan 2 za a Ninka maka Kayan .

Engr Ibrahim Said Uba
07/12/2023.

Shin nawa mataimakin shugaban kasa yake danƙawa wadanda suke kwance a asibitin bayan harin da sojoji s**a kai bisa kusku...
07/12/2023

Shin nawa mataimakin shugaban kasa yake danƙawa wadanda suke kwance a asibitin bayan harin da sojoji s**a kai bisa kuskure a garin Tudun Biri kan masu Mauludi?

SHUGABA TINUBU YA NUNA BACIN RANSA KAN HARIN BAM A KADUNAA yayinda yake mika  ta'aziyyarsa ga Gwamnatin jahar Kaduna da ...
07/12/2023

SHUGABA TINUBU YA NUNA BACIN RANSA KAN HARIN BAM A KADUNA

A yayinda yake mika ta'aziyyarsa ga Gwamnatin jahar Kaduna da iyalan mamatan da ma daukacin Najeriya. Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna kaduwarsa kan mummunan lamarin da ya faru na tashin bam a wani kauye da ke Tundun Biri a karamar hukumar Igabi a jihar.

Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mai tayar da hankali da sanya takaici mai radadi, inda ya bayyana bacin ransa matuka kan abinda ya kira mummunan asarar rayukan da ta auka wa Najeriya.

Shugaban kasar ya bayar da umarni na gaggawa kan a gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da yin kira da a kwantar da hankula yayin da hukumomi s**a sanya ido sosai kan lamarin.

Shugaban ya kuma umarci jami'ai masu ruwa da tsaki da su bayar da kulawar gaggawa ga wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda s**a rasu.

Chief Ajuri Ngelale

Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman

(Kan yada labarai da Jama'a)

Disamba 5, 2023

Rahama Sadau Ta Cika Shekara 30 Cif Da HaihuwaJarumar Fina-finan Kannywood Da Bollywood, Rahama Sadau Ta Cika Shekara 30...
07/12/2023

Rahama Sadau Ta Cika Shekara 30 Cif Da Haihuwa

Jarumar Fina-finan Kannywood Da Bollywood, Rahama Sadau Ta Cika Shekara 30 Da Haihuwa Yau Alhamis

Wace Irin Fata Za Ku Yi Mata?

DA ƊUMI-ƊUMI: Federal High Court Ta Bada Umarnin Rufe Asusun Jihar Kano Har Sai Gwamnati Ta Biya 'Yan Kasuwa Rusau In Ta...
06/12/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Federal High Court Ta Bada Umarnin Rufe Asusun Jihar Kano Har Sai Gwamnati Ta Biya 'Yan Kasuwa Rusau In Tayi Musu A Filin Idi

Rashin Sanin Makamar Aiki Ne Yasa 'Yan Kwankwasiyya Suke Zuwa Ƙasashen Ketare Domin Akawo Musu Ɗauki Kan Shari'ar Jihar ...
06/12/2023

Rashin Sanin Makamar Aiki Ne Yasa 'Yan Kwankwasiyya Suke Zuwa Ƙasashen Ketare Domin Akawo Musu Ɗauki Kan Shari'ar Jihar Kano

Tsohon magatakardan gwamnatin jihar kano Alhaji Usman Alhaji, lokacin ganduje ya gudanar da taron 'yan jaridu a jahar kano akan nasarar gawuna da garo akotu inda yayi tsokaci yace rashin sanin makamar aiki ne irin na 'yan kwankwasiya da har suke garzayawa kasashen ketare da sunan akawo musu ɗauki.

Haka zalika ya bada missalin cewa yanzu ana gudanar da shari'a a England ace wata kotu daga Nigeria sai tace ga abinda ta keso a gudanar zai iyu ?

To dan haka muna kira ga 'yan Kwankwasiyya dasu ƙaddara su karbi hukuncin da kotu tayi, tare da yin biyayya ga hukuncin da kotu tayi.

Haka ya yabawa alkalai da lauyoyi bisa bin doka da kwatanta gaskiya da s**a yi a cikin shari'ar gomnan jihar Kano.

Daga karshe muna addu'a Allah ya bawa gawun da garo nasara a kotun gaba, ya kara da cewa yana da yaki nin kotun qoli ma zata bi bayan sauran kotunan wajen tabbatarwa da gawuna garo kujerunsu, inji Alhaji Usman Alhaji.
Shugaban APC volunteer 4democratic na Nigeria.

Daga Shamsu Gwaska S.A Media 4mer SSG Na jihar kano

TUNA BAYA.. idan kunce a kashe su a shiga  daji a jefa musu Bomb shin kunsan masu jefa bomb din kuma kun san suwa za'a j...
06/12/2023

TUNA BAYA..

idan kunce a kashe su a shiga daji a jefa musu Bomb shin kunsan masu jefa bomb din kuma kun san suwa za'a jefawa.

Cewar ~ SHEIKH DR AHMAD GUMI.

Masu Mauludi Da Aka Sawa Bâm A Kaduna Ba Shahada S**a Yi Ba, Saboda Sun Mutu A Wajen Aikata Saɓon Allah Ne (Bidi'a), Cew...
06/12/2023

Masu Mauludi Da Aka Sawa Bâm A Kaduna Ba Shahada S**a Yi Ba, Saboda Sun Mutu A Wajen Aikata Saɓon Allah Ne (Bidi'a), Cewar Dr. Idris Dutsen Tanshi

Me za ku ce?

YANZU-YANZU: Tinubu Yayi Barazanar Korar Dukkanin Hafsoshin Tsaron Nigeria Saboda Kuskuren Tashin Bom A Jihar KadunaDaga...
06/12/2023

YANZU-YANZU: Tinubu Yayi Barazanar Korar Dukkanin Hafsoshin Tsaron Nigeria Saboda Kuskuren Tashin Bom A Jihar Kaduna

Daga Muhammad Kwairi Waziri

DA DUMI-DUMI: Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya, kan sojan da ya kashe marigayi Sheikh Goni Aisami, dake jiha...
06/12/2023

DA DUMI-DUMI: Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya, kan sojan da ya kashe marigayi Sheikh Goni Aisami, dake jihar Yobe.

Babu Wani Kuskure Cikin Wannan Jefa Bom Da Aka Yi Kaduna, Kuma Dole A Biya Diyya, Sannan A Hukunta Waɗanda S**a Aikata W...
06/12/2023

Babu Wani Kuskure Cikin Wannan Jefa Bom Da Aka Yi Kaduna, Kuma Dole A Biya Diyya, Sannan A Hukunta Waɗanda S**a Aikata Wannan Ta'addancin, Cewar Shiekh Adam Abdullahi Dorayi.

Innalillahi Wa'innah Ilaihi Raji'un..Allah yayiwa yarinya da Abba Gida-Gida ya ɗauki nauyin rashin lafiyarta tun daga na...
06/12/2023

Innalillahi Wa'innah Ilaihi Raji'un..

Allah yayiwa yarinya da Abba Gida-Gida ya ɗauki nauyin rashin lafiyarta tun daga nan gida har zuwa tafiya da ita ƙasar Indiya rasuwa yanzu. Allah ya gafarta mata.

GWAMNA NAMADI YA ZIYARCI CIBIYOYIN RABA KAYAYYAKIN NOMAN ALAKAMA.Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Gwamna Mallam Umar Namad...
06/12/2023

GWAMNA NAMADI YA ZIYARCI CIBIYOYIN RABA KAYAYYAKIN NOMAN ALAKAMA.

Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Gwamna Mallam Umar Namadi FCA Y’a Ziyarci Cibiyoyin Raba Kayayyakin Noman Alkama Wadda Aka Kaddamar A Makon Daya Gabata

Gwamnan Yakai Ziyarar Ne Domin Ganin Yadda Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Tsara Yadda Za’a Raba Kayayyakin Na Noman Alkama Ga Manoman Jihar Jigawa Tareda Da Tabbatar Da Kayayyakin Sun Isa Ga Manoman

Gwamnan Ya Ziyarci Kananan Hukumomin Kiyawa, Jahun Da Karamar Hukumar Miga Tareda Ganawa Da Wakilan Kananan Hukumomin Kan Yadda Sha’anin Raba Kayan Ke Gudana.

Abba Gida-Gida Ba Halastaccen Ɗan Jam'iyyar NNPP Ba Ne, Cewar Shugaban Jam'iyyar NNPP Na Ƙasa, Dakta Agbo MajorUwar jam'...
05/12/2023

Abba Gida-Gida Ba Halastaccen Ɗan Jam'iyyar NNPP Ba Ne, Cewar Shugaban Jam'iyyar NNPP Na Ƙasa, Dakta Agbo Major

Uwar jam'iyyar NNPP ta kasa, ƙarƙashin jagorancin Dakta Agbo Major ta ce gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ba halataccen ɗan Jam'iyyar NNPP bane saboda bai da rijista zama dan Jam'iyyar NNPP kamar yadda kotun Ɗaukaka Ƙara Ta yi hukunci.

Dakta Agbo Major ya bayyana haka a yayin tattaunawa da yan jarida a hedikwatar jamiyyar ta kasa da ke Abuja, yace sun aike wa Sufeto Janar na yansanda da takardar korafi dangane da rashin da'a da wasu korarrun yan jamiyyar ke aikatawa da sunan jamiyyar NNPP.
Dakta Agbo Major ya nuna rashin jin daɗinsa bisa abubuwan da ke faruwa a jihar Kano, Musamman Abinda ya shafi zanga-zanga da rufe wasu daga cikin titunan Kano, kalamai maras sa kyau ga ɓangaren Shari'a da masu sanya jar hula ke yi a Kano,wanda abun ban takaici ne da Allah wadai kuma ba zai haifar mana da mai Ido ba, wanda Jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke kitsawa tare da wasu waɗanda ba yan Asalin Jihar Kano bane, Kamar su Dipo Johnson da Kawu Alli da kuma Onu, wadanda dukkanin su korararru a jam'iyyar NNPP Ne.

Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa ya kara da cewa mun gayyaci jami'an tsaro da su bincike Dapo Johnson da yan koransa, akodayaushe muna karin haske cewa waɗannan mutane ba yaƴan Jam'iyyar NNPP ba ne kuma ba su Wakiltar Jam'iyyar a kowane mataki.

Hatta rashin bin kundin dokokin zaɓen kasa, wanda dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya ja aka yi fatali da dokokin Jam'iyyar NNPP ta shimfida, saboda san rai Kuma ya yi gaban kansa. Har ila yau tuni muka janye yarjejeniyar da muka kulla da su kuma za mu dauki matakin Shari'a, duk da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba shi ya Kirkiro Jam'iyyar NNPP, amma yana so ya yi mata kaka-gida.

Kokarin bunkasa fannin lafiya, a jihar Jigawa. Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana kudurinta na hada Kai da hukumomi da sa...
05/12/2023

Kokarin bunkasa fannin lafiya, a jihar Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana kudurinta na hada Kai da hukumomi da sauran kungiyoyi masu zaman kansu a fannin Lafiya don inganta harkokin Bada Lafiya ga al'ummar jihar Jigawa.

Gwamna Malam Umar Namadi shi ya Bada wannan tabbacin a lokacin daya karbi shugabannin Makarantar koyon aikin Jinya da Ungozoma ta IQRA'A Dake Dutse, wadanda s**a Kai masa ziyara a ofishinsa Dake gidan Gwamnati.

Gwamna Umar Namadi yace makarantun koyar da aikin Jinya da Ungozoma masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ma'aikatan Lafiya da Gwamnati ke dauka don cike gibin da ake dashi a fannin.

Muhammad Isma'el,
SA Photography and Publication.

Shugabannin NNPP masu adawa da Kwankwaso sun juyawa Abba baya.Sun goyi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na cewa gwamnan...
05/12/2023

Shugabannin NNPP masu adawa da Kwankwaso sun juyawa Abba baya.

Sun goyi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na cewa gwamnan Kano ba cikakken ɗan NNPP bane.

Jagoransu, Major Agbo ya yi tir da abinda wasu magoya bayan NNPP s**a yi wa alkalai.

Hukunce-hukuncen Kotun Daukaka Kara A Kan Zaben Gwamnan Jihar Kano, Plateau, Da Zamfara Sun Haifar Da Cece-kuce. Kungiya...
05/12/2023

Hukunce-hukuncen Kotun Daukaka Kara A Kan Zaben Gwamnan Jihar Kano, Plateau, Da Zamfara Sun Haifar Da Cece-kuce.

Kungiyar ‘yan kasa ta Arewa maso tsakiya (North Central Citizens Council) tare da wasu mutane da kungiyoyi da abin ya shafa, sun nuna matukar damuwa dangane da rashin daidaito da sabani dake cikin hukunce-hukuncen shari’a, musamman tun bayan zaben gwamna da aka yi a cikin watan Maris na 2023 a galibin jihohin Arewacin Najeriya.

Wadannan matakai sun haifar da rudani da rashin tabbas a fadin Arewa, lamarin da ya kara ta’azzara tarzomar da dama ta siyasa da cin hanci da rashawa s**a haifar. Kuskurewar gaskiya da gangan da aka yi ta hanyar zabar doka tsakanin Arewa da sauran al’ummar kasar nan na nuni da cewa babbar makarkashiya ce ta durkusar da Arewa ta hanyar gazawa da lalatawa.

Rashin tabbas dake cikin bangaren shari’a na haifar da babbar barazana a matsayin wani bangare na shirin dagula al’amura a yankin, wanda hakan ke nuni da hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ta dauka a jihohi irin su Kano, Filato, da Zamfara ba su dace ba, domin suna cin karo da juna.

A halin da ake ciki a jihar Kano, hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a kan karar Abba da APC ya haifar da korafe-korafe game da hurumin kotun a batutuwan da s**a shafi gabanin zabe. Ka’idar cewa al’amuran gabanin zabe, da s**a hada da na ‘yan takara da kuma daukar nauyin gudanar da zabe, sun kasance karkashin kulawa ta kebantacciyar al’amuran da s**a shafi gabanin zabe, ta tabbata a cikin hurumin zaben al'umma.

An sake maimaita wannan ka'ida a yawancin hukumomin shari'a, inda kotun koli ta sake tabbatar da hakan a shari'ar Peter Obi da INEC. Kotun kolin ta jaddada cewa batun gabatar da sunayen ‘yan takara abu ne da ke gabanin zabe kuma babbar kotun tarayya ce kadai ke da hurumin yanke hukunci a kansa.

Hatta kotun da ta fara yanke hukunci daidai gwargwado ta amince da cewa batun nade-nade abu ne na gabanin zabe. Ko da yake kotun ta gano cewa Abba Kabir Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin zaben fidda gwani, amma ta amince cewa ba ta da hurumin yin bayani kan lamarin. Duk da haka, hukuncin kotun daukaka kara a cikin wannan shari'ar ya saba wa ka'idojin da aka kafa.

Wannan yanke hukuncin kuskure ne kuma yana buƙatar gyara daga Kotun Koli, wanda ake la'akari da cewa nan ne fata na ƙarshe gaa talakawa.

Hukuncin kotun daukaka kara ya gurgunta manufar kasafta al’amuran zabe zuwa al’amuran da s**a shafi gabanin zabe da kuma bayan zabe. Ɗaya daga cikin mahimman ka'idodin doka shine tabbaci, kuma wannan hukuncin ya haifar da rudani a kan sikelin da ba a taɓa gani ba a cikin shari'ar zabenmu. Yarda da wannan shawarar tsayawa zai buɗe wani sashi a cikin hukunce-hukuncen zaɓenmu, wanda a ƙarshe zai nuna rashin amfani ga tsarin.

Yayin da ya zama dole a tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa sun bi ka’idojin zabe, shawarar da aka yanke na soke zaben Kano baki daya ya sanya ayar tambaya kan sahihancin tsarin dimokuradiyya. Za a iya cewa, wannan hukunci ya gurgunta ‘yancin jama’a na zabar shugabanninsu da kuma sanya karfin da ya wuce kima a hannun bangaren shari’a.

Wannan cece-kuce na nuna bukatar daidaito tsakanin bin doka da oda da mutunta ra'ayin dimokaradiyyar al'umma. Haka kuma, cece-kucen da ke tattare da sabanin da ke tsakanin hukuncin da kotun ta karanta da kuma abubuwan da ke kunshe a cikin takardar shedar gaskiya (CTC) na shari’a a zaben gwamnan Kano, ya haifar da shakku a kan gaskiyar dake tsarin shari’a. Wadannan bambance-bambancen sun haifar da rudani da cece-kuce a tsakanin al’umma, lamarin da ya kara zubar da amanar jama’a ke da ita a bangaren shari’a.

Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke kuri’u 166,000 da jam’iyyar NNPP ta samu a zaben gwamnan Kano ya sanya ayar tambaya kan daidaito da adalcin hukuncin da s**a yanke, inda ya kara da cewa a wannan shari’ar, kotun ta bayyana rashin bin ka’ida da kuma rashin bin dokokin zabe a matsayin tushen rushe kuri'un. Sai dai an samu kura-kurai makamancin haka a shari’ar Gwamna Adeleke, inda kotun daukaka kara ta yanke hukuncin soke zaben.

Ta hanyar soke kuri’un da ake ganin ba a bin ka’ida ba a Kano, kotu ta ci karo da hukuncin da ta yanke kan Gwamna Adeleke na jihar Osun, inda aka samu irin wannan kura-kurai amma ba a soke ba. Wannan rashin daidaituwa na amfani da ƙa'idodin doka yana lalata ƙa'idar daidaito a gaban doka kuma yana haifar da shakku game da rashin son kai na kotu.

Matsalolin da ake ta cece-kuce da cin karo da juna da ake gani a hukuncin kotun daukaka kara a kan wadannan shari’o’in zaben gwamnoni na da matukar tasiri ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya. Da fari dai, suna lalata ka'idar daidaito a karkashin doka, kamar yadda aka yanke hukunci iri ɗaya daban-daban, wanda ke haifar da ƙarancin tsinkaya da daidaito.

Na biyu, wadannan sabani suna zubar da amanar jama'a ga bangaren shari'a, yayin da 'yan kasar ke nuna shakku kan rashin son kai da amincin kotun. Na uku, suna haifar da wani yanayi na rashin zaman lafiya a siyasance da tashe-tashen hankula a cikin al’umma, saboda masu cin zarafi na iya yin amfani da hanyoyin da ba na shari’a ba don neman adalci.

A karshe dai tashin hankalin da ake son kaiwa jihohi irinsu Kano, Filato da Zamfara, inda ake kara samun tashe-tashen hankula a siyasance, ya nuna cewa da gangan ake yunkurin haddasa rikicin yankin.

Wannan abun na iya haifar da tashin hankali gaba ɗaya, wanda kuma zai iya haifar da babban rikici a ƙasa. Haka kuma, wadannan shawarwarin na da nufin rage wa Arewa cigaba da kuma kasa tsayawa da kafafunta da kuma yin takara da sauran sassan kasar nan.

Abubuwan da s**a kunno kai a bangaren shari’a a Najeriya na da ciki da matsaloli da sakamakon da ba a zata ba. Dole ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta yin gaggawar hana tabarbarewar zaman lafiya da zubar da jini.

Shari’ar zaben gwamnan Kano musamman ta ja hankalin jama’a sosai saboda yadda ake ta cece-kuce kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke. Wannan zubar da amana na jama'a na iya haifar da mummunan sakamako, ciki har da tashin hankalin al'umma, rashin zaman lafiya na siyasa, da rushewar doka da oda. A matsayinsa na jagoran Najeriya, Tinubu yana da alhakin magance wadannan abubuwan da s**a kunno kai cikin gaggawa.

A cikin wannan mawuyacin hali, kotun koli a matsayin koli na shari'a a Najeriya, dole ne ta taka muhimmiyar rawa wajen maido da kwarin gwiwar al'umma a bangaren shari'a. Ya zama wajibi kotun koli ta yi nazari kan hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ta yanke a shari’ar zaben gwamnan Kano da sauran jihohin Arewa. Ta yin haka, Kotun Koli za ta iya nuna jajircewarta na tabbatar da adalci da bin doka da oda, ta yadda za ta maido da imani ga bangaren shari’a.

Kotun koli, tilas ne ta yi nazari sosai kan hukunce-hukuncen da ke haifar da cece-kuce domin ceto mutuncin bangaren shari'a da ke kara tabarbarewa. Rashin magance wadannan matsalolin cikin gaggawa na iya yin tasiri mai nisa ga kwanciyar hankali da mutuncin Najeriya.

Rashin daukar mataki cikin gaggawa na iya haifar da mummunan sakamako ga al'ummar kasar, ciki har da rashin zaman lafiya da zubar da jini. Ya zama wajibi shugaban kasa ya gane cikin gaggawar lamarin tare da daukar kwakkwaran mataki don hana ci gaba da tabarbarewar mutuncin bangaren shari'a.

Bugu da kari, yana da matukar muhimmanci a fadakar da gwamnatin tarayya da kasashen duniya kan illar da ke tattare da rashin daukar mataki. Alhakin duk wani muhimmin al'amari mai ban tsoro da zai iya faruwa a sakamakon rashin gaskiya na bangaren shari'a zai kasance a kan wadanda s**a kasa yin aiki a lokacin da alamun gargadi s**a bayyana.

Sa hannu
Comrade Mohammed Eneji,
Coordinator, NCCC

Baturiyar Ingila Mai Kimanin Shekaru 62 A Duniya Ta Yi Saukar Al-Qur’ani Mai Girma A Jihar Kano!📸Daily Nigerian Hausa
05/12/2023

Baturiyar Ingila Mai Kimanin Shekaru 62 A Duniya Ta Yi Saukar Al-Qur’ani Mai Girma A Jihar Kano!

📸Daily Nigerian Hausa

Bunkasa harkokin gona a jihar Jigawa Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya yabawa kokarin Bankin Bunkasa harkokin g...
05/12/2023

Bunkasa harkokin gona a jihar Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya yabawa kokarin Bankin Bunkasa harkokin gone na nahiyar Afrika bisa tallafawa manoma don Samar da Wadataccen abinci ga al'ummar kasar Nan.

Gwamnan yayi wannan yabon ne a lokacin daya karbi bakuncin mahukuntan Bankin a ofishinsa, wadanda s**a zo don tattaunawa kan yadda za'a bunkasa harkokin aikin gona a jihar Jigawa.

Yace gwamnatinsa a shirye take data bunkasa fannin aikin gona don tallafawa manoma sun rubanya ribar da suke samu daga kayayyakin da s**a noma.

Muhammad Isma'el,
SA Photography and Publication.

Mutane 126 Ne S**a Rasu A TUDUN BIRI IGABI 😥Duk wada kuke gani a Photon nan, Ubangiji Allah ya karɓi rayuwarsu. Kadan ne...
05/12/2023

Mutane 126 Ne S**a Rasu A TUDUN BIRI IGABI 😥

Duk wada kuke gani a Photon nan, Ubangiji Allah ya karɓi rayuwarsu.

Kadan ne daga ciki s**a raunata. Ubangiji Allah ya karbi shahadarku Aameen Yaa Allah🙏🏼

Sadeeq Salis

Ƙungiyar Arewa Media Writer's Tayi Kakkausar S**a Kan Kashe Mutane Fiye Da Ɗari Da Jirgin Sojojin Najeriya Yayi.Daga Kun...
05/12/2023

Ƙungiyar Arewa Media Writer's Tayi Kakkausar S**a Kan Kashe Mutane Fiye Da Ɗari Da Jirgin Sojojin Najeriya Yayi.

Daga Kungiyar Arewa Media Writer's

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Marubutan Arewacin Najeriya tayi Allah wadai da kisan masu Mauludi da rundunar sojojin Najeriya tayi a Tudun-Biri dake ƙaramar hukumar Igaba a jihar Kaduna bisa kuskure.

Kungiyar Marubutan Arewa a kafofin sada zumunta Arewa Media Writers tayi Allah-wadai tareda kira ga gwamnatin Najeriya da tayi cikakken bincike don tabbatar da gaskiyar al'amarin abinda ya faru jiya a jihar kaduna.

Haka zalika Gomnati zata biya diyyar rayukan da s**a halaka a kuskuren jefa Bom da dakarun sojin Nigeriya s**ayi kan tawagar musulmai masu bikin Maulidi a garin Tudun-Biri, dakew karamar hukumar Igabi jihar Kaduna....

Da misalin karfe goma na daren jiya Lahadi 4/11/2023 al'ummar garin Tudun-Biri karamar hukumar Igabi s**a fuskanci mummunan tashin hankalin da yayi sanadin rasa rayukan mutane kimanin 126 a wani harin sama da jami'an soji s**ayi kan wasu gungun mutane da suke tsaka da bikin Maulidi.

A rahotannin da muka samu sun bayya na cewa, jami'an sojoji ne s**a jefa abun fashewar ne inda yayi sanadin halaka kimanin mutum 126 ciki har da maza mata yara da tsofaffi.

Zuwa yanzu dai dai hukumar soji ta dauki alhakin kisan gillar inda tace harin ya wakana ne bisa kuskure,a cewar rundunar soji ba da son ransu bane s**a halaka mutane....

Wannan irin mummunan kisan gillar yaja hankalin kungiyar Arewa Media Writers, a madadin mambobin kungiyar tun daga matakin kasa Jihohi 19 dake fadin Arewacin Najeriya har zuwa kananan hukumomin Arewa, muna kira da kakkausar murya ga gwamnatocin Najeriya da su gaggauta yin cikakken Kwa-kwaf kan lamarin tareda daukar matakin biyan diyyar rayukan da s**a salwanta a sanadin harin....

Irin wannan mummunan hari kan talakawan da basuji ba basu gani ba ya taba faruwa a jihar Borno kwanakin baya, inda mutane s**a halaka da dama a lokacin ma hukumar soji tace bisa kuskure ne harin ya faru.

Sshikenan rayukan bayin Allah ya ringa salwanta ba gaira babu dalili, da wannan ne Kungiyar Arewa Media Writers take kira ga biyan diyyar rayukan da s**a rasu a garin Tudun-Biri don kaucewa faruwar irin haka a nan gaba.

Hakika biyan diyya zai sa hukumomi su tsaurara bincike gabanin jefa abun da zai halaka mutane da yawa irin haka....

"Bai kamata mahukuntan kasar nan suyi shiru kan abunda ya faru a Kaduna ba, ina shugabannin mu na Arewa, da Sarakuna da ...
05/12/2023

"Bai kamata mahukuntan kasar nan suyi shiru kan abunda ya faru a Kaduna ba, ina shugabannin mu na Arewa, da Sarakuna da Malamai da 'yan siyasar mu? Ya kamata ku fito ku tsaya kai da fata, har sai an biya diya, tare da gudanar da kwakkwaran bincike kan gaskiyar aukuwar wannan mummunan abu ga 'yan uwanmu."

~ Inji Comr Abba Sani Pantami

Wannan Matashi Da Kuke Ganin Dan Garin Hashidu Dake Jihar Gombe Jiya Wasu Su Kaje Har Wajen Sana'ar Shi A Jihar Enugu S*...
05/12/2023

Wannan Matashi Da Kuke Ganin Dan Garin Hashidu Dake Jihar Gombe Jiya Wasu Su Kaje Har Wajen Sana'ar Shi A Jihar Enugu S**a Caka Masa Wuka

Yunusa Adamu Kero Matashi da yakesana'ar nama jiya wasu makiya Allah s**a afka masa da wuka ba tare da wani dalili ba s**a kashe shi har lahira.

Zuwa yanzu wannan karo na biyu kenan suna mana irin wannan kisan zalinci a 'yan uwan mu mazauna yankin wurin.

A shekarun baya akwai wani matashi daya yake sana'ar a caba a jihar Enugu wanda tautsayi yasa ya daiki wasu Fulani ashe cikin kayan su akwai bindiga ciki, suna zuwa checking point s**a gudu s**a barshi da kayan ana bin cikawa aka bindiga haka aka tsare tsawon kwanaki ana zalintar sa, kuma babu wani mataki da gomnatin ta dauka.

Da wannan ne muke kira ga Gomnati jihar Gombe tabi mana kadun 'yan uwan mu da suke zaune a jihar Enugu ake musu kisan zalinci.

Tabbas su suna taba 'yan uwan mu musulmai suna sharewa amma mu bamu isa mu taba su share ba b***e ma addinin mu ya haramta hakan.

Gomnatin jihar Gombe tabbas hakki ya rataya a wuyan ku a binciko mana Waɗan da s**ayi wannan kisan tare da ɗaukan mataki mai tsauri akan su.

Sanarwa Ta Musamman Ga Manoma Alkama!5th December, 2023 Yau saura Kwanaki 10 a Kammala Aikin rabon Tallafin Kayan Noma A...
05/12/2023

Sanarwa Ta Musamman Ga Manoma Alkama!

5th December, 2023

Yau saura Kwanaki 10 a Kammala Aikin rabon Tallafin Kayan Noma Alkama , Manoman da s**a samu Sakon Tallafin ta wayoyin su , su hanzarta zuwa Cibiyoyin da aka Tura su dan Karbar Kayan Tallafin Taki NPK 7, Urea 3, Irin Alkama 100kg , Maganin Kwari da Na Kashe Ciyawa.

Engr Ibrahim Said Uba
05/12/2023.

Address

Area 2 Mashood Abiola Road Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigerian News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share