Bidiyon da na'urar CCTV ta ɗauka ya nuna yadda wasu ɗaurarru suka danne wani mai gadi sannan suka tsere daga caji-ofis a Babban Ofishin 'Yan sanda na Parigi Moutong da ke lardin Sulawesi a Indonesia ranar 31 ga watan Janairu.
Kafofin watsa labaran ƙasar sun ce ɗaurarru bakwai ne suka tsere, kuma shida daga cikinsu suna fuskantar manyan tuhume-tuhume kan dillancin ƙwayoyi.
An gano gawawwakin Falasɗinawa 20 da sojojin Isra'ila suka kashe a watannin baya a yankin Zayed na Gaza.
An kashe mutanen ne lokacin da Isra'ila take yaƙi a yankin Gaza sannan aka binne su a wani babban kabari.
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta fara ɗaukar matakin tabbatar da cewa duka motocin da ke faɗin kasar an yi musu inshora don tabbatar da kiyaye hadura da kuma kare hakkin waɗanda haɗari ya rutsa da su, a cewar rundunar.
Wata motar sojin Isra'ila ta tarwatsa wani teburin sayar da kayan miya a gefen hanya a kasuwar birnin Tulkarem a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.
Yanayin hazo ya haifar da muMmunan karon motoci da dama a kan babbar hanyar Taihui a ranar 1 ga Fabrairu, a Puyang, da ke gundumar Henan a China, yayin da hanyar ta cika da ababen hawa saboda bikin Spring.
Fiye da motoci 100 ne suka yi hatsarin, inda wasu suka lalace sosai.
Bidiyon da aka fitar bayan sakin Falasdinawa daga gidajen yarin Isra'ila ya nuna yadda suka yi matuƙar ramewa da shan wahala a hannun Isra'ila, yayin da a gefe guda wani bidiyon ya nuna yadda Isra'ilawa da aka saki daga Gaza suke cikin ƙoshin lafiya da walwala.
Shugaban rikon kwarya na kasar Syria Ahmed al Sharaa ya sauka a kasar Saudiyya a ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje. Ana sa ran Sharaa, wanda ya karbi mulki bayan kungiyoyin da ke adawa da gwamnatin Bashar al Assad sun kifar da gwamnatin ƙasar, zai gana da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a Riyadh.
Zan iya auren mace irin Samira ta shirin Garwashi
Fitaccen ɗan wasan Kannywood Yakubu Muhammad ya yi ƙarin bayani dangane da irin rawar da yake takawa a cikin wasu fina-finai masu dogon zango da yake ciki waɗanda suka haɗa da Garwashi da Labarina da Gidan Sarauta.
Ɗaruruwan mutane sun taru domin murna bayan an saki wasu fursunoni Falasɗinawa duk a cikin matakan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.
Bayan Hamas ta saki wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a safiyar yau, Isra'ila ta fara sako fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da wasu da dama da aka yanke musu hukuncin daurin tsawon shekaru a gidan yarin Isra'ila.
Shin an kada gangar siyasa ne a Nijeriya?
Yanayin siyasa ya fara ɗaukar ɗumi a Nijeriya inda a cikin ‘yan kwanakin nan tsohon gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya soki gwamnatin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC kan yanayin yadda al’amura ke tafiya a ƙasar.
Wasu bidiyoyi da aka ɗauka sun nuna yadda jirgin sama ya kama da wuta a iska sannan ya faɗi, inda ya ƙona gidaje da motoci
Wani jirgin ɗaukar marasa lafiya a birnin Philadelphia na Amurka ya yi hatsari a ranar Juma’a da dare, ƙasa da minti ɗaya bayan ya tashi, lamarin da ya jawo gidaje da dama suka ƙone da motoci bayan faɗuwarsa.