AKH Multimedia

AKH Multimedia Media/News company

09/08/2024

Barkan mu Juma'ah!

09/08/2024

The oldest Market in Nigeria 📌

Please watch & Share!

Hotunan zanga-zanga a waya garuruwa a Najeriya
01/08/2024

Hotunan zanga-zanga a waya garuruwa a Najeriya

01/08/2024

Ya Zanga-zangar lumana ke wakan a garuruwan ku?

28/07/2024
CIKIN HOTUNA: Yadda Shugaban 'Yan Sandan Najeriya Ya Jagoranci Yi Wa Kwamandojin Shiya Na 'Yan Sanda Lakca Ta Musamman D...
28/07/2024

CIKIN HOTUNA: Yadda Shugaban 'Yan Sandan Najeriya Ya Jagoranci Yi Wa Kwamandojin Shiya Na 'Yan Sanda Lakca Ta Musamman Domin Suyi Aikin Su Cikin Ƙwarewa A Lokacin Zanga-zangar Da Ake Shirin Yi A Faɗin Ƙasar Nan

Idon Mikiya

Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar 13×13 ta gudanar da gangamin taron jaddada goyon baya ga Shugaba Tinubu a jihar KanoCikin bayanan ...
28/07/2024

Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar 13×13 ta gudanar da gangamin taron jaddada goyon baya ga Shugaba Tinubu a jihar Kano

Cikin bayanan da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana wasu daga cikin nasarorin da shugaba Tinubu ya cimma a cikin shekara ɗaya kacal waɗanda su ne s**a ja hankalinta wajen shirya gangamin taro na musamman domin yabawa gami da jaddada goyon baya a gare shi.

Nasarorin da ƙungiyar ta bayyana sun haɗa da:

1. Samowa ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai a kotun ƙoli, wanda hakan zai ba wa al'umma damar samun tsaro da zaman lafiya gami da wadatar kuɗaɗe a hannun jama'a.

2. Ƙirƙiro da sabuwar ma'aikata musamman domin kula da dabbobi, kiwo, da harkokin fulani domin gina tattalin arziƙi da wadata ƙasa da abinci.

3. Sake buɗe iyakokin Najeriya (Boda) domin ƴan kasuwa su fita su sayo kayan abinci da sauran kayayyakin buƙata su shigo da su Najeriya tayadda za a kawar da matsalar hauhawar kayayyakin masarufi.

4. Kafa sabuwar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma wadda ta haɗa Jihohin: Kano, Kaduna, Jigawa, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara tayadda arziƙi da cigaba za su wadata.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron, shugaban ƙungiyar ta 13×13 reshen Jihar Kano, Muhammad Adam ya ja hankalin matasa da ka da su yarda wasu su yi amfani da su wajen lalata ƙasarsu da rusa tattalin arziƙin al'ummarsu, "shugaba Tinubu yana da kykkyawan fata, Wallahi ba shi ne ya jefa ƙasar nan a cikin matsi da talauci ba, mu kyautata masa zato". In ji shi.

Taron ya samu halartar shugaban gangamin na ƙasa gabaɗaya, Aminu Warkal tare da ɗumbin magoya baya daga sassa daban-daban na Jihar Kano.

Hausa Daily Times

Gobe in Allah Ya kai mu,Monday!Me ku ka shirya za ku yi???
28/07/2024

Gobe in Allah Ya kai mu,Monday!

Me ku ka shirya za ku yi???

A da na  samu kyautar motoci har guda 75 saboda Waka, sannan na siya guda 70 da kudi na,.Amma Yaɲzu banda ko ɗaya saboda...
27/07/2024

A da na samu kyautar motoci har guda 75 saboda Waka, sannan na siya guda 70 da kudi na,.
Amma Yaɲzu banda ko ɗaya saboda yanayiɲ rayuwa Inji Mawaki Aminu Maidawayya

Wani faifan bidiyo da Hukumar Watsa Labarai ta Olympics ta fitar ya nuna yadda Mawaƙiya  Celine Dion ke yin waka a Hasum...
26/07/2024

Wani faifan bidiyo da Hukumar Watsa Labarai ta Olympics ta fitar ya nuna yadda Mawaƙiya Celine Dion ke yin waka a Hasumiyar Eiffel, yayin bikin buɗe gasar wasannin Olympics ta Paris 2024, a birnin Paris, a yau ranar 26 ga Yuli, 2024.

Kun yarda da furucin shugaba?
26/07/2024

Kun yarda da furucin shugaba?

KUNA CIKIN  BUTULU KO KUWA BA KWA CIKI?
26/07/2024

KUNA CIKIN BUTULU KO KUWA BA KWA CIKI?

Wai da gaske ba su san dalilin ba?
26/07/2024

Wai da gaske ba su san dalilin ba?

26/07/2024

Barkan mu da wannan babbar rana ta Jumu'a.Alah bamu Alkyarin ta

Farashin kayan gona a jiya Alhamis  27 ga watan Yulin 2024 a kasauwar Kamfanin Bobi da ke a karamar hukumar Mariga ta ji...
26/07/2024

Farashin kayan gona a jiya Alhamis 27 ga watan Yulin 2024 a kasauwar Kamfanin Bobi da ke a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

1. Masara N90,000 zuwa N95,000

2. Dawa N96,000 zuwa N100,000

3. Jan Wake N236,000 zuwa N240,000

4. Farin Wake N196,000 zuwa N200,000

5. Shinkafa N77,000 zuwa N80,000

6. Waken Suya N100,000 zuwa N103,000

7. Gyada N43,000 zuwa N45,000

8. Sabuwar Masara N68,000 zuwa N70,000

📸 Abubakar Usman Kamfanin Bobi

Da ɗumi-ɗumi: Al Hilal ta fara tuntuɓar Barca a hukumance domin fara tattaunawa akan Vitor Roque!Ƙungiyar ta Saudiyya na...
26/07/2024

Da ɗumi-ɗumi: Al Hilal ta fara tuntuɓar Barca a hukumance domin fara tattaunawa akan Vitor Roque!

Ƙungiyar ta Saudiyya na son ɗaukar ɗan wasan gaban na Brazil, Jorge Jesus na ganin Vitor Roque a matsayin ɗan wasa mafi da cewa da salon sa.

Barcelona ta zuba €30m da ƙarin €31m shekara ɗaya da ta gabata domin ɗaukar Tigrinho, amma kuma a yanzu dole su yanke abun da yakamata suyi.

Yanzu ya rage ga Vitor Roque domin ya yanke shawara akan makomar sa, zai yanke shawara akan yiyuwar komawar sa Al Hilal da wakilin sa.

Barcelona zata iya amincewa da tafiyar ɗan wasa domin daidaita yanayin tafiyar kuɗaɗen ta, don ganin tayi ƙoƙarin kawo Dani Olmo da Nico Williams.

• Fagen Wasanni

26/07/2024

ZANGA-ZANGA za a janye..
Ba a ƙara yi muku tawaye..
Idan kun ji wannan kiraye👇

1.Farashin FETIR ya karye..
2.Bodojin da ku ka rataye..
A buɗe abinci ya tumfaye..

3.Matasa na Birni da Ƙauye..
Ku hana idanun su hawaye..
Aikin yi a ko ina ya kewaye👇

In sharruɗan nan kun kiyaye..
Babu mai ƙara ɗaga kwalaye👌
Har akai ga wani waye-waye!

Allah Kaine Al-Hayyu (Rayayye)
Dan darajar manzon ka fiyayye..
Kar Ka bari ƙasar mu ta karye👏

Aammeenn!
(Musan Jami)

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AKH Multimedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share