BAMS TV

BAMS TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from BAMS TV, TV Channel, Zaria.

13/09/2024

Assalamu alaikum jama'a

Muna farin cikin shaidawa dukkan wanda ke cikin wannan gida mai albarka na Tv Hausa cewa, in sha Allahu nan bada daɗewa ba zamu cigaba da gudanar da ayyukan mu akan wannan manhajar ta facebook da WhasApp da YouTube dama sauran kafafen zamani.

Ku ziyarci shafukan mu na yanar gizo domin samun labarun Duniya, ko ka kalli sharhunan bayan labaru.

.com.ng/Bams Hausa Tv

Manyan Ƙasashe Guda Shida Da S**a Fi Yawan Masallatai A Faɗin Duniya1 — Kasar Indonesiya a ƙalla tana da Masallatai guda...
02/07/2024

Manyan Ƙasashe Guda Shida Da S**a Fi Yawan Masallatai A Faɗin Duniya

1 — Kasar Indonesiya a ƙalla tana da Masallatai guda dubu 800.

2 — Ƙasar Pakistan a ƙalla tana da Masallatai guda dubu 500.

3 — Ƙasar India, wadda a ƙalla tana da Masallatai guda dubu 350.

4 — Ƙasar Bangaladash, wadda a ƙalla tana da Masallatai guda dubu 300.

5 — Ƙasar Saudiyya, a ƙalla tana da Masallatai guda dubu 150.

6 — Sai Ƙasar Najeriya, wadda a ƙalla tana da Masallatai guda dubu 100.

Daga Usman Umar Katsina

02/07/2024
AL-AJABI: Matar da kwata-kwata ba ta jin yunwaMuluwork yar shekara 26 daga yankin Jimma dake Addis Ababa babban birnin k...
11/04/2024

AL-AJABI: Matar da kwata-kwata ba ta jin yunwa

Muluwork yar shekara 26 daga yankin Jimma dake Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia ta ce ta kwashe shekara 16 bata ci bata sha, bata cin abinci bata shan abun sha koda ruwa kuwa bata taba sha ba tun tana yar shekara 10 a duniya.

Fraministan Ethiopia ya taba sa an kaita asibitin ƙwararru a Dubai domin duba lafiyarta kuma likitoci sun aunata sun ce lafiyar ta kalau kuma dagaske babu alamun abinci a cikin kunɗinta.

Mahanga ta ruwaito matar tana da miji da ɗiya mace guda ɗaya. Ku kasance da shafin Mahanga anjima in sha Allah za mu kawo maku cikakken bidiyon binciken da aka yi akanta.... Kuyi following shafin Mahanga domin kallon wannan abun al-ajabi...

Sai ranar Sallah
08/04/2024

Sai ranar Sallah

Sau Shida Tana Ɗaukan Ciki Amma Jaririn Na Kaiwa Wata Takwas (8) Zai Mutu A Cikin CikiA harkar lafiya da sha'anin asibit...
03/04/2024

Sau Shida Tana Ɗaukan Ciki Amma Jaririn Na Kaiwa Wata Takwas (8) Zai Mutu A Cikin Ciki

A harkar lafiya da sha'anin asibiti ba nau'in abin al'ajabi, takaici ko tausayi da mutum ba zai gani ba.

Ta shigo dakin ɗaukar hoton ciki (Ultrasound Scanning) tare da takardar da likita ya rubuta mata. Nan ne fa shi abokina mai ɗaukan hoton ya ga an rubuta cewa a mata hoton ciki ne (Obstetric Ultrasound Scanning) domin ganin lafiyar jaririn dake cikin ta.

Ta hau gado aka daura abin yin hoto a cikin nata, bincike ya nuna cewa jaririn ya mutu a ciki bashi da rai duk da cewa cikin ya kai wata 8. Nan fa abokina ya rubuta sak**akon a takarda ya liƙe yace ta kaima likitan.

Sai ta tambaye shi; "dan Allah bawan Allah mai ka gani ne a sak**akon", sai yace taje wajen likitan zai mata bayani. Nan fa ta matsa dan Allah ya gaya mata, har tana cewa; "in ma wani mummunan abu ne ya samu jaririn ai dole ta ɗauki ƙaddara tun da ita musulma ce".

Ganin wai tana da tawakkali sai abokina yace mata gaskiya jaririn ya mutu a ciki, bashi da rai. Nan fa ta kwantsama ihu; "wayyo Allah na mutu na lalace, ciki na shida (6) kenan sai sun kai wata takwas (8) sai jaririn ya mutu a ciki". Tana fadi tana numfashi sama sama saboda baƙin ciki. Har zanin ta na kwance wa amma ko lura bata yi ba saboda ɗimauce wa.

Duk in naga irin wannan sai nace, Allah Sarki, wasu na zubar da ciki duk bayan wata wasu na neman shi gadan gadan. Tabbas rayuwa babu daidaituwa, Allah mai yadda Yaso. Allah Ya mana mai kyau.

Ina rokon Allah, alfarmar wannan wata mai daraja yasa duk masu neman Haihuwa su samu, masu juna biyu su sauka lafiya, marasa lafiya su samu lafiya, cikin rahama da jin ƙai na Ubangiji madaukakin Sarki.

Naku a kodayaushe Pharm. Musa A Bello Zaria
ABIN LURA: Wannan hoton ba na gaske bane, da na'ura mai ƙwaƙwalwa (computer/AI) na haɗa shi.

Murnar zagayowar ranar haihuwa ga Prakash Raj, ɗan wasan Indiya ta Kudu, darakta, furodusa, kuma mai watsa shirye-shirye...
01/04/2024

Murnar zagayowar ranar haihuwa ga Prakash Raj, ɗan wasan Indiya ta Kudu, darakta, furodusa, kuma mai watsa shirye-shiryen talabijin, an haife shi a ranar 26 ga Maris, 1965, a Bengaluru, Karnataka. Prakash yana cikin bukatu sosai saboda yana jin daɗin magana da Kannada, Telugu, Tamil, Malayalam, Marathi, Hindi, da Ingilishi. A lokacin aikinsa, Prakash ya fito a fina-finai sama da 400 a cikin wadannan harsuna. Ya taka rawar gani iri-iri kuma ana ganinsa a matsayin mai adawa. Ya fara aikinsa yana yin talabijin da fitowa a fina-finan Kannada a shekarun 1990.

Bayan haka, ya fara aiki a fina-finan Tamil da Telugu kuma ya zama sanannen tauraro ya lashe kyaututtuka da dama a matsayin Best Villain, Best Actor, and Best Supporting Actor. Shahararriyar rawar da ya taka ta Bollywood ita ce babban kauye a cikin 'Singham' (2011), da Soja Sargant Ustad a cikin 'Bhaag Milkha Bhaag' (2013). An ga Prakash a cikin fim din Rohit Shetty mai suna 'Golmaal Again', daya daga cikin fina-finan Bollywood da s**a samu kudin shiga a shekarar 2017. Ya samu lambar yabo ta National Film Award for Best Supporting Actor a cikin wasan kwaikwayo na siyasa na Mani Patnam na 1998 'Iruvar', lambar yabo ta National Film Award for Best Actor.

'Kanchivaram' (Tamil 2008), fim ne game da rayuwar masu saƙar siliki, da lambar yabo ta Fina-Finai ta ƙasa don Mafi kyawun Fim a Kannada don 'Puttakkana Highway' (2011), a matsayin furodusa. A cikin 'yan shekarun nan, Prakash ya fito a cikin fina-finai da yawa masu nasara, misalai sune 'Jai Bhim' (Tamil), 'K.G.F: Chapter 2' (Kannada) fayil na 400th, 'Major' (Telugu), 'Sita Ramam' (Telugu). 'Ponniyin Selvan: 1' da Ponniyin Selvan: 2 (Tamil), 'Salaam Venky' (Hindi), da 'Guntur Kaaram' (Telugu).

Wasu Halaye Dake Iya Lalata Lafiyar Mutum Cikin Shekaru KaɗanTabbas a wannan zamanin wasu nau'in rashin lafiya sun yawai...
27/03/2024

Wasu Halaye Dake Iya Lalata Lafiyar Mutum Cikin Shekaru Kaɗan

Tabbas a wannan zamanin wasu nau'in rashin lafiya sun yawaita ba k**ar da ba da zai yi wuya ace kasan masu irin matsalar sai dai a baka labari, Misali: Ciwon Koda (Kidney Disease), Ciwon Daji (Cancer), Ciwon S**ari (Diabetes), Cutan Damuwa (Depression) har ma da hawan jini (Hypertension).

Wasu daga cikin wadannan ciwukan yanzu sun yawaita, kuma suna k**a matasa sosai. Duk da cewa abubuwa da yawa ne ke iya haifar da su (Several Factors), Amma akwai halaye da s**a yawaita abin. Kaɗan daga cikin halayen su ne:

1. Yawan Shan Kayan Ƙara Ƙarfi (Energy Drinks): Wani kullum sai ya sha FE@RLÉSS da irinsu guda uku ko fiye da haka. Yanayin yawan sinadarin CAFFEINE dake cikin wannan abin nada ƙarfi, hasali ma shi yasa ake gargadi mai ciki da yara basa sha.

2. Rashin Motsa Jiki: Yanzu muna wani yanayi da mutane sun sangarce, tafiya 'yar kaɗan sai an hau adaidaita sahu (keke napep), mashin ko mota. Wanda hakan yasa ba'a samun mafi ƙarancin motsa jikin da ake bukata. Domin inganta lafiya, musamman lafiyar zuciya da jiki, ana so mutum yayi tafiyar aƙalla minti 30 a rana, jumulla mintuna 150 a sati.

3. Yawan Cin Abinci Zamani (Irin su Cake, Shawarma, Waken Gwangwani, Abincin Gwangwani da sauransu), abinda bature ke ce ma JUNK FOOD: Cin su jefi jefi ba matsa bane, amma mutum ya sa ma kanshi yawan cin su na da matsala domin ba abincin gina jiki bane su. Mutum sai yafi lafiya in yanacin abincin da aka girka ba wai irin wanda aka sarrafa shi ba kawai.

4. Shaye Shaye: Fara daga shaye shayen lemun kwalba/roba ba bisa ka'ida ba izuwa shaye shayen kayan maye. Wannan halin na cikin abinda ke lalata lafiyar mutum.

5. Yawan Tunani: Muna zamanin da yawan tunani yama mutane yawa, ko da tunani ne akan abinda basu da ikon canzawa. Yawan tunani bashi da wani fa'ida face ya haifar ma mutum da yanayi na rashin natsuwa da kwanciyar hankali. Hasali ma yanzu cutar damuwa (DEPRESSION) ya yawaita, kuma cikin musabbabin akwai keɓe kai cik

Yanda Abin Yake Kan Ƙarin Kuɗin Aikin Hajji Na Bana A Najeriya1. Akwai wanda s**a riga s**a biya kuɗin aikin Hajjin su n...
27/03/2024

Yanda Abin Yake Kan Ƙarin Kuɗin Aikin Hajji Na Bana A Najeriya

1. Akwai wanda s**a riga s**a biya kuɗin aikin Hajjin su na bana N4,699,000. Su za su cika N1,918,000 kudin su ya zama N6,618,000.

2. Wanda kuma ba su riga sun biya ba kuma suna da niyyan zuwa har yau 24th March, su za su biya N8,225,000 don zuwa aikin Hajjin Bana. (Ma'ana Gwamnati ba ta sa musu subsidy ba).

3. Ana so wanda s**a biya kuɗin farko su cika kudin nan da kwanaki 4 kacal, wato 28 ga wannan wata ko su rasa daman su na zuwa sauke farali.

Wannan matar Kirista ce, ta suma (she fainted),  ta Suma har sau biyu yau, saboda ta gwada yin Azumi taji yadda Musulmi ...
22/03/2024

Wannan matar Kirista ce, ta suma (she fainted), ta Suma har sau biyu yau, saboda ta gwada yin Azumi taji yadda Musulmi suke ji....
~ Ta tashi karfe 4:30 da rabi na Asubah taci Abinci k**ar yadda Musulmi suke yin Sahur, amma kafin karfe 10 na safe sai cikin ta ya fara tururi da tashin hankali.

Tace ada tana wasa da Azumin bata san haka ake ji ba, sai da aka cece rayuwar ta a wani Asibiti yau. Tace kiris ya rage ta mutu...🤣...
~ Tace duk masu yin Azumin Nan jarumai ne, maganar gaskiya kenan... Tun daga 4:30am har 6:30pm baka ci ba baka sha ba, wannan sai me kokarin gaske...

Kakakin majalisar Abbas ya yi mu'amala da mazabu da masu ruwa da tsaki a Zariya Kakakin majalisar wakilai Rt.  Hon.  Abb...
18/03/2024

Kakakin majalisar Abbas ya yi mu'amala da mazabu da masu ruwa da tsaki a Zariya

Kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Abbas Tajudeen, Ph.D, a karshen makon da ya gabata, ya tattauna da al’ummar mazabarsa, manyan shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a mazabar tarayya ta Zariya. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Abdullahi Krishi

Tattaunawar dai na daga cikin kudurin da shugaban majalisar ya yi na yin sa-in-sa da kuma jin halin da al’ummar mazabarsa ke ciki kai tsaye da nufin lalubo hanyoyin magance su.

Tun da farko dai shugaban majalisar ya yi buda baki a gidan iyalansa tare da ‘yan uwa da abokan arziki, inda ya tattauna da su.

Kakakin majalisar Abbas ya yi irin wannan ganawa da mazabarsa a ranar 15 ga Yuli, 2023, a lokacin da ya dawo gida bayan hawansa zama shugaban majalisar a ranar 13 ga Yuni, 2023.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Majalisar ya kai ziyara watan Ramadan inda ya raba kayan abinci da sauran kayayyaki ga kimanin mutane 55,000 a mazabar tarayya.

Wadanda shugaban majalisar ya zanta da su sun hada da dattawa, kwamitocin wucin gadi kan ilimi, kiwon lafiya, ICT da sa ido kan ayyuka, kungiyoyin tallafi, kungiyoyin mata da matasa, masu girma kansiloli, kwamitin zartarwa na karamar hukumar APC, kafafen yada labarai da mambobin kwamitoci daban-daban.

Da yake jawabi a ganawar daban-daban, manyan shugabannin kungiyoyin sun yaba wa shugaban majalisar bisa kokarin da ya yi na sanya murmushi a fuskokinsu.

Sun yi nuni da cewa shugaban majalisar ya sauya rayuwar da yawa daga cikinsu ta hanyoyi daban-daban tun bayan hawan sa, inda s**a yi nuni da cewa hakan na ci gaba da gudanar da ayyukan da ya yi tun kafin ya zama shugaban majalisar.

Sun kuma lura da abubuwan da ba a taba ganin irinsu ba ta hanyar ayyukan mazabu, wadanda shugaban majalisar ke jan hankalin mazabar tarayya tun hawansa.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta k**a wasu musulmi 11 da ake zargin suna sara ...
13/03/2024

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta k**a wasu musulmi 11 da ake zargin suna sara a lokacin azumin watan Ramadan.

Kano ta samu rinjayen al'ummar Musulmi, saboda tsarin shari'ar Musulunci - Shari'a - yana aiki tare da tsarin mulkin duniya.

Jami’an ‘yan sandan Islama, mai suna Hisbah, a duk shekara a cikin watan Ramadan, suna binciken gidajen abinci da kasuwanni.

"Mun k**a mutane 11 a ranar Talata da s**a hada da wata mace daya da ke sayar da gyada, ta tsinke gyadan da take sayar da ita, wasu kuma s**a sanar da mu," in ji Lawal Fagge pesin na Hisbah.

"Ku kasance maza kuma mun k**a mutane a duk fadin birnin musamman kusa da kasuwanni saboda ana gudanar da ayyuka da yawa."

Oga Faggae ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma ba a damu da wadanda ba musulmi ba.

Hisbah ta ce ba za ta sake ta ba bayan rantsuwar ta ce ba za ta sake yin kuskure ba.

Azumin Bana Zai Zo Wa 'Yan Najeriya Da Tsanani, Cewar ShettimaMataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin...
04/03/2024

Azumin Bana Zai Zo Wa 'Yan Najeriya Da Tsanani, Cewar Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya na sane da cewa azumin watan Ramadan mai gabatowa zai zo da ƙalubale masu tsanani ga akasarin ‘yan Najeriya saboda sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ɓullo da su.

Ya ce manufofin tattalin arziki da aka ɓullo da su na zuwa da ƙalubale da matsaloli, wanda zai zama “mafi tsanani ga talakawa.”

Daily Nigerian ta rawaito Shettima ya bayyana haka ne a yayin taron lacca karo na 29 na gabanin watan Ramadan da ɗaliban jami’ar Legas s**a shirya a Legas.

Shettima, wanda mashawarcinsa na musamman kan harkokin siyasa, Hakeem Baba Ahmed ya wakilta, ya yi kira ga 'yan ƙasa da su yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da ƙalubalen da tattalin arzikin ƙasa a halin yanzu cikin “nutsuwa”.

Ya ce: “Shugabancin Shugaba Tinubu ya gane cewa wannan watan Ramadan zai zo da ƙalubale masu tsanani ga yawancin ‘yan Najeriya."

“Hanyar zuwa inda muke a yau tana da tsayi kuma tana cike da ƙalubaloli da kuma kasawa mai ban tausayi don gina babbar damarmu."

“Sak**akon abubuwan da s**a faru a baya su ne ainihin abubuwan da muke fuskanta a yau, k**ar hauhawar tsadar rayuwa da kuma rashin amincewa da yunƙurin kawo ci gaba."

“Mu tuna cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala yana jarrabar bayinSa da sauƙi da kuma ƙunci, kuma yana roƙonmu da mu roƙe shi ya yaye mana ƙunci, da horo a lokutan yalwa."

“Muna fatan Allah ya nuna mana azumin watan Ramadan kuma ya karɓi ibadar mu,” in ji shi.

Ministan harkokin wutar lantarki na tarayyar Najeriya Mr Adebayo Adelabu ya ce, gwamnati ta yi odar tasoshin samar da wu...
04/03/2024

Ministan harkokin wutar lantarki na tarayyar Najeriya Mr Adebayo Adelabu ya ce, gwamnati ta yi odar tasoshin samar da wuta na tafi da gidanka har guda 10, a wani mataki na shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta a bangaren hasken wutar lantarki.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a birnin Abuja yayin wani taro da ya gudanar da kwamashinonin lura da mak**ashi da wutar lantarki na wasu jihohi 23 dake kasar, inda ya ce, domin cimma burin da aka sanya a gaba yanzu za a rinka aikin hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya wajen wadata kasa da wutar lantarki.

Ministan wutar lantarkin na tarayyar Njeriya ya bukaci al’ummar kasar da su kara hakuri ana daf da warware dukkannin matsalolin da suke haifar da cikas wajen samar da wadatacciyar wuta a kowanne bangare.

Mr. Adebayo Adelabu ya ci gaba da bayanin cewa, gwamnati ta gudanar da zuzzurfan bincike domin gano matsalolin, wanda yanzu kuma ana kan matakin gyara ne, inda ya ce a baya an yi amfani da matakan wucin gadi ne wajen warware matsalar wutar ba tare da an bi diddigin al’amarin ba tun daga tushe.

Ya ce har yanzu ba a samar da karin layin dakon wuta ba wanda zai iya tallafawa wadanda ake amfani da su da jimawa.

“Amma yanzu muna kan gabar tattaunawa da wasu kamfanonin kasar China guda biyu domin aikin manyan tasoshin wuta na zamani a gabashi da yammacin kasar wadanda da zarar tasoshin da muke amfani da su sun samu matsala nan da nan sai a sauya zuwa sabbin da aka samar, amma fa wannan aikin ba aiki ne da za a kammala shi cikin watanni shida ba ko shekara guda, kuma aiki ne da yake bukatar makudan kudade, domin a yanzuhaka idan har za a samar da tashar wuta mai karfin KV 330 ana bukatar a kalla tsakanin dala miliyan 30 ne zuwa miliyan 50.”

Ministan daga bisani ya bukaci jihohin kasar da su yi amfani da damarmakin da gwamnatin tarayyar ta samar musu wajen assasa tashohin samar da wuta mallakin kansu.

Innalillaahi wa'inna ilaihir rajuoonAllaah swt yayi ma Alh. Aminu Arrahmaniyya (Mai Saida kekunan saka) a Kofar doka ras...
31/01/2024

Innalillaahi wa'inna ilaihir rajuoon

Allaah swt yayi ma Alh. Aminu Arrahmaniyya (Mai Saida kekunan saka) a Kofar doka rasuwa, anyi Jana'izar shi bayan Sallah Isha'i.

Allaah yajiqan shi da Rahma, ya yafe mishi kurakuransa ya kyautata namu bayan nasu, Allaah swt ya jiqan Magabatan mu baki daya.

Address

Zaria

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BAMS TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Zaria media companies

Show All