Koken da wasu al'umma keyi a baya bayan nan bayan baiyanar pos a gidajen mai dake nan jihar Adamawa da taraba, Hada da batun na zaftare kudi da nufin charges na pos, A yau anyi tattaunawa mai tsawo tsakanin Hon Ahemd Lawan mai taimakawa Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri akan tsaro da zaman lafiya Alumma tare da shuwagabannin kungiyar Dillalan man fetur na jihar Adamawa da Taraba IPMAN.
Hon Aminu musa karofi daya kasance Darakta-Janar na Atiku Project a Najeriya, Ya bika sakon jinjina ga Hukumar Yaki da Talauci ta Jihar Adamawa (PAWECA), Karkashin jagorancin Dr. Michael Zira, Tare da Gwamna jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri..
Tabbas a yau 17 ga watan Disamba 2024 gwamnatin jihar Adamawa karkashin jagorancin mai girma gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta samu gagarumar nasara yayin da gwamnan ya kaddamar da shirin rage radadin talauci, inda ya samar da naira 50,000 kowannensu ga yan jihar Adamawa 60,000, Wannan shiri dai na daya daga cikin kokarin gwamnatin jihar na rage radadin talauci da kuma karfafawa ‘yan kasarta.
A halin yanzu ana ci gaba da bayar da kudaden sannan kuma dukkanin wadanda suka amfana 60,000 ana sa ran za a biya su kafin ranar 25 ga Disamba - Inji Abdulwahab Turakin Kabawa Kuma Turakin Modire, Member a cikin Sojojin baka na Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa.
Gwamnatin jihar Adamawa karkashin jagorancin Ahmadu Umaru Fintiri ta tallafawa Iyalan, Wanda sukayi Hadari watanni biyu da suka gabata a kan titin Jos zuwa Abuja, Motar mai kiran homa Bus dauke da mutane 18, Da kudi Naira Dubu dari biyu da Ashirin ko wani mutum.
Sai dai wannan tallafi na mutum 10 ne wadanda suka gabatar da Takardan shedan mutuwar Yan'uwan nasu, Su kuma saura kuwa ana jira su gabatar da takardan shedan sauran kafin bada wannan tallafin kamar yadda tsarin yake..
Hon. Abubakar Ibrahim Gombi AIG shugaban Kungiyar kare hakkin Bil'adama a Najeriya ta Creative Minds humanitarian foundation, Ya baiyana takaicin sah ga Gwamnoni inda yace ya kamata alumma kasar fahimci cewa wasu tsare-tsaren gwamnoni kasar ba sa aiki, Duk matsalar daga gare su take, ya kamata su gane manufofinsu ne suka jawo waɗan nan matsalolin.
Alh Umar Abubakar Mai' idde (Umaru Nana Ya'ilahi) Member a cikin sojojin baka na jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ya ce yana nan a kan bakansa na neman Wazirin Adamawa ya tsaya takara a 2027.
Cikakken bayani daga bakin Hon Muhammad Mayas daya kasance Daraktan Janar yada labarai ta jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Kan batun dakatar da shugabar mata na jam'iyyar Mrs Patricia Yakubu.
Program Wuro lafiya na kungiyar Search for Common ground.
Fm Gotel Yola a jihar Adamawa.
Shugaban Kungiyar kare hakkin Bil'adama a Najeriya ta Creative Minds humanitarian foundation, Hon Abubakar Ibrahim Gombi (AIG), Tuni yayi da kuma Ankaran da mahukunta na ɓangarorin gwamnatin baki daya kan sauke nauyin da Al'ummar kasar suka dora musu, Tare da bada shawarwari a kai.
Matashi daga Jam'iyyar PDP a jihar Kano, Kuma Daya daga cikin masu Taimakawa Tsohon mataimakin shugaban kasa Alh Atiku Abubakar Wazirin Adamawa akan yada labarai, Hon Sharfandeen Muh’d (Kantin Kwari), Ya kalubalanci tsarin da gwamnatin jihar Adamawa tazo dashi akan ƙirƙirar masarautu a jihar wanda shine batun da a yanzu yake yamutsa haza a jahar Adamawa.
Tattaunawa da Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Mr. Babachir David Lawan a hiran sa da Nasiru Adamu El-hikaya inda ya ce arewa za ta iya kirkirowa kan ta VAT ta hanyar karbar N5000 ga kowace saniya da za a kai kudu. Hakanan kan buhunan hatsi da sauran kayan noma. BD Lawan ya ce ba abun da yankin kudu zai nunawa arewa.
Shima Darakta Janar na Atiku Project Hon Aminu Musa Karofi yabi tsahun Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar na mayarwa sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume martani, Na cewar Atiku ko shekara 90 ya kai idan Allah yayi zai shugabanci kasar nan zaiyi, Amma dai ya bari Bola Tinubu ya gama shekaru 8 a mulkin kasar har shekara ta 2031 domin Atiku ya samu daman neman kujerar shugaban kasa.