Umabis TV

Umabis TV Gidan Sahihan Labarai.
(1)

Innanillahi wa'inna'ilaihi raji'un Yan bindiga sun kashe Nabeeha Dalibar ABU zaria da take matakin 400 LEVEL saboda iyay...
14/01/2024

Innanillahi wa'inna'ilaihi raji'un

Yan bindiga sun kashe Nabeeha Dalibar ABU zaria da take matakin 400 LEVEL saboda iyayen ta sun kasa hada kudin fansa. Allah Ubangiji ya jikanta ya karbi shahadar ta, Allah ya kubutar da sauran yan'uwan ta

Adam A zango na mai farin cikin cikin sanar da masoyan sa cewa Album din sa mai suna BABULOKACI Zai fito cikin watan Feb...
14/01/2024

Adam A zango na mai farin cikin cikin sanar da masoyan sa cewa Album din sa mai suna BABULOKACI Zai fito cikin watan Febuwarin 2024 Insha ALLAH!

Diyar Sarki, Fatima Ali Nuhu ta cika Shekara 20 da haifuwa.Wani fata kuke mata?
14/01/2024

Diyar Sarki, Fatima Ali Nuhu ta cika Shekara 20 da haifuwa.

Wani fata kuke mata?

Yadda aka dambace da baturen ƙasar Burtaniya mai suna Mr. Luke Layland, inda ya sha duka a hannun Shagon Yellow Ɗan zuru...
14/01/2024

Yadda aka dambace da baturen ƙasar Burtaniya mai suna Mr. Luke Layland, inda ya sha duka a hannun Shagon Yellow Ɗan zuru a gasar damben da s**a fafata a jihar Katsina.

Sabbin tashin hankali ga Betta Edu Kamar Yadda Tinubu Ya Kafa kwamitin don Binciken N-Power, da wasu shirye shirye dake ...
13/01/2024

Sabbin tashin hankali ga Betta Edu Kamar Yadda Tinubu Ya Kafa kwamitin don Binciken N-Power, da wasu shirye shirye dake karkashin hukumar ta

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya taya gwamnonin jam’iyyar PDP murnar nasarar da s**a samu a kotun koli.
13/01/2024

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya taya gwamnonin jam’iyyar PDP murnar nasarar da s**a samu a kotun koli.

Gwamnatin Borno ta sanar da lokacin Jana'izar kakakin Zulum.Gwamnatin jihar Borno tana sanar da ‘yan uwa da  da abokan h...
13/01/2024

Gwamnatin Borno ta sanar da lokacin Jana'izar kakakin Zulum.

Gwamnatin jihar Borno tana sanar da ‘yan uwa da da abokan huldar marigayi Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Borno Malam Isa Gusau cewa za a yi jana’izarsa a ranar Lahadi 14 ga watan Janairun 2024 da karfe 4:00 na yamma a babban masallacin Juma’a, a Abuja.

Isa Gusau ya rasu ne a ranar Alhamis a wani asibiti a kasar Indiya bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Ministan Muhalli, Malam Balarabe Abbas Lawal, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin hada karfi da karfe da...
13/01/2024

Ministan Muhalli, Malam Balarabe Abbas Lawal, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin hada karfi da karfe da za su kawar da dazuzzukan Najeriya daga masu aikata laifuka.

Allah shine mai yi a cewar dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna, ya ce kuma yana yi wa Gwamna Abba Ka...
12/01/2024

Allah shine mai yi a cewar dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna, ya ce kuma yana yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf fatan alheri bayan nasarar da ya yi a Kotun Ƙoli, ya baiyana haka ne a wata hira da yayi da BBC Hausa.

Sakon Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Saraki Ga Abba Kabir Yusuf Dole ne in tura saƙon taya murna ga gwamnan jihar Kan...
12/01/2024

Sakon Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Saraki Ga Abba Kabir Yusuf

Dole ne in tura saƙon taya murna ga gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa nasarar da ya samu a kotun ƙoli.

Nasarar da ya samu a ƙarƙashin tutar jam'iyyar NNPP ya nuna irin ƙarfin da jam'iyyun adawa suke da su da kuma ƙarfin dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

Bisa sakamakon kotu na yau, ina miƙa saƙon taya murna ga gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jagorancin da yake yi a jihar Kano. Har ila yau, ina masa fatan samun nasara da yin mulki cikin adalci da nutsuwa.

Tinubu Ya Nada Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai Ta Nijeriya
12/01/2024

Tinubu Ya Nada Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai Ta Nijeriya

12/01/2024

Gawuna Bazaizo ba inji Kotun Koli

Da duminsa: NNPP za ta ci gaba da rike Kano yayin da Kotun Koli ta soke korar Gwamna Yusuf
12/01/2024

Da duminsa: NNPP za ta ci gaba da rike Kano yayin da Kotun Koli ta soke korar Gwamna Yusuf

12/01/2024

Kotu ta dawowa da Abba Kuri'an sa dubu 165

12/01/2024

An Fara Yanke Shara'ar Kano

Zulum Ya Mika Ta'aziyyar Sa Bisa Rasuwar Mai Magana Da Yawun Sa, Isa GusauGwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zu...
12/01/2024

Zulum Ya Mika Ta'aziyyar Sa Bisa Rasuwar Mai Magana Da Yawun Sa, Isa Gusau

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana matukar alhinin rasuwar mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, wanda ya rasu bayan doguwar jinya a ranar Alhamis 11 ga watan Janairun, 2024 a wani asibiti a kasar Indiya.

Gwamna Zulum, ya bayyana cewa daukacin gwamnatin jihar Borno na cikin alhinin rashin wani ma'aikacin gwamnati mai kwazo.

Zulum ya tuntubi iyalan marigayin mai magana da yawunsa, inda Gwamnan ya mika ta’aziyyar sa ga abokai da abokan arziki, musamman ma ‘yan jarida.

Isa Gusau wanda ya taba rike mukamin mai ba Gwamna Zulum shawara na musamman kan hulda da jama'a da dabaru tun watan Yunin 2019, ya kuma taba rike mukamin a karkashin Sanata Kashim Shettima lokacin yana Gwamnan Borno.

Shirin ko ta kwana: an baza jami'an tsaro, a bakin gidan Gwamnatin jihar Kano.
12/01/2024

Shirin ko ta kwana: an baza jami'an tsaro, a bakin gidan Gwamnatin jihar Kano.

Zuwa yanzu Shara'ar Lagos ake gudanarwa a Kotun Ƙoli.
12/01/2024

Zuwa yanzu Shara'ar Lagos ake gudanarwa a Kotun Ƙoli.

12/01/2024

Titanoboa Maciji mai shekaru akalla miliyan 58 a duniya.

Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa har sun isa kotun koli inda za a yanke hukunci a yau Juma'a
12/01/2024

Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa har sun isa kotun koli inda za a yanke hukunci a yau Juma'a

LABARINA 😂 A gobe...Juma'a 🤔Firgigit Al'amin ya tashi daga bacci a cikin tsohuwar lalatacciyar bas ɗin Habu da ta jima a...
11/01/2024

LABARINA 😂 A gobe...Juma'a 🤔

Firgigit Al'amin ya tashi daga bacci a cikin tsohuwar lalatacciyar bas ɗin Habu da ta jima a cikin tashar a yashe. Nura Dantse da Rangila suna tsaye a kansa suna murmushi.

Damtse: Ango har kana iya bacci, kai da za a ɗaura aurenka gobe.
Rangila: Tashi mu je ka karɓi kudin da direbobi su ka tara ma ka, tun ɗazu ake neman ka.
Al'amin: (Cike da mamaki yana kallo tsohon kayan da ke jikinsa) Dantse wai ina jeep ɗin ne? Yanzu fa na gan ni tare da kai cikin manyan kaya a bayan wata ƙatuwar jeep mai raɓa"

Damtse da Rangila su ka fashe da dariya.

Nura Dantse: Kai dan Allah tashi mu je, talauci ne ya sa ka bacci sannan ya yaudare ka da mafarki.

Amma dai... Sai goben... 😢😜😂🤗🤗

Daga Yakubu M Kumo

Titanoboa - maciji mafi girma, mafi tsawo da aka taɓa gano yayi rayuwa na kusan shekara miliyan 58-60 da s**a gabata. Ya...
11/01/2024

Titanoboa - maciji mafi girma, mafi tsawo da aka taɓa gano yayi rayuwa na kusan shekara miliyan 58-60 da s**a gabata. Yana da tsayi ƙafa 42.7, nauyin sa ya kusan 1,135 kg.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi 'yan Najeriya da su yi amfani da sabon taken “No gree for anybody.”Kakakin rund...
11/01/2024

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi 'yan Najeriya da su yi amfani da sabon taken “No gree for anybody.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ACP Muyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja ranar Talata.

An Kashe Hakimin Kauye, Da Dan Sa Da Wasu Mutane A Sabon Harin Katsina
11/01/2024

An Kashe Hakimin Kauye, Da Dan Sa Da Wasu Mutane A Sabon Harin Katsina

Kotun koli ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan kararrakin zaben gwamnan jihar Kano.
10/01/2024

Kotun koli ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan kararrakin zaben gwamnan jihar Kano.

SISTER AMARACI KENANAmarachi Ma'aikaciya ce a Banki, tana bangaren marketing, shekarunta 32Kafin ta kashe kanta, ta rubu...
10/01/2024

SISTER AMARACI KENAN

Amarachi Ma'aikaciya ce a Banki, tana bangaren marketing, shekarunta 32

Kafin ta kashe kanta, ta rubuta wannan wasika, tana mai nuna yanke tsammani game da rayuwar duniya

A cewarta rayuwar tayi tsanani a Nigeria, ba zata iya jurewa ba, don haka ta zabi barin duniyar, tana mai bawa iyayenta hakurin rasa ta

Ta shiga Bandaki a Bankin da take aiki, sai ta sha guba, aka zo aka tarar da gawarta a Bandakin, a halin yanzu 'yan sanda suna kokarin tabbatar da rubutun hannunta don gano ko ita ta rubuta

Matsalar shine Amaraci bata san abinda zata je ta tarar ba, na tabbata da sai ta zabi kuncin rayuwar duniya akan na lahira

Shiyasa Sheikh Aminu Daurawa yace mutum ba addini dabba yake komawa, fahimtar addini da mu'amalartan Qur'ani shine maganin kowani irin damuwa da kunci

Allah Ya tsare mana imanin mu

Daga: Datti Assalafiy

Babban bankin Najeriya CBN ya rusa shuwagabannin bankunan Titan Trust, Union Bank, Keystone Bank da Polaris Bank.
10/01/2024

Babban bankin Najeriya CBN ya rusa shuwagabannin bankunan Titan Trust, Union Bank, Keystone Bank da Polaris Bank.

YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya nada Sheikh Bin Othman mukami a NAHCONShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Shuwagaba...
10/01/2024

YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya nada Sheikh Bin Othman mukami a NAHCON

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Shuwagabannin gudanarwa na hukumar aikin Hajji, inda ya turawa Sanatoci domin tantancewa.

Zulum ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 358.7.Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara ...
10/01/2024

Zulum ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 358.7.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na N358,732,146,000.00 da majalisar dokokin jihar Borno ta amince tare da gyara da ya kai na N18.1b.

Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan ne ya gabatar da kudurin kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima ga gwamnan a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a birnin Maiduguri ranar Laraba.

Da yake jawabi a wajen taron, Zulum ya bukaci shugabannin hukumomi da ‘yan majalisar zartarwa na jihar da su bi ka’idojin kasafin kudin yayin gabatar da takardunsu domin amincewa.

Gwamnan ya kuma yabawa shugabanni da ‘yan majalisar dokokin jihar Borno bisa amincewa da kasafin kudin akan lokaci.

10/01/2024

NDLEA: dalibai 6 cikin 10 a jihar Kano ke shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Address

Kyari Drive Street, Maiduguri
Yerwa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Umabis TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Umabis TV:

Videos

Share

Category


Other Yerwa media companies

Show All

You may also like