11/07/2023
[Fahimtata ce]
A Najeriya, daga cikin manyan dalilan da yasa Sufanci yake samu raguwar tasiri da kuma zaizayar mabiya, shine kafewa a matafiya ta gargajiya da kuma ƙin karɓar canji.
Duk wata fikira, ɗariƙah, ko mazhabi da baya karɓar canji ya kuma waiwayi ginin shi da tafiyar shi a zamanance, yana samun ƙalubale da ke iya jawo masa raguwar mabiya da kuma rashin tasiri. Wannan shine babban sirrin da yasa musulunci har yanzu yake samun karɓuwa, duk da matsalar mulhidanci da ake fama da ita, wanda ke alaƙa da wofintar da illimin falsafa da wasu sashin musulmi sukayi kamar Wahabiyawa da sauransu.
Duk da cewa akwai wasu dalilai dake jawo koma baya a wasu sassanni na ƙasarnan, kamar Siyasa, ƙarancin ilimi na mabiya Sufanci da kuma rashin yaɗa shi Sufancin ta hanyar koyarwa, amma dai matsalar gargajiyanci tayi matuƙar tasiri wajen sauƙaƙa yaƙar Sufaye daga abokan hamayyar su, wannan ne ma yasa da yawan ƴan boko ke yiwa shi Sufanci wani gani-gani.
Nazari zai tabbatar da hakan ne ga duk wanda ya kalli guraren da ake rage ƙarfin Sufanci a duniya, da kuma guraren da yake ta ƙara haɓaka. Misali ka ɗauki ƙasar Morocco, Egypt, Tunisia, Algeria, Sudan, Senegal, da ma Gambia a Afirka, ba komai yasa Sufanci har yau ya gagara ba, sai saurin karɓar canji na wayewa da sauye-sauyen manufofi da zasu dace da zamani ba tare da kaucewa asalin manufar Sufancin ba, wato gyara ko wankin zuciya.
Amma a ƙasashe irin Najeria, Ghana, Niger, Kamaru da sauransu, zaka samu sufancin bai cika dacewa da zamanin ba, hasali ma wanda yayi yunƙurin nusar da haka, na iya zama abin tuhuma, ko ma ƴan bani na iya su kore shi daga cikin Ɗariƙar.
Daga cikin alamomin rashin karɓar sauyi da ake fama da shi akwai takaita Zawiyoyi a matsayin wajen Wazifa da Zikiri kawai, akwai taƙaita fahimtar ilimi a matsayin karatun Addini kaɗai, akwai ƙin zamanantar da shi kanshi ilimin Addinin, akwai rashin zamanantar da tsarin shugabanci na halarori da zawiyoyi da ma dai sauran abubuwa da ƴan uwa zasu iya halartowa.