Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba

Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba, Digital creator, Masjid Aba Huraira, Ungwan Sarkin Fada, Wamba.
(1)

19/03/2024
14/03/2024

RAMADAN TAFSEER OBI 2024 MATA (Day 4)

08/03/2024

Muhadara akan Ramadan.

06/03/2024

MAZA MASU AURE, DAKE FAMA DA RASHIN
KUZARI, DA KUMA GAZAWA WAJEN GAMSAR DA IYALANSU.

Ku zaɓi ɗaya ko fiye da ɗaya ku ja gwada amfani dashi da iznin ALLAH zaka sami lafiya.
Idan mijinki nada fama da irin wannan larura kema zaki iya zaɓar wanda zaifi miki sauƙin haɗawa saiki haɗa masa.
1• Cin Ayaba biyu kullum da safe zai taimaka wajen kashe sanyin jiki infection,
Idan zai yiwu, zaki iya niƙa shi ayaban, zaki shanya tane a rana ta bushe, saiki niƙata ta zama gari, saiki sami zuma mai kyau, saiki haɗashi tare da zumar cokali biyu kibashi ya rinƙa sha,
Har maganin mata ma yanayi.
Sannan kuma zai sashi ya sami ƙarfi sosai ya kuma rinƙa samun yawan sha'awa.
2• Turmeric wato kurkum,
Yana kashe infection, ki rinƙa sakashi acikin abinci ko ki samu madara ki ɗan dafa kaɗan ki zuba tea spoon nashi, kibashi ya rinƙa sha ko rabin kofi ne, acikin madara.
Idan kuma bazai yiwu ba to kibashi a rinƙa girki dashi.
Yana ka kashe sanyi yana kuma saka namiji ya sami kuzari.
3• Ƙwai: Zaki sami ƙwan kaza guda 2, Sai a sami babban cokali 1 na garin habbatus sauda,
Sai a cakuɗa su sosai sannan a soya sama-sama, karya ƙone, sannan a cinye.
Wannan haɗin yana bawa namiji ƙarfi sosai idan anacinsa koda lokaci bayan lokaci me.
4• KANKANA: Kankana na ƙunshe da wasu sinadarai dake aiki acikin jikin ɗan adam, dake ƙara ƙarfin maza na zamani da ake kira (Vi**ra) a turance.
Don haka tana ƙara ƙarfin maza sosai.
Don amfani da ita, za'a shatane, mintuna 30 kafin fara jima'i.
Ana buƙatar a cinye har wannan farar tsokar da kuma 'ƴa'ƴan.
Kuma kada a sha lokacin da ciki na cike, amfi so asha kafin cin abinci, kuma a saurara bayan ansha zuwa mintuna 20 zuwa 30 kafin abita da abinci.
5• Ayaba: Tanada sinadarai dake ƙarawa namiji kuzari, sai aci guda uku ko biyu kafin jima'i da mintuna 30.
Kamar kankana ba'a son cinta da zarar an kammala cin abinci.
6• Namijin Goro: Cin namijin goro aƙalla guda biyu a rana ya kan dawowa namiji kuzarinsa.
An jarraba an tabbatar da hakan sakamakon wasu sinadarai dake cikinsa mai matuƙar fa'ida wajen samar da karsashi ga maza.
Faɗakarwa: Akwai buƙatar mu ƙauracewa amfani da maganin ƙarin ƙarfin maza na nasara batare da shawarar likita ba, saboda illolinsu ga lafiya.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

01/03/2024

Tarjamar Ma'anonin Al-Qur'ani Mai Girma.

29/02/2024

(01. Al-Islam).
Darasin Na 1 Akan Mas'aloli Masu Muhimmanci A Musulunci.

(Wanda Akayi Masa Haihuwa Ya Zaiyi)?

Akwai Wasu Hadisai A Wannan Sashen Wadanda Kwakwata Basuda Inganci Gasu Kamar Haka.
١۔ من ولد له ملود، فأذن في أذنه اليمنى، وأقام في أذنه اليسرى، لم تضره أم الصبيان۔
Wai Idan Akayi wa mutum haihuwa sau yayi wa yaron kiran Sallah A Kunyarsa Ta Dama Kuma Yayi Iqama A Kunyarsa Ta Hagu To Uwar Jinjirayo Bazata Cutarda Shi Ba.

Wannan Hadisin Bai Inganta ba Ka Duba.
١۔سلسلة الضعيفة (٣٢١)
٢۔ ضعيف الجامع (٥٨٨١)۔

٢۔ أذن رسول الله صلى الله عليه وسلم في أذن الحسن بن علي يوم ولد في أذنه اليمنى ، وأقام في أذنه اليسرى۔
Wai Manzon Allah S.a.w Yayi kiransa Sallah Kunyar Dama Kuma Yayi Iqama A Kunyar Hagu Wa Hassan Bin Abi Dalib A Ranarda Aka Haifesa.

Wannan Shima Bai Inganta ba Ka Duba.
سلسلة الأحاديث الضعيفة (٦١٢١)۔

٣۔ قول ابي رافع: رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم أذن في أذن الحسن بن علي حين ولدته فاطمة بالصلاة۔
Wai Abu Rafi'i Yace: Naga Manzon Allah S.a.w Yayi Kira A Kunyar Dama Kuma Yayi Iqama A Kunyar Hagu Wa Hassan Bin Ali A Ranarda Fatima Ta Haifesa Irin Kiran Da Akeyi Idan Za Ayi Sallah.

Shima Wannan Bai Inganta ba Ka Duba.

١۔ ضعيف ابي داود(٥١٠٥)
٢۔ هداية الرواة (١٣٨/٤)
٣۔ الإخبار بما لا يصح من أحاديث الأذكار (ص ٢٤٤)۔
Saboda Haka Dukkanin Su Ba'a Aiki Dasu .

Sannan Shima Taron Suna Bidi'ah Ne Domin Ko Hadisin Karya Ban Taba Gani Ba Akansa Amma Idan Akwai A Taimaka Mana.

Amma Ga Abunda Ya Inganta Ga Wanda Aka Haifa Masa Jinjiri.
١۔ يحمد الله۔
Yace Alhamduliah.

٢۔ يسجد سجدة الشكر۔
Yayi Sujudush Shukri.

٣۔ ان يقوم بتحنيك فم المولود بالتمر۔
Yayi Tauna Dabino Ya Sanya Ruwan Acikin Bakin Yaron ya Kasance Su Ya Fara Sha (Attahnik) Kenan.

٤۔ يحلق رأسه في يوم السابع ۔
Yayi Masa Aski A Rana Ta Bakwai.

٥۔ يتصدق بوزن شعره فضة۔
Yayi sadaka da nauyin sumar na Azurfa Idan Babu Ya Bada Kudi Kemar Wannan.

٦۔ ويقوم بختانه۔
yayi masa kaciya.

٧۔ ويعق عنه بشاة للبنت وبشاتين للولد ويجوز بشاة۔
Ya Yankawa Mace Akuyi Daya Ko Tunkiya Daya Idan Namiji Ne Kuma A Yanka Masa

28/02/2024

LADUBBA 30 NA AMSAN ADDU'A DA GAGGAWA.

Matakin farko shine mutum ya zama mai tsarkin zuciya kuma mai ƙoƙarin nisantar shirka da ALLAH.
Kamar zuwa wajen malaman tsubbu, boka da masu bugun ƙasa ko masuyin istikhara wa mutane sauransu.

1• Yin imani da ALLAH ne kaɗai ke biyan buƙatar bayinsa kuma shine ke amsa kiran bawansa kuma ya biya masa buƙatarsa.
Da kuma yiwa ALLAH biyayya da barin saɓa masa.
[Suratul Baƙarah ayata 186 ]
2• Yin addu'a da Ikhlas, kuma kada ka roƙi kowa sai ALLAH shi kaɗai a lokacin addu'arka da kuma sauran ibadu gaba daya.
[Suratul Bayyinah ayata 5].
3• Yin roƙon ALLAH da Sunayansa maɗaukaka.
[ Suratul A’araf ]
4• Mai addu'a ya fara da yabon ALLAH da girmama shi da yiwa ALLAH kirari, sannan ka roƙi abinda kake buƙata.
5• Sannan kayi salati ga Manzon ALLAH {s.a.w} domin duk addu'ar da babu salatin Annabi {s.a.w} a cikinta, ba’a buɗe mata ƙofofin sama.
6• Fuskantar alƙibla a lokacin yin addu'ar.
[Sahih Muslim]
7• Ɗaga hannuwa a lokacin yin addu'a.
Amma ba'a shafewa a fuska ko a jiki domin Hadisin da yake bayani akan shafar fuska bayan angama addu'a bai tabbata daga
Annabi {s.a.w} ba,
Idan ka gama addu'a sai ka sauke hannunka wannan shine ya tabbata daga manzon ALLAH {s.a.w}.
8• Ka roƙi ALLAH da cikin hannunka.
Ma’ana ka buɗe hannayan ka cikinsu kana kallon sama.
9• Ka riƙa samun yaƙini akan ALLAH yana amsa addu'arka.
10• Yawaita roƙon ALLAH a kowane lokaci sannan kada ayi gaggawa acikin Addu'a.
[Bukhari da Muslim]
Ma'ana kada kace yanzu-yanzu kake so kaga sakamako, kai dai kayi addu'a kuma kabarwa ALLAH zaɓi.
11• Halarto da hankalinka a lokacin addu'a da ƙoƙarin halarto ma'anonin abinda kake faɗi a yayin roƙon ALLAH.
12• Yin kwaɗayi da fargaba da ƙanƙantar da kai ga ALLAH a lokacin yin Addu'a.
[Suratul A’araf ayata 55]
13• Maimaita addua sau uku alokacin yinta.
[Bukhari da Muslim]
14• Nisantar cin haram da ƙoƙarin yin rayuwa acikin halal.
15• Ɓoye sauti a lokacin addu'a domin addu'a sirrice tsakanin bawa da ALLAH.
Ma'ana: Idan bawa zai roƙi ALLAH anaso ya halarto da abubuwa guda shida 6 a ransa:
• ALLAH ne kaɗai ake roƙo.
• Shi kaɗai yake biyan buƙata
• Shi kaɗai ne mawadaci, kowa faƙirine a wajansa ake nema.
• Idan ya hanaka babu mai baka•
• Yana da ikon ya baka.
• Roƙonsa dolene.
16• Yin addu'a alokacin da kaji kukan zakarah, domin a wannan lokacin mala'ikun Rahma suna kusa.
17• Yin addu'a ayayin da ladan ya gama kiran sallah, har izuwa a tada sallah, da yin addu'a bayan iƙama kafin kabbara sallah.
18• Yin addu'a abayan sallar Nafila.
19• yin addu'a a cikin sujjadar sallar farillah ko ta nafilah.
20• Saka iyaye suyi maka addu'a, musammam uwa.
21• Saka ƙananan yara suyi maka addu'a ko ka rinƙayi suna cewa Ameen, domin ALLAH yana amsa addu'arsu da gaggawa saboda su basu fara aikata zunubi ba.
22• Yin sadaka kafin addu'a ko bayanta yana taimakawa wajen karɓar addu'a.
23• Yin addu'a acikin dare, lokacin da kowa yake bacci, Domin ALLAH TA'ALAH yana sakkowa yana cewa: ina mai neman arzuƙi ya roƙeni na amsa masa, ina mai neman rahma ta ya roƙe ni na amsa masa kamar yadda yazo a hadithi.
24• Tawassili da wani aiki mai kyau da bawa yayi domin neman yardar ALLAH sai ka roƙi ALLAH kayi tawassili da wannan aiki, kamar yadda yazo a hadithi.
25• Addu'a acikin halin tafiya.
26• Addu'a a yayi shan ruwa ga wanda yayi azumi na farillah ko na nafila.
27• Yin addu'a bayan gama karatun Alƙur'ani.
28• Yiwa wani addu'a a bayan idonsa kaima mala'iku zasu roƙa maka irin abinda ka roƙawa ɗan uwanka.
29• Addu'ar mai tsananin biyayya ga iyayensa, shima ana amsa masa da gaggawa.
30• Addu'ar wanda aka zalunta, amma da zai raƙowa wanda ya zalunceshi gafara da shima ya sami sakamako mai kyau anan.
Waɗannan sune kaɗan daga cikin ladubba na addu'a wanda insha ALLAH duk wanda ya kiyayesu ALLAH zai amsa masa addu'arsa da gaggawa.
ALLAH ka amsa mana addu'o'inmu baki ɗaya.
Ameen ya ALLAH.

28/02/2024

Darasin Muka Saba Kawo Muku Duk Ranar Laraba Mai Taken.
(Al-Islam).
Wanda Muke Kawo Muku Mas'aloli Daban-Daban Masu Muhimmanci A Musulunci To Ga Na Wannan Satin.

Tambaya ?
Miye Hukuncin Wanda Ya Sanya Condom Kuma Ya Tara Da Mace Amma Kuma Baiyi Release Ba.

Amsa: Kamar Yanda Kuka Sani Musulunce Idan Kan Zakarin Namiji Ya Buya A Farjin Mace To Koda Bai Kawo Ba Dole Ne Dukkansu Suyi Wanka .

To Amma Akan Wannan Mas'lar Ta Samu Dabanin Malamai Kasantuwar Ba Nassi Akan Ta Domin Condom Sabon Abu Ne Ba'a Sansa Ba A Da .

Ga Yanda Malamai S**ayi Maganganu Har Gida Uku Akan Wannan .
1. Malaman Farko S**ace Dole Ayi Wanka Koda Ba A Kawo Ba Kuma Ko Wannene Kalar Condom Ne Koda Tsumma Ne Ya Daura.

2. Na Biyu S**ace Bazaiyi Wanka Ba Tunda Bai Kawo Ba Kuma Fatar Zakarinsa Bata Taba Fatar Farjin Ta Ciki Ba.

3. Na Uku Sai S**a Raba Abun Zuwa Gida Biyu.
A. S**ace Idan Abunda Ya Daure Zakarinsa Dashi Mai Kauri Ne Kuma Bai Kawo Ba To Bazaiyi Wanka ba.
B. Idan Kuma Mara Kauri ne To Dole Sai Yayi wanka .

Amma Ku Sani Dukkaninsu Ba Mai Nassi Akan Hakan Duka Intihadi ne Domin Ba Condom A Lokacin Farko Ballantana Ayi Nassi Akansa.

Saidai Manyan Malamai Dadama Sun Zabi Maganar Farko Domin Tafi Kwantarda Hankali.
Wato Sun zabi Cewar Ko Wane Kalar Condom Ne To Kawai Mutum Yayi Wanka Yafi Samarda Nutsuwa .

Ku Duba Wadannan Littattafan Domin Karin Bayanai.
1. Almajmu'u Sharhar Muslim Mujalladi Na 2 shafi Na 102.
2. Mawa'hibul Jalil Mujalladi Na 1 shafi na 308.
3. Annasikhu Wal Mansukh Min Sunnati Rasulillahi (S.A.W )
Littafen Mustapha Ibnl Adwy Shafi Na 114.

Allahu Aalam .
Zaku Iya Copy Da Share Wa Yan Uwa Musulmai Baki Daya.

27/02/2024

((Rantsuwa))
✅Ita Rantsuwa Kala 4 Ce .

✍️ Biyu 2 Daga Ciki Ba'a Musu Kaffara✅
✍️ Biyu 2 Kuma Ana Masu Kaffara ✅

👉Biyun 2 Da Ba'a Musu Kaffara Gasu Kamar Haka.
1. Rantsuwa Da Allah Akan Karya
Misali Mutum Ya Rantse Abu Kaza Ya Faru Kuma Yasan Karya Yake Kokuma Abu Kaza Bai Faruba Kuma Yasan Karya Yakeyi.

Ita Wannan Saidai Kayita Istigfari Kana Neman Gafara Amma Ba'a Mata Kaffara.

👉Ta Biyun 2 Kuma Itace Rantsuwa Da Mutum Ya Saba Fada A Bakinsa Ba Wai Yana Nufin Rantsuwa Bane Kamar.
Eh Wallahi A'a Wallahi Da Sauran Su Itace Allah Madaukakin Sarki Yace.
لا يؤاخذكم الله باللغو في أيمانك.

Sau Rantsuwa Guda Biyu Da Ake Yiwa Kaffara.

✍️Mutum Ya Rantse Cewar Sai Aikata Wani Abu Kuma Yaga Rashin Aikatawar Shine Mafi Alkhairi To Sai Yayi Kaffara Kawai .
Misali Mutum Yace Wallahi Bazai Sake Taimakawa Kaninsa Ba Kuma A Basa Shawara Yaci Gaba Da Taimaka Masa Sai Yace Ai Yayi Rantsuwa To Sai Ace Dashi Kawai Yayi Kaffara.

✍️Ta Biyun Kuma Itace Mutum Yayi Rantsuwa Cewa Zaiyi Wani Abu Kuma Yaga Cewar Ko A Nuna Masa Cewar Rashin Aikatawa Shine Mafi Alkhairi.
To Sai Yayi Kaffara Kawai.

To Ya Matakan Kaffara Su ?

Gasu Kamar Haka:
1. Ciyarda Mutum 10
2. Sutura Wa Mutum 10
3. Yanta Baiwa
4. Azumin Kwana Uku.

Kuma Yanda Ka Gansu Haka Ake Jerasu.

Ma'ana.
👉Bazaka Yi Sutura Wa Mutum 10 Ba Sai Ka Rasa Yanda Zakayi Ka Ciyar Dasu.

✍️Bazaka Yanta Baiwa Ba Saika Rasa Yanda Zakayi Kayi Sutura Wa Mutum 10.

👉Bazaka Yi Azumi 3 Ba Sai Idan Ka Rasa Baiwar Da Zaka Yanta.

👉👉Saboda Haka Ba Azumi Ake Farawa Dashi Ba.

✍️Maganar Ciyarwa Zaka Iya Dafa Abinci Kawai Sai Ka Rabawa Mutum Goma Daidai Wanda Yake Wadatarda Matsakaicin Mutum Iya Ci Daya .

✍️Shima Azumin Zaka Iya Yinsa A Jere Ko A Rabe.

Zaku Iya Copying Dakuma Sharing Domin Yan Uwa Su Anfana.

21/02/2024

Karatun Littafin Makarimul Akhlaq na Ibn Taymiyyah.

19/02/2024

Karatun Littafin Al-Adabul Mufrad na Imam Bukhari.

17/02/2024

MUHADARA
MAUDU'I -Hassada mugun ciwo
MAI GABATARWA- Sheikh Ibrahim Muhammad (MAI TAUHIDI) Mararraba Abuja.

13/02/2024

Muhadara akan Wajibcin Fahimtar Musulunci da Tauhidi da Riko dasu by Ustaz Bala Kargi.

05/02/2024

Karatun Littafin Adabul Mufrad na Imam Bukhari.

Address

Masjid Aba Huraira, Ungwan Sarkin Fada
Wamba

Opening Hours

Monday 18:25 - 20:00
Wednesday 18:25 - 20:00
Friday 18:25 - 20:00
Sunday 18:25 - 20:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Digital creator in Wamba

Show All