![GUDUN DUNIYA (1) ✅✅KU SAURARA KUJI 👂👂✅✅KARATUN LITTAFIN (ZUHUDU) MA'ANA GUDUN DUNIYA DA ABINDA KE CIKI ✅✅Bismillahir rah...](https://img5.medioq.com/021/180/192991340211804.jpg)
26/04/2023
GUDUN DUNIYA (1) ✅✅
KU SAURARA KUJI 👂👂✅✅
KARATUN LITTAFIN (ZUHUDU) MA'ANA GUDUN DUNIYA DA ABINDA KE CIKI ✅✅
Bismillahir rahmanir raheem ✅✅
Rahamar Allah Da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen Halitta annabi Muhammad s.a.w Tare da Alayensa da sahabbansa gaba daya ✅✅
Allah s.w. t a. Ma'abuci Daukaka da girmame girmame Yayi Albarka Ya kaDaitu Da Jika Da yabo, Kuma ya Tsarkaku Daga Abokin Tarayya ko kuma Karewa Ya Kadaitu Da buwaya Da wanzuwa✅✅
Allah S.w.t.a. ya sanya Mutuwa Tsakanin Halittunsa baki daya
Kusani mutum ne Talaka ko kuma Attajiri ma'abuci Dukiya ko kuma mai Tsoron Allah ne ko mai bautar Allah ne koda Dan Wuta ne Dukkansu Jinginannune Ga mutuwa Ba makawa Sai sun mutu ✅✅
KU SAURARA KUJI 👂👂✅✅
Hakika Karkata ga Rude ruden Duniya, da wasa Da mata Tareda Kide kiden Banza mara Amfani, Da Son Girma. da biyar son Zuciya, Da Amincewa ga wannan gida na duniya a matsayin shine Gidan Gaskiya Dukkansu Sunfito ne Daga Wahala....,......✅ Mu tara Gobe
ALLAH YA RABAMU DA DUNIYA LAFIYA
ALLAH YA KARFAFA MANA GUIWA ACIKIN NEMAN ILMI GA MALAMAN ALLAH ✅✅
DAN ALLAH KU TURAWA SAURAN JAMA'A DOMIN SU AMFANA 🙏🙏
✏
Laraba 26/4/2023 ✅