05/01/2026
Kungiyar Arewa Media Writers Ta Yi Kira Ga Shugaba Tinubu Da Ya Gaggauta Sauke Ministan Abuja, Nyesom Wike
…Kungiyar ta ce dole ne a dakatar da duk wani yunkuri da ke barazana ga dimokaradiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”
Kungiyar Marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Comr. Haidar H. Hasheem (Kano), ta nuna matuƙar damuwa tare da yin Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin k**a-karya, nuna wariya da cin zarafin ‘yan ƙasa, da ake zargin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, na aikatawa.
Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda ake zargin Ministan da amfani da ƙarfin iko wajen cuzgunawa ‘yan Arewa da ‘yan adawa, musamman saboda banbancin ra’ayin siyasa, abin da hakan ke tauye ‘yancin ‘yan ƙasa tare da zama barazana ga tsarin dimokaradiyyar Najeriya.
A cewar ƙungiyar, ana zargin Wike da amfani da hukumar EFCC da jami’an tsaro wajen tsoratarwa da musgunawa abokan hamayya, lamarin da ke haifar da fargaba, rashin adalci da rashin amincewa ga hukumomin gwamnati.
Kungiyar Arewa Media Writers ta kuma nuna damuwa kan yadda Ministan ke yin furuci da ayyuka masu ɗauke da wariya ga al'ummar Hausawa/Fulani, inda ta jaddada zargin da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya yi a baya-bayan nan, wanda yace ya samu wata masaniya daga mai jiya mai tushe dake nuna cewa hatta hukumomin EFCC, Wike ke amfani da su wajen matsin lamba ga yan adawa, haka kuma ya tabbatar dasa hannun Ministan wajen ƙoƙarin bata masa suna ta hanyar jingina shi da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci a kotu.
Kungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan zarge-zarge ba komai ba ne illa kiyayya ta kabilanci da siyasar adawa, wanda hakan ya saba wa ruhin haɗin kan ƙasa. Idan baku manta ba tun a lokacin da Wike ke Gwamnan Jihar Rivers, an samu rahotannin rusa masallatai, rufe shaguna da gidajen ‘yan Arewa, tare da korar su daga jihar, abin da har yanzu ke ci wa zukatan al’umma tuwo a ƙwarya.
Haka kuma ƙungiyar ta yi tsokaci kan sauke Sakataren Ilimi na Abuja, Dr. Danlami, wanda ɗan Arewa ne, inda ta ce yadda aka yi hakan ya ƙara nuna amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba, tare da mayar da shi aiki bisa wasu sharudda.
Ba wannan kaɗai ba, kungiyar ta kuma nuna damuwa kan zargin amfani da jami’an tsaro wajen tarwatsa rikici a helkwatar jam’iyyar PDP, inda aka ce har aka yi amfani da hayaki mai sa hawaye ga wasu gwamnoni ciki har da Seyi Makinde da Bala Muhammad, lamarin da bai dace ba ga shugabanni da kundin tsarin mulki ya tanadar musu da rigar kariya.
Kungiyar Arewa Media Writers ta jaddada cewa tsarin shugabancin Najeriya bai ginu kan kabilanci, wariya ko ramuwar siyasa ba, illa adalci, daidaito da mutunta ‘yancin kowa.
A ƙarshe, Kungiyar Arewa Media Writers tana kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta dakatar da duk wani yunkuri da ke barazana ga dimokaradiyya Najeriya, taka wa Ministan Abuja burki, ko kuma a sauke shi daga mukaminsa, domin kare martabar dimokaradiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Arewa Media Writers za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya, adalci da kare haƙƙin al’umma.
✍️✍️
Comr Nura Siniya
Chairman Arewa Media Writer's Katsina Chapter