01/07/2022
Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da harin da 'yan bindiga s**a kai karamar hukumar shiroro jihar Neja
A makon nan ne aka samu aukuwar wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar jama'a tare da yin awon gaba da wasu
Buhari ya ce babu zama, dole a ceto su, kuma zai tabbatar da hukunta duk wani dan ta'adda da ya shiga komar hukuma
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an ceto wadanda aka sace a wani hari da aka kai a wani wurin hakar ma’adinai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Buhari ya fadi haka ne yau da kuma bayyana harin a matsayin harin kai tsaye kan Najeriya masu bin doka da oda wanda ba za a bari ya tafi haka siddan ba.
A wata sanarwa a yau Juma’a mai dauke da sa hannun hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya kuma jinjina wa sojojin da s**a rasa rayukansu wajen dakile harin yana mai cewa kokarinsu ba zai zama na banza ba.
Majiyarmu ta Jaridar Punch ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sama da mutane 43 da s**a hada da sojoji 30 da kuma ‘yan sandan mobal bakwai a harin da aka kai ranar Laraba. A cewar mazauna yankin, an kuma yi awon gaba da wasu ‘yan China da 'yan Najeriya.
The Nation ta ruwaito sanarwar na cewa: “Muna girmama jami’an tsaron mu, musamman jajirtattun rayukan da s**a sadaukar da kawunansu wajen yakar muggan ayyukan ta’addanci. Sun kasance mafi kyawun abin da Najeriya za ta bayar kuma muna tunawa da kowannensu.