![TARON KUNGIYOYI DA JAMI'AN TSARO A GARIN ZARIYA.A yau lahadi hukumar yan' sanda na kasa shiyya zariya Nigeria Police for...](https://img4.medioq.com/808/951/941765778089517.jpg)
19/01/2025
TARON KUNGIYOYI DA JAMI'AN TSARO A GARIN ZARIYA.
A yau lahadi hukumar yan' sanda na kasa shiyya zariya Nigeria Police force Zaria city Division, bisa jagorancin CSP Kasim Abdul DPO Zaria city Division, ya jagoranta,
An shirya taron ne a ofishin hukumar yan' sanda dake kofar fada Cikin birnin Zazzau. Taron ya samu halartan kungiyoyi daba-daba, kungiyar masu gyaran Keke napep, da masu gyaran Babur, da masu haya da Keke mai kafa uku(Napep) da kungiyar Matasa, da, da kungiyar yan' kasuwa, da mahauta, da kungiyar marubuta, da yan' soshiyal mediya (Media Activist),da masu anguwanni, da dakatai,
Shugaban zaman CSP Kasim Abdul DPO Zaria city Division, ya bayyana jin dadinsa da irin gudunmuwa da hadin Kai da suke samu daga al'ummar anguwannin cikin birnin Zaria, da masu Sana'o'in, da kungiyoyi, da yan' kasuwa, wajen wayar da Kai wajen tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu,
Ya cigaba da yabama shuwagabannin kungiyoyi da masu anguwanni da jagororin al'umma, wajen kokarin basu bayanai a sirrance da bayyane wajen samar da maslaha da tsaro, domin dakile ta'addanci da barna, da ta'ammali da siyar da kayan shaye-shaye da sace-sace da sauran Laifuffukan daba-daban.
Anyi taron cikin nasara da hadin Kain da goyon baya. Domin tabbatuwar zaman lafiya a cikin birnin zariya da jahar Kaduna dama kasa baki Daya.
Rubutawa
Sir. Yusuf Yahaya Bamalli
Chairman kaduna Media Writers"
January 19th, 2025