01/09/2022
SAKO GA DUK WATA MACE DA KADDARAR RABUWAR AURE YA AUKA MATA.
Shi rabuwar aure kaddara ce, kuma ba karshen rayuwa ba kenan kuma, sau da dama abu zai faru da ɗan Adam yana mai kin wannan abin amma alkhairi ne a gare shi, don haka wannan ki ɗauke shi a jarrabawa.
Kiji tsoron ALLAH a cikin dukkanin lamarin ki zai ba ki mafita ya azurta ki ta inda ba ki taɓa zato ba, kuma ya ba ki Kyakkyawar rayuwa bayan wannan da kuma miji mai NAGARTA.
Kada kiyi tunanin ba ki samun irin mijin da ya rabu da ke, a'a rahmar UBANGIJI mai yawa ne kuma babu mai cire rai daga rahmar UBANGIJI sai mara rabo, shi kwanciyar hankali aure ba'a yawan dukiya bane ko sarauta ko daukaka, a'a a kulawa ne da samun Hakkokin aure dai-dai gwargwado, kada don kin fita wata gida na alfarma kice sai irin mijin ko fiye da shi, a'a ki dubi nagarta, kuma kada ki ki wani mutumin kirki saboda ba yi da abin duniya matukar zai iya rike ki babu Wanda yasan menene gobe za ta haifar, kuma ba ki san hikimar UBANGIJI ba da ya turo shi gare ki.
Za ki fuskanci jarrabawa iri iri, wasu su miki isgili, wasu su raina ki, abinda yake karya da gaskiya duk a cakuɗa ayi ta yaɗawa, kiyi hakuri, hakuri domin ALLAH ki kauda kai, za ki ga canji a gurin mutane daban daban wanda kuma ba ki taɓa zato ba.
Kada sabo da zama da miji ya sanya ki soyayya da kananun yara wanda ba auren ki za su yi ba, kawai sai dai shiririta, kada saboda rashin tsayayye ki tsaida mutumin banza, ko ki auka soyayya da wa'enda kawai ba auren ki za su yi ba, sunji kawai ke bazawara ce bari su zo su yaudare ki, ayi ta soyayyar sabon ALLAH, kada ki biye musu matukar kina son samun miji na gari kuma da mafita a rayuwar ki, ki kame kanki daga lalata ballagazanci na karshe shine ki kinyi aure kin fita, kizo kina kwanciya da wasu samari ko wani namiji wannan tozarta kanki ne da ya'ya da dangi kuma saɓon ALLAH ne mai girma.
Ki samu sana'a duk kankantar sa ki rike kina yi, kiji tsoron ALLAH kada ki zamo mai kwadayin abin duniya ki auka abinda wasu s**a auka .