27/03/2026
Wannan rashin lafiyar, zai shanye naira miliyan 50 zuwa 60 acikin aljihunka 🥲
Ciwon ƙoda mummunan ciwo ne, yana dagacikin cuta mai hatsarin gaske dake ake kamuwa dashi acikin al’umma
Saboda haka, ku bayarda hankalinku da lokacinku wurin karanta wannan rubutun mai amfani👇
————————————
Ƙoda shi ake kira “Kidney” da turanci, kowane mutum yanada ƙoda guda biyu acikin cikinsa
Menene amfanin wannan ƙodar?
Ƙoda tana amfani domin tace jini.
Ƙoda kamar tsintsiya ce dake share dukkan dattin dake acikin jinin ɗan adam
A kowace rana, ƙoda tana tace jinin mutum so talatin (30) zuwa arba’in (40)
Babu wani mashin ko na’ura da zai iya wannan aikin a sauƙaƙe
Tsarki ya tabbata ga Allah, subuhanahu wata’ala
————————————-
Idan ƙodar mutum ya tsaya da aiki, jinin jikinsa zai kasance gurɓatacce marar kyau har zuwa lokacin da yasamu lafiya
Idan aka samu gurɓataccen jini acikin jiki, sauran sassan jiki irinsu (Zuciya, hanta, ƙwaƙwalwa, hanji da tsokokin jiki) duk matsalar zata iya shafarsu
Wannan yasa idan mutum yana fama da matsalar ƙoda, jikinsa zai kumbura, tare da rashin kuzari da ciwon gaɓoɓin jiki
————————————
Duk mutumin da ƙodarsa ta gaza, yanada zaɓi biyu:
1. Za’a acigaba da yimasa wankin ƙoda abunda ake kira (Dialysis) da turanci
Shi wannan dialysis, wani mashin ne da ake amfani dashi domin wanke dattin jini zuwa wani ɗan lokaci
Kuma wannan mashin bazai iya aikin da ƙoda keyi ba, domin kuwa ƙoda na wanke jini so 30 zuwa 40 kowace rana. Amma dialysis so uku akeyi a acikin sati.
2. Mataki na biyu shine ayi tiyatar dashen ƙoda akan kuɗi naira miliyan 30 zuwa 40 😭
Wannan matakin na biyu, yafi ƙarfin talaka.
Bayan anyi tiyatar dashen ƙoda, akwai jinya da shan magani wanda shima zai iya cin miliyoyin kuɗi
Ko acikin garinku mutum nawa ka taɓa gani an yiwa tiyatar dashen ƙoda? Aiki ne mai matuƙar wahala da tsadar kuɗi wanda za’a iya sayarda dukkan kadarorin da iyalanku s**a mallaka a duniya 😭😭
——————————-
Menene mafita?
Wace hanya mutum zai bi domin kare ƙodarsa daga lalacewa?
1. Ku ajiye shaye-shaye (sigari, wiwi, giya ko ƙwayoyin magani ba bisa ƙa’ida ba)
2. Ku ajiye shan jiƙe-jiƙen kayan bauri da basuda amfani
3. Ku rage yawan cin gishiri acikin abincinku
——————————-
4. Idan kasan kanada ciwon hawan jini “high blood pressure” ko ciwon sikari “diabetes” to dole ka mayarda hankali wurin zuwa assibiti akai akai domin gwaji da rubuta maganin daya dace
5. Yawan shan tsaftatattun ruwa akai-akai. Dole mutum ya nemi tsaftatattun ruwansha tare da gujewa gurbatattun ruwansha
Ba kowane irin ruwa ake sha ba
6. Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki da yayan itace ko ganye, ku guje cin abinci mai kitse ko maiƙo sosai
7. Motsa jiki akai-akai (gudu, ƙwallon ƙafa, tafiya a ƙafa) da sauransu
———————————-
⚠️ Facebook ba assibiti bane, idan kana fama da matsalolin ƙoda ko kumburin jiki to kaje assibiti domin ganin likita a hukumance.
DR ALHASSAN NA BODINGA