04/11/2025
YANZU-YANZU: Burna Boy Ya Bayyana Ƙudurorin Sa Bayan Ya Karbi Addinin Musulunci.
Burna Boy Ya Karɓi Musulunci — Mawakin Duniya Ya Bayyana Dalilinsa Na Komawa Addinin Musulunci.
Fitaccen mawakin Najeriya, Damini Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, ya jawo hankalin Mutane bayan ya bayyana cewa ya karɓi addinin Musulunci.
Wannan magana tasa ta jawo cece kuce a duk faɗin duniya, musamman ma a shafukan sada zumunta, inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu.
A cewar Burna Boy, bai sami wani matsin lamba daga kowa ba, sai dai bincike da tunani mai zurfi ne s**a kai shi ga yanke wannan shawara.
Ya ce ya dade yana bincike akan wane Addini ne na gaskiya a rayuwa, kuma a ƙarshe zuciyarsa ta samu natsuwa da Musulunci.
“Na duba addinai da dama, na tambayi kaina menene gaskiya game da rayuwa da manufar ɗan adam. A ƙarshe, zuciyata ta kwantar da hankali da Musulunci — shi ya sa na karɓe shi,” in ji Burna Boy.
Mawakin ya ƙara da cewa shi Mutum ne mai ladabi da girmamawa ga dukkan addinai, kuma yana ganin cewa bai k**ata addini ko ƙabila su zama abin rarrabuwa tsakanin su ba.
Ya ce abin da yafi muhimmanci shi ne rayuwa cikin gaskiya, tausayi da zaman lafiya.
“Addini ba ya nufin nuna banbanci ko ƙiyayya. Abin da na fahimta daga Musulunci shi ne zaman lafiya, gaskiya da biyayya ga Ubangiji,” a cewar mawakin.
Burna Boy, wanda ya shahara da wakoki irin su “Last Last”, “City Boys”, da “Ye”, ya ce burinsa yanzu shi ne ya ci gaba da rayuwa bisa gaskiya da rikon addini, ba wai don yayi suna ko samun daukaka a duniya ba.
Labarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke nuna farin ciki da wannan mataki, yayin da wasu kuma ke tambaya ko wannan canji zai shafi salon wakokinsa a gaba.
Duk da haka, Burna Boy ya bayyana ewar Allah ne kaɗai mai yanke hukunci akan wani abu da ya shafi kasuwanci ko shahara.