09/01/2025
RAHOTO KAN TARON DA'IRATUL MUQADDIMIN ATTIJJANIYYA NA WATAN JANAIRU 2025
A yau, Khalifa Ibrahim Shehu Muhammad Surajo Maiduguri, wanda shi ne National Deputy Director General Operations FAG Fityanul Islam, ya jagoranci tarbar baki a wani muhimmin taro addu'o'i da aka gudanar a Zawiyyarsa dake unguwar Gomari Airport, Maiduguri.
Taron ya gudana ne a karkashin jagorancin kungiyar Da'iratul Muqaddimin Attijjaniyya Borno State, wanda yake kasancewa Sakataren wannan kungiyar a matakin jiha. Wannan taro yana daya daga cikin al’adu na kungiyar, inda ake gudanar da shi duk karshen wata domin yi wa Najeriya da sauran kasashen duniya addu’o’in samun zaman lafiya, ci gaba, da yalwar arziki.
A yayin taron, an gudanar da karatun Alkur'ani mai girma tare da addu’o’i na musamman don neman tsari daga matsalolin da duniya ke fuskanta, da kuma rokon Allah ya baiwa shugabanni hikima wajen tafiyar da mulki nagari.
Haka zalika, Shugaban kungiyar Da'iratul Muqaddimin Attijjaniyya Borno State Chapter, Sheikh Muhammad Abdullahi, ya jaddada mahimmancin hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma, tare da kira ga matasa su rungumi addini da zaman lafiya.
Wannan taro yana gudana ne a dandalin addini na Zawiyyatul Khalifa Shehu Ibrahim Muhammad Surajo Barham Islamic Center, Gomari Airport, Maiduguri, wanda yake zama cibiyar shirye-shiryen ayyukan kungiyar.
Kafin a tashi daga taron, an tattauna kan bukatar ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka a duk karshen wata domin dorewar addu'o'in neman dacewa ga kasa da duniya baki daya.
Daga karshe, Khalifa Ibrahim Shehu Muhammad Surajo Maiduguri, ya yaba da yadda aka gudanar da taron cikin tsari, tare da godiya na musamman ga kungiyar Fityanul Islam, JNI, NTA, da DANDAL KURA Radio, inda ya jaddada muhimmancin gudanar da irin wadannan ayyuka a kai a kai domin samun nasarorin da ake fatan cimmawa.
✍️ Rabiu Babayo
Yakubu Mustafa Grema
FAG/FIN/BORNO/MEDIA/TEAM, 09/01/2025