23/12/2024
Hamid Musa Zakariya, ɗan asalin jihar Borno, mutum ne wanda ake matuƙar yaba masa bisa halayensa masu kyau da kyawawan dabi'unsa. Shi mutum ne wanda ya keɓance kansa da ƙanƙan da kai, girmama mutane, da ƙwazo a duk wani al'amari da ya saka a gaba. Wannan hali nasa ya sa mutane suke ƙaunarsa kuma suke ɗaukarsa a matsayin abin koyi.
Hamid ya kware sosai a karatun Qur'ani, musamman a riwayar Warsh, kuma ya kasance mai ƙwazo a gasar haddar Qur'ani. A cikin gasar haddar izu sittin da tajweed, ya nuna bajinta da ƙwarewa, abin da ya tabbatar da irin jajircewarsa wajen neman ilimi da kyautata addini.
Baya ga wannan, Hamid mutum ne kyakkyawa, fari, dogo, kuma mai kyautata mu'amala da mutane. Zuciyarsa tana cike da son mutane da yin kyakkyawan hali ga kowa, abin da ke ƙara fito da ɗaukakarsa a cikin al'umma. Soyayya saboda Allah ita ce babban ginshiƙin alaƙar da kowa ke yi da shi, domin yana da kyakkyawan halin da ke jan hankalin mutane zuwa ga shi.
El-Mustapha Goni.....🖊️
Sun, Dec 22 2024.