Halarci Online Media

Halarci Online Media Wanna Shafi, Zai Ringa Kawo Muku Ingatatun Labarai Wadanda S**a Shafi Abubuwa Daban Daban Na Rayuwarmu Kamar; limi, Nishadi, Wasanni, Ban Al'ajabi Da Sauransu.

ABORIGINES Aborigin na Australiya su na da al'adu iri-iri da imani daban daban waɗanda s**a kasance daya daga cikin mafi...
26/12/2024

ABORIGINES

Aborigin na Australiya su na da al'adu iri-iri da imani daban daban waɗanda s**a kasance daya daga cikin mafiya daɗaɗɗun al'adun ci gaba a duniya. A lokacin da Turawa s**a yi wa Ostiraliya mulkin mallaka, sun ƙunshi al'ummomin da al'adu masu harsuna sama da 250 da fasaha daban-daban da ƙauyuka. Hotunan tarihi masu ban sha'awa da aka dawo da su, wasu sunyi fiye da shekaru 150, su na nuna matasa maza da mata sanye da kayan yaki k**ar yadda suke yi shekaru aru-aru kafin zuwan turawa.

Hotunan bayan yaƙe-yaƙe ne da akayi ne a kan iyaka da Ostiraliya waɗanda 'yan asalin ƙasar s**a ƙi yarda da turawan mulkin mallaka su faɗaɗa mulkin mallaka zuwa cikin ƙasarsu, su na kare yankunansu da al'adunsu akan abin da ya rage a yankinsu. Mayaƙan ƙabilar ƙarfafan mayaka ne waɗanda s**a yi amfani da mak**ansu da fasaha sosai kuma sun kware a dabarun yaƙi. Sojojin Birtaniyya s**a ɗauki shekaru da yawa don cin nasara a kansu. Ƙabilun galibi suna rayuwa ne a cikin ƙananan ƙabilun dangi na makiyaya tare da yankunan da galibi ke haifar da rikici tsakanin dangi, wanda ke haifar da fadace-fadace.

Yawan Jama'a

A kasar Australia tun daga Yuni 30, 2021, akwai Aborigin masu yawa 983,700, a tsibirin Torres Strait a Ostiraliya, wanda shi ne kashi 3.8% na yawan jama'arsu. Ana sa ran wannan adadin zai karu zuwa tsakanin 1,171,700 da 1,193,600 nan da shekarar 2031.

Rubutawa Muhammad Cisse.

A Rana Mai Kamar Ta Yau 25 Ga Watan Disamba Aka Haifi Tsohon Gwamnan jihar Kano Kuma Shugaban Riko na Jam'iyyar APC Dr A...
25/12/2024

A Rana Mai Kamar Ta Yau 25 Ga Watan Disamba Aka Haifi Tsohon Gwamnan jihar Kano Kuma Shugaban Riko na Jam'iyyar APC Dr Abdullahi Umar Ganduje. Yanzu Yana Da Shekaru (75) A Duniya

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje OFR, mutumin garin Ganduje ne ta cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. Ɗan siyasa, gogaggen ma’aikaci, masanin mulki a ilimance kuma a aikace, ya yi kwamishina har sau biyu, sannan kuma ya yi mataimakin gwamna Kano shi ma sau biyu, haka kuma yayi Gwamnan Jihar Kano A Tutar jama’iyyar APC Sau biyu na tsawon Shekaru 8.
A yanzu kuma shi ne Shugaban riko na jam'iyya mai mulki ta APC.

Matum ne shi mai haƙuri, kawaici, da kuma biyayya ga duk wanda ya girme shi ta kowace fuska wanda ka iya kasancewa girma na shekaru ko na harkar aiki.

An haifi Abdullahi Umar a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano a 1949. Ya fara karatun Kur'ani da Islamiyya a kauyensa inda ya fara samu ilimin addini.

🙏 HAPPY BIRTHDAY SIR 🎂 🥳 🎉 🎈 🎁 🎊

Daga Muhammad Cisse.

Dan Najeriya Umar Farouk Abdulmutallab da aka k**a da yunkurin tada bam a wani jirgin saman Amurka a shekarar 2009.A Ran...
25/12/2024

Dan Najeriya Umar Farouk Abdulmutallab da aka k**a da yunkurin tada bam a wani jirgin saman Amurka a shekarar 2009.

A Rana Mai Kamar Ta Yau 25 Ga Watan Disamba 2009 a ka k**a dan Najeriya Umar Farouk Abdulmutallab kan zargin yunkurin tada bam a wani jirgin saman Amurka a shekarar 2009.

A ranar Kirsimetin shekara ta 2009 ne aka k**a Abdulmutallab a kan hanyarsa ta zuwa Detroit a Amurka, inda kuma aka zarge shi da yunkurin tayar da bam a jirgin. Jami'an tsaron Amurka dai sun ce ya yi kokarin tayar da bom din ne wanda ya boye a wandonsa.

Hankulan jama'a dai sun karkata sosai ne a kan lamarin bayan kwanaki uku bayan kisan Anwar Al-Aw*laqi na kungiyar Al-ka'ida da wani jirgin saman Amurka yayi a kasar Yemen. Jami'an hukumar leken asirin Amurkan dai sun sha nanata cewa Anwar Al-Aw*laqi na da hannu a yunkurin tada bam din a jirgin saman Amurka a shekarar 2009.

Sun zargi Al-Aw*laqi da tunzura Abdulmutallab bayan da s**a hadu a kasar Yemen. Umar Farouk Abdulmutallab ya amsa laifukan da aka tuhume shi da aikatawa guda takwas a watan Octoban shekarar 2011. Daga Bisani Wata kotu a Amurka ta yankewa Umar faruk Abdulmutallab hukuncin daurin rai-da-rai, bayan da aka same shi da kokarin tayar da bam a wani jirgin saman Amurka.

Umar Farouk Abdulmutallab, dan shekaru 25 a lokacin, ya amsa laifin yunkurin tarwatsa wani jirgin saman kasuwanci na Amurka, a wani lamari da ake ganin yunkurin kunar bakin wake ne.

Abdulmutallab ya kone sosai lokacin da bam din da ya boye a kamfansa ya kasa tashi gaba daya, k**ar yadda masu gabatar da kara s**a ce. Akalla mutane 300 ne a cikin jirgin wanda ya taso daga Amsterdam na kasar Holland zuwa birnin Detroit na Amurka. Umar Faruk Mutallab wanda mahaifinsa Abdulmutallab, shahararren dan kasuwa ne kuma ma'aikacin banki, ya fuskanci tuhuma kan laifuka takwas da s**a hada da ta'addanci da kuma kisan gilla. Kungiyar Al-Qa*eda a yankin Larabawa da ke da hedkwata a kasar Yemen, ta ce ita ce ta dauki shirya harin.

Danginsa sun koka

Sai dai danginsa sun koka kan yadda mahukunta a Amurka s**a yi watsi da hujjojin da lauyoyin Abdulmutallab s**a gabatar.

"Muna kira ga sashen shari'a na Amurka da su sake yin nazari akan hukuncin daurin rai-da-ran da aka yankewa Umar Faruk Muttalab", a cewar sanarwar iyalin Alhaji Umar Mutallab da s**a fitar.

Haka nan kuma iyalan sun yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta ci gaba da goyan bayan da ta ke bayarwa wajen tuntubar gwamnatin Amurka domin tabbatar da an sake yin nazari akan shari'ar domin yin la'akari da hujjojin da lauyoyin Umar Faruk Muttalab din s**a gabatar a gaban kotun.

Daga Muhammad Cisse.

A Rana 25 Ga Watan Disamba A shekara ta 336 AD, cocin Kirista a Roma ya fara Yin bikin Kirsimeti.A lokacin Sarkin Roma C...
25/12/2024

A Rana 25 Ga Watan Disamba A shekara ta 336 AD, cocin Kirista a Roma ya fara Yin bikin Kirsimeti.

A lokacin Sarkin Roma Constantine A ka Fara yin Bikin, duk da a zahiri Romawa Ne s**a ƙirƙira, amma har yanzu ba a Sami Sunan tak**aiman mutumin da aka Tabbatar Da Shi ne Ya Fara Yin Bikin Ba.

ASALIN KIRSIMETI

Kirsimeti ya samo asali ne daga al'adun Ar*na da na Romawa. Romawa, su na yi bukukuwa biyu a watan Disamba. Na farko shi ne Bikin Saturnalia, wanda shi ne bikin makonni biyu na girmama Ubangijin aikin gona na Saturn.

A ranar 25 ga Disamba, su na yi bikin haifuwar Mithra, ubangijin Rana. Bukunkunan biyun sun kasance Masu ban sha'awa, da shaye-shaye.

Haka kuma a cikin watan Disamba, in da rana ba ta yin haske Saboda Sanyi, a al'adun maguzawa (Pagan) suna kunna wuta da kyandir Don Kawar Da duhu. Romawa Sun shigar da wannan al'ada cikin Bukukuwan nasu.

Yayin da addinin Kiristanci ya yaɗu a Turai, limaman Kirista ba za su iya hana al’adu da bukukuwan ar*na na al'ada ba, tun da ba wanda ya san ranar haihuwar Yesu, sai su ka mai da al’adar Ar*na (Maguzawa) ta zama bikin Ranar haihuwarsa. Tun da ba a Rubuta Ranar da aka haifi Kristi a cikin Littafin Bible Ba.

Bikin ya bazu daga Roma zuwa wasu majami'u na Kirista, kuma yawancin Kiristoci sun fara bikin haihuwar Kristi a ranar 25 ga Disamba.

Rubutawa Muhammad Cisse.

Sulaiman Abdul Aziz Al Rajhi dan kasar Saudiyya wanda ya sadaukar da duk dukiyarsa saboda Allah Sheikh Sulaiman bin Abdu...
24/12/2024

Sulaiman Abdul Aziz Al Rajhi dan kasar Saudiyya wanda ya sadaukar da duk dukiyarsa saboda Allah

Sheikh Sulaiman bin Abdulaziz Al Rajhi (Da Larabci :سليمان بن عبد العزيز الراجحي, An haife shi a shekara ta 1929 jigo ne a Masarautar Saudiyya kuma hamshakin attajiri. A shekarar 2011 mujallar Forbes ta kiyasta dukiyarsa ta kai dala biliyan 7.7, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 120 mafi arziki a duniya. Ya samu lambar yabo ta Sarki Faisal ta kasa da kasa (King Faisal International Prize) a shekarar 2012 saboda sadaukar da rabin dukiyarsa ga ayyukan agaji, da bude bankin Musulunci, da aiwatar da ayyuka gina kasa.

Tarihin Rayuwa

An haifi Sulaiman Al Rajhi a garin Al Bukairiyah da ke lardin Al Qassim a kasar Saudiyya, kuma ya taso ne a cikin saharar Nejd inda shi da dan uwansa Saleh s**a fara sana'ar hayar rakuma da ke daukar mahajjata cikin ayari a hamada zuwa garuruwan Makka da Madina.

Sulaiman Abdulaziz Al Rajhi ne ke da hannun jari mafi girma a bankin Al Rajhi da iyalinsa, wanda bankin a kullum yake bayar da rahoton ayyukan da s**a fi samun riba a tsakanin dukkanin bankunan Saudiyya. Bankin wanda ya kafa, tare da babban yayansa, Saleh, a halin yanzu shi ne shugaban gudanarwasa.

Haɓaka kasuwancin ƴan uwan ​​Al Rajhi da faɗaɗa ya samu ne sak**akon ambaliyar ma'aikata da s**ayi ƙaura zuwa Saudi Arabiya a lokacin haɓakar arzikin man fetur a shekarun 1970s. Al Rajhis ya taimaka wa musu aika abin da suke samu zuwa gida a kasashe k**ar Indiya da Pakistan. A shekara ta 1983, ’yan’uwan sun sami izinin buɗe bankin Musulunci na farko a Saudiyya, wanda zai kiyaye ka’idojin addini k**ar hana cin kudin ruwa.

Iyalan Al Rajhi sun ci gaba da kasancewa masu hannun jari na Bankin Al Rajhi, duk da cewa Sulaiman da 'yan uwansa sun raba jarin iyali sun zuba a harkar noma, da harkar karrafa, da sauran sassan masana'antu. Yanzu haka yana zaune a Saudiyya kuma yana da yara akalla 23.

Tallafi

Iyalan Al Rajhi, galibi a Saudi Arabiya ana daukar su a matsayin mafiya arziki a kasar a cikin wadanda ba yan sarauta ba, kuma yana cikin manyan masu bayar da agaji a duniya. Ya kafa Jami'ar Sulaiman Al Rajhi a garinsu, jami'ar daya kafa kyauta ba domin neman riba ba. Babban abin da jami'ar ta fi mayar da hankali a kai shi ne kiwon lafiya da kuma harkokin banki na Musulunci, amma kuma tana koyar da wasu darussan na daban.

A kowace shekara, gidauniyarsa tana tallafawa ayyukan agaji kusan 1,200 a yankuna 13, wadanda s**a haɗa da birane da garuruwa sama da 130 a faɗin Masarautar. Ana zabar ayyukan ne bisa bukatun al'ummar Saudiyya.

A watan Mayun 2011, ya sanar da cewa ya ba da gudummawar dukkan dukiyarsa ta dala biliyan 7.7 ga sadaka.. Ana daukar gudummawar da ya bayar a matsayin mafi girman kyauta a tarihin Musulunci. Yace ya dogara ga Allah, domin neman Aljanna.

Rubutawa Muhammad Cisse.

TARIHIN SARKI IDRIS NA KASAR LIBYA An haifi Muhammed Idris as-Senussi a ranar 12 ga Maris, 1889, ko 1890 a Al Jaghbub a ...
24/12/2024

TARIHIN SARKI IDRIS NA KASAR LIBYA

An haifi Muhammed Idris as-Senussi a ranar 12 ga Maris, 1889, ko 1890 a Al Jaghbub a Cyrenaica (lardi na Daular Usmaniyya a Libiya ta yau). Iyayensa su ne Muhammed al-Mahdi as-Senussi da Aisha bint Muqarrib al-Barasa. Idris ya kasance jikan wanda ya kafa kuma shugaban darikar Sufi na Senussi na Musulunci. A 1902 mahaifinsa ya rasu, kuma dan uwansa ya yi mulki har zuwa 1916 lokacin da Idris ya zama shugaban mulkin Senussi. A shekara ta 1920 ya karbi mukamin sarki (shugaban siyasa) na Cyrenaica.

Bayan yakin duniya na daya daular Usmaniyya ta Rushe kuma kasar Turkiyya mai cin gashin kanta ta b***e. Turkiyya ta mika lardunan Cyrenacia, Tripolitania, da Fezzan ga Italiya. Gaba ɗaya waɗannan larduna uku ana kiran su Libiya. Italiyawa sun ba Idris damar cin gashin kansa a cikin yankinsa kuma a cikin 1922 ya tsawaita mulkinsa a Tripolitania. Sai dai kuma daga baya a wannan shekarar Benito Mussolini ya hau kan karagar mulki a Italiya kuma ya kuduri aniyar karbe iko da yankuna uku na Libya kai tsaye. Italiyawa sun yi wa al'ummar Libya mugun zalunci. An tsare da yawa a sansanonin taro kuma an kashe sama da mutane 12,000. Idris ya gudu zuwa Masar a watan Disamba 1922.

Bayan da Italiya ta sha kaye a yakin duniya na biyu, Turawan Ingila da Faransa sun mamaye yankuna daban-daban na Libya. A watan Nuwamba 1949 Majalisar Dinkin Duniya ta ba da shawarar cewa Libya ta zama kasa daya da Sarki Idris ke jagoranta. Bayan shekara 1 ya kafa Masarautar Libya a hukumance kuma ya ayyana kansa a matsayin Sarki.

Libya ta zama kasa mai cin gashin kanta a ranar 24 ga Disamba, 1951, tare da Sarki Idris a kan karagar mulki.

Sarki Idris ya kasance mai ra'ayin addini irinna mazan jiya. Ya mallaki sojoji kuma yana da tasiri mai yawa akan majalisa. Yawancin talakawansa sun fi biyayya ga danginsu, kabilarsu, ko yankinsu fiye da Sarki. Idris ya bi manufar kulla kyakkyawar alaka da Turkiyya tare da nada Turkawa da dama a manyan muk**ai a gwamnati. Firayim Ministan farko na kasar, Sadullah Kologlu, Baturke ne k**ar yadda ministan harkokin wajen kasar, Abdullah Busayri. Kana kuma An dakatar da jam'iyyun siyasa.

A shekarar 1959 aka gano man fetur a libya. A cikin 'yan shekaru, Libya tana samun makudan kudade daga kudaden shigar man fetur kuma ta tashi daga daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya zuwa daya daga cikin masu arziki. Har ila yau, gwamnatin ta karbi miliyoyin kudade don ba da izinin gina da kuma kula da sansanin sojin Amurka a Libya da kuma taimakon raya kasa kai tsaye.

A watan Afrilun 1963 Sarki Idris ya ba da sanarwar cewa za a maye gurbin tsarin gwamnatin tarayya da tsarin bai daya. An soke majalisun larduna da tsarin shari'a, tare da mai da hankali a matakin kasa. Duk haraji da kudaden shigar mai sun tafi ne kai tsaye ga gwamnatin kasa.

Sojoji da masu matsakaicin ra'ayi da ke karuwa cikin sauri sun nuna rashin amincewa da iko da manufofin masu ra'ayin mazan jiya na Sarki Idris. An zarge shi da gwamnatinsa da cin hanci da rashawa. A watan Satumban shekarar 1969 a lokacin da sarki Idris ke kasar Turkiyya, wata tawagar sojoji karkashin jagorancin Kanar Muammar al-Qaddafi ta hambarar da gwamnatin Libya. Sarki Idris ya samu mafaka a kasar Masar. An yi masa shari’a a bayan idonsa a Libya kuma aka same shi da laifin cin hanci da rashawa a shekarar 1974. Ya rasu a ranar 25 ga Mayun 1983 a birnin Alkahira na kasar Masar yana da shekaru 93 a duniya.

Sarki Idris yayi aure sau biyar. Da Sau biyu a lokaci guda (1911-1922 da 1955-1958), Sarki Idris ya auri mata biyu. Ya haifi 'ya'ya maza biyar da mace daya; duk sun mutu tun suna yara.

Daga Muhammad Cisse.

Yau Shekaru 22 da Kafa Kungiyar Bo*ko Haram A Rana Mai Kamar Ta Yau 24 Ga Watan Disamba 2002 aka kafa kungiyar Bo*ko Ha*...
24/12/2024

Yau Shekaru 22 da Kafa Kungiyar Bo*ko Haram

A Rana Mai Kamar Ta Yau 24 Ga Watan Disamba 2002 aka kafa kungiyar Bo*ko Ha*ram

Mohammed Yusuf ne ya kafa kungiyar a shekarar 2002, Abubakar She*kau ya jagoranci kungiyar tun daga shekarar 2009 har zuwa mutuwarsa a shekarar 2021, duk da cewa kungiyar ta rabu zuwa wasu kungiyoyi bayan kashe Muhammad Yusuf da kuma a shekarar 2015.

Lokacin da aka kafa kungiyar, babban burinsu shi ne. "Tsarkake addinin Musulunci", ma'ana yada tafarkin sunni, da ruguza shi'a a arewacin Najeriya, imani da jiha*di da kuma kokarin kungiyar na samu karfin kifar da gwamnatin Najeriya.

Ƙungiyar ta haɗa kai tare da Isla*mic Sta*te of Iraq and Le*vant. Yan kungiyar sunyi kaurin suna ta bangaren rashin tausayi tun lokacin da s**a fara tada kayar baya a 2009, bo*ko Haram ta kashe dubunnan mutane, a hare-haren da ake kai wa 'yan sanda, da sojoji da fararen hula. Ta yi sanadin mutuwar yara da mutane fiye da 500,000 da kuma raba miliyan 3.3 da muhallansu. Bo*ko Haram ta ba da gudummawa ga samar da karanci Abinci da yunwa a yankin.

Daga cikin mutane miliyan 3.3 da rikicin ya raba da muhallansu tun daga watan Mayun 2013, akalla 280,000 ne s**a bar Najeriya s**a tsere zuwa Kamaru, Chadi ko Nijar.

Bo*ko Ha*ram sun kashe sama da mutane 6,600 a shekarar 2014 kadai. Kungiyar ta yi kisan kiyashi da s**a hada da kashe daliban makaranta 59 a watan Fabrairun 2014 da kuma yin garkuwa da jama’a ciki har da sace ‘yan mata 276 a Chibok a cikin watan Afrilun 2014. Cin hanci da rashawa a bangaren jami'an tsaro da take hakkin bil'adama da suke yi ya kawo cikas ga kokarin dakile tashe-tashen hankulan.

Rubutawa Muhammad Cisse.

An karbo daga Shaddad bn Aus (RA) Daga Annabi (SAW): "Jagora cikin dangogin laffuzan neman gafara (istigfari) da nau'uka...
24/12/2024

An karbo daga Shaddad bn Aus (RA) Daga Annabi (SAW): "Jagora cikin dangogin laffuzan neman gafara (istigfari) da nau'ukansa, shi ne, ka ce:

«اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْــتَـطَعْتُ، أَعُـــــــوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي؛ اغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ».

Ma'ana: "Ya Allah kai ne ubangijina babu abun bauta da gaskiya sai kai, kai ne ka halicce ni, ni kuma bawanka ne, kuma ina kan alkawarinka gwargwadon ikona, Ina neman tsarinka daga sharrin abun da na aikata, ina tabbatar maka da ni'imominka a kaina, ina kuma mai tabbatar da zunubaina; ka gafarta min; lallai babu mai gafarta zunubai in ba kai ba". Annabi (SAW) ya ce:

«وَمَنْ قَالَهَا مِنَ النَّهَارِ مُوقِنًا بِهَا فَمَاتَ مِنْ يَوْمِهِ قَبْلَ أَنْ يُمْسِيَ فَهُوَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ، وَمَنْ قَالَهَا مِنَ اللَّيْلِ وَهْوَ مُوقِنٌ بِهَا فَمَاتَ قَبْلَ أَنْ يُصْبِحَ فَهْوَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ».

Ma'ana: "Duk wanda ya karanta Zikirin nan da rana yana mai samun yakini da shi in ya mutu a cikin yininsa gabanin ya yi yammaci to lallai yana daga cikin yan Aljanna, wanda kuma ya fade shi a cikin dare alhalin yana da yakini da shi sai ya mutu gabanin ya wayi gari to lallai shi dan aljanna ne". Imam Bukhari ya rawaito shi.

Rubutawa Muhammad Cisse.

Kalli Motoci a Lokacin Yaki Da Sojojin Biyafara S**a Kera da kansu A Lokacin Yakin BasasaYakin basasar Najeriya da ake k...
23/12/2024

Kalli Motoci a Lokacin Yaki Da Sojojin Biyafara S**a Kera da kansu A Lokacin Yakin Basasa

Yakin basasar Najeriya da ake kiransa " Yakin Biyafara ",tabbas wahala ita ce uwar kirkira". Don a lokacin gwamnatin Najeriya ta toshe duk wata kafa da sojojin Biyafara zasu sami mak**ai. Wannan yasa yan Biyafara s**a rinka kera mak**ansu da kansu. Ba shakka sunyi kokari mutuka.

Hakan kuwa ya faru ne a lokacin da sojojin Biyafara ke kokarin kare kansu, hakika sun nuna hazaka da kirkire-kirkire ta hanyar fito da wasu mak**an yaki domin fatattakar sojojin tarayyar Najeriya.

Wasu daga cikin mak**an da s**a kera an sanya musu sunaye daban-daban dangane da aikin da suke iya yi. Misali, (the multi-barrel) da “Ogbunigwe”, wanda idan aka fassara shi zuwa hausa yana nufin, mai kisa da yawa.

Sauran kayan yakin da sojojin Biyafara s**a kera sun hada da masu cire nakiyoyi (nakiyoyin fasa mota), da manyan motoci, da tankunan yaki da masu sulke, da na’urar harba makami ta (Ojukwu air drop bomb ), da (Ojukwu bucket) da Gr***de Launcher, da dai sauransu.

Yakin da ya fara a ranar 6 ga Yuli 1967 ya ƙare a ranar 15 ga Janairu 1970. Yakin Wanda yayi sanadiyar kashe mutane kusan miliyan biyu akasarinsu yan kabilar Igbo, in da wadansunsu da yawa s**a mutu ta sanadiyar ja'ibar yunwa.

A ƙasa akwai hotunan kayayakin Sojoji masu sulke na Biyafara da Motocin Biyafara da aka fi sani da Red Devils. Akwai nau'ikan A, B, C, da D a cikinsu. A halin yanzu dai ana ajiye wadannan motocin a gidan adana kayan tarihin yaki na Najeriya da ke Umuahia, jihar Abia.

Daga Muhammad Cisse.

Dokta Thomas Stoltz Harvey, babban masanin cututtuka a asibitin Princeton, ya sace kwakwalwar Albert Einstein bayan ya y...
22/12/2024

Dokta Thomas Stoltz Harvey, babban masanin cututtuka a asibitin Princeton, ya sace kwakwalwar Albert Einstein bayan ya yi gwajin gawarsa a shekarar 1955:

Sata

Harvey ya sace kwakwalwar Albert Einstein kafin danginsa su shirya don binneshi. Amma daga baya ya roki dan Einstein, Hans Albert, ya bar shi ya rike kwakwalwar domin ya yi nazarin abubuwan da ke haifar da hazakar Einstein.

Abinda ya faru

A lokacin da Einstein ya mutu, a ranar 18 ga watan Afrilu 1955, sa'o'i 8 da mutuwar sa, a asibitin Princeton, dakta Thomas Stoltz Hervey masanin ilimin pathology yazo auna gawar Einstein don sanin hakikanin mai ya jawo dalilin mutuwarsa (Autopsy), sai ya faki idon mutane, da ya tabbatar da lokacin da ba a ganinsa, sai ya sace kwakwalwar Einstein.

Wannan mummunan labari ne, wannan al'amari ne da ya faru ba tare da iznin danginsa sa ba, Inji Hanoch Gutfreund daraktan aje kayan tarihi na Albert Einstein na Jami'ar Hebrew ta kasar Isra'ila, Einstein ne ya kafa jami'ar ta Hebrew kuma yana daya daga cikin manyan shugabannin ta, kuma shine shugaban kwamitin jami'ar. Ya barwa Jami'an duka rubuce-rubucen sa, da dukkan binciken sa, da dai sauransu wanda Gutfreund da kansa yayi amfani da su, kuma ya taimaka masa wurin zama babban masanin ilmin Physics wanda ake mai lakabi da magajin Einstein.

Harvey ba ya sace ƙwaƙwalwar Einstein don ya ajiye kayan tarihi k**ar yadda masu ajiye kayan tarihi s**a ajiye bindigar Annie Oakley ko gashin Neil Armstrong ko tarho din Hitila ko hular malafar Winton Churchill ba, a'a, Harvey ya sace kwakwalwar ne don ya gwada ya ga irin fasahar da Einstein yake da ita.

Wani binkice na haɗin gwiwa a California sun sanar da binciken farko na kwakwalwar Einstein, sunyi da'awar cewa kwakwalwar tana da ƙarin kaso na nau'ikan sel guda biyu, neurons da glia. Kana Einstein ya yi amfani da 100% na kwakwalwarsa.

A cikin shekarar 2010 an mayar kwakwalwar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami'ar Princeton, inda aka ajiye ta a ka kulle da makulli

Mutuwar Albert Einstein

Albert Einstein ya mutu ba jimawa ba bayan wani jini ya fashe a kusa da zuciyarsa. Lokacin da aka tambaye shi ko yana so a yi masa tiyata, Einstein ya ki, yana mai cewa, " Ina so in tafi lokacin da nake son tafiya. Ba ni da wani ɗanɗano na tsawaita rayuwa ta, na ci rabona; lokaci ya yi da zan tafi.

Kwanaki biyu kacal bayan mutuwarsa, a ranar 20 ga Afrilu 1955 an kona gawarsa a Ewing Cemetery & Crematorium a West Trenton, New Jersey a kasar Amurka.

Rubutawa Muhammad Cisse.

Tarihin Sahabbai Bilal ibn Al-Harith (RA)Abu Abd al-Raḥman Bilal b. al-Ḥārith (da Larabci: ابو عبد الرحمن بلال بن الحارث...
22/12/2024

Tarihin Sahabbai

Bilal ibn Al-Harith (RA)

Abu Abd al-Raḥman Bilal b. al-Ḥārith (da Larabci: ابو عبد الرحمن بلال بن الحارث ) (d. 60 / 679-80) Sahabin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallama) ne. Ya kasance dan Kabilar Banu Muzayna, wanda ya hadu da Manzon Allah (SAWW) tare da wasu gungun kabilarsa s**a musulunta a watan Rajab 5/626. Ya halarci wasu yake-yake a zamanin Manzon Allah (SAWW) da kuma yakoki a zamanin halifofi.

Bilal b. al-Harith wanda kunyarsa Abu 'Abd al-Rahman sahabi ne ga Annabi Muhammad (SAWW). Shi dan kabilar Banu Muzayna ne wanda ya hadu da Annabi Muhammad (SAW) tare da gungun 'yan kabilarsa a shekara ta 5/626 s**a musulunta. Yana zaune tare da dangin Banu Muzayna kuma yana yawan ziyartar Madina. Don haka sai aka ce masa al-Madani (daga Madina) a wurare da dama.

An ce Bilal ya nemi Annabi Muhammad (SAW) ya ba shi Wadi l'Aqiq a yankin Banu Muzayna wanda Manzon Allah (SAWW) ya yarda ya bashi. Annabi Muhammad (SAW) ya sadaukar da ma’adinan al-Qabaliyya dake kusa da Madina ga Bilal b. al-Harith kuma ya nada shi gwamnan yankin Hima kusa da Madina.

Bilal yana da gida a Basra. Ibn Hibban ya ce Bilal yana fataucin Lemon tsami ne wanda ake amfani da shi a matsayin tsiron magani da turare. Duk da haka, da alama yana rike da mukamin gwamnan Hima har zuwa rasuwarsa.

Bilal ya haifi 'ya'ya biyu ciki har da Hassan wanda aka alakanta shi da kafa mazhabar Irja'a a garin Basra. Ya rasu a shekara ta 60/680 a zamanin Mu'awiya yana da shekaru 80 a duniya.

Shiga cikin Yaƙe-yaƙe

Bilal ya halarci yakoki da Ghazwas da dama :

1, A cikin 5/626-7: Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihiwa Alihi Wasallama) ya aike shi ya yaki zuwa Banu Malik b. Kinana amma sai s**a gudu kafin ya isa wurin.

2, A 6/627-8: Ya halarci yakin Kurz b. Jabir al-Fihri.

3, A cikin 8/629-30: An nada shi kwamandan wani yaki. Haka nan kuma a wannan shekarar kafin Annabi Muhammad (SAWW) ya tafi Makka ya nada Bilal da wani sahabi wajen tara sojoji daga kabilar Banu Muzayna; sun yi nasarar tara sojoji dubu kuma sun halarci bude Makka.

3, Haka kuma Bilal ya halarci Yakin Dumat al-Jandal karkashin jagorancin Khalid b. al-Walid (RA).

4, A cikin 10/631-2: Lokacin da Annabi Muhammad (SAWW) ya aika Khalid zuwa Banu l-Harith b. Ka'b a Yemen, Bilal ya raka shi.

A bisa ruwayoyi da dama, Bilal b. Al-Harith ya halarci yakin Qadisiyya, Yakin Sham da Yakin Afirka a 27/647-8.

Rubutawa Muhammad Cisse.

Wajen aikin hakar ma'adinai mafi tsufa a duniya.Yan Afirka ne s**a fara shiga aikin hakar ma'adinai shekaru 43,000 da s*...
22/12/2024

Wajen aikin hakar ma'adinai mafi tsufa a duniya.

Yan Afirka ne s**a fara shiga aikin hakar ma'adinai shekaru 43,000 da s**a wuce. A cikin 1964 an gano mahakar hematite (Taman karfe) a Swaziland a Bomvu Ridge a cikin tsaunukan Ngwenya. Daga karshe an kwato kayayyakin tarihi 300,000 da s**a hada da dubban kayan aikin hakar ma'adinai da aka yi da duwatsu. Adrian Boshier, daya daga cikin masu binciken kayan tarihi a wurin, ya bayyana shekarun ma'adinan zai kai shekaru 43,200 kafin haihuwar Annabi Isa (AS) Taf Abin mamaki.

Wannan ma'adinan ba wai kawai yana da mahimmanci ga al'ummar Swaziland ba harma yana kunshe da tarihin ci gaban masana'antu na farko ga yankin Kudancin Afirka. An kuma haƙo ma'adinin ƙarfe da isar da shi zuwa wasu sassan yankin.

Ma'adinan Ngwenya yana kan iyakar arewa maso yamma na Swaziland. Ma'adinan taman na ƙarfe ya zama ɗaya daga cikin mafi daɗewar ma'adinan ƙasa a duniya, kuma ya kasancewar wurin aikin hakar ma'adinai na farko a duniya.

A kusan 400AD wasu mutane masu magana da harshen Bantu, sun zo daga arewacin kogin Limpopo. Manoma ne da makiyaya wadanda suke narka tama. Su na hako ma'adinan ta hanyar amfani da guduma masu nauyi sosai kuma sun yi cinikin ƙarfen a ko'ina cikin yankin.

A wannan wurin akwai wani tafki mai tsarki (Kamar Yadda Al'ummar wajen ke kiransa) wanda al'ummar yankin ke amfani da shi sosai. Al'ummar sun yi imanin cewa ruwan wannan tafkin na iya warkar da cututtuka daban-daban da kuma masifu.

Rubutawa Muhammad Cisse.

Masarauta Ta Soma Ne A Afirka A ranar 1 ga Maris, 1979, jaridar New York Times ta fitar da wata kasida a shafinta na far...
22/12/2024

Masarauta Ta Soma Ne A Afirka

A ranar 1 ga Maris, 1979, jaridar New York Times ta fitar da wata kasida a shafinta na farko da kuma shafi na goma sha shida mai taken Tsohuwar Masarautar Nubian. A cikin wannan labarin, an tabbatar mana da cewa: "Shaida ta daɗaɗɗiyar sarauta da aka sani a tarihin ɗan adam, kafin hawan sarakunan Masar na farko da al'ummomi da yawa, an gano su a cikin kayan tarihi na tsohuwar Nubia" (watau yankin arewacin Sudan da yankin kudancin Masar na zamani.)

An san masarautar Nubia da arzikin zinari, Nubia kuma ita ce wajen samun kayayyakin alatu k**ar turare, hauren giwa, wanda suke kaiwa a yankin Saharar Afirka zuwa wayewar Masar da Bahar Rum.

Maharba na musamman su zama masu ƙarfin soja ga sarakunan Nubian. Sarakunan Nubia a ƙarshe sun ci nasara kuma s**a yi mulkin Masar na kusan ƙarni guda.

Har ila yau abubuwan tunawa na Nubia sunan a Masar da Sudan ta zamani - a wuraren da sarakunan Nubian s**a gina birane, da dala (Pyramid) ta sarauta.

Mutanen Afirka daga yankin Sahara a yanzu sun fara ƙaura zuwa kogin Nilu a Nubia kusan 5000 (Kafin Haihuwar Annabi Isa AS). Sun zo da fasahar yin tukwane. Asalinsu makiyaya da farautar manyan dabbobi ne, daga karshe sun zama masunta da manoma. Da dadewa, wasu mutane sunyi ƙaura zuwa yankin daga kudanci, ta yadda al'ummar Nubia galibi s**a kasance su na cuɗanya iri-iri na mutanen Afirka.

Yawancin Nubians sun rayu a gefen kogin Nilu wanda ya karkata zuwa arewa ta cikin hamada. Manoma su na noma hatsi, da wake, ldabino, da kankana. Amma mahimmin abu shi ne garken shanunsu, wanda shi ne ma'aunin dukiya da matsayin zamantakewa. A cikin hamadar, 'yan kabilar Nubian suna hakar zinariya, da kuma sauran albarkatun ma'adinai. Su na sayar da shanu, zinare, da hauren giwa, fatun dabbobi, katako, turare, da dabino, Nubians sun yi ciniki tare da Masarawa, maƙwabtansu a arewa, da hatsi, kayan lambu, da giya da sauran kayayyakin da aka ƙera.

Daga Muhammad Cisse.

ZIKIRIN SAFE DA MARAICE اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَدَنِي، اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي، اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَص...
22/12/2024

ZIKIRIN SAFE DA MARAICE

اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَدَنِي، اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي، اَللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ أَنْتَ. اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْرِ، وَالْفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ (ثلاثاً)

Allahumma 'afinee fee badanee, allahumma 'afinee fee samAAee, allahumma 'afinee fee basaree, la ilaha illa anta. Allahumma innee a'oothu bika minal-kufr, walfaqr, wa-a'oothu bika min 'azabil-qabr, la ilaha illa ant. (3)

Ya Allah! Ka ba ni lafiya (aminci daga bala'i) a jikina. Ya Allah! Ka ba ni lafiya a jina. Ya Allah! Ka ba ni lafiya a ganina. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga kafirci da talauci kuma ina neman tsarinka daga azabar kabari. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. (sau uku).

Rubutawa Muhammad Cisse.

Tarihin Sahabbai SUHAIBUR RUM (RA)Suhayb dan Rum ko kuma Suhayb al-Rumi, wanda kuma aka fi sani da Suhayb ibn Sinan, ko ...
21/12/2024

Tarihin Sahabbai

SUHAIBUR RUM (RA)

Suhayb dan Rum ko kuma Suhayb al-Rumi, wanda kuma aka fi sani da Suhayb ibn Sinan, ko kuma a rubuta Suhaib, tsohon bawa ne a daular Rumawa wanda ya ci gaba da zama sahabin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama kuma zama sahabi la al'ummar Musulmi na farko. Ya Musulunta tun da wuri, yana cikin wadanda aka dandana musu azaba saboda imaninsu ga Allah (SWT) Suhaib sun Musulunta rana daya da Ammaru.

Ammaru yace, "Wata rana na hadu da Suhaib a kofar gidan Arkam bn Abul Arkam, a lokacin Annabi (SAW) yana ciki, sai nace masa, "Me kazo yi? Sai ya amsa mini da cewa, "kai me kazo yi? Sai na ce, Nazo da nufin shiga wajen Muhammadu, sai Suhaib yace, Nima hakan ne ya kawo ni". Sai muka shiga wajen Annabi (SAW), Sai ya bijiro mana da musulunci muka karba. Sannan muka zauna a gidan har yamma tayi. Sannan muka fito muna boyewa domin tsoron mush-rikan Makka.

Lokacin da zai yi hijra, mush**rikai sun tsare shi cewa bazai yi hijrar ba sai ya bar dukkan dukiyarsa, sai kuwa yabasu dukkan abinda ya mallaka. An ruwaito shi yana cewa, "Annabi (SAW) bai taba halartar wani guri ba sai na kasance na halarce shi, ban taba ganin wani abin tsoro a gaban sa ko bayansa ba sai na kasance na kare shi".

Uku daga cikin wadanda ba larabawa ba, wadanda s**a karbi Musulunci a farkon manzancin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wadanda s**a yi fice. Su ne Salmanu dan Farisa, da Bilal bn Rabah, wanda dan Asalin Abisiniya ne, ( Habasha) da Shu’aib, wanda aka fi sani da Rum. Wadannan mutane uku suna daga cikin makusantan Annabi Muhammad (SAWW) sun yarda da Musulunci a matsayin gaskiya, kuma sun ba wa addinin da ya ke tasowa wani abin tarihi na karbuwar duniya da zai samu. An ce Annabi Muhammad (SAWW) ya yi hasashen yaduwar Musulunci ta hanyar siffanta su a matsayin jagororin kabilun su; Suhaib daga Rum, Bilal na Abisiniya, da Salmanu na Farisa.

An san Suhaib ya ruwaito hadisi sama da talatin kuma uku daga cikinsu ana iya samunsu a cikin Saheeh Muslim.

Suhaib bn Sinan ar-Rumi ya rasu a Madina shekara talatin da takwas bayan hijira, a shekara ta 658 miladiyya yana da kimanin shekara saba'in. Sa'd bn Abu Waqas (RA) ne ya jagoranci sallar jana'izarsa, kuma an binne shi a Jannat al-Baqi, makabartar Musulunci ta farko da aka kafa a Madina.

Rubutawa Muhammad Cisse.

Tarihin "White House" (Fadar Shugabanci Ta Amurka)Fadar White House ita ce wurin zama da wurin aiki na shugaban Amurka. ...
21/12/2024

Tarihin "White House" (Fadar Shugabanci Ta Amurka)

Fadar White House ita ce wurin zama da wurin aiki na shugaban Amurka. Tana a Lamba 1600 Pennsylvania Avenue NW a Birnin Washington, DC , kuma ta kasance wurin zama na kowane shugaban Amurka tun John Adams a 1800. Ana amfani da kalmar "White House" a matsayin ma'ana ga fadar shugaban kasa da masu ba shi shawara.

A cikin White House Akwai dakuna 132, dakunan wanka 35, da Hakanan akwai kofofi 412, tagogi 147, murhu 28, matakala 8, da lifta 3.

White House ko kuma Maison Blanche da farasanci itace fadar shugaban ƙasar Amurka kuma a ciki yake zaune tare da iyalinsa a birnin Washington DC. An gina wannan hamshaƘin gidan a cikin shekaru takwas, wato daga 1792 zuwa 1800. Shugaban ƙasar Amurika na farko ne Georges Washington ya bada kwangilar gina wannan gida.

Ƙurraru ta fannin zanen gini guda bakwai s**a yi takarar zana wannan gida mai alfarma, to sai dai daga ciki, kwamitin da shugaban ya kafa ya gano cewar zanen wani ƙwararren magini mai suna James Hoban ɗan asalin Kasar Ireland shi ne ya fi gamsarwa.

An ɗora tubalin tushe na ginin White House ranar 13 ga watan Oktober na shekara ta 1792. Jimlar kuɗin da aka zuba wurin ginin, a lokacin sun tashi dala Amurka kimanin dubu 233, to sai dai idan aka misalta da darajar Dallar a yanzu an ƙiyasta cewar kuɗin zasu kai kusan dalla miliyan 7.

Shugaban ƙasar Amurka na biyu John Adams, shine ya fara zama a cikin White House ranar 1 ga watan Nowemba na shekara ta 1800. A lokacin da aka gina gidan ana kiran sa kawai fadar shugaban ƙasa. Shugaban kasar Theodore Roosvelt ne ya fara rubuta kalmar White House. Kuma ya fara hakan ne bayan sabon farin fentin da akayi wa gidan sak**akon gobarar da yayi a shekara 1814.

Wannan gobara ta faru cikin yaƙin da aka gwabza tsakanin Amurka da Ingila, (Yakin Neman Yancin Amurka) inda dakarun Ingila s**a kai hari a fadar shugaban ƙasar Amurkan s**a kona ta ƙurmus. Tunda daga shugaban Amurka na biyu John Adams har zuwa shugaba na 46 mai ci yanzu, wato Joe Biden duk wanda ya hau sai ya gudanar da wata kwaskwarima ga fadar White House, to sai dai ya zuwa yanzu kwaskwarima mafi tasiri, itace wadda shugaba Henri Truman yayi, wadda ta ɗauki tsawan shekaru uku daga 1949 zuwa 1952. Gaba ɗaya aka sabinta ofisoshi a wannan lokaci.

Sai dai kuma game da kayan ado da ƙyalliƙyali na cikin gidan, tarihi ya nunar da cewa, matar shugaban ƙasa John Fitzgerald Kennedy ce wanda yayi jagoranci Amurka daga 1961 zuwa 1963 ta ƙayata gidan.

Daga Muhammad Cisse.

Address

Zoo Road Kano
Maiduguri

Telephone

+2347044444645

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Halarci Online Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share