27/07/2023
KA KOYI AIKI KAFIN KA SAMU AIKI: Yanxu kake da Lokaci
Da yawan mutane jira suke sai aiki ya samu sannan su koyi aikin, bawai sun iya aikin ba kafin su nemeshi, kuma ba haka rayuwa take ba, aikin ake fara koyo da sanin yadda yake, sannan a shiga nema, tare da jiran ijaba ta ubangiji tukuna.
Duk wani aiki da kake nema a duniya, to ka koyi duk wani abu da yake da alaka da shi tun kafin kasamu aikin, saboda idan har kasamu aikin baka iya kome a ciki ba, zaka sha mamaki, kuma akwai every tendency na a sallameka baki daya daga aikin.
Kamar misalin masu son aikin NGO, duk wani abu da kasan yana da alaka da Excel, PowerPoint da Word ka koyesu da kyau ka iya, sannan ka san Communication Skills, ka san meye Monitoring and Evaluation, da sauran Management skills, ka koye su, ka karanta su, ka iya, da kyau, tun kafin ka samu aikin.
Ba sai ka samu aikin ba ko ankira interview, sannan zaka nemi koyon abu ba, dayawa suna missing opportunities da yawa, saboda bazai yiyu cikin 1 week ko 2 weeks da akayi fixing na interview dinka ba ka iya duk abunda ake bukata.
Shi yasa dayawa, wasu na samar wa wasu aiki, amma daga karshe, aje interview a cires su, duk da akwai inda da zarar an bada sunanka ka samu kawai, amma ba haka wasu wurarare suke ba, kowa ye yabada sunanka wasu sai sun maka interview, in baka san kome ba, kaga kayi embarrassing kanka, kuma kajawa wanda yabada sunanka abun magana.
Don haka duk me son yayi aiki a ko ina, first of all, learn skills related to the work, sai kajira ikon Allah.
Stay blessed.
Ahmad Aminu Ahmad esq.
+2347066309565
[email protected]