RGG TV

RGG TV We can Watch More Highlight Breaking News on RGG TV Online.com from anny Wehere in the World

Me zaku iya tunawa dashi a shekarar 2023 dake mana bam kwana ?Shekarar Miladiyya ta 2023 na Mana ban kwana. Wasu abubuwa...
30/12/2023

Me zaku iya tunawa dashi a shekarar 2023 dake mana bam kwana ?

Shekarar Miladiyya ta 2023 na Mana ban kwana. Wasu abubuwa sun faru a cikinta...na Al'ajabi da na iftila'in duk sun faru,, Kamar yadda mukayi Hasashen hakan wasu sun tabbata wasu kuma basu tabbata ba...

Haka zamu sake Hasashen wasu a 2024 k**ar yadda muke tsammani zata iya kasan cewa da sauyi mai inganci da kyakkyawan fata garemu da kasarmu bakidaya.... 🙏

Hafizu Balarabe Gusau
30/12/2023

27/10/2023

Watau indai albarka ce ta siyasa sai mutane sun ce Allah ya ɗebewa Dauda Kahutu Rarara Albarka................. Ɗalibai da aka ɗauke a FUG a cikin wata nawa aka ɗaukesu ? Talakawa nawa aka ɗauke a jihar Zmafara da katsina ? A cikin watannan ukku nawa farashin abinci yake a halin yanzu ?

Ka fito fili kace kana tauna tsakuwa dan aya taji tsoro ba sai ka kushe wani ka yabawa wani ba....😉

Hakkin alumma ba zai bari ka samu Albarkar siyasar da kake magana a kai ba ta kare son ra'ayinka a kan a jinginashi da kayi da na sanin....👌

Lallai wannan kam kada mu bari a bar yaranmu a baya wajen wannan rigakafin na Maleria da ya addabemu baji ba gani..........
03/10/2023

Lallai wannan kam kada mu bari a bar yaranmu a baya wajen wannan rigakafin na Maleria da ya addabemu baji ba gani........😉

25/09/2023

Dukkan 'yan takararmu da matsalar tsaron jiha s**ayi Campaign

'yan takarar Governors da 'yan majalisun tarayya da na jihohinmu duk sunyi yakin neman zabe da matsalar tsaron jihar Zamfara, uwa uba Shugaban kasa kuma. Yau zamfara na cikin mawuyacin hali kullum matsalar kwan gaba kwan baya takeyi Zamfara mun zama cibiyar barayain daji a kashe na kashewa ayi garkuwa da dumbin Al'umma kullum a sace na sacewa...😭

Ministan tsaro da Gwamna matukar baku kauda siyasa a gefe daya kun zauna tare da juna kun fuskancin matsalar da kuka ce itace zaku maida gaba a kai ba, lallai shakka babu biyan bukatunku kuke fifitawa fiye da abunda kuka ce zaku maida gaba a kai ke nan............

02/09/2023

A kwai fa 'yar karamar rashin dabara a wajen nan

A Kashe kudi wajen Dinner Ayi Lefe Manyan Akwati, Kuma Akai Amarya gidan Haya😁
U dawo da hankulanmu matasa 👌

Har yanzu muna da sauran lokacinka ai....cikin mulkinka muke ai.... 😉
02/09/2023

Har yanzu muna da sauran lokacinka ai....cikin mulkinka muke ai.... 😉

Abunda zai baka mamaki daga Mutanen garinmu Kano da wasu masu caccakar rashin dacewar Maryam Shetty A lokacin da Shugaba...
04/08/2023

Abunda zai baka mamaki daga Mutanen garinmu Kano da wasu masu caccakar rashin dacewar Maryam Shetty

A lokacin da Shugaba Buhari ke mulki ya ɗauko Dattijon da yace abincin naira 30 ya isa dukkan wani ɗan Najeriya ya ci ya ƙoshi, ya salon jagorancin ministan shi ya tafi damu ?

Amma Hassada ta cika mana ciki makil da rashin son ganin cigaban ƴan uwanmu matasa.. Kaico da halinmu 😥

04/08/2023

Shugaban Najeriya ya nemi Majalisa ta amince masa dan, ƙaƙabawa jam'huriyar Nijar ta kunkumi ciki harda katse musu wutar hasken Lantarkin daga Najeriya

04/08/2023

SHEHU JAHA

KOWA YA TAFI GA MAHAIFIYAR SHI

Wata rana Hatsaniya ta hada Shehu da matarsa, sai matar ta fusata ta shiga daki ta fara tattara kayan ta a jaka, sai Shehu ya shigo ya same ta ya ce: Ina za ki je ? sai ta kalle shi a fusace tace: Gun Mahaifiyata zan tafi...

koda jin Haka

Sai shima Shehu ya jawo jakar shi ya fara tattara kayan sa, sai tace ina kuma za ka ? sai ya ce: nima gun Mahaifiyata zan tafi, sai tace toh idan ka tafi wa zai kula ma da yayanka guda 6 ke nan ?

Sai Shehu yace: ke zaki tafi ga mahaifiyarki Nima zan tafi ga mahaifiyata suma sai su tafi
GUN UWARSU!! kinga Shikenan....👌

Højlund 🆚 Haaland... 👀Oga Mohammed 'Dan India Ace kunyo cefa ne mai k**a da nawa a nan makotana na kauye ?
03/08/2023

Højlund 🆚 Haaland... 👀

Oga Mohammed 'Dan India Ace kunyo cefa ne mai k**a da nawa a nan makotana na kauye ?

Wannan Dokokin da aiwatarwa kawai nan take sunyi dai dai Allah yasa suyi tasiri nan take........ga wadannan Sojojin da s...
30/07/2023

Wannan Dokokin da aiwatarwa kawai nan take sunyi dai dai Allah yasa suyi tasiri nan take........ga wadannan Sojojin da s**a kifar da hannun agogo baya... 😉

16/07/2023

Shawara ga Mai girma Gwamna Dr. Dauda Lawal

Matakin gaggawa kan Matsalar tsaro

Yanayin da ake ciki ya k**ata a dauki matakin gaggawa kan matsalar tsaron dake damu sassan unguwannin birnin Gusau da wasu kewayen Garuruwanmu.....

Misali ko da takaita Zurga-zurga ne daga karfe goma zuwa wani lokacin ya k**ata a aiwatar

Mai girma Gwamna birnin jiha sake yake barayi na shiga a ko yaushe suyi yadda s**a ga dama ya k**ata a dan dauki matakin emergency baya jiran sai an shirya kafin samun hadin kan manyan jami'in tsaron kasar nan irin wannan matakin.

A can baya tsohon Gwamna ya yi aiki da watse tashoshin Lalan da kwanar mai lena da wasu wuraren duk an dan samu saukin barazanar tsaron.. a wannan lokacin a birnin Gusau...

Jami'in tsaro su matsa kaimi wajen fita yawon Patron na dare ba ji ba gani ayi join da duk jami'in cikin matakin gaggawa halin da ake ciki har illah ma sha Allah..

Amma kamewa da yin gum har sai an jira matakin manyan jami'in tsaron kasar nan ba mafita bace, Domin kowa ya san yadda ake maida matsalar da ba a son ganin karshenta tana cigaba da cin wuta babu kakkautawa 👌

Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa a garuruwanmu bakidaya 🤲

Hafizu Balarabe 16/07/2023

30/06/2023

A kwai Matsala fa karin kudin Man nan zuwa dari 700 Shakka babu Al'amura zasu kara dagulewa... 😉

28/06/2023
Zamu tuna dasu Wajen bada Gudunmawar gina kasarmu...
09/09/2022

Zamu tuna dasu Wajen bada Gudunmawar gina kasarmu...

25/07/2022

Ku kalli Wannan Video yadda ake Samun kuddi a saukake a Internet... 👇

'Shugaba Buhari ne ya hana daukar ma'aikata a Najeriya', in ji ɗan majalisaWani ɗan Majalisar Dokokin tarayya a Najeriya...
02/07/2022

'Shugaba Buhari ne ya hana daukar ma'aikata a Najeriya', in ji ɗan majalisa

Wani ɗan Majalisar Dokokin tarayya a Najeriya ya ce akwai guraben aikin gwamnatin tarayya sama da dubu ɗari da ashirin amma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya hana a cike su.

Honorabul Sani Bala Tsanyawa, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Ayyukan gwamnati na Majalisar Wakilan Najeriya ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da BBC Hausa.

BBC Hausa ta rawaito cewa ɗan majalisar ha ce tun a shekarar 2019 ne Shugaba Buhari ya sanar wa majalisar dokoki ɗaukar matakin a lokacin da ya je zaurenta domin gabatar da kasafin kuɗi.

A cewarsa "Lokacin gabatar da kasafin kuɗi da (shugaban kasa) ya kawo wa majalisa, yake faɗa cewa ya dakatar da ɗaukan aiki a ‘mainstream civil service’ - wato ma’aikatan da ke a aiki a ma’aikatu na kwaryar aikin gwamnati."

Ya ce tun da shugaban ƙasar ya sanya wannan haramci ba a ƙara ɗaukar aiki ba a irin waɗannan ma’aikatu.

Sai dai a cewarsa an bai wa wasu ma'aikatun gwamnatin damar daukar ma'aikata saboda dalilai masu ƙarfi.

Bangarorin da aka yi wa rangwamen sun haɗa da na tsaro da lafiya - sak**akon barkewar annobar korona.

Ya kara da cewa “Daga shekara biyar a baya zuwa yau, bincikenmu ya nuna cewa ma’aikata dubu ɗari da talatin ne s**a bar aiki.”

“Wasun su ko dai sun mutu, wasu kuma sun yi ritaya, wasu kuma sun samu wani aikin na daban sun bar na gwamnatin tarayya.”

Ya ce amma a tsawon waɗannan shekaru biyar bayan sanya haramcin, mutum dubu shidda da dari bakwai ne kacal gwamnatin tarayya ta ɗauka aiki.

Sannan ya ce duk da haka har yanzu yawan guraben na kara yawa saboda a kodayaushe akan samu ma’aikatan da ke mutuwa ko ajiye aiki, to amma har yanzu ba a cire wannan haramci ba.

Sai dai ya ce akwai wasu hukumomin da a wani lokaci s**an dauki ma’aikata, k**ar babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar sadarwa ta kasa (NCC), amma ba a ma’aikatun kwaryar aikin gwamnati ba, waɗanda a turance ake kira ‘ministries’.

Sai dai kuma Sani Bala Tsanyawa ya ce sau da dama kwamitinsa ya gabatar da kudiri a zauren majalisar wakilai domin ganin an cire haramcin da aka sanya kan ɗaukar aikin amma lamarin ya ci tura.

Ya ce “Ni shugaban kula da harkokin gwamnati na majalisar tarayya tare da wasu mambobin majalisar mun kawo kuduri sau daya zuwa biyu kan cewa a ɗage haramcin ɗaukar aiki.”

Bala Tsanyawa ya ce majalisa ta yi kokarin ganin an kawar da haramcin ta hanyar kiran hukumar kula da ma’aikata ta tarayya da kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya domin bayar da bahasi.

A cewar sa hukumar kula da ma’aikata ta tarayya takan ce ba laifinta ba ne, domin babu mai ikon fitar da gurbin ɗaukar aiki a gwamnatin tarayya sai shugaban ma’aikata na gwamnatin tarayya.

Ita kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya takan ce ba laifinta ba ne domin shugaban kasa ne ya sa haramcin ɗaukar aikin, ba ita ba.

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsanancin matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa.

Kiyasi na hukumar kididdiga ta Najeriyar ya nuna cewa kashi 42.5 cikin ɗari na matasan kasar ba su da aikin yi.

Haka nan kuma kashi 21 cikin ɗari na matasan da suke aikin ba a biyan su albashin da ya taka kara ya karya.

24/04/2022

Mata Gareku

03/04/2022

KO YA HALARTA ZUBAR DA CIKI ?

DAN SAMUN DAMAN YIN AZUMI SHEIKH IBRAHIM SALEH ALHUSSAINI

27/10/2021

Address

Lagos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when RGG TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to RGG TV:

Videos

Share

Category


Other TV Channels in Lagos

Show All