Bauchi NEWs.com

Bauchi NEWs.com LABARAI DA DUMI DUMI DA GAWAKILANMU DAGA SASSAN KASANNA

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin dokar rancen dalibai, inda ya tanadi hukuncin zaman gidan gy...
04/04/2024

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin dokar rancen dalibai, inda ya tanadi hukuncin zaman gidan gyaran hali ga duk wanda ya kasa biyan bashin.

Game da batun biyan bashin, dokar ya nuna cewar mutum zai fara biyan bashin ne da zarar ya samu aiki kowane iri ne.

A cewar bayanan dokar, asusun ba zai fara shirin karbar bashin ba har sai bayan shekaru 2 da kammala aikin hidimar kasa.

Bayanan sun kara da cewar, wanda ya ci gajiyar rancen na iya neman karin wa'adi ta hanyar yin rantsuwa a kotu cewar bai samu aiki kowane iri ba kuma baya samun kudin shiga ta ko ina.

DA DUMI DUMIHukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da karin kudin wuta. Daga yanzu duk wanda ke biyan nai...
04/04/2024

DA DUMI DUMI

Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da karin kudin wuta.

Daga yanzu duk wanda ke biyan naira 66 a kw/h zai biya naira 225 a kowane kw/h daya.

Dangote ya fara sayar da litter mai ga Duloli lita 1 kan naira 1,225___________Babban kamfanin Matatar Ɗanyen Mai ta Ɗan...
04/04/2024

Dangote ya fara sayar da litter mai ga Duloli lita 1 kan naira 1,225
___________

Babban kamfanin Matatar Ɗanyen Mai ta Ɗangote Rifirenery, ta fara sayar da tataccen fetur ga ‘yan kasuwar cikin gida a ranar Talata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa an fara sayar da fetur ɗin ne a ranar Talata, tare da ruwaito bayanin daga bakin Babban Daraktan matatar, Devekumar Edwin.

Wannan gagarimar nasara dai wasu dillalan fetur na cikin gida sun tabbatar da hakan su ma, k**ar yadda ƙungiyar masu sayar da fetur a Najeriya s**a bayyana.

“Mu na da wadataccen fetur a ƙasa. Ana ci gaba da lodi da jigilar fetur zuwa wurare daban-daban ta ruwa da kuma ta kan titina.
“Jiragen ruwa ga su nan birjik sun yi layi, ana ci gaba da loda masu fetur ɗaya bayan ɗaya. Banda fetur kuma ana lodin man da jiragen sama ke amfani da su.

“Jiragen ruwa sun yi lodin lita miliyan 26, amma dai muna ƙoƙarin mu ga mun samu jiragen da zasu iya kwashe lita miliyan 37, domin sauƙaƙa jigila,” Haka Edwin ya bayyana wa Reuters.

Da ya ke magana kan fara sayar da mai ga ‘yan kasuwar cikin gida, Shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce sun amince za su riƙa sayen za a riƙa sayar masu da man dizal duk lita 1 kan 1,225 ($0.96), bisa yarjejeniyar cewa tunda da yawa za su riƙa saye.
Ya ce mambobin ƙungiyar IPMAN su na da gidajen mai kimanin 150,000 a faɗin ƙasar nan.

A halin yanzu ƙananan ‘yan kasuwa da masu daffo-daffo na nan na ƙoƙarin samun takardun yarjejeniyar karɓar basuss**a daga bankuna, domin su fara sayen mai daga Matatar Ɗangote.
Matatar Ɗangote ta fara tace dizal da man jiragen sama tun a cikin Janairu.

Yaya kuka kalli farkon tashin farashin na Dangote
?

Da dumi'dumi: Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sayar da jiragen saman shugaban kasa guda uku mallakin Nageriya Sak**ak...
01/04/2024

Da dumi'dumi: Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sayar da jiragen saman shugaban kasa guda uku mallakin Nageriya Sak**akon Tsadar kayan kula da Jirgin ya yi yawa.

Za a sayar da jiragen sama guda uku a cikin Jiragen Shugaban Kasa (PAF) don rage yawan kudin tafiyar da gwamnati.

A cewar jaridar The Nation, akwai jirage 10 a halin yanzu a Tawagar rundunar shugaban kasa - jet shida da jirage masu saukar ungulu hudu - wadanda za a rage su zuwa bakwai idan matakin da aka tsara ya tabbata.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa, rumbun adana abinci da wasu bata gari s**a daka wa wawa mallakin kamfanin Dan...
01/04/2024

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa, rumbun adana abinci da wasu bata gari s**a daka wa wawa mallakin kamfanin Dangote ne, ba na gwamnati ko na 'yan kasuwa ba ne k**ar yadda aka ruwaito tun da fari. Sakataren yada labarai na gwamnan jihar, ya bayyana wa DW cewa yanzu haka ana gudanar da taron gaggawa domin shawo kan lamarin.

Fadakarwa ta musamman ga yan uwa mausu azumi to ga goman karshe tazo
01/04/2024

Fadakarwa ta musamman ga yan uwa mausu azumi to ga goman karshe tazo

An fasa rumbunan kayan abinci na gwamnati da ‘yan kasuwa a Birnin Kebbi.An ruwaito cewa, fusatattun mutanen da s**a sha ...
01/04/2024

An fasa rumbunan kayan abinci na gwamnati da ‘yan kasuwa a Birnin Kebbi.

An ruwaito cewa, fusatattun mutanen da s**a sha karfin jami’an tsaro sun wawushe buhunhunan kayan abinci tare da buga wawa kan wata mota makare da kayan hatsi.

Ta wace hanya kuke ganin za a magance wannan matsala ta wawushe kayan abinci da a mafi yawan lokuta matasa ne ke yi?

Masjit Othman bin affan dake B, S, A, D, D, P watau gidan gona Bauchi ta gabatar da shan ruwan watau iftar a ran 19 ga r...
30/03/2024

Masjit Othman bin affan dake B, S, A, D, D, P watau gidan gona Bauchi ta gabatar da shan ruwan watau iftar a ran 19 ga ramadan shekara ta 1445AH karo NA biyu Karin ya kayatar kwarai tareda fatan sauran masallatai zasuyi koyi

ALBISHIR GA MAHAJJATA NA JIHAR BAUCHI. Mai girma Gwamnan jihar Bauchi ya biya 50% ga dukkanin mahajjata. Cikin kudin da ...
29/03/2024

ALBISHIR GA MAHAJJATA NA JIHAR BAUCHI.

Mai girma Gwamnan jihar Bauchi ya biya 50% ga dukkanin mahajjata. Cikin kudin da hukumar alhazai ta kara.

Hukumar alhazai ta ta kasa ta kara 1,918,032.9 Kusan naira miliyan biyu kenan. Yanzu mai girma Gwamna ya biya kaso 50% Manitaya zasu biya 959,016.45 mai Makon naira 1,918,032.9 da aka kara.

Wanda s**a riga s**a cika za'a dawo musu da kudin su wanda s**a tafi neman cuko to su sani Gwamna ya biya musu rabi. KO mezakuce

Kasurgumi danfashin dajinna DOGO GIDE YA MUTU Kasurgumin Dan Ta’adda Dogo Gide Ya Bakwanci Lahira.27/03/2024.Kasurgumin ...
28/03/2024

Kasurgumi danfashin dajinna DOGO GIDE YA MUTU

Kasurgumin Dan Ta’adda Dogo Gide Ya Bakwanci Lahira.

27/03/2024.

Kasurgumin Dan ta’adannan wanda akafi sani da Dogo Gide Ya Gamu da ajalinsa a sanadiyar mummunar rauni da yaji a dauki ba dadi da s**ayi da Sojojin Rundunar Operation Hadarin Daji a dajin Madada dake Karamar Hukumar Mulkin Maru ta Jahar Zamfara K**ar Yadda Jaridar Smart News s**a Ruwaito.

Jaridar Smart News ta ruwaito cewa Dogo Gide Ya bankwanci Lahira ne a wata Asibiti dake Unguwar Mabera ta Jahar Sokoto inda ake zargin wani Jami’in Tsaro Yakai Dan Ta’addar domin yin jinya a sanadiyar munanan raunukan da Dan Bindigar yaji yayin musayar wuta s**ayi da Jami’an Tsaro. Bayan mutuwarsa munsamu labarin binne Dan Ta’addar a Kauyen Dandalla k**ar Yadda Smart News s**a ruwaito.

Hakazalika An ruwaito cewa anyi nasarar K**a wannan Jami’in tsaro din gudanar da binciken alakarsa da nemawa wannan Azzalumi Magani.

Muna Rokon Allah Ya Kara Bawa Jami’a Tsaronmu Nasara.

ENGR ABBA KABIR YUSUF YA RAGEWA ALHAJAN JAHAR KANO KUDIN AIKIN HAJJI NAIRA DUBU DARI BIYAR  ( 500,000)        Sak**akon ...
28/03/2024

ENGR ABBA KABIR YUSUF YA RAGEWA ALHAJAN JAHAR KANO KUDIN AIKIN HAJJI NAIRA DUBU DARI BIYAR ( 500,000)

Sak**akon karin kudi har kimanin Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) da Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta yi akan kowacce kujerar aikin Hajji, ina farin cikin sanar da dukkanin maniyyatan jihar Kano cewar Gwamnatin Kano ta musu ragin Naira dubu dari biyar (500,000) akan kowacce kujera.

Wannan ragi da muka samar a yanzu haka na nufin duk wani maniyyaci da ya biya Naira miliyan hudu da dubu dari bakwai (4,700,000) kudin babbar kujera da wadanda s**a biya Naira miliyan hudu da dubu dari biyar (4,5000,000) kudin karamar kujera za sucika Naira miliyan daya da dubu dari hudu (1,400,000) ne kacal maimakon Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000).

GWAMNAN BAUCHI YA KARRAMA ALUMMAN GARIN DAƁE DA BUHU 200 NA SHINKAFA DA GERO. BAYAN SUN KYAMACI SACE KAYAN ALUMMAHGwamna...
28/03/2024

GWAMNAN BAUCHI YA KARRAMA ALUMMAN GARIN DAƁE DA BUHU 200 NA SHINKAFA DA GERO. BAYAN SUN KYAMACI SACE KAYAN ALUMMAH

Gwamnatin jihar Bauchi ta baiwa al’ummar garin Daben kasuwa da ke karamar hukumar Ganjuwa buhunan shinkafa da gero buhu 200 domin jin dadin kishin kasa da s**a nuna

Matakin dai ya biyo bayan wani yanayi da aka rika yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna yanda wata mota dauke da kayan abinci da ta fadi kusa da kauyen kuma jama’a s**a taimaka aka kwashe kayan ba tare da kwasar Ganima ba k**ar yadda ake yayi hakan a halin yanzu a Nijeriya.

A wani al’amari da ba a taba ganin irinsa ba a cikin ‘yan kwanakin nan, mazauna garuruwan Najeriya da dama sun yi ta yin awon gaba da dimbin kayan abinci da manyan motoci ke debowa na kasuwan ci da kuma fasa runbunan abinci a ‘yan kwanakin nan, a sassan Nijeriya

Saboda halin yunwa da fushi kan tashin farashin kayan abinci yasa wasu sata.

Da yake mika buhunan shinkafar da aka bayar, Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir wanda ya samu wakilcin kwamishinan al’adu da yawon bude ido na jihar, Abdu Hassan Said gwamnatin jihar Bauchi ta yabawa al’ummar Daben kasuwa bisa wannan aiki na rashin son kai. Da s**a nuna.

Gwamnan ya yabawa al’ummar kasuwar Daben musamman matasa da s**a nuna koshin kasar su da tsoron Allah s**a sanya aka rubuta sunan karamar hukumar su da jihar Bauchi da tawada zinare duba da yadda ake wawure kayan abinci a fadin kasar nan. Amma su s**a gyama ci sata.

Da yake karbar kayan abincin Sarkin Daben Kasuwa Malam Sanusi Sale ya gode wa Gwamnan bisa wannan karimcin ya kara da cewa Al'umma na da tarihin rashin laifi inda mutane ke zaune lafiya da juna.

Ya yi amfani da kafafen yada labarai wajen yin kira ga gwamnati da ta samar wa al’umma abubuwan more rayuwa k**ar ruwan makarantar sakandare, wutar lantarki da daidaikun cibiyoyin kiwon lafiya. A yankin.

DOMIN CIKA ALKAWARI: Gwamna Uba sani ya kaddamar da Gina Garin Tudun Biri wanda sojojin sama s**a Jefawa Bom bisa kuskur...
28/03/2024

DOMIN CIKA ALKAWARI: Gwamna Uba sani ya kaddamar da Gina Garin Tudun Biri wanda sojojin sama s**a Jefawa Bom bisa kuskure

Gwamnan jihar kaduna ya ce Domin cika alkawarin da muka yi na sake ginawa al’ummar Tudun Biri tare da rage radadin jama’a bayan harin da jiragen yaki mara matuki na sojoji s**a yi a yau na kaddamar da ayyukan k**ar haka:

- Gina titin alphalt 5.525 daga unguwar Tudun Biri zuwa titin filin jirgin sama.

- Gina Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko a Tudun Biri, da;
- Gina Cibiyar Samar da Fasaha ga al'umma.

Tun bayan harin da jirgin yaki mara matuki na soja, mun tallafa wa wadanda abin ya shafa, iyalansu da sauran al’umma da kayayyakin agaji ta hanyar KADSEMA. Taimakon likitanci da zamantakewa ga wadanda abin ya shafa da iyalansu suna ci gaba da gudana.

Haka kuma aiwatar da ayyukan Tudun Biri ya yi daidai da ajandar mu na kawo sauyi a karkara wanda ke da nufin dinke barakar da ke tsakanin al’ummomin karkara da birane, da farfado da tattalin arzikin karkara, samar da ayyukan yi da samar da sabuwar rayuwa ga al’ummarmu.

Gwamnan jihar Bauchi Sen Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi ya amince da sake nada Imam Abdurrahman Ibrahim Idris a ...
27/03/2024

Gwamnan jihar Bauchi Sen Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi ya amince da sake nada Imam Abdurrahman Ibrahim Idris a matsayin babban sakataren gudanarwa da kuma Alh. Nuru Adamu Jumba a matsayin shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Bauchi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Kwamared Muktar Gidado, a takardan da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Barr Ibrahim Mohammed Kashim.

Sanarwar ta bayyana amincewar mambobin kwamitin da s**a hada da: Imam Babangida Sulaiman, Mal. Mahmood Isa Duguri, Alh. Kani Dandija, Imam Hassan Zango, Mal. Baba Ahmed Balarabe da Sheik Hanza Zwall.

Sauran membobin sun hada da Sarkin Mararraba, Faisal Muhammad Burga, Barira Yau, Alh. Sulaiman Mohammad (Hakimin Lere), Alh. Ibrahim Samaila (Hakimin Warji) da Mal. Mustapha Mai kwano.

Gwamnan ya bukace su da su yi amfani da fasaharsu daban-daban wajen samar da wani muhimmin mataki na tabbatar da dorewar aikin Hajji a jihar Bauchi.

Sanarwar ta kuma yi kira gare su da suyi kokarin yin dai-dai da kudirin gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na tsarin ajandar ci gaban jihar Bauchi.

Muhammad Sani Yunusa
jami'in yada labarai na hukumar Alhazai

Wasu 'yan fafutika a Nijar da ke goyon bayan sojoji sun fara kalubalantar janar Tchiani kan rashin tsayar da wa'adin rik...
27/03/2024

Wasu 'yan fafutika a Nijar da ke goyon bayan sojoji sun fara kalubalantar janar Tchiani kan rashin tsayar da wa'adin rikon kwarya watanni takwas bayan hambarar da gwamnatin dimokuradiyya.

Dala Ta Yi Muguwar Faduwa A Safiyar Yau, Inda Ake Sayar Da Ita Naira 900 Zuwa Dubu Daya A Abuja
27/03/2024

Dala Ta Yi Muguwar Faduwa A Safiyar Yau, Inda Ake Sayar Da Ita Naira 900 Zuwa Dubu Daya A Abuja

Dole ne mu dauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda – TinubuShugaban kasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da a...
27/03/2024

Dole ne mu dauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “ayyukan da ba su dace ba” da masu garkuwa da mutane ke aikatawa a fadin kasar nan, yana mai cewa wadanda ke da hannu a irin wadannan munanan laifuka dole ne a kawo karshen su.

Shugaban ya bayyana haka ne a jiya ranar Talata a liyafar cin abinci na watan Ramadan tare da mambobin ma’aikatan shari’a na tarayya karkashin jagorancin Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Mai shari’a Olukayode Ariwoola.

Tinubu, wanda ya sake sabunta kudirin gwamnati na fatattakar ‘yan fashi, ya ce wadanda s**a koma sace yara matsorata ne, wadanda ba za su iya tinkarar karfin sojojin Najeriya ba.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da matakin a zaman majalisar na yau bayan sauraro...
13/03/2024

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da matakin a zaman majalisar na yau bayan sauraron ƙorafin da aka shigar kan hirar Sanata Ningi da Sashen Hausa na BBC inda ya yi zargin cushe a kasafin kuɗin ƙasar.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya tabbatar da ganin watan Ramadan na shekarar 144...
10/03/2024

Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya tabbatar da ganin watan Ramadan na shekarar 1445 bayan hijira.

Cikin wani saƙo da ya fitar a daren Lahadi, Sarkin Musulmin ya ce an tabbatar da ganin watan a sassan ƙasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargadi kungiyoyin kwadagon Najeriya a kan yajin aikin da s**a yi a farkon makon nan bisa m...
29/02/2024

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargadi kungiyoyin kwadagon Najeriya a kan yajin aikin da s**a yi a farkon makon nan bisa matsin rayuwa da al'umma s**a shiga. Sai dai shugaban ya ce ba gudu ba ja da baya a kan matakan da ya dauka, ya kuma bukaci al'ummar Najeriya da su kara hakuri komai zai daidaita nan da wani lokaci.

Shugaban tarayyar Najeriya ya amince da rahoton Oronsaye wajen hade wasu ma’aikatu wuri guda tare da rushe wasu Shugaban...
27/02/2024

Shugaban tarayyar Najeriya ya amince da rahoton Oronsaye wajen hade wasu ma’aikatu wuri guda tare da rushe wasu

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da aiwatar da rahoton Oronsaye wanda ya bayar da shawarar hade wasu hukumomin gwamnati wuri guda tare kuma da rushe wasu.
Shugaban ya amince da wannan shawara ce yayin taron majalissar zartarwar kasar da ya jagoranta a ranar Litinin 26 ga wata a fadarsa dake birnin Abuja.

Sojojin Nijar sun karya farashin shinkafaA yanzu za a sayar da buhu mai nauyin kilograme 25 na shinkafa a jika 13 da rab...
22/02/2024

Sojojin Nijar sun karya farashin shinkafa

A yanzu za a sayar da buhu mai nauyin kilograme 25 na shinkafa a jika 13 da rabi na CFA a birnin Yamai, Jika 13 da dala 135 a Dosso, jika 13 da dala 165 a Tahoua, Jika 13 da dala 185 a Maradi, Jika 14 daidai na CFA a Damagaram, Jika 14 da dala 75 a Diffa, Jika 14 da dala 25 a Agadez sai kuma jika 13 da dala 130 na CFA a Tillabery.

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada mahimmancin addu’o’i wajen ginuwar kasa, inda ya tabbatar da kud...
16/02/2024

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada mahimmancin addu’o’i wajen ginuwar kasa, inda ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa wajen tallafawa dukkan wasu hidin-dimu da s**a shafi addinai.
Ya tabbatar da hakan ne a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin tawagar kungiyar Tijjaniyya na duniya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass, ya ce malaman addinai na bayar da gagarumar gudummowa wajen samun nasara gwamnatin sa.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su koma ga Allah ta hanyar rike amanar juna da kishin kasa da kuma dauke kai daga duk wani abu da yake da nasaba da cin hanci ko rashawa.
Ya shaidawa bakin nasa cewa gwamnati na bakin kokarin cimma burinta na wadata kasa da abinci ta hanyar kawo sauye-sauye a harkar noma domin ganin Najeriya ta kasance mai dogaro da kanta wajen samar da abinci da kuma fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje. Ya ce a halin yanzu ma gwamnati ta yi odar dubban motocin noma domin samun damar noman amfani mai yawan gaske.
“Aikin da muke yi a halin yanzu ya yi daidai da koyarwa da muka samu daga manzon Allah, Annabi Muhammadu S-A-W, lura da jin dadin rayuwar al’umma, wanda ta sa za mu samarwa dukkannin asibitoci kayayyakin aiki na zamani, bayar da horo ga likitoci, ta yadda za su kula sosai ga marasa lafiya, haka kuma za mu tabbatar da ganin shirinmu na inshorar lafiya ya kai ga kan kowanne dan kasa.”
A kan batun aikin hajji kuwa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamantinsa a shirye take wajen goyon bayan duk wani tsari da aka tabbatar zai kawo sauki ga alhazan kasar a yayin aikin hajjin bana.
Da yake jawabinsa jagoran tawagar kungiyar ta Tijjaniyya na duniya Sheik Mahe Niass yabawa shugaban kasar ya yi bisa kokarin da yake yi a ko da yaushe wajen tabbatar da tsaro da hadin kan kasa.

Rikakken Dan Bindiga Kachal Duna Tagirke Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro A Jihar SokotoJami'an tsaro su samu nasarar k**a ...
15/02/2024

Rikakken Dan Bindiga Kachal Duna Tagirke Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro A Jihar Sokoto

Jami'an tsaro su samu nasarar k**a ƙasurgumin dan ta'addan da ya addabi Gabashin jihar Sokoto mai suna Kachalla Duna.

Alhamdulillah wannan dan tsakanin dai labarai masu daɗi ake ta samu dangane da abinda ya shafi matsalar rashin tsaro, muna Adduar ayi masu hukunci dai dai da abinda suke aikatama Al'umma bayan an kammala tatsar bayanai daga wurin su

Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba K Yusuf. Yace ya k**ata sauran gwamnoni su yi koyi da halin sa na ...
15/02/2024

Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba K Yusuf. Yace ya k**ata sauran gwamnoni su yi koyi da halin sa na yaki da yunwa.

Shugaban ya shawarci Gwamnonin da su yi koyi da Jihar Kano wajen tunkarar matsalar tara kayan abinci da ‘yan kasuwar ke yi don cin riba. Ya umurci Sufeto-Janar na ‘yan sanda, mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, da DSS da su sanya ido a kan rumbunan da wasu ke adana kayan abinci a fadin kasar nan duk domin cin riba da ‘yan kasuwa ke yi.

15/02/2024

DA DUMI DUMI

Rahotanni da muka samu daga jihar Kano na nuni da cewar Hukumar Hisba ta samu nasarar cafke shahararriyar matashiyar nan yar TikTok mai suna Ramlat princess.

Wacce ake zargin ta abaya bayan nan da yin wani bidiyo ashafin TikTok tana bayyana cewa duk namijin da zai aure ta sai ya auro mata wata matar wacce zasu ringa yin latata da ita.

A cikin wannan makon ne hukumar ta Hisbar ta samu nasarar kame matashiyar yar TikTok din nan Murja Ibrahim Kunya, wanda alkalin kotun shari'ar musulinci dake zama a unguwar PRP ta aike da ita zuwa gidan yari.

15/02/2024

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kafa hukumar da za ta rinka daidaita farashin kayayyaki, a wani mataki na rage karuwar...
15/02/2024

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kafa hukumar da za ta rinka daidaita farashin kayayyaki, a wani mataki na rage karuwar hauhauwar farashin kayan abinci a kasar.
Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja yayin wani babban taron masu ruwa da tsaki na tsawon yini biyu da aka shirya a kan sauyin yanayi, tsarin samar da abinci da kuma alkinta albarkatu.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mataimakin shugaban kasan ya ce idan an samar da hukumar, ita za ta kasance da alhakin fito da tsare tsaren daidaita farashin kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi, har ila yau za ta rinka kula da runbunan ajiyar kayan abinci mallakin gwamnati.
Ya ci gaba da cewa, wannan mataki da za a dauka daya ne daga cikin sabbin sauye-sauyen manufofin gwamnati na tabbatar da wadatar abinci da kuma ruwan sha ga ‘yan Najeriya cikin sauki.
“Gwamnatin tarayyar ta himmatu sosai wajen taimakawa kananan manoma ta hanyar shirye-shiryen bayar da tallafi daban daban domin dai karfafa musu gwiwar noman abinci, yin haka zai kasance wata hanya da za ta tabbatar da farfado da filayen noma.”
Mataimakin Shugaban kasar ya ce a yanzu haka akwai sabbin filaye masu fadin hekta dubu dari 5 wanda za a yi amfani da su wajen noman abinci, haka k**ar yadda ya ce zai yi matukar tasirin gaske ga wadatuwar abinci a kasa baki daya.
Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da da cewa, gwamnati tana hada kai da kamfanonin gine-gine domin su gudanar da akin sare dazuzzuka, ta yadda za a samu damar yin noma a cikin su.
A kan kalubalen tsaro kuwa wanda ya yi sanadin hana dubban manoma komawa gonakinsu, mataimakin shugaban kasar ya shaidawa mahalarta taron cewa,
“Ina son na ba ku tabbacin cewa, za mu yi amfani da matakan tsaronmu wajen kare gonaki da manoman kansu, ta yadda manoman za su samu damar komawa gonakinsu ba tare da fargabar za a kai masu hari ba.

Mai girma Gwamna jihar Bauchi ya Kaddamar da Gyaran Titin Dindima mai nisan kilomita 29 daga Yashi zuwa MainamajiGwamnan...
10/02/2024

Mai girma Gwamna jihar Bauchi ya Kaddamar da Gyaran Titin Dindima mai nisan kilomita 29 daga Yashi zuwa Mainamaji

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen rage radadin da ake ciki ta hanyar gina da gyara hanyoyi a karkara da birane, domin saukake sufurin fito da kayan Noma

Sannan yayi kira ga ‘yan kwangila da su tabbatar da kammala dukkan ayyukan da aka bayar domin amfanin ‘al'ummar yankin dama jihar Bauchi baki daya.

Ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da yake kaddamar da aikin gyaran hanyar Dindima mai tsawon kilomita 29 daga Yashi zuwa Mainamaji a
Da ya shafi yanki Bauchi da Alkakeri.



Mai girma Gwamnan yace aikin idan an kammala aikin zai inganta harkokin noma wanda wani bangare ne na manyan abubuwan da gwamnatin sa ta sa a gaba.

Taron ya samu halartar mai martaba Sarkin Bauchi, HRH Rilwanu Suleiman Adamu, kwamishinan ayyuka da sufuri da kuma na maadanai Da kuma shugaban riƙo na kananan hukumomin Bauchi.

Kakakin Soji: Harin jirgin yakin Amurka maras matuki a Iraki ya ingiza kawo karshen kawancen aikin soji da Amurka ke jag...
10/02/2024

Kakakin Soji: Harin jirgin yakin Amurka maras matuki a Iraki ya ingiza kawo karshen kawancen aikin soji da Amurka ke jagoranta
Gwamnatin Iraki ta fada jiya Alhamis cewa, harin da jirgin yakin Amurka mara matuki ya kai a gabashin birnin Bagadaza da yammacin Laraba ya sanya gwamnatin Iraki matukar bukatar kawo karshen ayyukan dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta.
Jirgin dai mara matuki ya yi ruwan bama-bamai kan wata motar jigilar harkar wasannin ta dakarun Hashd Shaabi a unguwar al-Mashtal, inda ya kashe a kalla mutane uku, ciki har da Abu Baqir al-Saadi, kwamandan Kataib Hezbollah, wata kungiya mai dauke da mak**ai da Iran ke marawa baya a Iraki mai alaka da dakarun Hashd Shaabi.
Kakakin sojan firaministan kasar Iraki Yahya Rasoul, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sojojin Amurka sun sake yin wani kisan gilla a tsakiyar wata unguwa a birnin Bagadaza.
Rasoul ya ce, "Wannan ta’adin ya sa gwamnatin Iraki, fiye da kowane lokaci, ke bukatar kawo karshen aikin kawancen kasa da kasa, wanda ya zama sanadin rashin zaman lafiya ga Iraki.

Address

Ahmadu Bello Way Bauchi
Lagos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bauchi NEWs.com posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bauchi NEWs.com:

Videos

Share

Category


Other TV Channels in Lagos

Show All