15/06/2020
FALALAR ZIKIRI
Allah Madaukakin Sarki ya ce:
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِ
Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni.
Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152].
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً
Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran.
Ya ku wadanda s**a yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41).
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً
Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman.
Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35]
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ وَلاَ تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna.
Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205].
Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, k**ar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa k**ar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).)
Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? S**a ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)
Kuma ya ce: "Allah madaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki daya zan kuance shi tsawon gaba guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa".( Bukhari (8/171), da Muslim (4/2061). Lafazin ruwayar na Bukharine.)
Daga Abdullahi Ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce; Ya Ma'aikin Allah! Shari'o'in Musulunci sun yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna wani abu da zan yi riko da shi. Ya ce: "Ku harshenka ya gushe face yana danye daga ambaton Allah". (Tirmizi (5/458). Da Ibn Majah (2/1246). Duba Sahihul Tirmizi (/139), da Sahih Ibn Majah (2/317).)
Kuma mai tsira da amincin Allah yace; "Wanda ya karanta harafi daya daga littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki daya saboda shi, kuma dukkan kyakkyawan aiki daya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cew Alif Lam Mim harafi ba ne. A'a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne".( Tirmizi (5/175) Duba Sahihul Tirmizi (3/9), da Sahihul Jami'us Sgir (5/340).)
Kuma daga Ukbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai yace; "Wane ne daga cikinku zai so ya fi kullum da safe zuwa koramar Budhan ko Akik, ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba ko yanke zumunta?" Muka ce: muna son haka. Ya ce; "Dayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah Mabuwayi Mai Daukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku, ayoyi hudu sun fi masa taguwa hudu, da kwantankwacin adadinsu na rakuma". (Muslim (1/553)