Faruq Sani Kudan tv news

Faruq Sani Kudan tv news Wannan shifi dan ciga da gudanar da ayyukan da s**a shafi Harka ne da kuma tallafawa al'umma wajan

14/07/2023
Jagoran Shiriya 🌹🌹
26/06/2022

Jagoran Shiriya 🌹🌹

07/05/2022

Assalamu alaikum yan uwa insha Allahu k**ar yadda muka saba kawomuku abubuwa cikin wannan Shafi to zamudawo saka makon wata matsala da tafaru kwana biyu insha Âlláh zamudawo muɗora daga inda muka tsaya.

Wassalam

17/04/2022

Assalamu alaikum 'yan uwa Barka da shan ruwa Allah Ta'ala ya karbi ibadunmu 🌹

10/04/2022

YANA DAYA DAGA CIKIN MALAMAI NA :

__Yahaya Raiyan jungle

“ Shima yana ɗaya daga cikin mutane da s**a Ilimantar, faɗakarwa, Nishaɗantawa. Yana daga cikin su ya bani ilimi sosai akan abin da ake kira da ɗaukar ( rufortas) sanan kuma ya nunamin hanyar da ake canza murya wato canza magana daga wani salo, zuwa wani salo.”

Kana ɗan Jarida abin kunya ne ace baka da wani salo, wanda za a ce kana amfani da shi wajan kawo rufortas. Inda ya ke min duk inda kaje kaga ana wani abu matsayinka na ɗan Jarida? To kazura ido sosai kaga maike wakana awannan wajan. Kasan shi maiɗaukar ' rufotas ' kasan shi duk inda yake bashi da gaskiya saboda shi ɓarawun labari ne. Yanzu ya ɗauka yanzu, ya sakashi akafar sada zumunta.

“ Haƙiƙa na amfanu da karatuntasa sosai. Ya koyar da ni salo, daban-daban kuma na godasu kuma naga amfaninsu, Allah Ta'ala ya sakawa da malam da alheri.”🌹

Shi: Yahaya Raiyan jungle, indai kana bibiyar gidajen (Radiyo) haƙiƙa zakajishi saboda shi babban ma'aikacin gidan radiyo kuma mai sanarwa ta siyasa ko biki kowata tallah idan wani kamfanin yana so, ko masu shirin fim, da sauransu.

Masha Allah malam ina godiya sosai ..

_FFaruq Sani KudanSFaruq Sani KudanKFaruq Sani Kudan

𝑻𝑨𝑭𝑺𝑰𝑹𝑰𝑵 𝑨𝑳-𝑸𝑼𝑹'𝑨𝑵𝑰 𝑴𝑨𝑰 𝑮𝑰𝑹𝑴𝑨 𝑨𝑹𝑨𝑵𝑨 𝑻𝑨 𝑩𝑰𝒀𝑼 𝑨 𝑫𝑨'𝑰𝑹𝑨𝑹 𝑲𝑼𝑫𝑨𝑵'Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem na Da'irar Kudan; ...
02/04/2022

𝑻𝑨𝑭𝑺𝑰𝑹𝑰𝑵 𝑨𝑳-𝑸𝑼𝑹'𝑨𝑵𝑰 𝑴𝑨𝑰 𝑮𝑰𝑹𝑴𝑨 𝑨𝑹𝑨𝑵𝑨 𝑻𝑨 𝑩𝑰𝒀𝑼 𝑨 𝑫𝑨'𝑰𝑹𝑨𝑹 𝑲𝑼𝑫𝑨𝑵

'Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem na Da'irar Kudan; sunshiga rana ta biyu cikin jawabin AL-ƙur'ani wanda wakilin 'yan uwa yake gudanarwa dukshekara Shaikh Muhammad Junaidu sani.

Malamin ya yi jawabi acikin Al-qur'ani mai tsarki inda ya taɓa ɓangare daban-dadan acikin Al-qur'ani da musalai dan Ilimantar da al'umma yadda mashinmancin azumin watan Ramadan ya ke.

Kudan media Forum
1/1443-pri 01/04/2022

JARIDA DON KARUWAR MUSULMI, AL-MIZAN TA FITO!Jaridar Al-Mizan bugu na 1541 ta fito, inda take cike da ingantattun rahoto...
24/03/2022

JARIDA DON KARUWAR MUSULMI, AL-MIZAN TA FITO!

Jaridar Al-Mizan bugu na 1541 ta fito, inda take cike da ingantattun rahotonni.

Babban labarinta a wannan mako shi ne:
Cikakkiyar hirar BBC da Sheikh Zakzaky
*Addininmu shi ne mafitarmu a kasar nan
*Rayuwata tana hanun Allah ne
*Kula da lafiyarmu ce a gabanmu

Sai kuma labarin: Yadda sha'ar Sheikh Abduljabbar ta gudana

Ga kuma labarin, Mahara sun kashe Hakimi da 24 a Zamfara

Ku hanzarta neman Jaridar ta wannan mako a guraren da kuka saba samun ta kan farashin nan na 250 kacal.

Kar kuma ku manta da ziyartar AL-MIZAN TV Channel a YouTube don ganin irin wainar da ake toyawa. Kuma ku danna mana Subscription da alamar kararrawa.

Muna godiya gare ku masu karatun mu.

Gayyata Zuwa Mu'utamar Na Matasa a Yankin KUDAN.Dandalin Matasan Harka Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Zakzaky (H)...
24/03/2022

Gayyata Zuwa Mu'utamar Na Matasa a Yankin KUDAN.

Dandalin Matasan Harka Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Zakzaky (H) Na Yankin Gabashin Zaria (Kudan Da Kewaye) Na Gayyatar Dukkan Matasan Harka Musulunci Musamman Na Wannan Yakin Zuwa Taron Ƙarawa Juna Sani (Mu'utamar) a Garin Ung. Allura.

Taron Da Za'a Fara Shi Da Yammacin Juma'a 25/03/2022 Zuwa Asabar 26/03/2022 Akwai Maudu'ai Masu Tarin Muhimmanci Da Malamai Zasu Gabatar a Wajen Wannan Taro.

Haƙƙin Shiga; ₦300 Kacal

Domin Tuntuɓa
08062469666
09049589194
07069463384
08029333121

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Wakilai daga Ƙungiyar Fulani ta Kautal Ko'e Fulbe, ta Harka Islamiyya sun ziyarc...
20/03/2022

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Wakilai daga Ƙungiyar Fulani ta Kautal Ko'e Fulbe, ta Harka Islamiyya sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa dake Abuja.

Jagora (H) ya ce, kai wa Fulani hari da ake yi ana yi ne da wata manufa. Sannan aikace-aikacen ta'addancin da ake da sunansu wata dasisa ce da aka ƙirƙira.

Ƙungiyar ta koka kan halin tsanani da Fulani ke ciki da kuma yadda ake ɓata musu suna, sannan sun jajantawa Jagora (H) a kan waƙi'ar da ta faru a Zariya.

Szakzakyoffice
20/03/2022

ZARGE-ZARGEN KARBAR KUDI DA SUNAN HARKA ISLAMIYYAShaikh Yakubu Yahya ya yi addu'a:"Daga karshe wadannan abubuwan da aka ...
20/03/2022

ZARGE-ZARGEN KARBAR KUDI DA SUNAN HARKA ISLAMIYYA

Shaikh Yakubu Yahya ya yi addu'a:

"Daga karshe wadannan abubuwan da aka taso da su daga baya, na maganar zarge-zargen ko an ci kudi, ko an kawo kudade, ko daloli, ana maganar ko dubu hamsin?

"Nace to, ni na yi alkawari InshaAllahu Ta'ala, kuma ina fatan Allah Ya taimake ni na cika, cewa ni ba zan kare kaina ba. Ba ranar da zan zauna don in kare kaina. Ni Yakubu Yahya ni ba zan kare kaina ba.

"Na'am, na san ina da rauni, ina da kura-kurai, ina da gazawa, amma ni ba zan kare kaina ba. Ba ranar da zan zo nan na wanke kaina. Amma ina da addu'a kuma ina yi kuma zan kara.

"Ina fata, ina rokon Allah, albarkacin Sahibul Asr Waz Zaman, Allah Ta'ala don soyayyar da kake wa Malam Zakzaky, da kusancinka da shi, don sirrin da ke tsakaninka da Muhammadur Rasulallah (S), don wurarenka masu tsarki da watanninka masu alfarma. Allah Madaukakin Sarki domin waliyanka da salihan bayinka, ina kamun kafa.

"Ina rokon Allah, Allah ina rokonka, ka karɓa min, daidai wannan lokaci Allah ka karɓa min; Duk mutanen da suke karbar kudi a Harkar nan, da sunan Malam (H) ko da sunan Harka, ko da sunan Shahidai ko 'Ya'yan Shahidai, a ofisoshin Gwamnati ne, ko a masarautun Sarakuna ne, ko a ofisoshin Jakadanci ne, ko a Hauzozi ne, ko a Mu'assasat ne, ko a hannun wasu Maraji'ai ne, Allah masu karɓa da wadannan unwani da wannan suna, ina rokonka Allah Madaukakin Sarki ka tona musu asiri.

"Allah ina rokonka duk abin da s**a karɓa, Allah ka sa ya zama musu bala'in duniya da lahira, Allah ka sa ya zama musu wutar Jahannama, Allah ka tona musu asiri. Allah kai musu mummunan cikawa. Allah kar ka bari su gama lafiya.

"Masu turo min 'text' kun ji amsarku. Wassalamu alaikum wa Rahmatullahi Ta'ala wa barakatuhu."

— Shaikh Yakubu Yahya a karshen jawabinsa na Nisf Sha'aban jiya Asabar a Katsina 19/3/2022.

FIKIRAR HARKA TANA SAMUN CI GABA: To har walayau kuma, abin da ainihin aka kafu a kai aka ginu akai, don ita fikira tana...
03/03/2022

FIKIRAR HARKA TANA SAMUN CI GABA:

To har walayau kuma, abin da ainihin aka kafu a kai aka ginu akai, don ita fikira tana samun cigaba, daga loƙaci zuwa loƙaci. Mukan ta ƙoƙarin mu bayyanawa mutune, cigaba a fikira ba canzawar fikira ba ne, akwai banbamcin tsakinin sauyi, wato canzawa gaba ɗaya, da kuma cigaba, to wasu in s**a ga an samu cigaba s**an ce an canza ne.

To waɗannan irin kalmomin muna ƙoƙarin mutane su fahimci banbanci tsakanin canji, wato abin nufi da canji, mutum a ce ai ya canza, ma'ana ya tashi daga abin da ya ginu akai a da, ya koma wani abu daban. Don wasu suna kallon mu akai, suna ma zargin mu da cewa; an canza, wato ma'ana an canza daga abin da aka taso akai. Wato k**ar an canza manufa ko ma alƙibla kenan, daga inda ake nufi, sai aka zo aka sauya, aka ce ana kaza.

“ Alal misali, 'yan zuhudu su sun ga da can ana rayuwar Taƙashshur da gujewa duniya da sauransu, amma kuma yanzu sai s**a ga ana shan shagali ( a ganin su fa)? Ba wai shagalin ake sha ba. Sai s**a ga an fara jin daɗi, har ma ka ga mutum ma ainihin yana girki da Gas, saboda tsananin shan shagali da jin daɗi.

“ Ko kuma ka gan shi har yana hawa mota, kuma ka ga gidansa ma har akwai shimfiɗa, shimfiɗar ma ta ledar Roba. S**a ce ah! Ai an canza, an saka leda a gida! Kuma ana girki da Gas! Sannan kuma ana hawa mota Bitil! Kuma har akan yi abinci ma har da Ƙwai a cikin abincin! To shi kenan, sai s**a ce ai an sauya, an saki hanya. To wanda s**a san abin da nake faɗi yanzu, sun san abin da nake faɗa, don sun san wasu sun yi irin waɗannan abubuwa ɗin, sai s**a tafi, s**a ce Zuhudu kawai!

Wasu kuma ana nan, ana nan s**a zo, s**a ce an canza, da can Ahlus-sunnah ake yi, yanzu kuma an ko ma ana shi'a! Da can an ginu ne akan sunnah Malikiyya, sai kuma yanzu aka zo, ana cewa shi'a “ Ja'afariyya, saboda haka an canza daga abin da ake akai. Sai s**a tafi abin su. 'Yan Zuhudu s**a tafi, 'yan Tawayiya s**a tafi.

Cikin Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a wani audio da yi acikin garin Zaria loƙacin ana fosanta.

__@ faruq Sani Kudan ( Abban Jeedah)

Manzo Rahama (S) Yana cewa Na Fuskanci Kalubale Akan wasiccin Ali Ɗan Abu Ɗalib Fiye Da yadda Na fuskanta a farkon saƙon...
01/03/2022

Manzo Rahama (S) Yana cewa Na Fuskanci Kalubale Akan wasiccin Ali Ɗan Abu Ɗalib Fiye Da yadda Na fuskanta a farkon saƙonnan..

Mal. Aliyu R/Gado Yanzu haka a wajen Maului Imam Ali a Garin Kudan .

Kudan media Forum
1/3/2022

Bikin Saukar Karatun Alqur'ani Daga Madarasatul Fudiyyah Kudan.A yau Alhamis 22 ga watan Rajab, 1443(H) wanda yayi dai-d...
24/02/2022

Bikin Saukar Karatun Alqur'ani Daga Madarasatul Fudiyyah Kudan.

A yau Alhamis 22 ga watan Rajab, 1443(H) wanda yayi dai-dai da 24/02/0/2022, Madarasatul Fudiyyah Kudan ta gabatar da gawurataccen bikin saukar karatun Alqur'ani mai tsarki ga ɗalibanta kimanin su Talatin (30) karo na 4.

An fara gabatar da taron ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar, inda dubbannin al'umma su tuɗaɗo daga ciki da wajen Kudan domin samun tabarrukin wannan taro, inda mahalartar su haɗa kowane ɓangare na fahimta tun daga ɓangaren ƴan uwa ƴan Shi'a, Ɗariƙa da Izala.

Bayan gabatar da gwajin ɗaliban da suyi saukar daga wasu daga cikin Malaman Isilamiyun Ɗariƙa na cikin garin Kudan, inda Malaman suke karanto kowane waje daga cikin Alkur'ani inda su kuma ɗaliban suke ƙarasawa. Sannan sanyawar albarka ya biyo baya daga Malaman zuwa ga ɗaliban.

Shaikh Abdulhamid Bello Zaria, shine ya kasance babban baƙo mai jawabi a wajen, a cikin jawabin Malam ya jaddada muhimmancin Alkur'ani ga al'umma tare da ankarar da ɗaliban muhimmancin kiyaye abinda su karanta ɗin da kuma aiki da abinda su karanta. Sannan Malam Ya sanya musu albarka tare da addu'ar neman kasancewar dukkanin al'umma cikin waɗanda zasu rabauta a sanadin Alkur'ani mai girma.

Bayan gabatar da jawabin godiya ga mahalarta daga wakilin ƴan uwa na garin Malam Junaidu Muh'd Sani, sai addu'ar kammalawa wanda babban baƙo ya gabatar, sannan a sallami ƴan uwa mahalarta. Alhamdulillah.

— Kudan Media Forum
24/02/2022.

Shaikh Adamu tsoho: Kwalliya tabiya kuɗin sabulu Alhamdulillah!!Bayan bibiyar tarihi da nayi wanda ɗan uwa ( Idris shi'a...
21/02/2022

Shaikh Adamu tsoho:

Kwalliya tabiya kuɗin sabulu Alhamdulillah!!

Bayan bibiyar tarihi da nayi wanda ɗan uwa ( Idris shi'a jos), ya yi dan gane da tarahin Shaikh Adamu. Yadda naji ya bayyana nasabarsa da tsa-tsansa tundaga yarintarsa har zuwa girmansa, har zuwa matakan karatunsa, haka zalika yadda zakaji tarihin yadda mahaifinsa ya zamto ɗaya daga cikin mutanen 14 da aka kwaso su daga Bauchi zuwa garin Jos awannan can loƙacin.

“ Haka zalika yadda zakai duba da waɗannan bayin Allah su na da banne acikin wannan duniya, daga cikin tarihin da naji na Shaikh Adamu tsoho, yadda ya gudanar da karatun ''Alo'' awannan loƙacin. Batun yanzu ba su na da banne acikin halittun da Allah Ta'ala ya yi .

“ A cikin Rubutun da Idris shi'a jos ya yi naji ya taɓo wani fanni na bayin Allah k**ar Shaikh Muhammad Turi da Shaikh mukutar sahabi, yadda su ke cewa da Shaikh Adamu! ya k**ata ace ya yi aure. Cikin zantukan Shaikh Adamu yadda naji ya na cewa shi ba yanzu zaiyi aureba sai ya kasance Shaikh turi ya yi masa wata magana wadda ya ke cewa '' malam Turi ya akan ce to na shirya ya naushe ni sai nai haɓo ko na yi auren (Dariya)''. Inji Shaikh. Kaji zancan bayin Allah kai kasan haɗin Allah kenan.

" Marubucin tarihin ya yi wani tsokaci akan loƙacin da Shaikh Adamu ya fara kai ziyara zuwa ga Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a garin Zariya, bayan futuwarsa daga kurkukun Shagari a shekarar 1984 loƙacin Shaikh Adamu tsoho ya kai wa Shaikh Zakzaky ziyara a wancan loƙacin. Cikin zantukan da malam ya yi musu matuka da gaske naji daɗi sosai, bayan jaje da s**a yiwa Shaikh Zakzaky daga bisani kuma s**a jaddada bai'a gare sa gaba-da-daga zancan da malam ya yi musu yaja hankalina sosai inda malam Zakzaky ya ke ce musu '' ita Harka ɗin nan aiki ne kawai mutum zai tsayu da shi har ƙarshen rayuwarsa". Daga bisa Ni kuma naji daɗin yadda malam Hafizahullah ya yi musu nasihohi k**ar yadda ya saba a dukkan wani loƙaci idan aka ziyarce shi.

" Hakan zai ƙara maka yaƙini akan waɗannan bayan Allah da Allah Ta'ala ya haɗa ruhikanmu bisa yadda muke biye da su muke anfanuwa da su da nasihun da suke yi mana a ko da yaushe.

'' lallai naji daɗin wannan tarishi na Shaikh Adamu tsoho wanda dan uwa '' Idris shi'a jos ya gabatar acikin rubutunsa na tarishin malam.

Allah ya ƙarawa su malam Hafizahullah lafiya da kariya daga sherin azzalumai ƙasar nan da ma na duniya.

'' Ni faruq Sani tare da mahaifiyata da Abbana da sauran 'yan uwa na maza da mata muna ta ya malam Adamu tsoho Jos murna da ƙara cika shekara 60 masu albarka.

Faruq Sani Kudan
21/2/2022/ 1443

Lallai Wannan Al'amari (Addinin Allah) Babu Makawa Zai Tabbata.— Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina.A cikin jawabin su Shaik...
17/02/2022

Lallai Wannan Al'amari (Addinin Allah) Babu Makawa Zai Tabbata.

— Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina.

A cikin jawabin su Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina ga ƴan uwa na Da'irar Kudan a ranar da su kai masa ziyara 15/02/2022* ya sake tabbatar da cewa lallai wannan al'amari addinin Allah zai tabbata da taimakon Allah(T) inda yake cewa; “Bin wannan tafarki ɗin da wannan hanyar da wannan karantarwar, to lazim ne na tabbatar addini, k**ar yadda idan kace a kawo 'Tuwo' to kana nufin har da 'Miya' sabida Miya lazimin Tuwo ne, hakanan idan kace a kawo Tawada kayi rubutu to kana nufin harda Alƙalami, sabida alƙalami lazimin Tawada ne. To haka bin wannan tafarki ɗin shi lazim ne na tabbatar addini. Wannan ƴar ƙanƙanuwar jama'a ɗin da za'a samu waɗanda su cancanta Allah Yayi amfani dasu, to dasu Allah zai yi amfani ya tabbatar da addini.

“Wannan tabbatar addinin lazimi ne madamar ana kan wannan tafarki ɗin, ba makawa ne kawai, k**ar ashana da takarda idan ka kyarsa ashana ka kanga akan takarda, idan kaga wannan takardar bata k**a ba sai dai idan jiƙe take da ruwa, amma idan har a bushe take to zata k**a. Manzon Allah (s) yana cewa “Allah zai taimaki al’ummar nan da raunanan mu ne (waɗanda basu iya kare kansu) da addu'o'insu, da sallolinsu, da tsarkin zuciyarsu. Waɗannan abubuwan guda uku dasu Allah zai taimaki al’umma, idan mutum ya tsare waɗannan abubuwan guda uku to Allah Yayi alƙawarin zai kawo taimakonsa. Kuma Allah tabbatar da hakan kafin yanzu.

Yaci gaba da cewa; “Waɗannan raunanan da ake ganin ba'a bakin komi suke ba, a kaita azabtarwa to dasu Allah Yayi amfani ya taimaki addini, addini ya kafu. Shehu Usmanu Ɗanfodiyo shima abinda ya faru kenan. Shima anan ganin wasu ƴan tsirarun mutane ne, fulani ne sun addabi mutane ayita ƙoƙarin ayi maganinsu, dasu ne Allah Yayi amfani wajan tabbatar da addini. Wannan ma abinda zai faru kenan Insha Allahu.

“Imam Khumaini(Q.s) ma abinda ya faru kenan. Ta ita yiwuwu mutum ya dubi faɗin ƙasa yayi tambaya yace yanzu duk mutanen nan zasu bada goyon baya al'amarin nan ya tabbata? To abin ba anan yake ba, ba'a yawa ne ba, “Kammin Fi'atin Ƙalilatin ne, galabat Fi'atan Kasiratan Bi'iznillah” tsiraru ake buƙata, kai hatta ma faɗin ƙasa ma ba shine ma'auni ba, abinda ke ma'auni shine Muminai waɗanda zasu bautawa Allah Ta'ala yadda yake son a bauta masa.

“Idan aka samu wani gari ko wani ƙauye wanda a ƙalla tamanin bisa ɗari (80%) sun karɓi da'awa (Harka) kuma zasu iya bata kariya, su ciyar da ita gaba, su sadaukar Allah Ta'ala yana iya amfani dasu, zai yiwu daga nan abin yayi naso yaje makwafta daga nan kuma ya faɗaɗa yake ko ina, a tarihin musulunci hakanan ne, wasu ƴan tsirarun mutane ne Allah Yayi musu jarabawa suci jarabawa daga nan Allah Ya kwashe su ya kaisu Madina daga Madina musulumci ya yaɗu yanzu ya mamaye duk duniya. Duk duniya yanzu musulunci yana nan ko ina.

“To idan aka samu Allah Yayi mana irin wannan tagomashi ɗin, a samu wani gari ko wani yanki ko wani wuri idan ya zamo an samu karɓuwar da'awar koda tamanin s**a karɓa su shirya su sadaukar to Allah Ta'ala zai yi amfani dasu (idan sun cancanta) ya haskawa saura. Haka ya da Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo lokacin da aka kareshi daga Ɗagyal ya koma Gudu daga Gudu ne Allah Ya farar da abin ƙarshe ya dawo Sifawa ya tafi Sokoto daga kuma abubuwa s**a yaɗu ko ina”.

A wani ɓangaren kuma yake cewa; “Shi kafuwar addini lazimin aikin ne, tabbatuwar addini lazimin aikin ne, madamar za ayi bara'a da wula'a su tabbata, kuma ayi aiki na Tablighi, ayi aiki na irshadi, matukar akwai malami kuma akwai almajirai ai magana ta ƙare. Ba magana ce ta ƙungiya ba, a'a murshidi da masu karɓar irshadi. Ka karanta tarihi ka gani, duk tarihin Annabawa murshidi ne da masu karɓar irshadi to dasu ne Allah yake tabbatar da addini, don haka lokaci ne, kuma shi kansa jiran wannan lokacin shima ibada ne. Sabida haka ana bukatar hakuri”.

“Sabida ba wani abune wanda ba zai yiwu ba, idan kace Mustahili ne (abinda ba zai yiwu ba) to sauri kake. kana gani za'ayi baka, ko kuma idan ka mutu sai a fasa. To Lallai abun ba haka bane, koda ka mutu (kana kan hanyar) zaka samu ladan assasawa sai wasu su ƙarasa. To zai yiwu kawai, madamar kan wannan tafarkin ake to zai yiwu, babu abinda zai hana shi yiwuwa. Allah Ta'ala Ya taimake mu”.

— Wani yanki na jawabin Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina ga ƴan uwa na Da'irar Kudan da su kai masa ziyara a ranar 15/02/2022.

Naƙaltowa; Abubakar Ibrahim Kudan.

NISFU RAJAB; An Gabatar da Ayyukan Ranar 15 Ga Rajab A Husainiyyatu Rasulil-Akram Kudan.Ɗaliban makarantar 'Ma'ahad Rasu...
17/02/2022

NISFU RAJAB; An Gabatar da Ayyukan Ranar 15 Ga Rajab A Husainiyyatu Rasulil-Akram Kudan.

Ɗaliban makarantar 'Ma'ahad Rasulil-Akram Kudan, sun gabatar da ayyukan ranar 15 ga watan Rajab (Nisfu Rajab) a Husainiyyatu Rasulil-Akram Kudan.

An gabatar da addu'o'i, karatun Alkur'ani da sauran azkarori (A'amal Ummu-Dawud) ne cikin jam'i domin samun tabarrukin juna a cikin Husainiyyar Makarantar.

Allah Ta'ala Ya amsa ibadun mu, Ya sanya mu daga cikin waɗanda a yiwa rahama a wannan rana ta 15 ga watan Rajab mai alfarma.

— Ma'ahad Rasulil-Akram Kudan.
17/02/2022.

𝐉𝐚𝐠𝐨𝐫𝐚𝐧𝐚 '𝐘𝐚𝐧𝐜𝐢𝐧 𝐊𝐚𝐬𝐚𝐭𝐚  𝐍𝐢𝐠𝐞𝐫𝐢𝐚🇳🇬🇳🇬
12/02/2022

𝐉𝐚𝐠𝐨𝐫𝐚𝐧𝐚 '𝐘𝐚𝐧𝐜𝐢𝐧 𝐊𝐚𝐬𝐚𝐭𝐚 𝐍𝐢𝐠𝐞𝐫𝐢𝐚🇳🇬🇳🇬

MALAMANMU SIRRIN SAMUN NASARAR MUSHAHID MALAM AMINU HARIS; Allah sarki bawan Allah gwanin sadaukarwa, ya kasance ɗaya da...
11/02/2022

MALAMANMU SIRRIN SAMUN NASARAR MU

SHAHID MALAM AMINU HARIS; Allah sarki bawan Allah gwanin sadaukarwa, ya kasance ɗaya daga cikin Malaman Fudiyyah dasu sadaukar da lokacinsu wajan bada gudummawa musamman a ɓangaren koyar da karatun Alqur'ani ga dukkannin ɓangarorin yara da matan aure, sannan tsayayyen Haris daya taimaka wajan ingantuwar ɓangaren Faretin yara, sannan ɗaya daga cikin turakun da da'irar Kudan ke tsayuwa da gudummawarsu. Allah Ya sakawa su Malam da mafi kyakkyawan sak**ako.

MALAM SABITU KHALID; Malamin Fudiyyah wanda yake koyar da darasin Fiqhu (Hukunce-Hukunce) sannan shine shugaban makarantar Fudiyyah na dukkanin ɓangarorinta. Ya kasance jajirtacce kuma tsayayyen jigo ga ɗalibai, sannan yana daga cikin turakun da s**a riƙe da'irar Kudan ta hanyar sadaukar da komi nasu domin cigaban ƴan uwa. Ƙoƙarin Malam Sabitu bai ɓuya ga kowane ɗan uwa na da'irar Kudan da kewaye ba. Allah Ya sakawa su Malam da mafi kyakkyawan sak**ako.

MALAM AMINU IBRAHIM; Ya kasance Malamin Fudiyyah wanda gwani wajan koyar da yaren Larabci kuma masanin tarihi, wanda ke kula da ɓangarori da dama na daga abinda ya shafi ɗaliban Fudiyyah, sannan tsayayyen jigon da bisa taimakonsane ɗaliban Fudiyyah na ɓangaren Fareti su kafa kyakkyawan tarihi a Harka. Malamin daya kasance tsayayyen jigo a da'irar Kudan wanda da taimakonsa ne da'irar Kudan ta kai matakin da take yanzu. Allah Ta'ala Ya sakawa su Malam da Alkhairih.

MALAM ABDUL-AZIZ YAHYA; Ya kasance Malamin Fudiyyah wanda ya riƙe ɓangaren Tajwidi ga ɗaliban Fudiyyah bangaren Islamiyyah, sannan jigon da bangaren Tahfizul-Qur'an ta tsayu bisa taimakonsa. Malam Abdul-Aziz yana daga cikin jigogin dasu taimaka wajan ciyar da da'irar Kudan gaba. Allah Ya sakawa su Malam da mafi kyakkyawan sak**ako.

MALAM UMAR MUHAMMAD; Malamin daya riƙe ɓangaren koyar da Hadisi a ɓangaren yara ƴan Fudiyyah da matan aure, sannan Haris wanda ya bada gudummawa wajan inganta ɓangaren Fareti har Kudan ta kasance abin kwatance a Harka. Da taimakon Malam Umar ne ɓangaren Tahfizul-Qur'an ta wanzu har ta kai matakin da take a yanzu, sannan Malam Umar yana daga cikin tsayayyun Burazun da da'irar ba zata taɓa mantawa da gudunmawarsu ba. Allah Ya sakawa su Malam da Alkhairih.

Ya Allah Ka sani wadannan bayin naka dama wasunsu, sun sadaukar da dukkanin abinda su mallaka wajan amfanar da al'umma, sun zaɓi su sadaukar da dukkanin jin daɗin rayuwar duniya domin kyautata lahirarsu. Ya Allah ka amshi sa'ayinsu, Ka kyautata rayuwarsu ta nan duniya sannan kayi musu kyakkyawan tanadi a ranar lahira. Malamanmu abin alfaharinmu.

ABIN DA YA KAMATA KAYI A SOCIAL MEDIA!Abin da ya sa zanyi wata 'yar magana dan gane da wata 'yar matsala da nagani gawas...
06/02/2022

ABIN DA YA KAMATA KAYI A SOCIAL MEDIA!

Abin da ya sa zanyi wata 'yar magana dan gane da wata 'yar matsala da nagani gawasu 'yan uwa sauda yawa basu da wani abu ako da yaushe anan kafar sada zumunta ''SOCIAL MEDIA'' abin da ya shafi, facebook da sauran kafafan sadarwa na social media. A ko wanne loƙaci basu da wani abu azuciyarsu face yin maganganu marasa ma'ana ga babban aikin da ke ga bansu amma bashi suke yi ba. hankalinsu yana kanwasu abubuwa waɗanda bazasu amfani sauran al'umma ba da ma Ita kanta Harkar.

Kana amsa sunanka kai! wakilin Harka ne acikin garinku kuma kana kirankanka da cewa kai Dan media ne ma'ana (DAN JARIDA); amma ga abin da ya dace ace kayi acikin garinnaku amma bashi kake yi ba. Ana yawan yin abin da zai amfani al'umma acikin garinku wanda za'a '' Ilimantar, Afaɗakar, Anishaɗantar, da dukkanin al'umma baki ɗaya, amma sai ya kasance cewa su waɗannan mutane gasu suna da fashinta akan facebook da sauran wurare gasu, da yawanyin Rubutu tare da magana acikin kowanne irin loƙaci. Sannan kuma ga shirme akansu da baragada da sauransu, amma kusani cewa Sayyid Zakzaky (H) ya yi magana akan sabon safi.

To tunda ance abuɗe sabon shafi a yi aiki tare kuma abin da ya wuce ya wuce kenan muna sabon shafi ne. To kai me yasa bazakayi koyi da maganar da Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H ) ya ce ba baku da wani abu kudai! Face magana mara mashin manci. Kusa fashintar nan da kuke da ita wajan janhankalin mutane ta yadda zasu ƙara fashintar wannan manufar ta Sayyid.

Ina kira ga 'yan uwa masu ra'ayi irin wannan dan Allah sumaida hankalinsu akan abin da ke gabansu acikin garuruwansu dukkanin wani taro da akayi sumaida hankalinsu, wajan ko wanne irin tarone saboda akwai abin da zasu ɗauko wanda al'ummar nan da muke tare da ita tana da buƙatar sa. Acikinmu zuwanku wajajan yana da gayar muhimmanci sosai, bawai karinƙa zama a cikin wani waje ba acikin garinku ana yin taro, amma ko ''post'' ɗaya baza aganiba da an tambaye ka sai kace wallahi baka san'ayi bane shi yasa.

Allah yasa mu'ilimantu da dukkanin abin da alƙalimanmu suke rubutawa.

Faruq Sani Kudan
6/2/2022

HIJABI...! Daga__ Shafin marhuma Hauwa'uMa'anar Hijabi na haƙiƙa shine kare kanki daga dukkanin wata ƙofa da zata haifar...
02/02/2022

HIJABI...!

Daga__ Shafin marhuma Hauwa'u

Ma'anar Hijabi na haƙiƙa shine kare kanki daga dukkanin wata ƙofa da zata haifar da alfasha a tsakaninki da al’umma. Shiyasa ma a kiraye sa da ‘Hijab’ ma'ana makari ga mace ko katanga tsakaninta da duk wanda ba muharraminta ba.

Shi Hijabi na zahiri (wannan ƙyallen da matan mu ke yafawa) ma shine ƙadai Hijabi ga mace ba, shi wannan Hijabi ne na zahiri, amma akwai Hijabi na baɗini daya k**ata muke la'akari dashi.

Baki ma yana da hijabin daya k**ata a kangesa daga barin furta duk wata kalma ta haram, sanann Kunni ma yana da nasa hijibin na katangesa daga sauraron haram. Kowace gaɓa a jikin mutum an sanya masa ƙa'ida a Shari'a ta yadda za muyi tasarrufi dasu. Wanda kuma wuce gona da iri wajan tasarrufi dasu kan iya jefa mu ga halaka.

Ya Allah Ya azurta Matanmu da Mazanmu da aiki da cikakken Hijabin zahiri dana ɓadini a dukkanin motsinmu.

— Abbakar Ibrahim Kudan
01/02/2022

TARBIYYAR 'YA'YAMATA GA YARANSU! : daga Bintou Khaleel Kaduna Da farko dai ita tarbiyyah za'a iya cewa wata ''open behav...
01/02/2022

TARBIYYAR 'YA'YAMATA GA YARANSU! : daga Bintou Khaleel Kaduna

Da farko dai ita tarbiyyah za'a iya cewa wata ''open behavior'' ne ma'ana bayyanannan ɗabi'a ne, da bata 'ɗoyuwa gaskia,Wanda zamu iya cewa wata abace da kowane dan adam zai so ya kasance a rukuni na mutane masu shi. Sannan tarbiyyah wata abace dake defining mutum ,wato tana fassara mutum.

Haka kuma babu wasu ba'adi na mutane da aka keɓe akace su kaɗaine akeso s**asance masu tarbiyya,
Abin kula dangane da tarbiyyar yara shine, kafin fa uwa ta bada tarbiyyah lallai saiya kasance itama taci ta kuma tasha daga tarbiyan nan. Akan bada ''orientation'', ga matan aure sosai dangane da tarbiyyan 'ya'yansu amma a nawa ganin sainake ga ya k**ata ace yan mata, ma ana taimaka musu da irin wannan, saboda 'at the end of the' itama watarana uwace, kuma kafinnan ma a gida intanada ƙanne lallai zata taimakawa iyayenta gurin tarbiyyan ƙannenta.

''To a process na bada tarbiyyah yanada kyau ya zamana dukkan wani abu me kyau da zaki ɗaura yaro a kai ya taso yaga kema da kanki kin ɗabi'antu da yinsa. Misali: ta yaya kikeso ɗanki ya kyautata zamantakewarsa da sauran 'yan 'uwansa yara, bayan ke kin kasance maifaɗa aji. Don fitarda ''Good informationai dole sai an sami good data's''! A gaskiya ga uwa mai bada tarbiyya completely ɗinta,
anason ta kasance ne abin koyi.

TARBIYA GA 'YAMACE...

Ga ''ya mace budurwa kuma tarbiyyah me kyau itace babban gatan da zatayiwa rayuwarta da ahalintama baki daya. To bayan haka kuma dole tarbiyyah tana tafiya ne hand in hand da addu'o'i, Normal akwai yaran da zakaga lallai iyayen na ƙoƙarin burin basu tarbiyya.

Amma jarabawa sai tasa kaga k**ar basu akewa tarbiyyanba, to irin wa'innan yaran akan dage musu da addu'a, ba ɗaukewa inda da yawa
iyayenmu ke kuskure kenan duka. Lallai duka sam, baya daga cikin (Strategy) na bayarda tarbiyya. Psychologically akwai process daya k**ata abi da tarbiyyan irin wa'innan yaran, bayan fahimtar yanayinsu da sauransu insha Allah.

Wanne shi ne zai ƙara inganta rayuwar yara maza da yara mata, hatta su kansu 'yanmatan da ma sauran iyayenmu namu batu na gaskiya ita tarbiyya tana da mashinmanci Ali wanne waje idan kaje ana ganin yanayin ɗabi'arka ansan wancan daga gidan tarbiyya yake kuma bazai taɓa wulaƙantaba a duk inda yaje saboda tarbiyyar da iyayensa s**a bashi ko s**a bata .

Insha Âlláh nan nake cewa ina kira da 'yan uwa na mata mutsaya ƙyamwajan gyara tarbiyyar 'ya'yanmu ba sai munjira mazanmu sunzo sunyi mana ba saboda su basu acikin gida suna wajan ne man abincin da zamuci, ko da yaushe muke tare da yaran nan acikin gidajenmu. Sannan kuma 'yanmata gaskiya sai su tsaya sungyara goben su, saboda 'ya'yan da zasu haifa Susami tarbiyya mai kyau.

Zantawarmu: Bintou Khaleel Kaduna kenan a yau talata.

Shiryawa: Faruq Sani Kudan
1/2/2022

TARIHIN WASU MASOYA BIYU!🌹🌹To da yake sanadin wani Rubutu da ya yi naga rubutun ya birgeni har ya kai da nayi masa like,...
30/01/2022

TARIHIN WASU MASOYA BIYU!🌹🌹

To da yake sanadin wani Rubutu da ya yi naga rubutun ya birgeni har ya kai da nayi masa like, wato bana mantawa ya yi rubutu akan alaƙar Shaikh Zakzaky, da Abduljabar bana mantawa da wannan loƙacin to sai na yi masa mana daga nan kuma sai mukaci gaba da yin magana tsakaninmu bisa haka dai muka ciga da yiwa junanmu kulawa da yin magana har ta kai ga soyayya ta shiga tsakaninmu loƙaci ɗaya naji ya kwantamin azuciyata. Ba da jimawa naji ina sanshi, shima sai ya baiyana min irin sanda yake min to sai ya kasance munfara bawa junanmu photunan mu loƙacin bana mantawa sai da na bashi photona guda uku, sannan ya bani nashi guda ɗaya zuwa wani loƙaci kuma ya ƙara bani. Gaskiya nayi mamakin yadda naga ina da samari waɗanda suke sona kuma naƙi natseda wanda nake so. Amma shi dandanan ya karɓo acikin zuciyata.

Wakilinmu: to gaskiya a wannan loƙacin yadda nakeji azuciyata wallahi! Babu wani wanda nake so fiye dashi awannan lokutan, munɗauki loƙaci kafin mufara haɗuwa shi dan ina ga munkai kusan wata guda, ba muga junaba ba wallahi bada jumawaba na ce masa ina san yazo wajena ina sanganin dan Allah sai dai kafin yazo wajena sai na fara naiman wata buƙata tawa wadda nake san ya magancemin ita, to sai ya kasance loƙacin sai ya ce min wallahi bashi da kuɗi, amma shi duk abin da zaiyi yafisan ya gayawa mutum gaskiyar magana batare da ya jamai rai ba. To sai naji wani abu azuciyata sai nace yana sona kuwa, wata zuciyar kuma sai tace amma kisani gaskiya ya gayamin bawai yayimin ƙarya bane kokaɗan sai nayi masa uziri. Nan bada jimawaba sai naji yakirani awaya ya ce (my love ), insha Âlláh abin da kika ce min kina so Allah ya nufa kuma ya bani saboda haka nima zansai miki abin da kikacemin kinaso, sai nayi farin ciki sosai, sai nace masa amma ''My love'' sai yaushe zakazo ne wajena sai ya ce min nanda ranar Lahadi, insha Allahu zanzo ana cikin haka kawai sai Lahadi tayi sai mukayi waya dashi da safe sai nake cewa mai kake san zakaci ne sai yace duk abin da Allah ya h**e kawai ya yi ba'atsawaitawa rayuwa my love, sai nace masa to nan da karfe nawa zaka taso sai ya ce min insha Allahu nan da ƙarfe 12 narana zan iya tasowa loƙaci na cika sai na kirashi awaya sai yace min yanzu haka yafito daga wanka ne .

Wakilinmu: kasan daga yin wannan wayar tamu sai naƙara kiransa sai naji cewa yanzu haka ya taso ya kawo wani gari, duk da cewa banriƙe sunan garinba da ya cemin sai nace insha Allahu my love Allah ya tsare minkai daga sherin ƙarfe zuwa can sai naji kiranwaya sai yace min yanzu haka yana cikin garinmu sai nace kai dan Allah to kasami ɗanmashin ya kawoka filin masallaci idi. Ana haka sai yace min to sai yasami ɗan mashin sai ya ɗaukosa izuwa inda nace masa yana sauka sai ya kira ni yace my love yanzu Allah yayimin sauka a inda kikace min, sai nace masa insha Allahu kajira ni yanzu za'azo atarerbeka zuwa can sai nayiwa ƙawata magana ga inda yake sai na bata wayata sai nace kije filin masallaci idi kitarbosa, nan kowa yazura ido yaga inda zaiɓulo zuwa can saigashi suntawo tare yana binta abaya sai nan kowa ya ganshi ( Gashi yaro mashi kyakkyawa da shi gafuska ga hanci duk Allah ya bashi ga kyanhali da sanin daraja da mutuncin da sanin ya k**ata akan ɗan Adam); .

Wakilinmu: bada jimawaba nace masa ina wuni my love sai ya ce min lafiya lau sai nace masa ya hanya kuma sai ya ce min Alhmdllh, sai nace masa garuwa nasan kasha hanya sosai yau, sai ya ce min dan Allah ina zuwa. Sai naji yace min yana wani Rubutu ne yau (Shaikh yaƙub Yahaya Katsina), zaifita neman magani sai na ce masa insha Allah bada jimawaba sai yace min yagama loƙacin da yace min zaiyi wannan rubutun ina ta kallan kyakkyawar fuskarsa ina farinciki da zuwansa. Zuwa can kuma sai nace masa kaci abincin my love sai yace tunda zuciya taga abin da take so maizatayi da abinci sai naji wani iri kuma sai nace azuciyata Allah ya barmu tare da masoya na gaskiya masu sanmu sai nace masa kasan wani abu baka zo dawuri ba ya k**ata ace kaci abincinnan saboda kai na da fashi sai yace sai na fara ci nace indai haka ne zai sa ka ci baka da damuwa sai naci zuwa can shima sai yaci.

Wakilinmu: bayan mungama ganawa da junanmu sai loƙacin tafiya ya yi nan muka hawo mashin muka tawo izuwa bakin t**i. zamuje tashar mota dan ya hau mota ya koma gida, cikin ikon Allah sai aka samu mota zuwa garin nasu, duk da cewa gashi garin yayi hadari yace min zaitafi bada jimawaba sai ya kirani sai yace min wallahi ''Gosulo'' ya taresu akan hanya kuma garuwan sama anayi gaba ɗaya sai hankalina ya tashi sosai nake cewa ko zaka dawo kakona ne zuwa safiya sai katifi sai yace a'a', cikin ikon Allah zai isa gida lafiya ana haka sai mukaci gaba da yin magana a ''facebook''. Cikin hakan kuma sai Allah ya kawo jarabawa sai wayarsa ta ɗauke gaba ɗaya sai hankalina ya tashi sosai nakasa natsowa sai na miƙa komai zuwa ga Allah ( Ta'ala ) sai nayi al'wala nayi sallah domin Allah ya tsaremin shi daga dukkan sheri na duniya. Wajan ƙarfe 12:5 na dare sannan Allah ya yi masa sauka gida saboda tsabar gosulo akan hanya kuma garuwan sama anyi sosai, kawai sai naji kiran waya ta sai naga kiransa ne sai naji yace min yanzu Allah ya nufa na sauka gida lafiya sai nace masha Allah naji daɗi amma munga jarabawa sosai wallahi.

Wakilinmu: tafiya ta tafi har akazo wani loƙaci Allah ya nufa akace gashi yau za'asa ranar auranmu amma kuma kasan komai sai Allah ya nufa zaiyuwu ana cikin haka kuma sai magana ta manya wato ''Iyayanmu'' s**a shiga cikin maganar auran, zuwansa gida mahaifinsa bayan yayimasa magana cewa yana neman aure sai yace to tunda kanaso kace mata kawai tasanar da mahaifinta atseda magana. Cikin haka nagayawa mahaifina ga halin da ake ciki, mahaifina ya yi farin ciki sosai ya ce to shi kenan kice masa ya turo manyansa kawai bayan man sayan sunzo anyi magana har aka yanke shawarar bada sadakin aurena nan take s**a fara bada sadakin aurena s**ace nan da wani loƙaci zamu bada sauran.

Wakilinmu: kasan komai sai Allah ya nufa 'yar wata turjiya muka samu tsakaninmu akan wani yanayi bazan iya gaya maka shi ba. Amma dai har yanzu muna gudanar da soyayyar mu k**ar yadda take da kuma muna da burin yin aure atsakanin mu .

Wani tarihin wasu masoya kenan wanda kuma har yanzu suna tare duk da fuskantar wani ƙalobale da s**a fuskanta. Auran kuma cikin ikon Allah za'ayi shi . Lallai waɗannan masoya suna san junansu k**ar yadda ita masoyiyar ta bai yana yadda soyyaya ta so take kuma har yanzu suna tare da junansu, abin da mu zamuce Allah ya nuna mana wannan loƙaci na auran su mai ɗunbun tarihi.

Daga:__ Abban Jeedah
30/1/2022

Address

Saban Gari Kudan 0019
Kudan

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Faruq Sani Kudan tv news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Faruq Sani Kudan tv news:

Share

Category


Other Kudan media companies

Show All

You may also like