14/03/2024
HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI (11)
Daidai da Fatawowin Ayatullah Sayyid Khamene’i (H)
HUKUNCE-HUKUNCEN RAMAKON AZUMI
Mas’ala ta 727:
“A bisa Ihtiyadi na Wajibi, (wajibi ne) mutum ya rama abin da ya kubuce masa na Azumin watan Ramadan kafin zagayowar watan Ramadan ta gaba. Da zai ki ramawa (har Ramadan ta zagayo) to wajabcin ramakon bai sauka a kansa ba, kuma ya wajjaba a kansa ya bayar da Fidiya na Mudu dayan abinci a madadin kowace rana da ya jinkirta ramakonta. Amma Fidiyan baya ninkuwa bayan haka, komai tsawon lokacin da ya jinkirta yin ramakon.”
Wato wajibi ne idan mutum ya sha Azumin Ramadan saboda uzurin shari’a, to ya rama Azumin kafin wata Ramadan din ta sake zagayowa in har ya samu halin hakan, idan har bai rama ba da gangan ko bisa sakaci, har wata Ramadan ta zagayo, to ramakon yana nan a kansa sai ya rama a tsawon rayuwarsa, sannan kuma wajibi ne ya yi kaffaran jinkirin da ya yi na rashin rama Azumin har wata Ramadan ta zagayo.
Kaffara din shi ne Fidiya (wato Ciyarwa), sai ya bayar da Mudu daya (750gram) na abinci, k**ar su Shinkafa, ko Masara, da mak**antansu ga Talaka, a madadin kowace rana da aka bi shi Azumin bai rama ba, idan azumi uku ake binsa misali, to zai bayar da mudu ukun abinci kenan ga Talaka a madadin kowace rana daya, sannan kuma ya rama Azumin daga baya.
Shine aka ce, Fidiya din ba ya sake ninkuwa saboda jinkirin ramakon bayan wannan na farkon. Wato, in dai Ramadan din farko ta zagayo shikenan, yanzu ramako ne da ciyar da mudu daya a madadin kowane Azumi daya, ko mutum bai rama din ba har wata Ramadan ta sake zagayowa, ko ma Ramadan goma aka yi a gaba bai rama ba, kaffaran jinkirin dai yana nan a mudu daya a madadin rana dayan da ake binsa, bai karuwa ko maimaituwa saboda jinkirin ramakon da ya sake yi.
Amma a baya kun ga an yi bayani akan banda marasa lafiya da s**a sha Azumi saboda ciwo, kuma ciwon ya cigaba musu bai warke da za su iya ramakon ba har wata Ramadan ta zagayo, su an fadi hukuncinsu a baya. Haka ma an fadi masu uzurin ciki da goyo da tsufa da sauransu. A nan ana magana a kan wadanda ba wadancan ba ne.
Mas’ala ta 728:
“Wanda ya karya Azumi da gangan a cikin watan Ramadan, ya zama wajibi a kansa baya ga ramakon Azumin da ya sha, ya kuma hada da yin Kaffara, duk daya ne shin ya san wajabcin yin Kaffara a kanshi idan ya karya Azumi da gangan a Ramadan ko bai sani ba. Bai zama wajibi sai ya yi Kafffara din da gaggawa ba, sai dai bai halatta masa ya jinkirta irin jinkirin da za a lissafa shi a matsayin mai kyale da kuma sakaci a duban urfi ba.”
Wato idan mutum ya karya Azumi da gangan, ko da a lokacin bai san cewa hukuncin wanda ya karya Azumi da gangan a Ramadan shi ne ya rama ya kuma yi Kaffara ba, sai daga baya ya sani, to a duk lokacin da ya sani, ko shekara nawa ne da s**a gabata ya karya azumin da gangan, ba zai ce ai lokacin bai san haka ne hukuncin ba, wajibi ne bayan ya rama Azumin, ya kuma yi Kaffaran karya Azumi da gangan a watan Ramadan.
Na’am, ba wajibi ne mutum ya gaggauta yin Kaffaran ba, amma bai halatta masa ya zama mai sakaci da rashin muhimmanta Kaffaran ba, ta yadda a ‘urfi’ (yanayin duban mutane) za a kalle shi a matsayin wanda bai damu da hakkin Allah da ya doru a kansa na Kaffara din ba.
Kaffaran shan Azumi da gangan shi ne Azumi 60 a jere, ko ciyar da Talakawa 60 abinci, bisa bayani da sharuddan da za su zo a nan gaba. Saboda haka duk wanda zai yiwu masa sai ya yi kokarin ganin ya yi shi tsakaninsa da Allah har ya zama abin da ke wuyansa ya sauka.
Mas’ala ta 729:
“Wanda bai azumci watan Ramadan na shekaru masu yawa ba, ya zama wajibi a kansa ya rama su bakidayansu. Idan yana kokonto (shakka) a kan gwargwadon (adadin) Azumin wajibin da ake binsa, to sai ya rama gwargwadon da yake da Yakini a kansa. Idan kuma yana kokonto (shakka) ne a kan shin Azumomin da ya sha din da gangan ne ko bisa Uzuri (karbabbe a shari’a) ne, to a nan ya zama masa wajibi ya rama Azumin, amma ba wajibi ne ya yi Kaffara ba.”
Wato idan misali an bi ka wasu adadi na Azumi a Ramadan, sai wata Ramadan din ma aka bi ka wasu adadi, wata ma aka bi ka wasu adadin, duka sai ka kasa kiyaye gwargwadon adadin da ake binka a dukkansu gabadaya, kana shakka akan sun kai 20 duka, ko basu kai ba, amma kana da tabbacin lallai sun kai 15 misali, to a nan, abin da yake wajibi a kanka shi ne ka rama adadin da kake da yakininsa (tabbacinsa), wato 15 din a bisa wannan misalin. Idan kuwa dama ka san adadin, shikenan duk adadin ne ke kanka, sai ka rama.
Idan kuma a cikinsu ka manta dalilin da yasa ka sha Azumin misali, sai ka fara shakka akan cewa, lokacin da na sha Azumin nan da gangan na sha, ko kuwa uzuri ne wanda shari’a ta yarda da shi yasa na sha Azumin a lokacin? To a nan, tunda shakka kake yi, baka da tabbaci to za ka rama Azumin ne kawai ba tare da Kaffara ba. Amma idan kana da tabbaci (yakini) a kan cewa Azumin ka sha ne da gangan ba bisa uzuri na shari’a ba a lokacin, to wajibi ne ka rama ka kuma yi Kaffaran shan Azumi da gangan a watan Ramadan.
Mas’ala ta 730:
“Idan ya zama mutum ba zai yiwu ya yi Azumin watan Ramadan ba, kuma ba zai iya rama Azumin kafin zagayowar watan Ramadan mai zuwa ba, saboda raunin jiki, to duk da haka ramakon bai fadi a kansa ba, wajibi ne ya rama a duk lokacin da zai yiwu masa.”
Wato a nan, ana nufin wadanda ba rashin lafiya ba ne uzurinsu, kawai uzurin rashin kuzari ko kwari ne. Kamar misalin yarinyar da ta Balaga, ta cika shekara 9 lissafin Qamariyya, sai ya zama ta jaraba an ga sam ba za ta iya yin Azumi a Ramadan ba, ko ta yi wasu ta sha wasu, kuma har bayan Ramadan din bata samu kwarin jiki da za ta iya rama duk Azumin da ake binta kafin wata Ramadan din ya zagayo ba, saboda har yanzu bata yi kwari ba, to duk da haka ramakon yana nan a kanta bai fadi ba, har zuwa ta kai matsayin da jikinta zai yi kwarin da za ta iya rama Azumin ba tare da ta shiga cikin tsananin da za ta kasa jure masa ba, ko da bayan shekaru nawa ne. Irin wannan ramako ne kawai a kansu, babu kaffaran jinkirin ramakon, matukar saboda raunin jiki ne.
Mas’ala ta 731:
“Wanda bai yi Azumi ba a cikin watan Ramadan saboda rashin lafiya, idan ciwonsa ya cigaba har zuwa watan Ramadan ta gaba, to ramakon Azumin ya fadi a kansa (ba sai ya rama ba), amma wajibi ne a kansa ya bayar da Fidiya na Mudun abinci ga Talakawa a madadin kowace rana da ya sha Azumin.”
Wato idan ciwo ne yasa ka sha Azumi, kuma ciwon (rashin lafiyan) ya cigaba maka ba ka warke daga gare shi ta yadda za ka iya rama Azumin ba, har wata Ramadan ta zagayo, to yanzu ramakon Azumin ya fadi a kanka, abin da ke wajibi a kanka shi ne, ka bayar da Mudun abinci (shinkafa, ko masara, ko Alk**a, da sauransu) ga Talakawa, mudu daya a madadin kowace rana da ka sha Azumin. Idan ka yi haka, ka sauke abin da ke wuyanka a wajen Allah Ta’ala, Insha Allah.
Amma idan ka sha ne saboda ciwo, sai ka samu saukin da za ka iya ramawa kafin wata Ramadan din, amma sai baka rama ba bisa sakaci, har wani uzuri ko ma rashin lafiya ya sake bijiro maka, har wata Ramadan ta zagayo a wannan halin, to a nan ramakon yana nan a kanka, kuma sai ka hada da Kaffaran jinkirin ramakon Ramadan, wanda aka ce shi ne bayar da Mudu daya a madadin kowace rana, tunda an samu lokacin da ka samu lafiyar da ya k**ata ka rama azumin, amma ka yi sakacin ramakon har damar ta wuce.
Mas’ala ta 732:
“Idan Mukallafi bai yi Azumin watan Ramadan ba saboda rashin lafiya, ko saboda Haida, ko Nifasi, sai kuma ya yi wafati (ya rasu) kafin karshen watan Ramadan din, to bai zama wajibi sai an rama wadannan ranakun da ya sha a madadinsa ba.”
Da yake ana rama wa wanda ake bi bashin Sallah ko Azumi idan s**a rasu ba su yi su ba, wanda bayani zai zo a nan gaba a kan hukunce-hukuncen ramakon Azumin wanda ya rasu ana binsa bashi din. To idan ya sha Azumi saboda rashin lafiya, ko mace ta sha Azumi saboda jinin Haila ko jinin Haihuwa da ya zo mata a cikin watan Ramadan, amma kafin kammala wannan watan Ramadan din har ta fita, sai ta rasu a cikin watan, to yanzu ba wajibi ne a rama mata Azumin da ta sha saboda wadannan uzirorin da aka ambata ba. Sun fadi a kanta gabadaya.
Mas’ala ta 733:
“Wanda ya Suma, kuma ya cigaba da kasancewa a wannan halin na Suma da rashin sanin halin da yake ciki tsawon yini ko fiye da haka, to bai zama wajibi a kansa ya rama Azumin kwanakin da yake cikin wannan halin ba.”
Akwai wadanda s**an suma, ko su shiga halin da sam ba su sanin wa ke kansu (abin da likitoci ke kira ‘Coma’), wani sai ya yi kwanaki a hakan kafin ya farfado. To tsawon kwanakin da mutum ya kasance a wannan halin, babu Azumi a kansa har zuwa ya farfado. Sai ya farfado ne, sannan za a fara lissafin Azumin da za a bi shi bashi saboda rashin lafiya a gaba, amma can tunda yana cikin wani hali na Suma, to azumin ya fadi gabadaya a kansa, ba za a hukunta hakan a matsayin k**ar rashin lafiya da aka saba da ita wadda mutum ke farke a hayyacinsa ba.
Mas’ala ta 734:
“Ya halatta ga mai rama Azumin watan Ramadan, matukar lokacin ramakon bai kure ba, ya karya Azumin kafin Azahar (kafin Zawali), amma bayan Zawali, bai halatta ya karya ba. Idan kuwa ya karya Azumin ramakon Ramadan bayan rana ta yi Zawali, to wajibi ne a kansa ya yi Kaffara, kuma Kaffaran wannan shi ne ciyar da Talakawa guda goma (10) abinci, idan kuma bai da halin hakan, to sai ya yi Azumin kwanaki uku (baya ga sake Azumin da ya karya din).”
Wato idan ana binka bashin Azumin Ramadana, sai ka dauki azumi da nufin ramako, to kana da damar ka ga dama ka karya azumin kafin rana ta yi Zawali, amma da zaran rana ta yi zawali kana azumin, to ba ka da damar karyawa, wajibi ne ka kai Azumin in har ba da wata lalura karbabbiya a shari’a ba ne. Idan ka karya bayan Zawalin rana da gangan, to ka yi laifi, sai ka rama Azumin, sannan kuma ka yi kaffaran karya Azumin ramakon Ramadana da gangan. Kuma kaffara din shi ne ka ciyar da Talakawa goma abinci su koshi, ko kuma idan ba ka da halin yin hakan, to ki yi Azumi na kwanaki uku.
Za mu cigaba insha Allah.
— Saifullahi M. Kabir
3 Ramadan 1445 (13/3/2024)
Whatsapp: 08062911212